Showing 66001 words to 69000 words out of 88313 words

Chapter 23 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

mu ke ce?"

"Yeee Aunty. Sannu da zuwa". Babyn tafaɗa tana me rungume ta

A time ɗin Maimuna har ta fito daga kichen don duba waye ne? Ganin Azeeza tsaye Baby rungume da ita sai ta tsaya a wurin ta kasa motsa wa tana kallon ta

Azeeza shigo wa tayi ta rufe ƙofan kafin ta bi Maimunan da kallo

Sai a lokacin Maimunan ta yafa wa fuskar ta fara'a tana mata sannu da zuwa

Ɗauke kai tayi a kanta tabi parlour'n da kallo tana me taɓe baki, sai kuma taja hannun Baby suka yi kan kujerun ta zauna tana ɗaura ta a kan jikin ta. Ta kalli Maimuna da har yanzu take tsaye a wurin tace, "Ina shi Yaya ABUL KHAIRIN wurin sa na zo?"

"Yana ciki". Ta amsa mata cikin sanyin murya

"To ki kira min shi".

Bata yi musu ba tayi hanyar ɗakin ABUL KHAIRI, Nocking tayi kafin ta tura ƙofan da sallama ta shiga

ABUL KHAIRI na kwance a kan gadon sa daga shi sai dogon wando yayi kifa ciki tare da ɗaura kansa a kan pilow, idanun sa a lumshe suke tamkar me barci, be buɗe su ba duk da ya ji sallaman Maimunan

Ita kuma ganin sa a haka da sauri ta duƙar da kanta murya na rawa tace, "dama Aunty Azeeza ce ta zo sai tace in Kira ka".

Jin hakan sai ya buɗe idanun sa da suka sauya kala suka sake ƙanƙance wa a kanta, da kallo kawai ya bi ta fuskar sa a matuƙar ɗaure. Sai da ya gama ƙare mata kallo kafin ya mayar da su ya rufe

while Bata san ma Yana yi ba domin kanta a ƙasa yake. Jin yayi shiru sai ta ɗago kai tana kallon sa, "ko dai barci yake yi?" Tayi maganar a fili tana sake leƙen sa

Sai ya buɗe idanu kawai suka haɗa ido

Da sauri ta sad da kanta ƙasa cikin ruɗe wa har ƙafafuwan ta rawa suke

"Out". Yayi maganar a maƙoshi fuskar sa a haɗe

Juya wa tayi da sauri ta fice tana rufo masa ƙofa, sai ta tsaya a wurin tana dafe ƙirjin ta kamar wacce tayi gudun tsere

"Ke ina yake?" Cewar Azeeza da ta hange ta

Shiru Maimunan tayi don bata san me zata ce mata ba

"Ba dake nake yi ba? Kar fa kiyi tunanin don kin aure shi kina da wani matsayi ne a gidan nan, da ke da banza duk ɗaya..." Maganar nata ne ya ƙage sanda taga ABUL KHAIRI ya buɗo ƙofan ya fito yana sakar mata wani banzan kallo

Hakan yasa itama Maimuna ta juya ga bayan ta ta ganshi, da sauri ta janye idanun ta ta soma taka wa zata wuce kichen

Shi kuma tuni ya tako ya isa kan kujera ya zauna a wanda yake kallon Azeeza. Sai ya mayar da kallon sa ga Maimuna da har ta kusa shige wa kichen ya kirayi sunan ta

Cak ta tsaya tana juyo wa ta sauke idanun ta a kanshi, duk da ta san sunan ta ya kira amma tsaban ruɗe wa don bata taɓa jin ya kira ta da sunan ta ba, sai tace masa, "na'am Ni kake kira?"

