Showing 60001 words to 63000 words out of 88313 words
Chapter 21 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
da kallo, "ko meye ya firgitar da ita haka?" Yafaɗa a ransa yana me sake mamaki sosai. Ajiyan numfashi ya sauke jin ta buɗe ƙofan ta shigo, yaja motan suka tafi
A cikin motan ta saka takalman nata da socks tana faman ajiye numfashi wasu hawayen na sake zubo mata
Duk yana lura da ita amma ko ci kanki be ce mata ba har suka nufi school ɗin nasu, ya sauke ta a waje ya juya ya tafi ba tare da ya furta mata komi ba
Da kallo kawai ta bi motan tana tamke bakin ta jin wani kuka ya taho mata, "ga shi ko karya wa bata yi ba amma ya tafi ya barta babu ko sisi, wannan ai cin zalun ne". Haka ta gyara fuskar ta tana shige wa cikin makarantan
Sanda Batool ta ganta sosai tayi murna don bata yi zaton zata zo ba, nan suka rungume juna cike da ɗoki, tuni Maimuna ta manta baƙin cikin ta ta ga ƴar uwa
Sai da Malam ya shigo suka rabu, yana fita kuma suka dasa daga inda suka tsaya, Batool ɗin ta siyan musu abin break tunda ita ta ce, "bata zo da ko sisi ba".
Suna tare har aka tashi har su Amir sun zo wurin ta, ganin ABUL KHAIRIN be zo ba har zata bi Aƙilu ya sauke ta a gida sai ga shi ya zo. Dole ta sauko zata nufi motan nasa, amma Baby ta maƙale mata, "wai sai ta bi ta". Da gudu ta sauko ta nufi motan ABUL KHAIRIN
Shima yana ganin ta ya fito yana ɗaukan ta ya rungume yana faɗin, "Oyoyo Auta na ƴar makaranta".
Tana washe baki tace, "Yaya zan bi ku, wai Aunty Batool ta ce baza ku je dani ba?"
"O'o zamu je dake mana idan har zaki zauna damu".
"Yeeeeee". Tafaɗa tana murna a jikin nasa
Sumbatan ta yayi a kumatu yana kallon Aƙilu drever yace, "ka kawo mata kayan ta idan kun koma". Daga haka ya juya ya saka ta a motan; ta wajen zaman sa, sannan shima ya shiga ya rufe
Sai a lokacin Maimuna itama ta sami shiga, baya ta shige ganin Babyn har ta koma kujeran me zaman banza, haka yaja motan suka tafi Baby na ta musu surutu, shi kaɗai yake amsa ta don ita Maimuna nauyin sa yasa ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi bare ta biye mata, sai murmushi kawai da take yi
A haka suka isa gidan suka fito, Baby na maƙale da ABUL KHAIRI har ɗakin sa
Ita kuma Maimuna ɗakin ta ta shige ta tuɓe kayan ta, sai da ta ɗan watsa ruwa don taji daɗi kafin ta shirya cikin riga da skert ƴan kanti, rigan me ruwan madara ne tana da dogon hannu sai collar a wuyan, sai skert ɗin ja da hulan sa, sun mata cif sosai kasancewar Robber ne kayan, sai a lokacin ta fita parlour'n don ta kira Baby itama tayi mata wankan
A lokacin suna zaune da ABUL KHAIRI a Parlour ya biye mata sai faman surutu take mishi tana ba shi labarin school, shi kuma yana latsa wayan sa yana amsa mata da, "um". Daga shi sai Singlet a jikin sa da gajeren wando. Tunda Maimuna ta fito ƙamshin turaren ta ya ziyarci hancin sa sai ya ɗago kai ya zuba mata idanuwan sa, be iya ɗauke su ba saboda wani irin abu da ya ji ya ziyarce sa a lokaci guda wanda ya haddasa mishi mutuwar jiki da wani irin faɗuwar gaba, har be san sanda ta ƙariso inda yake ba ta janye Baby a jikin sa, sai a lokacin ya dawo hayyacin sa yana janye ido a kanta tare da lumshe su
Ita kuma tuni ta ja hannayen Baby za su wuce ɗaki
Be san sanda ya furta, "ina kuma zaki je? A mean Ina zaki je da ita?"
