Showing 3001 words to 6000 words out of 88313 words
Chapter 2 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ta'ajiye saman table ɗin, ta miƙe da sauri don zuwa ɗauko abun goge wa tun kafin ya natse a cikin cerfet ɗin
Mi ƙe wa yayi da sauri ya saka mata ƙafa, sai jin ta tayi a ƙasa timm a ruf da ciki, hakan yasa ta bugu sosai har ta bige haɓan ta, duk da Allah ya so ta cerfet ɗin ɗakin me taushi ne, amma sai da taji zafi sosai wanda yasa ta saki ƙara me haɗe da kuka
Shi kuwa tuni ya koma mazaunin sa tamkar ba shi ne yayi aika-aikan nan ba, sai ma ɗauke kai da yayi yana faɗin, "idan na ƙirga biyu baki bayyana a gaba na ba, wlh sai na fitar miki da haƙora".
Babu shiri ta yunƙura ta tashi, ta rarrafo gaban sa tana ci gaba da kukan ta har da ƙara Volume
"Rufe bakin". Ya daka mata tsawa da faɗan hakan
Da sauri ta saka hannu ta kama bakin ta tana runtse idanu jikin ta na mazari
Kallon ta kawai yake yi yana nazartan ta, sai ya ja dogon tsaki cike da takaicin abinda ya tuna yana cewa, "ta shi ki je Toilet ki ɗauko abin Moping ki gyara min wajen, shashashan yarinya".
Still jikin ta na rawa ta tashi tabi umarnin abinda yace mata
Shi kuwa kwanciya yayi yana lumshe idanuwan sa, shi kaɗai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin, har yanzu ya kasa samun nutsuwa a zuciyar sa, yasan halin Ziya sarai, ya kuma san me zata iya aikata wa tunda ba hankali ne da ita ba, dole ya nemo mafita, fushi ba nasa bane yanzu, shawaran da zuciyar sa ta ba shi dashi zai yi amfani..
Har Maimuna ta gama gyara wajen be ma sani ba, sai buɗe idanu yayi ya hangi bayan ta ta buɗe ƙofa ta fice, tsaki ya ja cike da tsanar yarinyan, shi fa gaskiya ba ya tunanin zai iya rayuwa da wannan tatsitsiyan yarinyan, kallon ta kawai yake yi tamkar wata munafuka, sabida kullum a shiru-shiru take, irin su ne sumui-sumui kasau.. macijin ƙaiƙayi
Tashi yayi ya gyara zaman sa ya soma cin abincin sa.
▪️▪️▪️
Koda ta fita babu Mamy a parlour'n, don haka ta tsaya ta share hawayen ta da suke kwaranya saman fuskar ta, ɗakin su ta wuce kanta tsaye
Tana shiga Batool dake zaune gefen gadon ta, har ta rigada ta gama shiryawa ma, ta miƙe da sauri ta nufo ta tana tambayan ta "lafiya kika daɗe baki dawo ba?"
Duƙar da kanta ƙasa Maimuna tayi, hawayen da ta tsayar dasu don dole sai ga su sun soma kwaranya, dama ƙiris take jira ayi mata magana, sai ta soma gunjun kuka
Hankalin Batool a tashe ta riƙo ta tana sake tambayan ta "ko wani abun yayi mata?" Don itama ta rigada tasan halin Yayan su akwai mugunta
Ganin ta kasa yin mata magana, sai ta hau share mata hawayen tana bata haƙuri, "Sorry Sister kiyi haƙuri, kin san halin Yayan namu mugunta ne fal cikin sa, haka nan zamu riƙa haƙuri har Allah ya kawo ƙarshen zaman mu tare, ya haƙuri kinji ki dena kuka".
Shashsheƙan kuka take yi tana saka hannu itama tana share hawayen nata da suka ƙi tsaya wa, ba tare da tace uffan ba sai ajiyan zuciya da take faman sauke wa
Hannun ta Batool ta riƙo cike da tausayin ta tace, "kiyi haƙuri kinji? Yanzu mu je ki sauya kayan ki mu tafi".
