Showing 42001 words to 45000 words out of 88313 words

Chapter 15 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

sun gama koke-koken su, da alhinin ganin yayan nasu, sai suka shiga kichen don ɗaura musu abincin dare

Inda kuma Mamy da Abba suka ci gaba da tattaunawa a palon, Abba yana sake tausan ta tare da ƙara mata ƙwarin gwiwa

Ajiyan zuciya Mamy ta saki, tana share ƙwallan da suka sake cika mata idanu, ta kalle sa tace, "yanzu Ni Abban su zuciya ta rawa take yi sosai, ina ga kamar baza muyi wani nasara ba, babu wani shaida da nake dashi da zan tabbatar ba Baba na ne yayi kisan kan nan ba, ni kaina ban yi tunanin za mu iya tsallake yau ba".

"Haka ne, amma ai Allah shi ne ya san dai-dai, kuma shi muke roƙo, idan har ABUL KHAIRI ba shi ne yayi kisan kan nan ba, Wlh sai ya fita, tunda Allah ya baki ƙwarin gwiwar gudanar da Shari'an nan yau har kuma kika yi nasara, to insha Allahu shi zai taimaka miki, amma dole ki yi bincike ta fannin yarinyan, ya kamata ki gano ƙawayen ta da kuma waɗanda take mu'amala dasu don samun shaidu sosai, ta hakan ne ma zaki gano idan tana mu'amala da wasu maZan".

Jinjina kai Mamy tayi cike da gamsuwa, tace, "insha Allahu zuwa gobe zan fita in bincika, amma Abban su abinda ke raina yanzu shi ne, yanda zan gano yarinyan da take shiga gidan ABUL KHAIRI, wacce ta yiwa me gadin gidan ƙaryan cewa ita ƴar uwan Baba na ne".

Gyara zama sosai Abba yayi yana kallon ta, yace, "akwai wacce take zuwa gidan sa ne?"

"Eh haka me gadin yace min, ta taɓa zuwa gidan ta nemi ya barta ta shiga, ita ƙanwar Baba na ne, to ya bar ta ta shiga, kuma yace min a ranan da suka yi faɗan ta sake shiga gidan, shi ne shigar ta na ƙarshe".

"To idan ko haka ne, ya zama dole ki gano ko wace ce, shin wa kike zargi?" Abba yace hakan yana kallon ta

Numfashi taja kana tace, "Ni ina zargin Azeeza ce, domin tun sanda ta zo gidan nan kwanakin baya, naji tayi wasu maganganu wanda ya tabbatar min da cewan tana son ABUL KHAIRI, wannan ya ɗarsa min zargin tabbas ita ce zata bi shi har gidan gonan sa, kuma yanda me gadin ya fasalta min ita, dai-dai da Azeeza ce".

Shiru Abba yayi na ɗan soconni, kana yace, "to yanzu ya zamu yi idan ita ce?".

Mamy tace, "abinda ke raina kenan Abban su, Azeeza baza ta yarda ta zo kotu ba ko da kuwa mun gano cewar ita ce ta shiga gidan, idan ma da akwai abinda ta sani duk da ba na zargin ta da ita ce ta aikata, kuma ban san ma yanda za'a yi in gano ita ce ta shiga gidan ba ko ba ita ce ba, iyayen ta baza su taɓa yarda da abinda zan je musu ba, ka san halin su".

"Haka ne, tabbas akwai rikici, yanzu dai ki je kiyi sallah tunda ana kira, idan na dawo masallaci zan faɗa miki hanyar da zamu ɓullo wa al'amarin, idan ma ita ce dole za'a gane".

