Showing 12001 words to 15000 words out of 88313 words
Chapter 5 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ba sa yi, domin da gani kasan ba sa gajiya da junan su, sun yi romancing tamkar zasu haɗiye juna, daƙyar suka haƙura suka sake koma wa Toilet suka sillo wanka, sannan suka yaɗa zango a kan dainning; ko kayan kirki babu wanda ya saka a cikin su, abinci suke ciyar da juna cike da nishaɗi tare da soyayya me tsananin garɗi, domin ji suke yi tamkar babu wani mahaluki a duniyar su sai su kaɗai.
Bayan sun gama kujera suka koma suka kwanta a tare saman Three sitter Suna hiran su.
Sai ƙarfe 05:40pm. Sannan suka yi haraman tafiya, kayan su suka maida suka fito a tare riƙe da hannun juna suna ma junan su kallon soyayya, suna magana ƙus-ƙus babu me ji sai dariya suke yi, har mota ya kai Ziyada, ta zauna tana kallon sa tamkar baza su rabu ba, sun daɗe a wajen kafin taja motan tabar gidan
Shi kuma nufan cikin gidan gonan yayi, inda masu aiki suke nan ya ƙarisa, ya kira su ya saka su aiki wajen ɗebo masa Fruits ɗin da Mamy ta buƙata, komi da komi sai da ya saka aka ɗibo masa, har kaji da su kifi, zabi, talo-talo, kasancewar duk yana kiwon su a gidan, sai da ya saka aka yayyanka mishi kafin aka zuba a buhu suka kai mishi mota, daga nan shima ya shiga motan ya nufi gida.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*ZIYADA ALH. MUH'D IYAAL*
Ziyada ɗiya ce ga Alh. Muh'd Iyaal, da matar sa Hajiya Turai, ita kaɗai Allah ya ba su, kuma sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, duk abinda take so shi take yi babu harara ko tsangwama a rayuwan ta, sai dai mahaifin ta yana bala'in son tayi karatu me zurfi, wanda hakan ne yaja tsaiko ga auren su da ABUL KHAIRI, wanda sun shafe tsawon shekara biyu suna tare.
Ziyada bata da ƙawa aminiya sama da Rahina, tun suna yara suke tare har kawo girman su, ita ma dai yarinyan masu kuɗi ne, kuma gaba ɗaya school ɗin da suka yi tare suke yin sa tunda Allah ya haɗa jinin su, duk da cewa anguwan su ba ɗaya ba.
Tun farko Rahina da ta fara ganin ABUL KHAIRI ta kamu da tsananin ƙaunar sa, sai dai babu ta hanyar da ta samu damar sanar masa, kasancewar shi ɗin saurayin Ziyada ne, kuma shi kansa ABUL KHAIRI be taɓa bata ƙofan da zata iya sanar dashi ba, domin shi mutum ne me yawan ɗaure wa mata fuska, ko kaɗan ba ya shiga harkan mata sai da ya haɗu da Ziyada, ita kaɗai ce macen da ya taɓa so, kuma ita yake ganin zai ci gaba da so har ƙarshen numfashin sa.
Sagir ɗa ne ga ƙanwar Hajiya Turai mahaifiyar Ziyada, lokacin da yana ƙarami Hajiya Turai (Mom) ita ta riƙe sa kafin ta haifi Ziyada, kasancewar ba sa haihuwa, ita kuma ƙanwar ta a time ɗin tana da yara biyu, sai shi Sagir ɗin na uku, shiyasa ta bata shi har zuwa sanda zasu samu na su
Koda suka haifi Ziyada sai Sagir yaci gaba da zama a hannun su har tasowar Ziyada, sai ya zamana koda yaushe Ziyada na hannun Sagir, sabida ba ƙaramin ƙaunar ta yake yi ba, Allah ya haɗa jinin su matuƙa, sun shaƙu fiye da tunanin mutane, idan ka gansu sosai za su ba ka sha'awa saboda ƙaunar da suke yiwa juna, har time ɗin da Sagir ya tafi ƙasar Ghana inda yake karatun sa na degree a can
A lokacin ne kuma suka haɗu da ABUL KHAIRI tunda shima a can yake karatu, sai Abokantaka ya shiga tsakanin su, ga shi kuma duk abu ɗaya suke karanta Shiyasa koda yaushe suna tare, har sanda suka gama, kuma suka ɗaura Masters ɗin su, izuwa lokacin sun zama aminai sun shaƙu sosai, tamkar ƴan uwan juna.