Juyo wa tayi tana kallon sa, sai dai yanda idanun sa ke yawo a kanta sai ta duƙar da kai ƙasa tace, "dama na ce maka zan mata wanka ne ai". Domin lokacin da ta iso wurin tayi masa magana but be ji ba tsaban hankalin sa ba ya jikin sa
"Dawo da ita Ni zan mata, ki je ki sama mata abinci saboda bata ci komi ba". Yayi maganar a hankali a kuma wani yanayi me kama da yana cikin wani hali
Ita kuwa Maimuna sosai hakan yayi mata daɗi a rai, memakon yayi mata magana a yanda ya saba yau ne kaɗai ta ji ya taɓa mata magana a cikin sanyi matuƙa kuma a tausasan kalamai, shiyasa da sauri ta saki hannun Babyn tayi kichen zuciyar ta cike da farin ciki, haka kawai take jin matuƙar sanyi a ranta, duk da wani gefe na zuciyar ta ta dangana hakan ne da kasancewar akwai Baby a wurin shiyasa yayi mata magana a hankali. Cikin sauri take girkin har jikin ta na rawa, gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa don har ɓarar da abu take yi
ABUL KHAIRI ne ya shigo jin ɓari a tunanin sa ko wani abu ne, da kallo kawai yake bin ta
Ita kuma ta duƙa tana kwashe albasan da suka zube wanda ta yanka ta zuba a Plate
"Lafiyan ki ƙalau kuwa..?"
Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa don bata ji motsin sa ba sai maganar nasa, hakan yasa har taji tsoro
"Ke wai lafiyan ki lau? Tsoron me kike ji ko wani abun kika gani?"
"A'a dama.." sai kuma tayi shiru
"Dama me? Idan ina miki magana ba kya iya ƙarisa min abinda na tambaye ki zaki ci tumu a gidan nan wlh, ki mayar da hankali a kan abinda kike yi". Daga haka ya juya ya bar kichen ɗin, a lokacin ne ya ji ana Nocking sai ya nufi bakin ƙofan don duba wa
Aƙilu drever ne da ɗan akwatin Baby ya taho mata da shi
Gaisuwar sa kawai ya amsa tare da amsar akwatin ya kulle ƙofan ya wuce ɗakin sa.
Shi ya shirya Baby don har yayi mata wankan, sannan suka dawo Parlour suka zauna, har ta fara surutu sai kuma ta fara mishi ƙorafin, "yunwa take ji."
Kallon ta yayi yana shafa mata kai yace, "Auta na rigima ki bari ta kusa gama wa yanzu zata kawo kinji? In kunna miki kallo ko?"
Gyaɗa mishi kai tayi tana langaɓe wa a jikin sa
Sai da ya kunna mata sannan ya miƙa mata Remote control ɗin yana faɗin, "yauwa Auta na ga shi kiyi ta kallon ki bari in duba Auntyn naki".
Amsa tayi, shi kuma ya tashi ya wuce kichen ɗin don duba Maimuna
Lokacin har ta gama sake taliyan da tayi a cikin coolar tana haɗa musu zoɓo fresh
Ya shigo yana faɗin, "wai me kike yi har yanzu?"
Da sauri ta juyo a tsorace har tana ɓaro da jug ɗin zoɓon ya kiɓe a ƙasa, "wayyo Allah". Tafaɗa tana saka hannayen ta biyu a baki idanun ta gaba ɗaya a waje tsaban tsoro
Wani kallo ya aika mata da shi cike da haushi yace, "wai ke kina da hankali kuwa? Uban me kike wa tsoro haka da duk shigo wa ta sai kin tsorata? Kina da hankali kuwa Ni ne kika maida dodon ki?"