Daga haka Abba miƙe wa yayi ya wuce Toilet ɗin parlour'n don ɗauro alwala

Inda Mamy ta miƙe itama ta wuce kichen tana ce ma su Maimuna, "su bar girkin su je su yi sallah tukunna, kafin su dawo su ci gaba". Tana faɗa musu hakan ta wuce ɗakin ta


Su ma ɗaki suka wuce don bin umarnin ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 24*

*________* Ana jibi za'a koma COURT, ƴan sanda suka isa gidan su Azeeza suka ƙwamuso ta, iyayen ta basu san hawa ba basu san sauka ba aka zo aka tafi da ita, ita kuwa da tasan laifin ta tuni ta tsure sai kuka take yi tana roƙon iyayen ta da, "kar su bari a tafi da ita, wlh ba ita ce tayi kisan ba". Amma haka ƴan sanda suka tasa ƙeyan ta suka wuce da ita

Kai tsaye police station aka wuce da ita

Babu jima wa sai ga Mamy ita da me gadi sun je, lokacin da me gadin ya ganta sai ya tabbatar musu da cewa, "ita ce tazo gidan ABUL KHAIRI".

Numfashi Mamy taja kafin tace wa me gadin, "to zaka iya tafiya Malam Iro, amma zuwa jibi ka tabbatar da ka zo court domin bayar da sheda kaji?"

"Insha Allahu Hajiya zan halarta".

Bayan tafiyan sa sai Mamy ta nemi ganin Azeeza, har inda aka ajiye ta ta shiga, amma duk yadda taso Azeeza tayi mata bayanin ko ta san wani abu? Ta ƙi cewa komi illa kuka da take tayi, hankalin Mamy ya tashi matuƙa, "kar dai ace ita ce tayi kisan?" Babu yadda ta iya haka ta fice ta koma office ɗin Asp Shazali, inda ta tambaye shi, "ya labarin gyara wayan ABUL KHAIRI?"

Yayi mata bayanin, "sun gyara, kuma duk sun bincika akwai bayanan da ya faɗa a kotu, sannan kuma Abun mamaki Numban da aka kira su dashi ranan da aka sanar musu da kisan, shi ne dai aka kira shi dashi a ƙarshen call ɗin da yayi, kuma sun samo inda aka yi register da layin amma sun je basu samu me shagon ba, an tabbatar musu cewa wajen sati Uku kenan da barin sa wajen, be sake dawowa ba".

Jinjina kai Mamy tayi, kana kuma tace, "Asp idan babu damuwa nima ina son ka bani Numban, sabida ina son nayi bincike a kai, sannan ina son sanin wajen".

"Babu damuwa ai, bari in rubuta Miki". Nan ya rubuta mata address ɗin da Numban ya bata

"Amma don Allah ina neman alfarma, don Allah kar ku taɓa wannan yarinyan idan har taƙi muku bayani, kawai ajiye ta za ku yi har zuwa ranan shiga kotu, na san yanzu a tsorace take, duk wani abinda ta sani zata yi bayanin sa a kotu, kuma ba wai ina zargin ita ce tayi kisan ba, amma hakan zai iya yiwuwa, abinda yasa nace ku taimaka min wajen kamo ta, sabida na san ko na buƙaci ganin ta baza ta zo ba, amma yanzu iyayen ta za su ɗauka ku ne kuka kama ta".

"Ok Barrister, insha Allah baza muyi mata komi ba".

Sallama taya masa ta tafi.



                 Tana isa gida ta tarar da Uncle Sani yana ta jaraba wai, "a kan me za su saka ƴan sanda su kama mishi ɗiya? ai duk abinda ke faruwa ya sani, ɗan su yayi kisan kai amma ana son liƙa wa ɗiyar su, kuma wlh idan basu sako mishi ƴar shi ba sai sun ga abinda sai biyo baya". Jaraba dai kala-kala haka yake sauke musu a gida

Abba na jin sa be ce mishi komi ba, kuma be hana sa ba

Mamy na shigowa ya koma kanta, fata-fata yayi mata, tana ba shi haƙuri amma ko sauraron ta ya ƙi yi, sai da ya gaji don kansa kafin ya tafi ya bar su.