*ABUL KHAIRI* yana yawan jin labarin Ziyada a bakin Sagir, tunda ba shi da abun yabo sai ita, domin har ABUL ya kan tone sa yace masa, "ko dai da ita za'a yi?" Sai Sagir yayi dariya kawai, don ba ya ba sa amsar komi, kuma shi ABUL be taɓa damuwa ya san ta ba, duk da kuwa yana yawan jin suna waya da Sagir, be taɓa amsa su gaisa ba ko da Sagir ɗin ya buƙaci haka, shi dai karatun sa kawai ya saka a gaba
Har zuwa sanda suka gama suka dawo gida gaba ɗaya, inda ABUL KHAIRI ya soma aiki a Companin Abban sa na sarrafa amfanin gona, kasancewar shima Abba ya gada ne wajen Mahaifin sa, sai dai yanzu haka ya bunƙasa Companin fiye dana da, har wasu abubuwan da ya shafi kayan saka wa suke yi, wanda ake haɗa su da adduga, sabida a Companin suke yin addugan, wancan kuma abun da ABUL KHAIRI ke so kenan, shiyasa ma ya buɗe gidan gona yake kiwo, don yana son shuka.
Yanzu haka Sagir ya koma wajen iyayen sa da daɗe wa, sai dai yana zuwa gidan su Ziyada tunda ya zama ɗan gida, yana da ɗakin sa idan yaga dama ya kwana a can, idan kuma yaga dama ya koma gidan iyayen sa.
Lokacin da suka gama school ne, ABUL KHAIRI ya kai masa ziyara a gidan su Ziyada, to, wannan shi ne farkon haɗuwar su, wanda ya jawo soyayya a tsakanin su, don tun a farkon haɗuwar su suka kamu da ƙaunar juna, kuma shi ABUL be yi sanya ba ya sanar mata, inda ya amsa Numban ta a nan take, kuma duk a gaban Sagir aka yi hakan, domin shi ne ma ya ba shi ƙwarin gwiwan bayyana mata
Sai dai abinda ABUL ya kasa fahimta, gaskiyar soyayyar da Sagir ke yiwa Ziyada tun tana ƙarama, duk yawan maganar da Sagir ke yi na Ziyada be sa yayi la'akari da hakan akwai ƙauna ba, idanun sa ya rufe lokaci ɗaya da soyayyar Ziyada, burin sa kawai ya ƙulla tashi soyayyan
Shi kuma Sagir ganin abokin nasa da ita Ziyadan gaba ɗaya sun afka ga junan su, sai shi kuma ya danne nasa soyayyar da yake da ninyar sanar da ita a lokacin, sai ya ci gaba da ba su gudummawa a tasu soyayyar ba tare da sun san me ke cikin ransa ba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Washe gari Asabar Mamy da su Maimuna kasuwa suka wuce, za su taya Mamy sayayyar kayan Uncle Abbas, basu dawo ba sai yamma.
The following day gaba ɗaya yaran suka shirya don ziyarar Kakannin su, ABUL KHAIRI ne zai kai su
Koda suka gama shirya wa, motan suka wuce suka shiga suna jiran sa, don shi a time ɗin be rigada ya shirya ba
Amir ne ya zauna a gaba, sai su Batool a baya, hira suke tayi har sanda ABUL ya fito, yayi shirin sa na manyan kaya dakakkiyar shadda maroon Colour, sai tashin ƙamshi yake yi, yana shiga cikin motan suka nutsu waje ɗaya, be bi takan su ba yaja motan ya nufi bakin Gate, me gadi na buɗe masa Gate ɗin; ya cilla motan waje.
Tafiyan mintuna sha biyar suka isa gidan Alh. Sunusi mahaifin Abba
Fitowa suka yi suka yi cikin gidan gaba ɗaya, ABUL KHAIRI na biye dasu a baya.