Da sauri ta zame ƙasa jikin ta na rawa ganin ya nufo ta, "don Allah kayi haƙuri Yaya, wlh kuskure ne.."
"Kuskuren uban ki, da alamu baki da hankali ko zan koya miki shashashan yarinya".
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 32*
*________* Har ta fara hawaye don a tunanin nata dukan ta zai yi
Sai ya daka mata tsawa a kan, "ta tashi ta gyara wajen if not kuma zai sauya mata kamanni ne yanzu". Daga haka ya ɗau coolarn ya fice fuska ba fara'a
Numfashi ta saki da sauri wasu sabbin hawayen suna sake wanke mata fuska, gaba ɗaya sai jikin ta yayi sanyi Yanzu, ita kanta ta rasa meyasa take firgita haka duk sanda ya shigo.
Sai da ta gyara wajen kafin ta sake haɗa wani ta fita da shi Parlour. A ƙasa ta gansu suna zaune sun bararraje suna cin taliyan, sai kawai ta saki baki ganin har shi yake cin abincin. Ganin zai ɗago kai tayi saurin ɗauke idon ta a kanshi tana ƙarisawa wajen su tare da tattaro nutsuwar ta, a gaban shi ta ajiye ba tare da ta ce uffan ba ta miƙe zata wuce ɗaki
Sai Baby tayi saurin cewa, "Aunty ke fa baza ki ci bane?"
Juyo wa tayi tana kallon ta, sai kuma ta saci kallon ABUL KHAIRI
Kansa na ƙasa yana ta zuƙulƙulan taliyan sa don ba ƙaramin daɗi yayi masa ba
"Aunty zo mu ci mana".
"A'a ku ci Auta na Idan kuka gama zan ci Ni".
"A'a Aunty don Allah ki zo kinga tare muke ci ko a gida ai".
Ganin ta ƙi motsa wa sai ABUL KHAIRIN yayi magana ba tare da ya ɗago kai ba, "kina son ta fahimci wani abu ne salon ta kai mu gaba ko?"
Jin hakan ne yasa ta tako ta zauna gefen Baby suka saka ta a tsakiya, tuna wa tayi bata ɗauko nata Plate ɗin ba sai ta tashi ta je ta ɗauko ta haɗo musu da Cups, ita ta zuba musu zoɓon sannan ta zuba nata abincin. A hankali take cin abincin duk a takure, idan ta kai cokali ɗaya sai ta jima kafin ta sake ɗibo wani kanta na ƙasa
While Baby na ta musu surutu
"Ki yi shiru mana Auta, baki san ba'a surutu ba idan ana cin abinci?"
"Na sani mana Yaya, ai ana koya mana a islamiyya".
"Yauwa big Girl to ci abincin ki. Ki ɗauko min Coke".
Ɗago kai Maimuna tayi ta kalle shi, ganin shima kallon ta yake yi yasa ta gane da ita yake yi, sai ta tashi ta nufi wajen Fridge ɗin ta ɗauko ta kawo mishi, sai da ta zuba mishi a Cup kafin ta miƙa mishi
A lokacin da zai amsa sai da hannun su ya taɓa na juna, da sauri ta janye nata hannun jin wani abu ya tsarga mata wanda har ta so ta zubar da coke ɗin
Yayi saurin riƙe Cup ɗin yana sakar mata wani banzan kallo wanda ya sa ta lokaci ɗaya ta sauke kai ƙasa jikin ta ya fara rawa. Tsaki yaja yana miƙe wa tare da Cup ɗin a hannun sa ya koma kan kujera, sai da ya ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya kafin ya soma sha yana kallo
Daƙyar Maimuna ta ci gaba da cin abincin duk ta gama takure wa. Suna gama wa ta kwashe komi ta nufi kichen Baby na biye da ita a baya. Sai da ta wanke komi sannan suka fito, ɗaki ta wuce ita kuma Baby ta koma wajen ABUL KHAIRI suna ci gaba da kallon su
Sai da aka kira sallan la'asar kafin ya ce, "ta je wajen Maimuna tayi mata alwala". Shi kuma ya wuce ɗakin sa ya ɗauro nasa alwalan ya wuce masjid.