Babu musu Maimunan ta nufi wajen gadon, inda Batool ɗin har ta fid do mata kayan da zata saka irin nata; da taji ta shiru bata dawo ba
Saka kayan tayi riga da skert na atamfa, fuskar ta kawai ta gyara ta saka Hijab ɗin ta kalan na Batool ɗin suka fito, sai da suka je ɗakin Mamy suka ce mata "sun tafi" kafin suka fito, drever ya ɗauke su suka bar gidan
Gidan su Juwairiyya ƙawar su, wacce suke school tare zasu je, mahaifiyar ta bata da lafiya shi ne suka yi mata alƙawarin zuwa duba ta.
Suna fita babu daɗe wa, su ma su Amir da Baby suka dawo daga school; school Bus ɗin su ta ajiye su a bakin Gate.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Sanda Ziyada ta fito daga gidan gonar ABUL KHAIRI, itama kai tsaye gidan su ta nufa, tana yin horn me gadi ya wangale mata Gate ɗin ta shige ciki, bayan ta fito daga cikin motan ta rufe ta nufi ciki
Momyn ta na parlour'n ƙasa tana kallo ta shigo ba tare da tayi sallama ba, sai ma kwaɗa wa mahaifiyar nata kira da take faman yi
"Kaiii wannan kira haka Daughter kamar zaki bani wani abun? Lafiya dai?"
Ƙarisowa tayi ta zauna kusa da ita tana shigewa jikin ta tamkar wata ƙaramar yarinya, sai dai tsaban sangarta ta da aka yi ne yasa ba ta shakkar shigewa jikin iyayen nata ko agaban waye kuwa
Shagwaɓa ta soma mata tana ƙorafin, "yunwa take ji"
Momy shafa kanta tayi tana faɗin, "ban da abun ki Daughter don kina jin yunwa sai ki zo kina min kiran mafarauta? Ai sai ki saka naji tsoro wlh, don zan yi tunanin wani abun aka yi miki".
Dariya Ziyada ta ƙyalƙyale dashi tana cewa, "kai Momy ke dai kin cika tsoro".
Murmushi kawai Momyn tayi, kana ta soma kwaɗa kiran me aikin su
Tana zuwa, taba ta umarnin ta kawo ma Ziyada abincin ta
Amsa mata tayi ta juya da sauri don cika umarnin ta.
Babu jimawa ta dawo da abincin ta kawo mata, sannan taje ta ɗauko mata drinks a fridge ta ajiye mata ta juya
Abincin Ziyada take ci suna hira da Momy, har sanda ta gama ta miƙe tana cewa, "Momy wai yaushe Dady zai dawo ne? Na matsu ya dawo wlh coz Ina da maganar da zamu yi".
"Mun yi waya dashi yanzu, zuwa 08:00pm. Yace zai shigo". Momy ta bata amsa da faɗin hakan
"Ok bari inje in ɗan yi wanka Momy zafi nake ji".
"To agwagwa Sarkin wanka".
Buga ƙafa ta soma yi tana mata shagwaɓa, wai don tace mata agwagwa
Sai da Momyn ta lallaɓa ta kafin ta wuce sama inda ɗakin ta yake
Tana shiga wankan ta soma yi, ta sauya kayan ta zuwa farar t.shirt dogo har gwiwar ta, sai ta saka leggings kalan ruwan ƙasa, ko ɗankwali bata saka a kanta ba tunda dama ba ta saba sawan bane, zama tayi kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun ɗakin nata, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana faman duba wayan ta, tsaki kawai ta dinga ja saboda ganin ABUL KHAIRI be kira ta ba, har ta danna masa kira saboda sosai take sha'awar jin muryan sa, duk da kuwa yanzu suka rabu but ya rigada ya sabar mata da koda yaushe suna manne a waya, sai kuma ta katse tana maida akalan kiran ga ƙawarta Rahina, tana jin ta amsa call ɗin ta gyara zaman ta tana jingina bayan ta a kujeran
"Hello Rahy kina gida ne?"
Daga can Rahina ta amsa mata tana me faɗin, "lafiya dai ta samu ne in zo?"