Kafe ta yayi da ido kamar bazai yi magana ba, sai kuma ya gyaɗa mata kai yana me lumshe idanun sa

Kamar an tsamo ta daga ruwan zafi haka take tafiya har ta ƙarisa wajen sa kanta a ƙasa

"Yaya ina ta gaishe ka baka amsa ba?" Inji Azeeza tana tauna chewing gum cikin salon son burge sa domin ta dawo da hankalin sa kanta, don ta ga ba ta ita yake yi ba

Be kalle ta ba ya sanya hannu ya jawo Maimuna yana zaunar da ita kan cinyoyin sa

A take ita da shi numfashin su ya ɗauke sabida abun da ya ziyarce su daga ƙasar ƙafafuwan su har ƙwaƙwalen su. Lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me tamke bakin sa. While ita kuma tsaban ruɗe wa har suman wucin gadi tayi don ta kasa gasgata itan ce a zaune a saman cinyan sa

Azeeza kuwa tsaban tashin hankali bata san sanda ta zabura zata yar da Baby dake jikin ta ba

Ai da sauri ita ta tashi da kanta tana zama dirshan a ƙasa tabi Azeezan da ido

Hannayen sa ya sanya ya zagayo da su a jikin Maimunan yana me ƙara ƙanƙame ta, daƙyar ya iya buɗe idanun sa da suka sake ƙanƙance wa ya kalli Azeeza fuska babu fara'a yace, "What did you come to do at my house?"

Kasa magana ma tayi tsaban baƙin cikin ganin Maimuna a jikin sa

Shi kuma ganin hakan sai ya saki killer smile yana sake matso da kansa kusa da kunnen Maimuna. Ganin tana mutsu-mutsu duk ta gama diririce wa a hankali yace da ita, "KE ba na son muna-furci ki kama kanki".

Tsit Maimuna tayi tana ƙara lafe wa a jikin sa idanun ta a rufe ruf

"Ehem ina jin ki, me kika zo min a gida?"

Daƙyar ta iya danne baƙin kishin da take ji tace, "amma da kai kaɗai nake son magana".

"Ok da Ni kaɗai? To yanzu Ni da wa kika gan ni?". Sai ya kamo hannun Maimunan yana matse shi cikin nasa yace, "ita mata ta ce, sai kuma Baby dake wurin, you can say whatever you want. Baby come here". Ya ƙare maganar da kallon Baby

Baby dake zaune dirshan a ƙasa tana kallon su da sauri ta tashi ta yo wajen sa ta zauna, tare da jingina jikin ta a nasa ta manne sa

"Ok I hear you".

Babu yanda ta iya Azeeza cike da haushin Maimuna ta kalle ta ta galla mata harara duk da kuwa ita ba ganin ta take yi ba, domin har yanzu ta kasa buɗe idanuwan ta, "Yaya How did you get married I don't know?"

Wani kallo ya sakar mata kafin yace, "Who are you and until I get married I will tell you?"

"Because Ni Masoyiyar ka ce, kuma ko ba komi Ni ƙanwar ka ce Yaya ABUL, be kamata ka wulaƙanta Ni ba, ina son ka Yaya, meyasa Ni baka aure Ni ba sai ita? Ai da Ni ka dace tunda ka rasa wacce kake ƙauna".

Tun soma maganar ta Maimuna ta buɗe idanun ta tana me ɗago kai tare da kafe ta da idanu

While ABUL KHAIRI ganin haka sai ya saka hannayen sa ya riƙo fuskar ta tare da juyo da fuskar tana kallon sa, ido cikin ido suke kallon juna kana yace, "Wai haka Wifey you agree we are not compatible?"

Ƙifƙifta idanu ta soma yi, sai kuma ta daure ta tsayar da su a cikin nasa kamar yanda shima yake bin ta da kallo, ta so ta jure abinda take ji amma ina tuni ta mayar da su ta rufe ruf

Ganin haka yasa ya hura mata iska. Tana buɗe ido ya sakar mata murmushi yana me ɗage mata gira, "You are silent. Are you ok?"

