Showing 27001 words to 30000 words out of 88313 words

Chapter 10 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

ya miƙe yana ɗaukar keey ɗin motan sa ya fita da mugun sauri, Allah ne kaɗai ya kai sa wajen motan sa, don be san ma inda yake jefa ƙafafuwan sa ba, motan ya shiga yaja ya figa ya bar Companin da mugun gudu kamar zai tashi sama.

             Kai tsaye gidan gonan sa ya wuce, wani irin mugun horn yake saki har sai da Gate man ya buɗe masa Gate ɗin, figan motan yayi ya shige a tsiyace, ilai kuwa abinda yake zato ne, ya hangi motan Ziyada a ciki. Be yi ƙwaƙƙwaran parking ba ya fito ya nufi cikin gidan da mugun sauri ransa a matuƙar ɓace.




**** ***** ******* *********

            Lokacin da ABUL ya shige da motan sa ciki, a lokacin ne Azeeza ta sauka daga keke napep, tana hangen sanda ABUL ɗin ya shiga gidan, hakan yasa tayi saurin biyan me napep ɗin kuɗin sa ta ƙarisa ciki, me gadi na shirin rufe ƙofa ta taho tana gaishe sa

Nan da nan ya washe baki yana amsa wa, tare da tambayan ta kwana biyu wai, "bata zo ba?"

Murmushi tayi tace, "Baba kenan, ai yanzun ma saƙo nazo amsa wajen Yaya ABUL, kuma naga kamar yanzu ya dawo ko?"

"Eh eh yanzun nan ya dawo, amma fa ina ga ba lafiya ba! sabida yanda na gansa kamar hankalin sa a tashe ne".

"Eyya! To bari in shiga wajen sa, ga wannan babu yawa". Ta miƙa masa 3k

Amsa yayi yana ta zuba mata godiya kamar ta ba shi garin

Ita kuwa bata bi ta kansa ba ta shige abun ta, dama tana son ne su haɗu sabida maganar da ta zo mishi dashi, ita a ganin ta idan har zai so ta, to ta amince zata ba shi jikin ta kamar yanda Ziyada take yi, tunda ai bata fi ta da komi ba a jiki ba, don haka itama a shirye take ta ba shi jikin ta in dai zai so ta, shiyasa ta biyo shi nan don su yi magana

Amma kuma tana shiga taga motan Ziyada, ta rigada ta shaida motan nata ne tunda ta ganta wancan zuwan, tunda motan guda biyu ne, daga na ABUL sai nata. tsaki taja tana nufan bayan windown kamar yanda tayi wancan karon, so take yi ta tabbatar da me suke yi kafin ta burma ciki, don ya san cewa ta san me yake yi, inyaso ma ta ɗauke su hoto ta tona masa asiri wajen iyayen sa idan har be yarda da abinda tazo mishi dashi ba, tayi alƙwarin duk hanyar da zata bi sai tabi don ta mallake sa, shiyasa ta saki wani miskilin murmushi taƙarisa windown da sauri tana saka hannu ta buɗe a hankali, babu Lock hakan sai yayi mata daɗi, ta saka hannu ta ɗage labulen da ya kare mata ciki.

              A lokacin ne ABUL KHAIRI ya saka hannu ya kwashe Ziyada da mari, tsaban gigita sai da tayi ƙasa daɓas tayi zaman ƴan bori tana kwatsa ihu

Jiki na rawa Azeeza ta ciro wayan ta ta hau yin musu Video, zuciyar ta fari ƙal tsaban farin cikin abun da ta gani yana shirin faruwa

Yana huci ya matso kusa da ita ya saka hannu ya shaƙo mata wuya

Yanda Ziyada taga idanun sa sun juye sun zama jazur tamkar tattasai, har wani ƙyalli suke yi wanda ke nuni da hawaye ne a ciki, sosai ta firgita da yanayin sa, ga shi ya shaƙe mata wuya ba damar tayi magana illa ƙaƙari da ta hau yi kamar zata mutu

Tsaban fushi ma ya kasa yin magana, daƙyar ya iya tattaro numfashin sa dake ƙoƙarin ɗauke wa daga gangan jikin sa, tare da tattaro miyau ɗin bakin sa da ya kafe ya ce da ita, "Ni ABUL KHAIRI zaki ci amana? Ni?.. abun da na hana ki aikata wa shi kike aikata wa a bayan idanu na ko? Wlh Ziyada ban taɓa jin cewa son da kike min ƙarya bane da har zaki iya bayar da kanki ga wani bayan Ni, yanzu asirin ki ya tonu, I hate you ZIYADA! I hate you so much, i will never be able to marry you tunda har kika haɗa Ni da wani, a kan kishin ki zan iya kashe ki Wlh". Sai ya saki wuyan nata yana miƙe wa daga durƙushen da yayi a gaban ta, cikin hawaye yace, "fitan min a gida yanzun nan ko in kashe ki, na tsane ki! Kar ki sake zuwar min gida, ba na son sake ganin fuskar ki ZIYADA, I hate you..!" abun da yake ta maimaita wa kenan cikin raunin murya yana kuka kamar mace

Sosai idan ka kalli Ziyada zaka ga ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya, domin tunda ta gane inda ya dosa ta tabbatar da asirin ta ne ya tonu a wajen sa, sai tayi suman wucin gadi, sai dai hawaye dake zubar mata kamar famfo ta kafe sa da manyan idanun ta da suka sauya kala lokaci ɗaya tsaban tashin hankali...

Sai da ya daka mata tsawa yana bata umarnin, "ta fice masa a gida." kafin nan ta dawo hankalin ta

Cikin kukan da kamar ana yankan naman jikin ta tsaban ruɗe wa ta hau ba shi haƙuri, tana faɗin, "ya tsaya yaji, ita baza ta taɓa cin amanar sa ba."

Wani irin haushi maganar nata ya ba shi, nan da nan ya saka hannu ya fincike ta yayi waje da ita, ya jefar da ita a bakin ƙofan yana me garƙame ƙofan sa, a nan bakin ƙofan ya zube yaci gaba da tsiyayar da hawayen sa, zuciyar sa na ƙuna tamkar zata fito

Itama tasowa tayi da rarrafe ta jingina da ƙofan tana kuka tana mishi magiyan, "ya buɗe kar ya rabu da ita, baza ta iya rayuwa babu shi ba, sharri ake mata ƙarya ne, bata karya masa alƙawari ba, dashi kaɗai zata iya rayuwan jin daɗi."

Lumshe ido yayi, wasu zafafan hawaye suna sake sulmiyo masa, sosai ransa ke raɗaɗi sabida babu abinda yake hango wa sai Ziyadan sa tare da Saleem a kan gado ɗaya suna cin amanar sa, "yanzu duk ƙaunar da ya gwada mata ashe zata iya ba da kanta ga wani bayan shi? Mene ne ya rage da ba ya mata? Komi yana mata na jin dadi da zai iya mantar da ita ko wani ɗa namiji, amma ko kaɗan bata ga haka ba, sai da tabi hanyar da zata bi ta bayar da kanta ga wani, wanda hakan shi ne babban kuskuren ta, bazai taɓa iya auren ta ba idan har wani namijin ya kusance ta, yana da matuƙar kishi, duk son da yake mata zai iya rabuwa da ita in dai a kan haka ne."

Jin ta dame shi da kuka sai ya tashi ya shige bedroom Yana sake rufo ƙofan.



         ◾▫️◾▫️◾

       Komi da ya faru sai da Azeeza ta naɗa, wani irin farin ciki ne ya mamaye ta tamkar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, ganin yanda komi ya wakana a wajen su, tabbas tana jin cewa aikin ta ya zo da sauƙi, domin tasan cewa tunda ABUL KHAIRI ya furta ya rabu da ita, to tabbas ba ta tunanin zai koma mata, tasan yanzu aikin ta zai soma

Da sauri ta janyo wayan ta waje tayi serving ɗin videon, ta juya tayi bakin Gate zuciyar ta fari ƙal.



                ◾▫️◾▫️◾

        Ziyada ta ƙi tashi a wajen sai kuka take yi tana buga masa ƙofa tamkar zata karya, sosai ta fita hayyacin ta, sai kiran sunan sa take yi tana ba sa haƙuri.

    ABUL KHAIRI dake kwance a kan gado ya danne kan sa da pilow, amma duk da haka yana jiyo bugun ƙofan da take yi. Miƙe wa yayi ya fice a matuƙar fushi, yana zuwa ya buɗe ƙofan, sai ta biyo ƙofan ta faɗo kan ƙafafun sa, janye ƙafafuwan sa yayi ya fito ya soma rufe ƙofan

Da sauri ta tashi ta rungume sa tana me sake fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi, sosai take kuka wanda ya hana ta yin magana illa faɗin, "sorry! Sorry." kaɗai da take yi

Ɓanɓare ta yayi a jikin sa ya ture ta yana kallon ta da jajayen idanuwan sa, abun takaicin ma duk baƙin cikin da yake ji da abinda tayi masa, sake jin ƙaunar ta yake yi na shigan sa, tabbas idan ya tsaya a wajen ta komi zai iya faruwa

Janye idanun sa yayi daga kallon ta ya juya da sassarfa ya nufi motan sa

Biyo sa tayi tana kuka tana roƙon sa, har da sake shige wa jikin sa tayi

Amma ina tuni ya ɓanɓare ta yayi wurgi da ita yana kallon ta yace, "Wlh if you touch my body again I will surprise you ZIYADA". Motan sa ya shige ya ja ya nufi bakin Gate Yana buga uban horn

Da sauri me gadi ya buɗe masa jikin sa na rawa, shi kuma ya fice.

       Ziyada zube wa tayi a nan ƙasa tahau birgima kamar wacce ta hau iska, kuka sosai take yi tana faɗin maganganun da ba'a jin ta

Da sauri me gadi ya ƙariso wajen ta yana faman bata haƙuri

Amma ko kulasa bata yi ba

Dole ya tashi ya koma bakin aikin sa ya zauna yana faman kallon ta, a ran sa yana mamakin abinda ya haɗa su yau suka yi baram-baram na tsiya, domin tunda yake be taɓa ganin sun yi faɗa makamanciyar wannan ba, duk da sau tari yana jin hayaniyan su wani lokacin. Jinjina kai yayi a ransa yana cewa, "cabb! yau waɗannan masoyan ko me ya haɗa su?".

       Ziyada kuwa sai da ta gaji don kanta kafin ta miƙe ta faɗa motan ta ta figa tabar gidan tamkar mahaukaciya.



◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️

      Kai tsaye ABUL KHAIRI gida ya wuce, yanda yake buga shegen horn sai da ya tsorata me gadi, da gudu ya buɗe masa ya shigar da motan a tsiyace, wani wawan birki yaja ya fito ya nufin cikin gidan.

               Maimuna na zaune a Parlour ita da Sa'ima, (ƴar wajen Umma Salamatu, ƙanwar Abba ce, Sa'ima ita ce ɗiya ta biyu a wajen ta, me sunan Batool Fatima ita ce ta farko, amma suna kiran ta da Ummee, tayi aure har da ɗiyar ta ɗaya)

Sa'ima sa'annin su Maimuna ce itama.

    Suna cikin hira suna dariya suka ji ya bugo ƙofan ya shigo, da sauri dukan su suka soma gaishe shi

Amma ina be ma san suna yi ba ya nufi ɗakin shi

Yanda suka gan sa sai da duk kan su suka tsorata, sabida yanda fuskar sa babu fara'a sai faman huci yake yi, idanun sa sun yi jazur

"Keee anya Angon naki lafiyan sa ƙalau? Me ke damun sa?" Cewar Sa'ima tana kallon Maimuna

Ita kuma hararan ta tayi tace, "ban son haka fa wlh, ki dena".

Dariya Sa'ima tayi tace, "wlh Maimuna dariya kike bani, gwara ma ki dena haka wlh kun dace, Ni ina miki fatan samun Ya ABUL, sabida ba ƙaramar Sa'a kika yi ba idan kika same sa, ai Ni tunda Batool ta faɗa min abinda ke faruwa nake Allah-Allah na zo inji ƙarisan labarin, wlh har kwana nayi roƙon Allah yasa ku mallaki junan k.."

Duka Maimuna ta kawo mata, dole tayi shiru tana miƙe wa da sauri tana mata dariya, sai ta kuma cewa, "Allah ba batun wasa ba Maimuna, baza ki je ki ji mene ne ya ɓata wa gwarzon naki rai ba?"

Tashi Maimuna tayi tabi ta tana cewa, "wlh Sa'ima sai na fasa miki baki idan na kama ki, kuma da Mamy zan haɗa ki".

Sa'ima tuni ta shige ɗakin su

Maimuna tabi bayan ta itama da gudu

Batool na kwance tana sharan barci, sai ji tayi an faɗo kanta, da sauri ta buɗe jajayen idanun ta ta sauke a kan Sa'ima dake son tsallakawa ta jikin ta ta guje wa Maimuna

Ita kuwa Maimuna tuni ta dakata ma tana cewa, "wlh ki dena ba na so Sa'ima".

Ita kuma sai mata dariya take yi har a lokacin tana jikin Batool bata gama sauka ba

Ɗaga mata duka Batool ɗin tayi tana faɗin, "wannan wani irin wulaƙanci ne ina barci zaki faɗo kaina?"

Riƙe cinyan ta inda ta bige ta tayi tana cewa, "Batool ke muguwa ce wlh, shi ne zaki yi min wannan banzan dukan don na hau jikin ki, wani nauyi ne dani?"

Harara Batool ta balla mata tana cewa, "a'a uwar baki da nauyi ne, kina ji da wannan shegen jikin naki kamar dutse kike ce min baki da nauyi?"

Maimuna kuwa me zata yi in ba dariya ba

Nan dambe ya kaure a tsakanin Batool ɗin da Sa'ima, sai dukan juna suke yi suna cacan baki, ga shi gaba ɗayan su babu me haƙuri cikin su

Maimuna na gefe tana tiƙan dariya, musamman yanda suke tsinan kansu sai abun yake bata dariya.

    Dayake sun san babu Mamy a gidan ta tafi gidan su Abba ita da Baby da Amir, daga can zata wuce anguwan su zata duba Uncle Shamsu, an aiko jikin sa ya tashi, sannan daga can sai ta biya ta gidan su

Abba kuma be daɗe da fita a gidan ba ma.


             Wani irin hautsine wa cikin Maimuna yayi da ta wulƙa ido ta hangi ABUL KHAIRI tsaye a bakin ƙofa yana riƙe da belt ɗin wandon sa, idanun nan nasa tamkar ma yanzu ne suke ƙara juyewa tsaban jan da suka yi


       A dai-dai lokacin ne su ma su Batool suka hange sa, ai tuni sun dakata daga jefawa junan su pilown da suke yi, sun nufi ƙarshen gadon suna ƙanƙame jiki tare da zare idanuwa kamar sun yiwa sarki ƙarya an kama su.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 17 & 18*

*________* Yanda ran ABUL KHAIRI yake a matuƙar ɓace ga shi ya samu inda zai huce, shiyasa ya haɗa su har Maimuna yayi musu mugun duka, ga shi babu damar guduwa, tun suna neman ceto har suka gaji sai kuka da suke yi, babu wanda yafi jibga sai Maimuna, kamar an aiko mishi da jaka haka yake kiman ta, tunda duk yafi jin haushin ta

Maimuna baiwar Allah, abinda bata taɓa ji bane ya faru da ita, duba da yanda take ba me rashin ji ba, shiyasa zai yi wuya ka ga an bige ta ko da a school ne, ita rabon ma da ace an bige ta tun tana ƙarama ƙila, duk saurin hannun Ummun su ba ta dukan ta, shiyasa abun ya zo mata a wani irin baƙon yanayi, nan da nan ta sume sabida tsaban firgita

While ABUL KHAIRI be San ma ta sume ba, jibgan su kawai yake yi, sai da gaba ɗayan su ya farfasa musu jiki, su Batool duk an yi musu haɓo, Maimuna ma ba'a maganar ta

A dai-dai wannan lokacin ne Abba ya dawo gidan, kukan su kawai ya jiyo ya zo yana dukan ƙofan, sabida tuni ABUL ya rufe ƙofan

Sai da yaji muryan Abban su yana kiran sunan sa kafin ya dakata da dukan nasu, ya nufi ƙofa ya buɗe yana kallon Abban

Yayinda Abba tuni ya shigo ciki yana bin su Batool da kallo, cikin tashin hankali ya kai duban sa ga ABUL KHAIRI wanda ke tsaye kamar an shuka sa, cike da ɓacin rai yace, "Me suka yi maka kayi musu wannan dukan? Shin kana cikin hankalin ka kuwa?"

Ihun da Sa'aima ta saki ne yasa Abba ya nufe su da sauri, ganin Maimuna bata numfashi ne yasa ta saki wannan ƙaran

Sosai hankalin Abba ya tashi ganin Maimuna ba ta motsi, ga shi kanta duk ya jiƙe da jini, wanda takamaime ma ba'a san inda taji ciwon ba

A fusace Abba ya ɗago kai zai yiwa ABUL KHAIRI magana, amma sai yaga babu shi, da sauri ya nufi ƙofa ya fita yana me kwaɗa masa kira

ABUL KHAIRI da har ya shige ɗakin sa ya mayar da ƙofa ya rufe, dole ya fito yana amsa kiran Abba jin kamar zai tsaga gidan

Yana fitowa suka ci karo ya wanka masa mari a fuska, cikin fusata yace, "haukan naka ya kai har ka kashe musu ɗiya ko? To wlh muddin wani abu ya same ta sai na kai ƙaran ka wajen hukuma, shashasha mara tunani, wuce muje ka ɗauke ta mu tafi asibiti".

Da sauri ABUL KHAIRI yayi gaba dafe da kuncin sa, sosai ya tsorata da yanayin da mahaifin sa ya nuna masa, shi kansa be san abinda ya aikata ya kai haka ba saboda hankalin sa ba ya jikin sa, zugin abinda Ziyada tayi masa ne sai ya fanshe a kansu. Sosai ya sake tsorata ganin yanda Maimuna ko numfashi ba ta yi duk jikin ta jini, ga su Batool sun tasa ta gaba suna ta kuka kamar ransu zai fita, su ma duk ciwuka jikin su

Sai da Abba ya daka masa tsawa sabida tuni ya fita tunanin sa, sannan ne ya ɗauke ta suka yo waje gaba ɗaya har su Batool, don su ma dole su ga likita da wannan raunin da suka ji.

    Sai da suka isa can da kamar mintuna goma, sannan Mamy ta kira wayan Abban su tana tambayan sa, "bata ga su Batool ba, sannan ta ga ɗakin su a birkice duk jini bata san me ke faruwa ba?"

A nan Abba yake sanar mata da komi, don dama ya ƙi kiran ta ne kar hankalin ta ya tashi

Sosai kuwa hankalin nata ya tashi, nan da nan ta juya kan mota ta nufo asibitin bayan ta sauke su Amir, tana zuwa ta hange su a reception, daga Abba sai su Sa'ima da aka gama musu dressing inda suka ji ciwon, hannayen su ne kawai ya farfashe, sai haɓon da suka yi a hanci duk kan su

Babu ABUL KHAIRI a wajen, don tuni Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login