Showing 54001 words to 57000 words out of 88313 words
Chapter 19 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
lazimi, a lokacin ne har ta samu damar bin ɗakin da kallo, kawai sakin baki tayi tana bin ko ina da kallo, a ranta kuma tana mamaki da kuma farin cikin ganin duk wannan daulan ɗakin ta ne, me ya fi wannan daɗi?
Lumshe idanuwan ta tayi tana sake buɗe wa a lokaci ɗaya, a hankali ta tashi ta ninke sallayan ta ajiye, sannan ta fice don taga gidan, duk da a ranta tunanin ABUL KHAIRI kawai take yi, "ko ya shigo mata a jiya sanda tayi barci?" Shi ne bata sani ba, bata san ya zaman nasu zai kaya ba. Da wannan tunanin nata ta gama zagaya ko ina, ɗakin nasa ne kawai bata yi gigin shiga ba don zuciyar ta tuni ta kawo mata tunanin nan ne nashi ɗakin, sai ta koma nata ta cire hijabin jikin ta ta ninke ta mayar sannan ta fito ta wuce kichen, yunwa take ji shiyasa gwara ta nemi abinci ya fiye mata alkhairi
Abu me sauƙi ta haɗa, daga ruwan tea da ta dafa ta sake shi a flaks, sannan ta soya ƙwai biyu ta ɗauko bread duk ta Kai saman dainning, ajiye wa tayi ta zauna ta ɗiba ruwan zafin ta haɗa tea a Cup, ta sha da bread ɗin tare da ƙwan da ta soya.
Bayan ta gama ta gyara wurin, shima ABUL KHAIRI duk ta ajiye masa abun da zai buƙata sannan ta wuce ɗakin ta, wanka ta shiga ta fito ta nemi kayan saka wa, riga da zani ne raffer na atamfa, sun yi mata kyau sosai kuma sun yi mata Cass a jikin ta, kasancewar ta ba me girman jiki ba komi nata ɗan dai-dai ne tubarakalla Masha Allah, tayi kyau matuƙa bare ita ba baya ba wajen iya ɗauri, matsalan ta kawai bata iya kwalliya ba, saboda bata saba ba ko kaɗan, idan ta shafa Powder da jan-baki ya wadatar da ita, amma kuma tunda tana da kyau sosai take yin kyau, yanzun ma ta fito a Amaryan ta sak sai walƙiya take yi
Zama tayi a kan gadon ta tana tunanin kuma me zata yi, sai duk taji ta wani iri sabida rashin sabo, gani take yi kawai komi kamar a mafarki wai yau ita ce tayi aure? Kuma auren ma ABUL KHAIRI shi ne mijin ta? Sai kawai ta hau yin dariya tana tallabo kumatun ta, a fili ta furta, "oh wa ya ga Maimunatu Amarya, wlh gani nake yi kamar ba gaske ne ba zan ji Batool ta tashe Ni. To wai Ni ya rayuwata zata kasance a gidan Yaya ABUL? Shin ta ya ya zaman mu zai kasance? Abun da kunya wlh". Sai ta sake darawa lokaci ɗaya tana jin ƙwalla na cika mata ido na tausayin kanta da kanta, sosai take jin tausayin kanta matsananciya ya kama ta, tana jin kuma kamar baza ta iya wannan sabon rayuwar ba. Kwanciya tayi tana me lumshe idanun ta sai ga hawayen ciki sun zubo, bata yi yinƙurin share wa ba illa janyo wayan ta dake kan gadon da tayi ta soma latsawa, Mamy ta soma kira don sosai tafi jin kewar ta
Ring biyu ta ɗauki wayan. Ita ta soma kiran sunan Maimunan bayan da tayi mata sallama
Cikin matuƙar ɗoki da rawan murya ta amsa ta tana cewa, "Mamy nayi kewar ki. Yaushe zaki zo?"
Dariya daga can Mamyn tayi tace, "Haba ɗiya ta kar ki saka Abban ku yayi mana dariya bayan na gama cika baki a kanki".
Dariya itama Maimunan tayi kana ta gaishe ta cike da kunyar ta
Mamy ta amsa cike da farin ciki tana tambayar ta, "ya ta kwana?" Kafin kuma ta tambaye ta, "Ina ABUL KHAIRIN?"
Ita kuma tayi mata ƙaryan, "ya shiga wanka".
Daga nan Abba ta ba wa wayan suka gaisa yana ta tsokanar ta
Ita kuma sai dariya take yi tana ɓoye fuskar ta
Da Mamy ta amshi wayan take faɗa mata, "ga su Batool nan za su taho yanzu".
Ai nan ta dinga murna tana faɗin, "Mamy me zan dafa musu?"
Dariya daga can su Mamy suka yi, don har su Aunty Naana suna jin ta
Mamy tace, "ke da kike Amarya ina ke ina girki? Kar ki soma ki girka musu komi don su ma ba daɗe wa za su yi ba, za su zo su sake gyara miki gidan ne".
Kamar zata yi kuka tace, "to Mamy".
Daga nan kuma suka yi sallama ta kashe wayan, miƙe wa tayi sabida zumuɗi ta koma Parlour zaman jiran su.
Babu jima wa kuwa sai ga su sun zo, duk ƴan uwa ne gaba ɗaya ƴan bikin suka zo don ganin ɗaki, dayake wasu a lokacin za su tafi shiyasa suka yo zuga, da su Aunty Naana aunty Rufaida yayyin Maimunan duk suna nan, tunda a nan aka yi bikin gaba ɗaya ba'a kai Maimuna can Kaduna ba, dangin Mahaifin ta ne kawai suka yi tasu bikin a can, kuma daga ƙarshe suka taho nan, har da su yanzu a ganin ɗakin amarya tunda yau za su koma, sai su Aunty Fatima ƙanwar Mamy, da kuma Zee me jego.
Sosai Maimuna tayi murnan ganin su har da ƙwallan ta
Su kuma su Aunty Rufaida sai tsokanar ta suke yi da faɗin, "ƴar ƙanwar mu ta zama babba".
Ita sai dai tayi dariya ta ɓoye fuskar ta a jikin Batool
Haka suka zazzagaya gidan ko ina suka gani, sannan suka gyara mata abun da ya kamata, har ɗakin ABUL KHAIRI sun so shiga amma sai dai suka ji shi a garƙame, da suka tambaye ta, "ina yake?"
Tace musu, "ya fita".
Duk sun yarda shiyasa suka ci gaba da harkokin su
Su Aunty Naana da suka gane tamkar wani abu be faru ba, ai nan suka saka ta a ɗaki sukai ta mata lectures ta yanda zata kama ABUL KHAIRI a hannun ta
Ita kuwa kunya duk ya rufe ta kamar ta nitse
Aunty Naana da tafi su zafi har make ta tayi tace, "sai ta ci uban ta idan ta sake rufe fuska, gwara ta tsaya ta saurari abinda suke faɗa mata don idan bata yi wasa ba sai ta titsiye ta ta maimaita abinda suka faɗa mata kaf".
Dole ta nutsu ta mayar da hankalin ta sabida ta san zata aika in dai Aunty Naana ce
Daga ƙarshe da za su tafi suka ce mata, "ta cire kayan nan ta saka ƙananan kaya. Kar kuma ta sake saka wasu kaya a gidan nan idan har ba ƙanana ba".
Da "to". Ta bi su dashi jiki na rawa ta sanya wanda Zee ta ciro mata, duk ta takura amma babu halin musu
Hijabi ta sanya ta rako su har waje da za su tafi kamar zata yi musu kuka, daɗin abun ma an bar mata Batool tunda ita ba yanzu zata tafi ba shiyasa taji ɗan dama-dama
Suna tafiya suka dawo parlour'n suka zauna
Batool ta ƙwage murya tana tonon Maimuna da faɗin, "Amarya Amaryan Yayan mu".
Da sauri Maimunan ta rufe mata baki tana zaro ido tace, "keee wlh yana ciki".
"Ɗan girman Allah fa?". Batool ɗin tafaɗa da sauri itama tana zazzare ido
Dariya sosai ta ba wa Maimuna, sai kawai ta hau mata dariyan tana nuna ta da yatsa
Dukan ta Batool tayi tana hararan ta tace, "ba na son sharri kinga har kin sa ciki na ya ɗuri ruwa, wlh sai in tashi in koma".
Daƙyar Maimunan ta tsayar da dariyan nata tana rufe bakin ta tace, "wlh da gaske nake miki yana ciki babu inda ya je".
Tsaki taja Batool ɗin tana gyara zaman ta, sai kuma ta kalli ƙofan ɗakin sa sannan ta mayar da idanun ta kan Maimuna, ƙasa-ƙasa tace, "amma shi ne kika yiwa su Aunty Naana ƙarya?"
"To me zan ce musu bayan kina gani suka buga ƙofan yaƙi buɗewa? Idan ban ce musu haka ba kinga baza su haƙura ba kin san halin Aunty Naana".
"To tashi mu je ɗakin ki don zan fi sake wa a can, nan ba wurin zaman mu bane".
Dariya Maimuna tayi tana miƙe wa tabi bayan ta, "kai Batool ban san ki da tsoro ba wlh".
Itama dariyan tayi tace, "hmm ai naga da alamu kin soma manta Yaya ABUL ne tunda kika shigo gidan shi, amma Ni ban manta waye shi ba, koda yake kina da hujjar ki me ƙarfi, ƙila yanzu tunda kin zama matar shi bazai miki komi ba, amma Ni idan ba so nake in Koma wa su Mamy da ƙafafu a karye ba ai gwara in kama kaina".
Tsaban dariya Maimuna har da faɗa wa kan gado
Batool ta maka mata duka a cinya tana cewa, "yanzu kin zama muguwa ko? Kema da alamu ya koya miki muguntar daga kwana da shi sau ɗaya".
Tana dariyan tace, "ke dai ki rufe bakin ki kar ya ji ki wlh don babu ruwa na".
Kama bakin ta kuwa Batool ɗin tayi tana matsowa kusa da Maimunan, tsaban gulma ya ci ta kamar dole sai tayi ta ɗan rage murya tace, "to bani labarin fisrt night ɗin naki? Me ya faru don Allah?"
Sai kawai Maimuna ta soma zazzare ido tana faɗin, "ke rufa min asiri don Allah, Ni fa yarinya ce har yanzu wlh, kuma kin san Yaya.."
Tsakin da Batool ɗin taja shi yasa tayi shiru, tana hararan ta tace, "dalla rufe min baki, su Mamy sun san ke yarinyan ce suka yi miki Aure? tunda haka ne nima zan yi auren nan in huta tunda baza ki bani labari ba".
Maimuna tace, "hmm Batool kin san dai babu abinda zai faru kema neman magana ne dake, idan akwai ai bazan ƙi faɗa miki ba, Ni wlh ban ganshi ba tun sanda suka fita da Yaya Sulaiman jiya".
"Allah Sarki Sister na tausaya miki, ko ya ya zaman ku zai kasance da shi? Amma kuma be kamata ki zauna haka ba wlh idan Ni ce babu na mijin da zai wulaƙanta Ni haka, ai dole wlh sai ya bani kula wa ko ya ƙi ko ya so, tashi maza yanzu ki je ki taso shi, ai ma be kamata ki bar shi yana yin abinda yaga dama ba, ya ƙuntata miki kuma ya je shi yayi farin ciki".
"Ni kuma ce miki nayi ya ƙuntata min? Don Allah ki ƙyale Ni kinji".
"Allah wlh sai kin je kin taso shi kinji ma na rantse, idan ba haka ba sai dai in kira Mamy in sanar mata komi, yanda ya bar ki jiya ke kaɗai kika kwana don uban ki ba ƙuntata miki yayi ba? Wataƙil ma ko barcin kirki baki yi ba shi ya je yana sharan nashi".
Maimuna ɓata fuska tayi tace, "Ni kike zagi ko? Kin san dai yanzu Ni matar yayan ki ne kuma dole ki ce min Aunty, yanzu babu wasa a tsakanin mu".
Hararan ta Batool ɗin tayi tace, "don ina faɗa miki gaskiya? Tashi dalla ko in Kira ta wlh".
Ƙin tashi Maimunan tayi tana sake ɓata fuska don dai Batool ɗin taji shakkar ta ta barta, amma da ta ga ta ɗauki waya ai da sauri ta tashi tana cewa, "to ga shi na tashi ko malama. Wlh ni har kin fara saka min ciwon kai".
Bata saurare ta ba sai ma jawo hannun ta da tayi tana fadin, "baza ki gane bane Maimuna, idan kika tsaya sanya kina jiran sanda Yaya ABUL zai karkato gare ki kina da jan aiki, ai ke ce zaki riƙa shige masa wlh, duk wani haƙƙi nasa ki je ki sauke masa, yanzu ba wani abu fa nace kiyi ba, zuwa zaki yi ki taso sa ki ce mishi ga Breakfast ɗin sa".
Ita dai Maimuna bata ce komi ba illa sauraron ta da take yi, har sanda ta ajiye ta a gaban mirror tana mata kwalliya
Sai da tayi mata light make-up kafin tace, "yauwa to ko ke fa, har fuskar taki ta sake yin kyau, yanzu cire hijabin nan". Kafin ma tayi magana har ta saka hannu tana cire mata
"Haba kiyi min a hankali mana". Maimunan tafaɗa tana hararan ta
Banza tayi mata tana janye hijabin ta wurgar saman gado, sai ta washe baki kawai tana bin Maimunan da kallo riƙe da ƙugu. "Kai my sister don Allah ki kalle ki fa".
Ɗago kai tayi tana kallon kanta a Madubin tana kallon yanda kayan suka lafe mata a jiki, cike da kunya tace, "wai kina nufin haka zan je?"
"Eh mana. Gaskiya kinyi kyau wlh. Tashi mu je in raka ki".
"Kai wlh bazan iya zuwa ba ai wannan iskanci ne sai yayi zaton na kawo kaina ne".
Taɓe baki Batool ɗin tayi tace, "sai me? Dama haka kuke ai matan hausawan nan, ke dashi kun zama ɗaya meye kuma na kunya? duk abinda zai ce sai dai yace, abinda ke cutar daku kenan, na rantse da Allah da Ni ce a ranan farko sai na fara shiga zuciyar miji na ko ya ƙi ko ya so sai nayi kane-kane a ciki".
"Allah ya sa dai kema bahaushiyan ce".
"A'a amma Ni kin san nayi gadon su Hajiya Mama ce, kuma kin san ita Banufiya ce don haka Ni babu ruwa na da Hausa wa da kuma gidadancin su".
Tsaki Maimuna taja tace, "hauka. Kanki ake ji dai domin ko kin ƙi ko kin so ke bahaushiya ce, kuma daɗin abun ma Hausawan sun fi Nufawan kamun kai".
"To tashi mu je dai." Ta ja ta suka fice, har bakin ƙofan ɗakin ABUL KHAIRI ta kaita, kana ta juya ta tsaya a bakin ƙofan ɗakin Maimunan tana leƙen ta, ƙasa-ƙasa take ce mata, "baza ki buɗe ba".
Tura baki Maimunan tayi kafin ta soma Nocking a hankali
Ganin haka sai Batool ɗin ta iso wajen ta ta hau buga ƙofan da ƙarfi
Da sauri ta riƙe mata hannu tana zare ido, cike da tsoro da murya ƙasa-ƙasa tace, "na shiga uku Batool don Allah ki bari".
"To kiyi Nocking da kyau idan ba haka ba zan ta buga ƙofan wlh, kuma idan ya fito ɓoye wa zan yi".
"To naji naji zan yi please".
Sai Batool ɗin ta juya da gudu har tana cin tuntuɓe jin kamar ana taɓa ƙofan za'a buɗe
Ita kuwa Maimuna sandare wa tayi a wurin idanun ta a waje tana kallon ƙofan.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 30*
*________* Yana buɗe ƙofan ya sauke idanun sa a kanta, wani irin abu ne ya tsarga mishi ganin ta a irin wannan shigan da be taɓa ganin ta ba, duk yanda ya so ya janye nashi idanun daga kallon ta amma ina ya kasa, daga sama har ƙasa yake bin ta da kallo ba tare da ya ko ƙyafta su ba
Ita kuwa yanda taga wannan kallon nashi tuni ya sanya ta rawan jiki, saboda gani take yi kamar zai duke ta yanda fuskar sa yake a ɗaure. Daƙyar ta iya haɗo kalmomin bakin ta wajen faɗin, "uhm.. hmmm dama..." Sai kuma ta rasa abun faɗa illa murɗa yatsun ta da take yi hawaye har sun soma cika mata ido, dole ta sauke idanun ta ƙasa saboda kallon da yake mata yanzu, cikin rawan murya sosai ta furta, "Break..fast.. naa..yi.." shiru tayi ganin ya juya ya shigewar sa tare da rufo ƙofa.. da sauri ta saki ajiyan zuciya hawayen dake maƙale a idanun ta suka zubo mata sanda ta lumshe su. Jin an dafa ta a firgice ta juya don ta manta akwai Batool a gidan, a tunanin ta ko shi ne
Dariya sosai yaso kama Batool, amma sai ta rufe bakin ta ta janyo mata hannu suka yi ɗakin ta. Suna shiga ta sake ta ta dinga mata dariya. "Wlh ke babban matsoraciya ce, ban taɓa tunanin haka kike ba sai yanzu.. wayyo Allah na". Sai ta sake kwashe wa da dariya har da riƙe ciki. "Kin ga yanda kika yi kuwa?"
Hannu Maimunan ta saka tana share hawayen fuskar ta kafin tace, "baza ki gane bane wlh na tsorata, nayi tunanin duka na zai yi da yake min wannan kallon shi ne yasa jiki na yake rawa duk na tsorata, kuma kinga da irin kayan da naje wajen sa wlh shi ya ƙara tsorata ni". Ta ƙare maganar tana zama bakin gadon ta har da dafe kai
"Ke banza ce ai, wannan kallon shi ake ce mishi alamun nasara, taya idan baki tafi da hankalin shi ba zai tsaya kallon ki? Wlh ni na tabbata shigan ki ne ya ɗauke mishi hankali. Kinga da haka wata rana shikenan zaki shiga zuciyar sa, kar ki damu ƴar uwa da sannu komi zai wuce".
"Kina nufin in ci gaba da yi wata rana ya make Ni kenan? Ke baki san yanda naji bane kamar in nitse tsaban kunya".
Batool tace, "ai kuwa zaki nitse wata rana, ke fa sokuwa ce ba mijin ki bane?"
"Kar ki sake ce min sokuwa". Cewar Maimunan tana banka mata harara
Taɓe baki ita kuma tayi tace, "to tunda kinyi baki yanzu ai sai ki rama. Ni kinga bari in je in ci wani abun don ban yi kari me kyau ba". Ta ƙare maganar da yin hanyar ƙofa ta fice.
Maimunan bata ce komi ba illa ɗaukar hijabin ta da tayi ta rataya tabi bayan ta. A kan dainning taga Batool ɗin tana haɗa tea. Zama tayi gefen ta tana cewa, "mu ga wayan ki in yi turi saboda in samu abun taya Ni hira".
Cikin ƙasa-ƙasa da murya Batool ɗin tace, "ba ga Yaya ABUL nan ba kin samu shi ne zai taya ki hiran ai".
Ɗaukan wayan tayi bata ba ta amsa ba ta shiga File manager ta soma duba waƙoƙi, tana yi tana saka wa idan yayi mata sai ta tura
A haka suke zaune babu wanda ya sake magana, illa Batool ɗin dake bin waƙan idan Maimuna ta saka, tana yi tana kurɓa tea ɗin ta
Wayan ce ta soma ringing, ganin Sulaiman ne sai Maimuna ta ɗauki wayan tana kara wa a kunne, cikin ɗoki da murna ta amsa mishi sallaman da yayi, "tace Yaya na ina kwana".
"Amarya kina lafiya? Ya Angon naki?"
Cike da kunya tace, "kai yaya bayan ma baka zo