Gyaɗa masa kai tayi don ta kasa ma magana

Matso da fuskar sa kusa da nata yayi har yana ɗaura mata bakin sa a kan kuncin ta, a hankali ya furta, "wlh idan na sake magana kika yi min shiru zan baki mamaki". Ya ƙare maganar yana me ɗago kai still fuskar sa yalwace da murmushi, sai kayi tunanin wani abun kirki ya faɗa mata

Ita kuwa Azeeza kasa jure wa tayi ta ɗauki jakan ta da gudu tayi bakin ƙofa hawaye na kwaranya a fuskarta

Da kallo ya bi ta har ta fice. Sai lokaci ɗaya ya ɗauke murmushin nasa yana bin Maimuna da kallo da kanta ke ƙasa. Har ya buɗe baki zai yi magana sai ya tuna da Baby a wurin, hannun sa ɗaya ya saka ya ɗaura a kan Babyn, kana kuma ya ƙara matso da bakin sa kusa da kunnen Maimuna ya raɗa mata, "dalla tashi min a jiki Bagidajiya".

Kafin ma ta tashi tuni hawaye sun cika mata idanu, daƙyar ta iya motsa wa ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gadon ta da gudu ta soma kuka, bata san meyasa ba sosai taji haushin kalman da ya faɗa mata, shiyasa kawai taji kukan ya taho mata kuma baza ta iya riƙe sa ba

Baby ne ta shigo ɗakin tana faɗin, "Aunty Yaya ya ce ki zo ki duba girkin ki".

Sai a lokacin ma ta tuna ta aza shinkafa, da sauri ta ɗago tana me share hawayen ta a ɓoye, ta miƙe ba tare da ta kalli inda Babyn take ba ta fice, ita kuma tabi bayan ta

Yana zaune a parlour'n be tashi ba, sai dai yanzu wayan sa yake danna wa

Maimuna ko kallon inda yake bata yi ba tayi kichen da sauri kamar ana ingiza ta

Da kallo yake bin ta har ta shige, sai ya taɓe baki yana mayar da idanun sa ga Baby da ta zo ta zauna gefen sa tana mishi surutu, biye mata yayi yana ci gaba da latsa wayan sa.


        Maimuna tana shiga kichen ɗin ta duba shinkafar ruwan da ta zuba har ya ƙone yana shirin ƙauri, dama dafa biyu tayi masa ruwan kaɗan ne a ciki wanda ta sauya, sai tayi sauri ta kashe gas ɗin ta kwashe shinkafan a coolar, ta sauke tukunyan kafin ta ɗauko miyan dake ajiye ta sake kunna wa ta ɗaura a kai don yayi ɗumi. Tana nan tsaye duk ta rasa me ke mata daɗi a jikin ta, gaba ɗaya ta rasa kuzarin ta jin ta take yi kamar har yanzu tana jikin ABUL KHAIRI, ƙamshin turaren sa duk ya mamaye mata jiki da hanci, rasa ma meye takamaiman abinda ke damun ta tayi, haushin sa take ji ko kuma haushin Azeeza ne da ta janyo mata har yace mata Bagidajiya ta kasa gane wa. Lumshe idanuwan ta tayi zuciyar ta na ci gaba da buga wa kamar wacce har yanzu take jikin sa, sai kuma ta buɗe su tana bin kanta da kallo a ranta tana tunanin, "meyasa yake ce mata Bagidajiya mene ne makusanta? Meyasa ba ya ƙaunar ta ne? Me tayi masa?" Tana son sanin, "shin meye aibun ta yake nuna mata tsana?". Janye tunanin tayi ta mayar da hankalin ta kan miyan, yana zafi ta juya ta kashe gas ɗin, ta ɗauki coolar ta sake shi tunda dama ɗan kaɗan ya rage, ta kwasa ta fita. Kai tsaye kan dainning ta nufa ta jera

Sai da ta gama wahalan jerawa kafin yace da ita, "ta kawo mishi nan".

Babu musu ta kwasa ta kai gaban sa, ta ajiye masa har ruwa da lemon Coke da tasan yana sha ko da yaushe, sai ta zuba mishi nashi a Plate sannan ta zuba wa Baby, ita kuma ta tashi ta nufi ɗaki

Da kallo ya bi bayan ta har ta shige kana ya mayar da idanun sa kan Baby dake wasa da wayan sa da ya ajiye, yace, "Ajiye wayan ki ci abinci".