Da motan sa ya tafi shiyasa ya wuce yayi musu siyayyan kayan fruit da gashashshen kaza, ya haɗo wa Baby da su chocolates da zata riƙa tafiya da su school sannan ya dawo gida.
Ganin babu kowa a Parlour sai ya wuce ɗakin Maimuna kanshi tsaye, da sallama a bakin sa ya shiga
Wanda lokaci ɗaya kamar an firgita Maimuna ta tashi daga kwancen da take a saman gado sun kifa ciki tana koya wa Baby Home work, Kallon da yake mata yasa ta duƙar da kanta duk jikin ta rawa yake yi zuciyar ta na bugu
Sai da Baby ta rungume shi sannan ya ɗauke kai daga kallon ta yana bin Babyn da kallo, sai kuma ya mayar kanta ya ce, "Zo ki amsa".
Da sauri Maimuna ta sauko daga kan gadon don ta san da ita yake yi tunda ta ga ledojin hannun nasa, by mistake ta ɗago kai ta kalle shi ta ga har yanzu ita yake kallo, wannan karon harara ya dalla mata yana sake tamke fuska, hannun ta na rawa ta saka ta amshi ledan
Saurin haɗa wa da hannun ta yayi da ledan da ta riƙe yayi mata riƙon da dole sai ta ji zafi
Da sauri ta ɗago kanta tana kallon shi
Ya sake sakar mata wani irin kallo me haɗe da gargaɗi, a hankali ya furta, "muddin baki dena nuna firgitan nan naki ba zan koya miki hankali wlh". Daga haka ya zame nasa hannun yana jan Baby da ta kafe su da ido
A sage ta ja ƙafafuwan ta ta bar ɗakin tana me haɗiye kukan da ya taho mata, "shin ya zata yi da ranta? Bata san meyasa take firgita haka ba duk idan ta ganshi? Meyasa be gane wa ne?". Sai da ta fita Parlour sannan ta duba abubuwan dake cikin ledojin, sai ta saka fruits ɗin a cikin Fridge sannan ta wuce da Kazan kichen, sai da ta kai ta ajiye kafin ta ɗauki ledan Chocolates ɗin Baby ta nufi ɗakin ta
Suna nan a zaune, shi yana kan drowan gadon, Baby kuma na saman gadon ta manne a jikin sa, a haka ya ci gaba da koya mata Home work ɗin
Maimuna kanta tsaye ta wuce ta ajiye mata ledan don ta san na Baby ne tunda ana siyan mata ko a gida, sai ta juya ta fice don baza ta iya sama a ɗakin ita da shi ba
Bata daɗe da fita ba ya fito riƙe da hannun Babyn tana ɗauke da book ɗin ta, wajen Maimuna ta nufa shi kuma ya wuce nasa ɗakin
"Aunty ya ce ki ƙarisa min Home work ɗin". Cewar Baby tana zama gefen Maimunan
"To". Kawai ta ce mata ta amshi book ɗin ta ci gaba da koya mata yanda zata yi.
Bayan sun gama ne ta wuce kichen don ta nema musu abincin dare tunda lokacin kusan ƙarfe biyar da rabi ne, ganin ya ci abincin ɗazu shiyasa ta zaƙe yanzu ta soma shirya lafiyayyen abinci. Tare da Baby suke ta kai komon su cikin Kichen ɗin har ta gama komi wajen goshin magriba, don lokacin har wasu masallatan sun soma kiran Sallah, shinkafa da miya tayi musu, ta sake ɗumama gasashshen kazan tare da musu zoɓo me daɗi sosai, a lokacin har yayi sanyi don ta saka a Fridge, ta kwashe komi ta kai dainning ta shirya
Lokacin ABUL KHAIRI ya fito daga ɗaki ya wuce masallaci
Ita kuma Maimuna ta ja hannun Baby suka wuce ɗakin ta suka yi nasu sallan a can, sai da suka idar ne ta kira Mamy suka gaisa gaba ɗaya mutanen gidan, sannan ta ba ma Baby wayan tana ta musu shirmen ta; ita kuma ta shiga Toilet yin wanka.