Sai da Ziyada ta saki numfashi kafin tace, "ina buƙatar ki wlh, akwai maganar da nake so muyi dake yanzu idan babu damuwa".
Rahina tace, "ok gani nan yanzu ɗin kuwa, dama ina kwance ne ina huta wa, amma yanzu zan zo".
"Ok sai kin zo". Ziyada tafaɗa tana cire wayan daga kunnen ta. Ajiye wa tayi tare da kwanciya tana rufe idanun ta.
Kamar mintuna 20 sai ga Rahina ta shigo ɗakin da sallaman ta
Tashi Ziyada tayi tana kallon ta tare da amsa mata
Rahina ta ƙariso ta zauna gefen ta tana faɗin, "ƙawata lafiya dai, kin ga yanda idanun ki suka yi ja, meke faruwa?"
Ɓata fuska Ziyada tayi tana shafa fuskarta, sai kuma ta cire hannun tana maida idanun ta kan Rahinan tace, "wlh Bie ne yake son bani matsala Rahy, na rasa ya zan yi". Taƙarishe maganar tana buga tagumi tamkar zata yi kuka
Hannu Rahina ta saka ta zame mata tagumin tana cewa, "dama maganar ba ta wuce na gizo da ƙoƙi, yanzu kuma me ya faru? Mene ne ya haɗa ku?"
Haɗe hannayen ta waje ɗaya tayi idanun ta a kan Rahinan tace, "kin san yanda Dady yake da burin in yi karatu me zurfi, ko kaɗan ba ya son maganar aure na da Bie da nake ta kawo masa, yace dole sai nan da two years sannan na haɗa degree ɗina, kuma kin san halin ABUL KHAIRI yana da taurin kai da kafe wa a abu ɗaya, shi yaƙi ya gane matsalan da nake ciki, yanzu a kan abinda be kai ya kawo ba ya dage bazai kusance ni ba dole sai mun yi aure, iyakan sa romancing ko kaɗan yaƙi ya bani haɗin kai, kuma zafin kishin sa ya hana Ni zuwa ga wani, wlh na kai limit ɗin da bazan iya jure wa ba, jiya munyi tsiya-tsiya dashi don nace zan nemi wanda zai biya min buƙata ta tunda shi bazai iya ba, shi ne yayi fushi sosai yaƙi nema na, Ni kuma na kasa jure wa sai na bi shi gidan gona amma kuma yau ma ya sake wulaƙanta Ni don na sake yin masa maganar". Taƙarishe maganar nata da jan numfashi fuskarta cike da damuwa
Rahina da ta zuba mata idanu tana sauraron ta, wani daɗi ne ya kamata, sai dai bata nuna a fuska ba sai ma nuna alhinin ta da tayi, ta saka hannu ta riƙo na Ziyadan tana faɗin, "to ke me kika yanke yanzu?"
"Shawarar ki nake nema Rahy, gaskiya Ni na gaji, bazan iya jira har muyi aure ba, kullum sai dai ya tada min da sha'awa amma babu biyan buƙata, ga shi kuma Saleem yana ta bibiya na naƙi ba shi dama, Ni yanzu na yanke shawara ne zan ba ma Saleem dama ba tare da sanin Bie ba, don wlh bazan iya bin ra'ayin sa ba, sai dai zuciyata tana cike da tsoron idan muka yi aure da Bie ya gane na ba da kaina a waje, ban san me zai faru ba ranan, don na san kashi na ya bushe, don wlh duk son da yake min zai iya rabuwa dani, Ni kuma tsoro na ya rabu dani, domin bazan iya rayuwa babu shi ba, Bie nawa ne Ni kaɗai, babu macen da ta isa ta shiga tsakanin mu ban kawar da ita ba". Sai tayi shiru tana maida idanun ta kan Rahina, sai kuma taci gaba da maganar, "Rahy ke kaɗai ce ƙawata da zan iya faɗa mata sirri na da Bie sabida tsantsan KISHI NA a kan ko wace mace, Yanzu shawaran ki nake nema, me kike ganin ya kamata in yi?"