*****
Hajiya Falmata na zaune a parlour'n suka shigo dukan su da sallama, amsa musu sallaman tayi cike da fara'an ganin su, ta soma musu lale marhaba
Zama suka yi suka soma gaishe ta cikin girmamawa
Ta amsa cike da fara'a tana tambayan su mutanen gida.
Nan shima Alh. Sunusi ya fito daga ɗakin sa, ganin su ya saka shi washe fuska cike da farin ciki ya soma tsokanar su yana ƙarisowa wajen, kusa da ABUL KHAIRI ya zauna yana dafa shi yana sake tsokanar sa cike da farin ciki.
Dariya duk kan su suke yi, don sun san halin Dady akwai son tsokana musamman idan ya tasa ABUL KHAIRI a gaba, sun fi ɗasa wa sosai, shi kansa ABUL yafi sakin jiki dashi
Nan suka soma hira cike da barkwanci suna kwasan dariya, har shi ABUL KHAIRIN da be cika sakin jiki a gaban ƙannin sa ba, su ma sun sake sosai, illa Maimuna ne kaɗai da ba ta iya surutu sai dai tayi dariya kawai.
A lokacin sai ga Umma Hassana itama ta zo da yaranta biyu, ƙanwa ce wajen Abba, kuma tserayan su da ABUL KHAIRI be fi shekara uku ba
Nan gidan ya sake hautsine wa, ana ta hira da dariya.
A gidan suka wuni har zuwa sallan azahar, sai da su Dady da ABUL tare da Amir suka je masallaci suka dawo, kafin suka yi haraman tafiya.
Daga nan gidan su Mamy suka wuce, a anguwan da suke har yanzu a nan Hajiya Mama mahaifiyar su Mamy take, sai dai yanzu gidan gaba ɗaya uncle Abbas ya gyara shi, ya rushe yayi Plet, Part ɗin sa daban; na Hajiya Mama daban, sai ƴan aiki da ya zuba mata masu yin mata komi da komi, duk da a yanzu akwai yarinyan Hajiya Fatima ƙanwar su Mamy (suna kiran ta Aunty Fatima, tana aure a Kaduna, ɗaya daga cikin ƴan uwan Mijin Ummu mahaifiyar Maimuna shi ke auren ta, sai dai ita yanzu tana Zaria sabida mijin ta a can yake aiki)
sunan yarinyan Humaira, kasancewar sunan marigayiya A'isha taci, itama ƙanwa ce wajen su Mamy da ta rasu da daɗe wa
Humaira Sa'ar Amir ne, yanzu haka ta dawo wajen Hajiya Mama da zama ne, wajen shekara ɗaya da dawowar ta, tunda ta dawo uncle Abbas shi ke ɗaukan nauyin ta na komi, har school shi ya saka ta.
Uncle Abbas be taɓa aure ba, karatu kawai yake yi har kawo yanzu da ya sami wata ƴar cikin anguwan nasu zai aure ta, kuma har a yanzu ɗin be dakata a karatun ba, don a halin yanzu degree na uku yake yi, saura four months ya gama, be cika zama ba yana tafiye-tafiye ne sabida yanayin aikin sa. Wannan auren ma da zai yi su Mamy suka matsa mishi, don shi a nashi ra'ayin be shirya aure yanzu ba, ba wani shekaru ne dashi ba, tunda yanzu ba zai fi 36years ba.
▪️▪️▪️
Hajiya Mama tayi murnan ganin jikokin nata, nan tayi ta haba-haba dasu, su kuma suna faman tsokanar ta tunda sun fi saba wa da ita sosai, kasancewar ta me sakar musu fuska, shiyasa suke wasan jika da kaka
Humaira itama tana cikin su ana ta hira, dayake sun saba da ABUL, nan ta shige masa suna ta hira tare, ya bata wayan sa suna ɗaukan pictures, idan suka yi kuma sai su koma kallo suna dariya, idan ita ce bata yi kyau ba a hoton, ko ta ɓata hoton; ya dinga dungure mata kai kenan yana faɗin, "ta ɓata masa waya da munin ta". Ita kuma dayake akwai sokonci irin na ƴan fari, sai tayi ta masa shagwaɓa tana zumɓura baki a kan, "baza ta yarda ba, sai dai a sauya wani" haka zai biye mata su yi ta ɗauka.
Su kuma su Batool suna gefen Hajiya Mama suna tiƙan dariyan labarin da take basu, wani abubuwan duk labaran iyayen su take faɗa musu, idan kuma suna da tambaya sai suyi mata
Baby ne kaɗai babu ruwan ta, tunda ta shigo ta kwanta abunta sai barci.
Da za su tafi Hajiya Mama sai da ta tilasta wa ABUL a kan, "lallai su wuce gidajen Uncles ɗin su; su gaishe su."
Shi ba kasafai yake son zuwa ba, don ya tsane su matuƙa sabida yanda su ma ba sa son su, amma babu yanda ya iya tunda Hajiya Mama ta tilasta mishi.
Gidan Uncle Shamsu suka soma zuwa, yana nan dai kamar yanda yake, tun sanda ya taɓa samun hatsari ƴan daba sukai mishi dukan tsiya, shikenan kuma ƙafafuwan sa da suka samu karaya suka ruɓe, aka yi ta magani ana ɗori ba'a dace ba, yanzu haka an yanke masa ƙafa ɗaya, kuma be taɓa yin aure ba tunda tun kafin yayi aure abun ya same shi.
Mahaifiyar shi da mahaifin shi Kawu Shehu sun daɗe da rasuwa, yanzu shi kaɗai yake rayuwa a gidan, sai kuma ƙanwar sa Aliya dake taimaka masa daga gidan auren ta, tana kawo masa abinci, wataran ta turo ƴaƴan ta su gyara masa gidan, su kula dashi, duk da dama ƙafa ɗaya ne ya rasa.
Suna zuwa suka gaishe sa, ABUL KHAIRI yace, "su tashi su tafi". Da za su tafi haka ya ajiye masa tsibirin kuɗi suka bar shi da godiya yana zubar da hawaye, babu abinda yake tunawa sai tozarcin da suka yiwa A'isha marigayiya, sanadiyar Fyaɗen da suka yi mata shi da abokan sa ta rasa ranta, sai gashi a cikin ƴan uwan ta suke taimakon sa, don Mamy idan ta samu dama koda yaushe tana zuwa duba sa, kuma ta ajiye masa kayan dubiya me yawan gaske, idan har bata samu damar zuwa ba, sai ta aiko drever ya kawo masa, har yanzu ita take saka wa ana duba masa ƙafan, sosai likitoci suke kula da shi a gidan. Ummu ce kaɗai (Ameera) ba ta mishi wannan taimakon, domin har yanzu taƙi manta abinda suka yi musu, musamman ma Uncle Sani da tafi tsanar sa, ko biyar ba ta basu nata, kuma ko ta zo garin ba ta neman su, ko Hajiya Mama zata nace sai ta je, to ba ta zuwa, sai dai ta haƙura ta ƙyale ta, domin har yanzu Ummu halin ta na nan, sai dai baka taɓo ta ba.
Daga nan gidan uncle Sani suka wuce, shima dai mahaifinsa Kawu Bala ya daɗe da rasuwa, sai mahaifiyar sa Umma tana nan a raye, sai dai ta tsufe sosai sabida talauci, ko fitowa ba ta iya yi sai da dalili
Sulaima matar Uncle Sani ƴaƴan ta biyu, namijin Salihi sunan sa, yanzu haka ya kai ABUL a girma, sai dai shi ABUL ɗin ya ba shi shekaru kusan uku, sai ƙanwar sa Azeeza me shekaru 20 sa'ar Zee ce ita
Yaran sun tashi babu tarbiyya ko kaɗan, sabida yanda uwar su da suke kiran ta Umma Sulaima ta ɓata su matuƙa, dayake itama ba ishashshen tarbiyya ne da ita ba tunda tsohuwar karuwa ce, bare kuma akai ga uban su, yanda kuka ga uncle Sani yana matashi, haka shima Salihi yake, ba ya jin magana ko kaɗan, shaye-shayen nan babu wanda be sha.