Amsa mishi tayi ta ajiye tare da janyo nata ta soma kaiwa baki

Shima haka abincin ya soma ci a ransa kuma yana tunanin, "meyasa Maimuna ta tafi bata ɗibi nata ba?" Sai kuma ya taɓe baki a ran nasa ya sake cewa, "ita ta jiyo, idan yunwa ya illata ta zata fito".

            Yana gama cin abincin ya shige ɗaki abin sa ya bar Baby zaune tana cin nata.





                      ******

              Ita kuma Maimuna tunda ta shiga ɗaki kwanciya tayi ta rufe idanun ta, duk abinda ya faru zuwan Azeeza komi ke dawo mata, ta rasa meyasa abun ya tsaya mata a rai, bata taɓa tunanin wai akwai ranan da ABUL KHAIRI zai bari ta hau jikin sa ba a yanda yake nuna mata rashin ƙauna. Saurin buɗe idanuwan ta tayi tana tashi zaune, a fili tace, "Oh me ke damu na? me zai sa hakan ya dame Ni bayan yayi ne don Aunty Azeeza." Sai taja tsaki tana tashi ta shiga Toilet, Bata jima ba ta fito tana koma wa ta zauna kan gadon, yunwa take ji sosai ga shi kuma ba ta ƙaunar ta zauna tare da shi tana cin abinci, hakan yana matuƙar takura ta baza ta iya ci gaba da jure wa ba. Tashi tayi kuma ta nufi ƙofa ta leƙa don ta duba ƙila ya gama ci, ai kuwa bata ganshi ba sai Baby dake zaune, da sauri ta fito ta nufi wajen tana tambayar Babyn, "ina yake?" Cikin raɗa

Baby ta faɗa mata, "ya shiga ɗakin sa".

Hakan yasa ta ɗan saki jiki ta zuba abincin taci. Tana gama wa suka wuce ɗaki don yin Sallan Asar da aka kira Yanzu.



       Bayan sun idar book ɗin ta ta ɗauka ta soma karatu

Ita kuma Baby tuni ta fice Parlour wasan ta.












                   ******


           Koda ABUL KHAIRI ya je Masallaci yana dawowa mota ya ɗauka ya sake fita a gidan. Kansa tsaye gidan gonan sa ya wuce, me gadi yana buɗe masa Gate ya shigar da motan sannan ya fito, gaisuwar me gadin kawai ya amsa ya shige ciki. A kan sofa ya zauna yana sauke numfashi tare da lumshe idanuwan sa, shiru yayi na ɗan wani lokaci babu abinda ke dawo masa a rai sai rayuwar sa da suka yi da Ziyada a gidan. Duk tunanin ta ya addabe shi ya rasa ya zai yi, sai kawai ya tashi ya fita ya ja motan sa ya bar gidan, ko kaɗan yanzu ba ya iya zama a gidan duk da ransa na so, sabida kawai tuna Ziyada hakan ke sake ɗaga masa hankali matuƙa. Tuƙi yake yi gaba ɗaya babu kuzari a jikin sa, yana kaiwa gida ya fito ya shiga ciki. A kan Baby dake barci idanun sa suka faɗa, garin wasan ta barci ya kwashe ta a wurin. Janye idanun nasa yayi ya nufi ɗakin sa, har ya taɓa ƙofan zai shiga kuma sai ya fasa ya wuce ɗakin Maimuna.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 35*

*________* Murɗa ƙofan yayi ya shiga da sallama a bakin sa

Maimuna dake kwance a kan gado da littafin ta a hannu, ta ɗago idanu tana kallon sa ta amsa mishi sallaman tana tashi zaune da sauri

"Zo ki dafa min ruwan Lipton ki kawo min ɗaki". Yafaɗa sannan ya juya ya fice

Tashi tayi ta ajiye littafin ta fita, kichen ta shiga ta girka masa ruwan ta zuba a Cup ta fito, sai a lokacin ma ta hangi Baby dake kwance a ƙasa tana barci. Wuce wa ɗakin sa tayi ta bude ƙofan ta shiga bayan tayi sallama

Ba shi cikin ɗakin da alamu yana Toilet ne

Shiyasa tayi saurin ajiye masa ta fita, wajen Baby ta nufa ta ɗauke ta ta mayar kan kujeran, sai ta koma ɗaki taci gaba da karatun ta, bata jima ba ta tashi ta wuce kichen don nema musu abincin dare.





▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

        Azeeza kai tsaye gida ta wuce tana ta kuka

Tunda ta shiga gidan Umma Sulaima ta kalle ta sai ta hau mata dariya tana faɗin, "Allah na gode maka da hakan ta faru, kaɗan ma kika gani wlh muje zuwa".

Uncle Sani ne ya fito daga ɗakin sa jin kukan Azeezan na yawaita yake faɗin, "wai lafiya me ya faru ne Ƴar Baba me aka yi miki?"

Cikin kuka tace, "Baba ABUL KHAIRI ba ya ƙauna ta, gidan sa naje ya wulaƙanta Ni a gaban wancan shegiyar matar tasa, Baba wlh tallahi idan har be aure Ni ba mutuwa zan yi don Allah Baba ka taimaka min".

"Azeeza ya kike so in Yi ne? Taya zan saka ya aure ki bayan ba gani na da mutunci yake yi ba? Gwara ki haƙura ki samu wani ko wane ne zan goya miki baya amma ban dashi".

"Shikenan Baba tunda ba ka ƙauna ta, ai kana da hanyar da zaka bi domin ka ga ya aure Ni, ba damuwa tunda ka fi son in shiga duniya shikenan". Tayi maganar tana wuce wa ɗakin Kakar su

Bin Bayan ta yayi shima ya shiga yana kiran sunan ta

Kaka tace, "ka dai ji kunya wlh, idan har ka bari jika ta ta shiga duniya wlh Sani Ni da kai ne a gidan nan, tunda ita uwar ta ba ta ƙaunar haɗin kai meyasa baza ka goya mata baya ba tunda ta nuna tana son yaron nan? Aure fa ba wasa ba in kuma ka fin son shiga duniyar ai shikenan".

Ita dai Azeeza kuka take ta yi kanta a jikin Kakar tasu

Ita kuma tana rarrashin ta

"Shikenan zan je wajen Deebizan muyi magana tunda haka kike so ki zubar min da mutunci a wurin su".

"Yo ta zubar maka da mutunci ko dama tun tuni ka zubar da kayan ka? Ai ka bar shiri tun rani. Idan da ace Deebiza ba me kyakykyawar zuciya bace ba na tunanin zata sake kallon mu da idon rahama sabida abubuwan da suka faru a baya, ga shi ƙanwar ta ita ta ƙullace mu har yanzu ba ta mana kallon arziƙi, tunda tayi aure bata taɓa tako wa gidan nan da sunan gaishe mu a matsayin ƴan uwan ta ba. Hmm rayuwa kenan".

"Ni fa Umma har yanzu ba na tunanin na yiwa Deebiza wani abun da zai saka nayi nadama". Uncle Sani yayi maganar cike da fushi, kana kuma ya kalli Azeezan yace, "ki kwantar da hankalin ki ƴar Baba, muddin ina numfashi sai kin auri wanda kike so, ABUL KHAIRIN banza da hofi shi wane ne da har zai ƙi son ki yake son wulaƙanta ki? Ba abun murnan sa bane ma ace kina son sa? Da me ya fi ki da zai riƙa jan miki aji? Ki kwantar da hankalin ki goben Nan insha Allahu zan je gidan nasu in same Iyayen nasa kuma zamu yi magana".

Washe baki Azeeza tayi tana tashi daga jikin Kakar cike da murna tace, "yauwa Baba na na gode sosai, shiyasa na fi son ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login