Ajiyan zuciya Rahina ta sauke a hankali, ta ɗan muskuta zaman ta tana cewa, "tun farko dama nayi tunanin hakan zai iya faruwa ƙawata, wannan hanyan nake ta son nuna miki amma soyayyar ABUL KHAIRI ya rufe miki ido, sam kin kasa gane daɗin rayuwa, ke a ganin ki ABUL KHAIRI kaɗai zaki iya wa tanadin kanki, wa ya faɗa miki ana haka? Ai yanzu duniya ta waye wlh, idan kika ga mace tana zaune ba ta wannan harkan, to, tabbas bata waye bane, kinga kuma ke kina Big Girl ace kin zauna har yanzu baki san karatun nan ba, wlh maza da yawa suna kallon ki a wayayyiyan yarinya ce, but sai an zo aga ba haka ba, ina ce irin haka ne Saleem ya gani wajen ki yake son ƙulla alaƙa dake? amma kuma kin ƙi ba shi haɗin kai, kin yi watsi da zafafan Guys da suka zo wajen ki duk a kan ABUL KHAIRI, uhm ƙawata zan wayar dake abinda har yanzu kika kasa gane wa, shi fa wannan abun idan kika yi, wlh ba ABUL KHAIRI ba, ko da gogaggen ɗan duniya ne wanda ya san kan mata; ya fita ajikin wannan ya shiga jikin wancan, to sai kin so zai iya gane kin taɓa irin wannan harkan, yanzu duniya ta waye komi kika gani an rigada an tanadi mafitan sa, akwai wacce zan haɗa ki da ita ƙawata ce me siyar da maganin mata, wlh duk ƙwaƙwan mijin ki idan ya aure ki bazai taɓa gane namiji ya kusance ki ba, ke in faɗa miki ma; magungunan da zata baki kina amfani dashi kafin bikin ki tuni kin koma kin ɓame koda kuwa kin taɓa haihuwa ne, ko budurwa baza ta nuna miki budurci ba".
Tuni fara'a ya baibaye fuskar Ziyada saboda jin maganar ƙawarta, cikin zaƙuwa tace, "kina ganin ABUL KHAIRI bazai taɓa gane ba na tare da budurci na ba?".
Ɗan gajeren tsaki Rahy ta saki tace, "me aka yi akai ABUL KHAIRI ƙawata? Shi da be san ma kan komi ba sai idan ya aure ki".
Washe baki Ziyada tayi tana gyaɗa kanta, "Gaskiya ne Rahy, Bie be san wannan harkan ba, dani kaɗai yake iya haɗa jiki, tunda har yaƙi kusanta ta, to ina ga babu macen da Bie zai iya kusanta a faɗin duniyar nan idan har ba aure aka yi musu ba, na yarda da shawaran ki kuma zan bi".
Murmushi Rahina ta saki cike da murnan cin Nasara, kana ta sake gyara zaman ta taci gaba da ɗaura ta kan turban da take so, sai da tasan komi yayi tasiri a zuciyar Ziyada kafin ta tashi tayi mata sallama tace mata "zata tafi gida".
Rahy na fita Ziyada ta ɗauki wayan ta ta soma ƙoƙarin neman layin saurayin ta Saleem, shi kaɗai ta yarda zata iya harka dashi sabida shi zuciyarta tafi aminta dashi, domin dai a komi ABUL KHAIRI ba zai nuna wa Saleem ba, sai ma shi yafi shi, sai dai kuma zuciyarta ABUL KHAIRI take tsananin ƙauna ba wanin shi ba, shi kaɗai take iya kallo a masoyi kuma mijin da zata iya rayuwan aure dashi, tana mishi wani irin mahaukacin so da baki ma bazai iya faɗan sa ba, ta rigada ta sallama zuciyarta ga ABUL KHAIRI kamar yanda shima ya rigada ya mallaka mata nashi tuni.
Three missed calls tayi masa amma be ɗauka ba, don haka ta tura masa Text message a kan "su haɗu Gobe"
Kashe wayan tayi sabida kar ma ABUL KHAIRI ya same ta, a ranta tana fatan Allah yasa kafin goben ya sauya ra'ayin sa, ba sai ta je ga Saleem ba.