Tunda suka shiga gidan ABUL KHAIRI ke faman yamutsa fuska sakamakon tozali da yayi da ƙaton kwatan dake tsakiyar gidan, har yanzu dai gidan nan ne da Mamyn sa tayi rayuwan ƙunci da azaba a ciki, be sauya ba sai ma lalace wa da ya sake yi.
Su dai su Batool tuni sun isa ƙofar ɗakin Umma Sulaima suna kwaɗa sallama
Daga ciki ta amsa musu tana ba su umarnin shigowa
Shiga suka yi gaba ɗayan su
Da idanu take bin su har ta gyara zaman ta daga kwancen da ta tashi, yamutsa fuska kawai take yi tana amsa gaisuwar su cike da gadara da iyayi, kafin kuma tace, "ku kuma daga ina haka?"
"Daga gida muke Umma, mun zo muku ziyara ne". Cewar Batool tana washe baki, don ita babu ruwan ta da irin tsanar da suke musu
Taɓe baki Umma Sulaima tayi tace, "lallai kam, ai naga ziyara, ko dai an turo ku yin wani muna-furcin? Ita ina uwar taku take?"
Yanzun ma dai Batool ce ta ba ta amsa tana murmushi, "Mamy na gida ta ce a gaishe ku, tare da Yaya ABUL muke yana waje".
"To me zan mishi? In CE dai bazai shigo ba? To ya ruɓe a can mana, Ni dai ba fita zan yi ba".
Batool tace, "ai kin huta rabon naki ya wuce ki, ina Aunty Azeeza ne wai?"
Wani shegen harara Umma Sulaima ta buga mata tace, "kee! Uwar ki zan ci wlh, an ce miki Ni irin fatararren Kawun ku ne da zan je ina roƙo wajen ku? Da shi da uwar taku ba ku da abinda za ku bani sai ma Ni in baku".
Dariya Batool ta kwashe dashi jin abinda ta faɗa, Amir na taya ta, ita dai Maimuna nata ƙasa-ƙasa take yi tana ƙumshe baki
Ai kamar sun kunna Umma Sulaima ta fara sababi tana zagin su
Kuma suka ƙi tashi bare su dena dariyan da suke yi, sai kallon ta da suke yi
Ai kuwa tayi ta ƙunduma musu zagi tana kiran sunayen iyayen su tana aibata su.
*ABUL KHAIRI* dake tsaye bakin ƙofa yana jin duk abinda suke yi, ya banko labulen yana kallon su fuska babu fara'a, ya daka musu tsawa a kan, "su fito"
Tashi suka yi jikin su na mazari, don basu yi tunanin yana nan kusa ba tunda daga can tsakar gidan suka bar shi
suna fita itama ta biyo su tana ci gaba da sababi, sai ta koma kan ABUL tana zagin sa
Shi kuwa be ma bi ta kanta ba suka shige ɗakin Umma mahaifiyar Uncle Sani.
A lokacin ne Azeeza ta shigo gidan tamkar an jeho ta, ganin Umman ta na sababi sai ta soma wurwurga idanu cikin gidan tana faɗin, "Umma ina Yaya ABUL ɗin?"
Nan Umma Sulaima ta sake cika da takaicin ɗiyar ta, bata kai ga magana ba; taga Azeezan ta nufi ɗakin Kakarta da gudu tana washe baki
A time ɗin ABUL har ya sako ƙafa zai fito suka ci karo, ai da sauri yaja da baya yana sake ɗaure fuska ganin Azeeza ce
Ita kuwa bata damu ba illa washe baki da ta sake yi tana faɗin, "Yaya ashe ka zo? Ina gidan Gwaggo Maria ( ƙanwar Mahaifin ta) aka zo aka bani labarin zuwan ka, sannu da zuwa yaya, ina wuni?"
Duk maganar da take yi da kallo yake bin ta, kafin yace, "bani hanya na wuce".
Babu musu ta matsa mishi, sai ma time ɗin taga su Batool, sai ta sakar wa Batool murmushi tana cewa, "ƙanwata ashe har da ke aka zo? Shi ne