Bayan ta fito ta amshi wayan ta sannan ta je ta yiwa Babyn wanka, ta ɗaura mata towul a jiki tunda babu kayan ta a ɗakin, ita kuma ta zira doguwar riga ta sa Hijab ta tayar da Sallan Isha'i. Baby na biye da ita don itama tuni ta saka nata hijabin a kan towel ɗin.
Suna idar wa ta cire rigan ta mayar da towel ta koma gaban mirror tayi shafe-shafen ta
"Nima aunty kiyi min kwalliya". Babyn tafaɗa sanda ta manne a jikin ta
"Nima ba kwalliya nake yi ba Auta na, kuma kin san dare ne idan kika yi barci zai caɓe miki a fuska".
"To nima ki saka min irin ƙamshin ki ina so".
"To zan saka miki bari in gama". Maimunan ta bata amsa tana ci gaba da abinda take yi
Sai kallon ta take yi Babyn sai kuma tace, "Aunty wai yanzu ke matar Yaya ce ko?"
"In ji wa ya faɗa miki?" Ta tambaye ta tana tsayar da abinda take yi
"In ji su Mamy mana, sun ce min yanzu nan ne gidan ki dana tambaye su ina kuke ranan nan? Shi ne suka ce min kuna gidan ku, amma aunty Nima Ina son ayi min aure ayi min irin gidan nan".
"To ai ba a yiwa yara aure sai kin girma". Maimuna tafaɗa tana dariya
"Allah na girma, kinga ai da kaɗan Yaya Amir ya girme Ni ko?"
"Eh haka ne".
"To ayi min aure da Yaya Shureim Ina son sa".
Waro ido Maimunan tayi tace, "kee. Waye ya faɗa miki ana ma irin ku aure? Ai sai kun girma, kar in sake jin kin faɗa kinji?"
"To Aunty, ki saka min kaya na".
"Ok bari in gama shafa miki man sai ki ɗauko a ɗakin Yaya".
"To".
Sai da ta gama mata kafin tace mata, "ta je ta ɗauko".
Tana fita itama kuma ta tashi ta zare hijabin jikin ta ta nufi gaban sif ɗin ta ta soma duba wanda zata saka, doguwar riga ta ciro na barci me ɗan kauri
Tana shirin zame towel ɗin ne ABUL KHAIRI ya shigo ɗakin riƙe da hannun Baby
Da sauri ta riƙe gam tana zare idanu lokaci ɗaya ta firgita sai ga ta a ƙasa a durƙushe
Da kallo kawai yake bin ta da shi kamar wanda zai cinye ta, saurin janye numfashin sa yayi yana sake tsare ta da ido, sai dai tuni ya sake ɗaure fuska yana faɗin, "uban meyasa kika aike ta ta ɗauko kaya ke baki da ƙafafu ne?"
Shiru Maimuna tayi kanta a ƙasa zuciyan ta na bugun uku-uku
"Ba dake nake yi ba?" Ya daka mata tsawa
"Kayi haƙuri don Allah".
Tsaki yaja yana faɗin, "tashi mu je ki gyara mata tunda ke kika aike ta ta zubar. Tashi mana".
Da sauri ta tashi sai dai ta kasa motsa wa, ganin kallon da yake mata baki na rawa ta ce, "um.. dama zan saka kaya ne".
"Wuce dalla uwar me kike da shi da zaki ɓoye min?" Yayi maganar a zafafe yana nuna mata hanya
Da sauri ta wuce lokaci ɗaya hawaye na sauko mata
Shima bin bayan ta yayi idanun sa a jikin ta suka shiga ɗakin nasa.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST