Showing 48001 words to 51000 words out of 88313 words
Chapter 17 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
GARI* na facebook, dariya suke yi duk su biyun
Baby ta faɗo da gudu cikin kichen ɗin, wajen Maimuna ta nufa tana sanar mata da saƙon Mamy
"Me bakin kwaɗayi ke ko? Sai na yanka bakin wlh". Cewar Batool tana hararan ta
Ita kuwa sai cinno mata baki tayi tana sosa goshin ta
While Maimuna na dariya bata ce komi ba
Batool ta sake cewa, "to uban wa kike cinno wa baki? Wuce dalla idan mun fito sai ta ɗauko miki".
Kuka take shirin yi domin har ta fara murza ido zata fara
Sai Maimuna ta riƙe mata hannu tana cewa, "A'a Autana kar kiyi kuka kinji ƙyale wannan Auntyn naki, Bari in gama wannan sai muje in baki ko?"
Gyaɗa kanta tayi tana cire hannun nata a idon, sai kuma ta soma tsalle-tsalle a dole sai ta gano abinda Maimunan take yi, dayake tsawon ta bazai kai ta hango abinda ke cikin tukunyan ba
Dariya Batool dake kallon wayan ta takwashe dashi
"Ke kuma dawa?" Maimuna ta tambaye ta tana juyo wa tana kallon ta
"Wlh labarin nan ne ya bani dariya, wai fa wata ce tayi tambayar wai, "shin maza suna shagwaɓa ne?" Shi ne wani ya bata amsa. "Sai kin ɗaura shi a kan Nono zaki ga zahiri".
Dariya Duka suka saki daga ita har Maimunan, inda Maimunan take cewa, "halan a Twitter ne?"
"Wlh kuwa. Bari ma kiji wani, wata ce tace, "dama azumi 300 ake yi". Sai wani ya bata amsar, "da yanzu duk zuri'ar ku kiristoci ne".
Nan ma dariya suka sake kwashe wa dashi
"Wlh sai kin ma gaji da jin irin wannan rainin hankalin, bari dai mu fita duk ki gani a zahiri, kwanaki ma naga an yi posting ɗin su ai a wani group ..Sirrin ƴa mace.. a facebook, wata ce tayi wai tana neman posting ɗin twitter tayi missing shi ne ake ta turo mata, baki ga yanda na sha dariya ba ranan kina barcin nan, na so in tashe ki amma sai na ƙyale ki, sai kuma wannan matsalan ta Kunno Kai na Ya ABUL shi ne ya mantar dani".
Murmusawa kawai Maimuna tayi tana kakkaɓe hannayen ta da ta gama ɓare Maggi ta zuba a girkin, sai kuma tace, "Ai group ɗin nan ina son shi ana ƙaruwa sosai wlh".
Batool zata yi magana sai ɓarin da Baby tayi ya katse ta, tace, "wannan yarinyan ba kya ji wlh, dama yaushe zaki zauna haka nan baki yi ɓari ba, dalla fice a nan".
Kuka ta fashe dashi zata fice a guje
Sai Maimuna ta riƙe ta tana cewa, "kiyi shiru ƙyale ta kinji? Mu je in baki sweet ɗin". Sai kuma ta kalli Batool da ita har ta mayar da idanun ta kan wayan ta domin ya ɗauke mata hankali. "Batool ɗan kwashe min albasan nan don Allah kafin in dawo."
Batool bata kula ta ba don ma ba ta ita take yi ba
Ita kuma Maimunan tuni ta fice riƙe da hannun Baby.
Suna shiga ɗakin su shi kuma Abba ya shigo da sallama
Amir dake kallo ya amsa mishi yana mishi sannu da zuwa
Amsa shi yayi ya wuce ɗakin Mamy, sallama yayi ya shiga
Mamy ta amsa shi tana ɗago kai daga latsa computern da take yi, sannan tayi mishi sannu da zuwa
Ya amsa yana zama kan kujera yace, "agogo Sarkin aiki".
Murmushi Mamy tayi tace, "Ayya Abban su yanzun nan na fara fa, ban daɗe da dawowa ba aka ce min kun fita".
"Eh wlh, Sagir ne yazo gaishe mu, shi ne kuma nace ya raka Ni wani waje. Amma an dace ko?".
Gyara zaman ta sosai tayi tana fuskantar sa sai tace mishi, "Eh naga mutumin kuma mun tattauna dashi, amma Abban su akwai wanda ya tambaye ka game dani a yau ɗin nan?"
"Kamar ya ban gane ba?" Yayi maganar shima yana kallon ta
"Ina nufin a game da aiki na, ko akwai wanda ya tambaye ka inda naje ko ci gaban da ake samu?"
Shiru Abba yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma yayi dariya yace, "kai ku dai louyoyin nan sai a hankali, yanzu kuma wani abun zaki gano kenan?"
Itama dariyan tayi kafin tace, "ai Abban su ba na son wani ya san inda naje ne da abinda nake yi ne saboda tsaro".
"Haka ne kuma, nima na san da wannan ai, sai dai babu wanda ya tambaye ni, duk da dai mun yi waya da Abbas yau kuma mun tattauna a kan matsalan, ya tambaye Ni ci gaban da ake samu amma ba muyi maganar zancen ki na zuwa ƙauye dubo inda aka siya layin nan ba, sai kuma Sagir yanzu da yazo gaishe mu yake tambayar ki, shi ne nace mishi kin fita, amma ban sanar mishi ga inda kika je ba".
Ajiyan zuciya Mamy ta sauke, sannan ta mayar da idanun ta kan computern ta, sai dai ba aikin taci gaba da yi ba illa faɗa wa zuzzurfan tunani da tayi
Sai da Abba yayi magana har sau biyu bata ji ba, kafin ana ukun ta ɗago kai tana kallon sa
"Me kace ne Abban su?" Ta tambaye sa stiil tana kallon sa
"Wannan tunanin me kike yi haka? Anya ba kya takura wa kanki? Yanzu daga magana har kin faɗa tunani me zurfi haka?"
"Kayi haƙuri dan Allah wlh wani abu nake tuna wa".
Ɗan tsira mata ido yayi, sai kuma yace, "to faɗa min abinda ya faru da kika je ƙauyen".
Nan ta faɗa mishi komi
Sai shima kawai yayi shiru yana me faɗa wa tunani
Dama ta san hakan zai faru, abinda ke ranta dole shima zai kawo hakan, bata ce komi ba dai ta tashi ta shige Toilet, kamar mintuna biyar ta fito tana nufan computern ta ta rufe
"Amma wa kike zargi?" Abba yayi maganar yana kallon ta
Sai da ta zauna kafin tayi ajiyan zuciya tace, "Abban su har yanzu dai tunani na be bani wanda nake zargi ba, ni kaina abin yana ɗaure min kai wlh, na rasa ya zan yi, amma kai da wanda kake tunani ne?"
"Eh akwai wanda ya faɗo min a rai, duk kwatancen nan da mutumin nan yayi miki dai-dai ne dashi, amma taya zai kasance shi ne?"
"Wa kake zargi Abban su?" Tayi maganar cikin zaƙuwa da ji
Murmushi yayi yace, "ki bari don Allah hasashe ne". Sai ya tashi yana ci gaba da faɗin, "bari inje akwai inda zan je, zuwa dare zan dawo insha Allah".
"To amma baza ka faɗa min ba?"
"Idan na dawo zamu yi maganar kinji? Domin akwai shawaran da nake so in baki". Yayi maganar yana kallon ta tare da gyara wa hulan sa zama
"To shikenan sai ka dawo".
Fita yayi ya bar ta cikin tunani, ta jima a wurin ita kanta bata san iya lokacin da ta ɗauka ba tana faman tunani, sai da taji kiran sallan magriba kafin taja numfashi fuskar ta cike da damuwa ta tashi ta wuce Toilet don ɗauro alwala.
_Please kuyi haƙuri da wannan, kaina ke ciwo wlh daƙyar nayi muku._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 27*
*________* *COURT*
Yau ma kotun cike maƙil da mutane, inda aka soma gabatar da Shari'a cikin tsari. Wayan Azeeza aka soma kunna bidiyon da tayi musu aka saurara
Bayan an gama sai Brr. Sharif ya tashi yace, "ya me Shari'a kamar dai yanda muka saurari wannan videon ne, tabbas a ciki ABUL KHAIRI yayi iƙirarin sai ya kashe Ziyada, kuma ga shi ya cin ma burin sa, don haka ya me Shari'a ina so ayi duba da wannan kalaman nasa a yanke mishi hukunci nan take sabida shi ne ya kashe ta. Na gode ya me Shari'a". Sai ya koma ya zauna
"Brr. Khadeejah ko kina da wani shaidar da zaki iya gabatarwa?"
"Eh ya me Shari'a". Tafaɗa tana tashi tsaye
"Ok muna sauraron ki".
"Ya me Shari'a ina son a gabatar min da Malam Sadau Aliyu".
"Idan Malam Sadau na kusa ya fito".
Fitowa yayi ya tsaya
Mamy kuma tazo dai-dai wajen sa ta tsaya tana cewa, "Malam Sadau kotu zata so ta san abubuwan da ka sani game da lokacin da aka zo aka siya Simcard a wurin ka?"
Gyara tsayuwar sa yayi sosai kafin ya soma ba da bayani tiryan-tiryan kamar yanda ya sanar wa Mamy
Bayan ya gama sai Mamy tace, "ya me Shari'a ina so in gabatar da shedata ta gaba wanda Sadau zai tabbatar mana da shi ne wanda ya siya Simcard a wurin sa. Sagir Alh. Muh'd Iyal".
"Sagir Alh. Muh'd iyal ya fito".
Sagir dake cikin mutane tun kiran Sadau da aka yi ya soma zufa, gaba ɗaya fuskar sa ta jiƙe da zufa, be taɓa tunanin asirin sa zai tonu lokaci ƙanƙani haka ba, don haka ya ma kasa fito wa kanshi na duƙe. Sai da aka sake maimaita sunan shi kafin ya samu ya fito jikin sa a sanyaye
"Sadau wannan shi ne mutumin da yazo wurin ka ya siya Simcard?"
"Eh tabbas shi ne wanda yazo ya siya, kuma ya dawo yayi min barazanar barin wurin zuwa nan da ɗan wani lokaci".
Jinjina kai Mamy tayi zuciyar ta babu daɗi, ta kalli Sagir ɗin tace, "zaka iya mana bayanin abinda ka sani?"
Hannun sa dake rawa ya saka a fuskar sa yana sharce gumin sa, daƙyar ya iya buɗe baki yace, "ban san komi ba game da abinda kuke magana akai, hasali ma lokacin da abun nan ya faru ba na nan ina wurin aiki na".
Murmushin takaici Mamy ta saki tana jin idanuwan ta na son ciko wa da hawaye, sai ta juya ga Alƙali tace, "Ya me Shari'a Sagir shi ne wanda ya kashe ƴar uwan sa Ziyada, kuma shi ne wanda muka kama dumu-dumu da kiran layin ABUL KHAIRI da police ya sanar musu da kisan kan bayan ya aikata ya gudu, shi ne yayi ƙoƙarin laƙaba wa ABUL KHAIRI bisa hujjar sa mara tushe, ina roƙon kotu da ta tursasa shi ya faɗi gaskiya".
Alƙali sai da ya gama rubutu kafin ya ɗago yana kallon Sagir yace, "ka sanar mana da abinda ka sani kar ka wahalar da mu, domin muddin aka gano gaskiya kotu zata tuhume ka da ɓata mana lokaci da kayi, muna jin ka ka sanar mana da abinda ya faru tun kafin ƴan sanda su yi bincike akai, idan ba kai kayi kisan ba taya ka sanar musu cewa an yi kisan?"
Tsit kotun tayi suna sauraron abinda zai faɗa
Inda shi kuma jikin sa na rawa sosai duk ya fita hayyacin sa wanda zai sa ka gane be da gaskiya, kuma dubun sa ta cika da be yi zaton hakan ba, haƙiƙa yau yana nadamar abinda ya aikata, be san da wani ido zai kalli iyayen sa da mutanen da suka san shi ba...
"Muna sauraron ka". Cewar Alƙali
"Ziyada ƴar uwa ta ce kuma na taso da ƙaunar ta tun muna yara, sai dai abin baƙin cikin tun sanda na kawo Aboki na ABUL KHAIRI gidan mu ya ganta sai ya nuna yana son ta, itama hakan ne a wurin ta, inda suka ƙulla soyayya ina ji ina gani bayan tarin soyayyar da nake mata, wanda na tabbata Aboki na ya san da hakan amma be nuna min ba, kanshi kawai ya sani a wannan lokacin, Ni kuma hakan yasa na ɓoye tawa soyayyar da zummar in cire ta a zuciya, but hakan ya gagara, kullum zuciya ta tana gaya min hanyar da zan bi don ruguza tasu soyayyar domin samun Ziyada a matsayin mata ta, wanda har na je wa iyaye na da maganar amma suka nuna in aje zancen gefe tunda mahaifin ta ba yanzu zai mata aure ba, duk sanda aka tashi sai su nema min auren ta, duk wani alaƙar dake tsakanin ABUL KHAIRI da Ziyada na sani saboda yana sanar min be ɓoye min komi, wanda Ni kuma hakan ke matuƙar ƙona min rai nayi iya ƙoƙari na wajen na hana sa domin kishin da nake yi dashi, a kullum sai na riƙa faɗa masa rayuwar da suke ɗauka a matsayin wayewa su daina hakan haramun ne, wanda Ni kuma ina yin hakan ne domin ya dena shiga gona ta. kwatsam sai na gano cewa Ziyada tana tarayya da wani bayan ABUL KHAIRI, ta rigada ta sallama kanta gare shi, sai abin yayi min ciwo matuƙa har na tafi gida neman ta domin in nuna mata soyayya na kuma in CE mata Ni kaɗai ne wanda ya kamata ya keta ta ba wani ba, amma ban cid da ita ba, sai na wuce kai tsaye gidan gonan ABUL KHAIRI wanda na san a can zan same ta, a waje na bar mota na na shiga ba tare da sanin me gadi ba. Sanda na shiga tana zaune a Parlour, Bata Yi tunanin komi ba ta tarbe Ni da fara'a, amma hakan be sa abinda nake ji a kanta ya ragu ba, domin sosai naji zafin sallama kanta da take yi a wurin wani na mijin. Kai tsaye na nuna mata idan har hakan take so Ni zan iya mata sabida ina matuƙar ƙaunar ta, tayi mamakin zantuka na har ta ruɗe lokaci ɗaya da ta san na san abinda take aikata wa, amma cewa da nayi sai dai ta dawo waje na in maye mata gurbin wancan. Sai tace, "sam ita bata taɓa ɗauka na a matsayin wanda zata iya aura ba, ta ɗauke Ni a matsayin Yaya ne wanda muka fito ciki ɗaya, kuma ABUL KHAIRI kaɗai zata iya aura". Share hawayen sa yayi kafin yaci gaba da faɗin, "naji zafin maganganun ta ƙwarai domin ban zata zata ƙi Ni haka ba, inda zuciya ta ja Ni naso nayi amfani da ita ta ƙarfi da yaji, amma ita taƙi yarda tana kuka a kan, "in ƙyale ta baza ta taɓa tarayya dani ba domin Ni Yayan ta ne," Ni kuma ban saurare ta ba, haka muka yi ta tirka-tirka a kan dole sai na cin ma buri na, wanda tsautsayi ya ja Ni na ɗauki wuƙa domin in Yi mata barazana, amma kuma sai ta buga hannu na garin ƙwatan kanta na caka mata wuƙan ba tare da sani na ba". Kuka ya fashe dashi a sanda yazo nan a zancen sa. "Haƙiƙa nayi nadamar abinda na aikata a wannan lokacin duk da ba'a son Raina bane, Amma tsautsayi ya ja Ni na aikata abinda zai zo ya rusa min gaba ɗaya rayuwa ta, na rasa ya zan yi ne shiyasa na bar gawan a nan na fita jiki na na rawa, babu wanda ya gan Ni shiyasa na yanke shawaran kawai in Kira ƴan sanda in sanar musu bayan na kira ABUL KHAIRI ya je gidan, hakan zai sa kawai su kama shi a matsayin wanda yayi kisan, ina da tabbacin ABUL KHAIRI bazai taɓa ganin gawan Ziyada ya barta haka ba ba tare da ya taɓa ta ba, wannan ne zai sa kawai duk wani abinda za'a iya zargi na ya goge".
Gaba ɗaya kotun ta ruɗe da hayaniya, iyayen Ziyada kuwa kuka sosai suke yi da jin asalin labarin, wanda suka raina tun yana ƙarami shi ne ya zama makashin ƴar su ɗaya tilo da suke matuƙar so? Haƙiƙa yau suna dana-sanin abinda suka aikata a gare shi, da basu kawo shi gidan su ba da duk hakan be faru ba
ABUL KHAIRI kuwa dake tsaye da hand cuff a hannu, idanun sa a ƙasa sai tsiyayar da hawaye yake yi, sosai abinda Sagir ɗin ya faɗa ya matuƙar girgiza shi, hawayen kawai da yake zubar wa su suke rage masa raɗaɗin da yake ji a ransa.
Sai da Alƙali ya buga gudumar sa kafin suka yi shiru, inda ya ɗauki lokaci yana rubutu kafin ya ɗago yace, "a bisa hujjojin da aka gabatar da kuma amsa laifin shi da Sagir yayi, kotu ta wanke ABUL KHAIRI da zargin kisan kan da ake mishi. Shi kuma Sagir kotu ta yanke mishi hukuncin kisan kai ta hanyar rataya bayan an yi masa horo me tsanani". Sai ya buga gudumar sa yana miƙe wa
Haka kotun suka haɗa baki wajen faɗin, "koooootuuuuuu". Kowa na miƙe wa
Inda ka ga ahalin ABUL KHAIRI kowa murna yake yi tare da godiya ga Allah da yau ya nuna musu wannan ranan
While shi kuma yana tsaye a wurin da yake ya lumshe idanuwan sa hawayen ciki suna ci gaba da kwaranya, bazan iya faɗa muku irin baƙin ciki da ɗacin da yake ji a zuciyar sa ba, duk da a wani gefe yana me farin cikin wanke shi daga zargin da ake mishi, yau ya sami free a matsayin sa na wanda ake tuhuma da kashe rai.
gefe ɗaya kuma mutane sai Allah wadai da halin Sagir suke yi, gaba ɗaya kotun ta hargitse da hayaniya, ana fita ne ma tamkar ba a yi
Iyayen Ziyada sai kuka suke yi musamman Mom ɗin ta, haka shima iyayen Sagir ɗin, duk kunya ya cika su ga dangi ta ko ina.
Su Abba dai tuni sun tarkata sun fice tunda aka kwance ABUL KHAIRI, basu tsaya hira da ƴan jarida ba suka yi gida, gaba ɗaya gidan ya cika maƙil saboda masu taya su murna, ƴan uwa da abokan ariziƙi har da maƙota sai shigowa suke yi
Lokacin itama Zee mijin ta ya kawo ta, cikin ta ya tsufa sosai haihuwa ko yau ko gobe, tare da mutanen gidan mijin nata suka zo taya su murna
Dole su Ummu suka tashi suka ɗaura girki tunda ga su su da ba yanzu za su tafi ba ma, baza a zauna haka nan ba.
Lokacin su Maimuna su ma suka dawo school, suka cidda wannan daddaɗan labarin. Lokacin ma ABUL KHAIRIN yana ɗaki har yayi wanka an ba shi magani sabida zazzaɓin da ya rufe shi, dayake dana barci shi ne ya samu barcin ya ɗauke shi.
Da ake mayar da zancen ne su Maimuna suka ji wanda yayi kisan, ai sai Batool ta tashi tsam ta shige ɗakin su
Tana shiga ta faɗa kan gadon ta ta soma kuka