.
_Uhmmmm Mu je zuwa fans._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧*LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A* ✍️
*JIKAR LAWALI CE* ✍️
*Wattpad UmmuDahirah* 👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*NASIHA*
'''Sallah ta ƙwarai, ingantacciya, wadda aka yi ta cikin tawali'u da ƙasƙan da kai, tana haskaka zuciya, ta tsarkake ta, kana tana koya wa mai yin ta tsintar hanyar Ibada da abubuwan da suka rataya a kansa, waɗanda suka shafi Ubangijin sa, don kuwa ta sallah ɗin ce girma da ɗaukakar Ubangiji za su tabbata a zuciyar sa. Sallah tana sa mutum ya zama sahihi, mai gaskiya da riƙon amana, mai fahimtar abubuwa, mai kunya mai auna kome yake yi, mai yawan kyauta. Tana daɗa nuna masa cewa dai Allah Ɗaya ne, yana kuma jin tsoron sa, yana kuma girmama shi. Ta yin Sallah ne yake inganta rayuwar sa, ya tsarkake zuciyar sa, ya nisanci ƙarya da makirci, zamba, fushi da fariya, gaba, tauye wa mutane haƙƙi, rowa, ƙeta da rashin biyayya, da dai sauran miyagun halaye.
Sallah Ibada ce ta zuci da ta jiki. Mai yin ta zai haskaka da harshen Allah. Yin Sallah shi ne babbar alamar cikar imani, mafi darajar hanyoyin Ibada, kuma hanya mafi tabbata ta nuna godiya ga Allah saboda tarin baiwar da ya yi mana. Yin watsi da Sallah yana nesanta mutum da Allah, ya rasa rahamar sa da falalar sa da jin ƙan sa.
Martabar Sallah ta kai ma cewa mutum ba ya iya barin ta a cikin ko wane hali ya sami kansa. Dole ya kawo ta ko yana tafiya ko yana gida, ko cikin tsoro ko cikin aminci. Allah yasa mu dace.'''
*________________________________*
*PAGE 3&4*
*________* Sai da ya gama cin abincin sa kafin ya tashi ya nufi cikin Toilet, wanka yayi ya fito ɗaure da towel, be saka kaya ba sai da ya tsane jikin sa ya shafa Lotions sannan ya shirya cikin farin yadi, ɗinkin tazarce da yaji aiki da brown ɗin zare, turare ya fesa sama-sama ya zauna a gefen gadon sa. Wayan sa ya ɗauka ya soma neman Numban Ziya sabida zuciyar sa da ta hana sa sukuni, sai dai jin wayan a kashe yaja dogon tsaki yana wulwula ta a kan gadon, ya dafe kansa da hannu biyu tare da runtse idanun sa gam, zuciyar sa wani irin suya take masa tare da zafi, gaba ɗaya ta hana sa sukuni, shi ya rasa meyasa ya zama soko wawa a kan ƙaunar Ziyada ne, ko kaɗan ba ya iya jure fushi da ita, idan har suka samu saɓani shikenan ya rasa farin cikin sa da walwalan sa har sai ya samo mafita, idan kuma ba haka ba ya dinga zama kenan cikin ƙunci yana shan wahala da zuciyar sa. Soyayyar da yake ma Ziyada ya wuce kwatancen mutum, yana mata wani irin mahaukacin so tare da tsantsan kishin ta, wanda idan har ya rasa ta ba ya jin zai sake mintuna biyu a duniya, kallon fuskar Ziyada kaɗai ya ishe sa samun farin cikin duniya.
Numfashi ya fesar yana cire hannayen sa daga kan shi, ya miƙa hannu tsakiyan gadon da ya jefa wayan sa ya wawura ya soma typer mata Text, sassanyan kalamai me haɗe da ban haƙuri ya rubuta ya tura mata. Riƙe wayan yayi a hannu ya tsira mata idanu ba tare da ya ajiye ba, babu abinda zuciyar sa ke tsimaye sai son ganin kiran ta, ko kuma samun reply,