          Sosai Mamy ta shiga damuwa, dama ga shi ba shiri suke yi ba har yanzu, tun sanda ta bar gidan Uncle Sanin, ya tabbatar da ya rasa ta har abada lokacin da ta auri Abba, shikenan jituwa yayi ƙaranci a tsakanin su, duk alkhairin da Mamy zata yi musu ba sa ganin hakan, gaba ɗaya ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata, haka ma matar sa Umma Sulaima, ita wannan kishi ne yayi mata yawa, har yanzu gani take yi Uncle Sani na son Mamy, shiyasa ta tsane ta sosai.


         Umma ( Mahaifiyar Uncle Sani) ita dai duniya ta koya mata darasi, shiyasa tayi sanyi yanzu, duk sanda Mamy tazo gidan tana amsar ta hannu bibbiyu, a ɗakin ta ma take sauka. Mamy tana da haƙuri shiyasa har yanzu take bibiyan su duk da ta san ba sa ƙaunar ta, duk wani abinda ya faru baya ta manta dashi, ita so take yi su ƙulla zumunci sosai, tunda su ne dangin mahaifin ta, su kaɗai ke gare ta, baza ta so su raba hanya ba, ga shi yanzu abinda ya biyo baya na maganar ABUL KHAIRI, duk da shawaran da Abba ya bayar amma sai da saɓani ya sake shiga tsakanin su, wanda ba hakan ta so ba, tunda ga shi ƴan sanda suka kamo Azeezan amma Uncle Sani ya zo gidan su yana tijara, a ganin sa su ne suka kama ta.


      Yanda Mamy ta tayar da hankalin ta ne, dole Abba ya koma bata haƙuri da tausar ta, domin faranta masa rai haka ta nuna masa babu komi ya wuce.









            *RANAR SHIGA COURT*

           Yau ma duk ƴan uwa da abokan arziƙi sun hallara a court ɗin, inda ta cika maƙil ko ta ina, ga ƴan jarida a gefe suna jiran su samu na yaɗawa. Su Uncle Sani wannan karon har da su sun biyo sahun ɗiyar su.


     Bayan Alƙali ya zauna a kujeran sa, sai kowa ya koma ya zauna ciki girmamawa

Asp Shazali shi ya fara gabatar da wayan ABUL KHAIRI, inda yayi musu bayanin duk abinda ke ciki, sannan ya miƙa aka ba ma Alƙali

Alƙali bayan ya duba ya tabbatar da abinda ABUL KHAIRIN ya faɗa gaskiya ne

Asp Shazali ya ƙara da faɗin, "ya me Shari'a har yanzu muna kan binciken layin da aka kira mu dashi ne, kuma bamu samu wani abu akai ba, sannan mun gano cewa Numban da aka yi kiran ABUL KHAIRI aka tabbatar masa da kisan, shi ne wanda aka yi amfani dashi wajen kiran mu aka sanar mana". Sai ya duƙar da kansa cikin girmamawa kana ya koma ya zauna

Bayan Alƙali ya gama rubuta bayanan, sai ya ɗago kai ya ce da lauyoyin, "idan akwai me magana a cikin ku zai iya fara wa".

Mamy ta miƙe tace, "ya me Shari'a zan so kotu tayi duba da bayanan da Asp Shazali ya kawo, ta gane cewa ABUL KHAIRI ba shi ne yayi kisan kan nan ba, wani ne daban yayi sannan ya laƙaba masa, bincike ya nuna tabbas kiran sa aka yi aka sanar masa, kuma kotu ta tabbatar da hakan tunda ga shaidu nan, sannan ina son in gabatar da sheda ta ta gaba wanda zai nuna cewa text ɗin da aka yi masa tare da hotunan da aka turo masa gaskiya ne, hakan zai bamu damar gane tabbas Ziyada tana tarayya da wasu mazan bayan ABUL KHAIRI".

"Kotu ta baki dama". Alƙali ya faɗa yana me kallon ta

"Na gode ya me Shari'a, ina son a gabatar min da Rahina Sulaiman".

"Rahina Sulaiman idan tana nan ta fito". Cewar Maga-takarda

Rahina dake zaune cikin mutanen kotun, ta miƙe ta nufo gaban kotun

Mamy ƙarisa wa kusa da ita tayi tace, "zan so ki gabatar da sunan  ki a gaban kotu domin kowa yaji, da kuma alaƙar ki da marigayiya Ziyada".

"Suna na Rahina Sulaiman, kuma Ni ƙawa ce kuma Aminiya ga Ziyada".

"To a zaman ki da ita zaki iya sanar damu halayyar ta, ina nufin mu'amalar ta da samari? Da kuma yawan samarin nata? Shin ABUL KHAIRI shi ne kaɗai saurayin ta ko kuma akwai wasu wanda kika sani?"

Shiru Rahy tayi tana kallon mutanen wajen, sai kuma tace, "eh saurayin ta ɗaya ne Ni dai dana sani wato ABUL KHAIRI, kuma tunda muka taso muna tare da ita har girman mu, ban taɓa ganin ta da wani saurayi ba, domin soyayyar da take ma ABUL KHAIRI shi ne silan da yasa ba ta iya kula kowa, tunda ta sha ce min ABUL KHAIRI yana da kishi a kanta, kuma muddin ya ganta tare da wani zai iya rabuwa da ita, wanda kuma hakan yasa ta dena kula kowa sai shi kaɗai".

Mamy tace, "kina nufin har ta mutu bata da wani saurayi sai shi?".

Cikin sanyin murya tace, "a'a kafin ta rasu tayi saurayi guda ɗaya wanda take kulawa ba tare da sanin ABUL KHAIRI ba, wanda shi ne ABUL KHAIRIN ya ganta tare dashi a hoto".

Murmushi Mamy tayi, domin abinda take son ji kenan, "to ki faɗa mana alaƙar dake tsakanin su? Kina da masaniyar hotunan da aka turo masa?"

Rahina cike da ƙwarin gwiwa ta gyaɗa kanta, domin ta ɗau alƙawarin bayyana gaskiya saboda ta kuɓutar da ABUL KHAIRI, baza ta so a kama shi da laifin kisan kai ba a yanke masa hukunci ba tare da ya aikata ba, tana son sa kuma tana ganin wannan damar ne kaɗai zai sa ta mallake sa tunda babu Ziyada a duniyar, idan har ya samu damar kuɓuta daga sharrin da aka yi masa, to, ta hakan ne zata same shi ya zama nata, shiyasa sanda Mamy tazo wajen ta domin jin ta bakin ta, ta yanke shawaran faɗan gaskiya ba tare da ta ɓoye ba. Ɗago kai tayi ta kalli inda ABUL KHAIRI ke tsaye, sai hawaye ya cika mata ido saboda tausayin sa da taji ya tsarga mata...

"Rahina muna sauraren ki, kiyi mana bayani da bakin ki yanda zamu fahimta". Mamy ta katse mata tunanin ta

Ajiyan zuciya ta sauke kana taci gaba da faɗin, "Saleem shi ne saurayin da Ziyada take mu'amala dashi a ɓoye ba tare da sanin kowa ba, illa Ni da nasan komi, kuma babu shakka cikin jikin ta nasa ne domin bata taɓa mu'amala da kowa ba sai shi, abinda yasa hakan kuwa saboda ABUL KHAIRI ya ƙi bata wannan damar, ya ƙi yarda su aikata zina har sai idan sun zama mallakin juna, wadda ita kuma ta kasa jure wa har hakan yake kawo saɓani a tsakanin su, wannan dalilin ne yasa tazo waje na neman shawaran yanda zata yi". Shiru tayi tana share hawayen fuskar ta, sai kuma taci gaba. "Ni ce na bata shawaran ta ƙulla alaƙa da Saleem ba tare da sanin ABUL KHAIRI ba, tunda shi yana da kishi kuma idan yaji zai iya rabuwa da ita duk son da yake mata, Ni kuma wannan damar nake so domin raba su". Sai ta ɓarke da kuka ta kasa ci gaba da maganar

Gaba ɗaya kotun tsit yayi kowa na sauraron abinda Rahinan ke faɗi

"Muna sauraron ki Kici gaba". Mamy tafaɗa tana kallon ta

Cikin shashsheƙan kuka tace, "Tun sanda na ɗaura ido na a kan ABUL KHAIRI nake matuƙar ƙaunar sa, sai dai ko kaɗan be taɓa min kallon yanda nake masa ba, nasha nuna mishi hanyoyi da dama domin ya gane soyayyar da nake masa, amma be taɓa nuna min wani alama da ya gane manufa ta ba, ban sani ba ko be gane bane ko ya gane nufi na nuna min ne kawai bazai yi ba ko a'a da gasken dai be gane bane? Amma haka naci gaba da tusa kaina wajen sa duk saboda ina ƙaunar sa, sai dai ganin ba na gaban sa Ziyada ce kaɗai yake iya mata kallon soyayya, sai zuciya ta ta soma bani shawara yanda zan yi in raba sa da Ziyada domin Ni na shiga zuciyar sa, wanda na rigada na gane muddin akwai Ziyada a tare dashi, to, Ni bani da sauran amfani a wajen sa, bazai taɓa kallo na a matsayin masoyiya ba, wannan dalilin ne yasa sanda Ziyada ta nemi shawara a waje na sai naga na samu damar raba su ta hanya me sauƙi, sai na bata shawara tayi mu'amala da Saleem a ɓoye ba tare da sanin sa ba, sannan kuma nabi duk hanyar da zan bi domin ganin na samu hujjojin da zan iya nuna wa ABUL KHAIRI domin ya yarda da taci amanar sa, shiyasa nake bibiyan su duk inda suka je ina ɗaukar su hotuna, kuma na tura masa tare da text a kan, "Ziyada tana cin amanar sa ba tare da sanin sa ba". Wanda Ni nasan cewa dole ne sai ya rabu da ita, domin na san halin sa sosai na kishin da yake dashi, to, a ranan da abun ya faru haƙana ya cin ma ruwa, domin a ranan ne Ziyada ta zo gidan mu cikin tashin hankali tana kuka sosai, take sanar dani duk faɗan da suka yi dashi, Sosai labarin da ta bani ya faranta min rai, amma yanda ta nuna min tayi nadama tana son koma wa ta bashi hakuri sai hankali na ya tashi, na san soyayyar da ke tsakanin su me girma ne, zai iya yiwuwa ABUL KHAIRI ya yafe mata muddin ta nuna nadamar ta, sai na zigata na hana ta koma wa, shawara ta tayi amfani a ranan, domin bata koma gidan sa ba, amma kuma ta kasa jurewa zuwa washe gari ashe ta koma ba tare da ta sanar min ba". Numfashi taja idanun ta jage-jage da hawaye. "Wannan shi ne iya abinda na sani, kuma ta sila ta suka samu saɓani".

Alƙali ɗauke idanun sa yayi a kanta, inda ya ci gaba da rubutun sa

Ita kuma Mamy ta koma ta zauna

Alƙali ɗago da kansa yayi yace, "Barrister Sharif kana da tambayoyin da zaka yi mata ne?"

"A'a ya me Shari'a".

"Ok Barrister Khadeejah kici gaba da gabatar da shedar ki idan kina dashi, ke kuma zaki iya koma wa ki zauna". Ya ƙare maganar da kallon Rahina

Tashi Mamy tayi tace, "ina son gabatar da sheda ta ta gaba Malam Iro".

Malam Iro ya fito gaban kotu

Inda Mamy ta ƙarisa tayi masa tambayoyi kamar yanda tayi masa sanda taje gidan gonan ABUL KHAIRI

Be rage daga bayanan da yayi mata ba a wancan lokacin, haka ma yanzu ya sake maimaita wa



Sannan Mamy tace, "tana son zata gabatar da Azeeza Sani Bala".
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

                  *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                      *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login