Showing 6001 words to 9000 words out of 88313 words
Chapter 3 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
but har mintoci suka shuɗe babu kiran Ziyada, dole ya ajiye wayan ya miƙe ya nufi gaban dressing mirror, ya ɗauki farin Wrest watch ɗin sa ya soma ɗaura wa a tsintsiyan hannun sa na dama, gaba ɗaya fuskar sa babu fara'a. Sai da ya gama saka wa sannan ya koma gefen gadon ya zauna, ya janyo cover Shoes ɗin sa dake ƙasan gadon ya soma zira wa, bayan ya gama ya miƙe tare da wayan sa da keey ɗin mota ya fice
Be shiga ɗakin Mamy ba tunda ya ga ba ta a Parlour, sai ya fice kansa tsaye
Sai dai yana fita haraban gidan ya haɗu da Abba da dawowar shi kenan, shi ya maido dashi ba da son ransa ba, a kan "zai raka sa wajen gaisuwa," haka suka koma ciki ABUL KHAIRI na zumɓura baki a ran sa, don dai bazai iya ce ma mahaifin sa wajen budurwa zai je ba, tunda har yanzu babu wanda ya san labarin Ziyada a gidan su, kuma shi ba kasafai yake son ƙarya ba.
Sai da Abba ya ci abinci kafin suka sake fita shi da ABUL KHAIRI.
Ba su daɗe da ficewan ba su Batool suka dawo
Lokacin Mamy na kichen tana ɗaura abincin dare
Don haka Hijab kaɗai suka cire suka shiga kichen ɗin taya ta, tunda gaba ɗaya tare suke haɗuwa su yi komi na gidan, Mamy ba ta son masu aiki shiyasa suke yi da kan su, duk da ita ɗin ba mazauniyan gida bane tana zuwa aikin ta, su kuma su Batool suna zuwa school, shiyasa idan da safe ne da wuri suke tashi su haɗa Breakfast su yi aiyukan su, wanki ne kaɗai suke da me musu, itama nan ƙasan layin su gidan ta yake, ita da kanta take zuwa ta kwasa taje tayi ta kuma goge, sannan ta dawo musu dashi
A cikin su kuma duk wanda ya riga dawowa zai ɗaura girkin rana, idan Mamy ta dawo Office da wuri sai ta ɗaura, idan kuma su Batool sun riga ta dawowa school sai su ɗaura, dayake ma Exams suke yi na S.S 2 Third time, that's why ba sa daɗe wa suke dawo wa.
Maimuna ita ta saki aikin kichen ɗin, ta koma Parlour don share wa, sai dai ma tuni Amir ya gama share wa yana ƙoƙarin yin Moping ne
Karɓa tayi tana masa dariya da cewa, "Ina kai ina aikin nan Amir? ina Auta na da ta barka kana aikin mata?"
Dariyan shima yayi yana faɗin, "wannan uwar son jikin, tana can ta hangame baki tana sharan barci a ɗakin Mamy, kuma ma ai baza ta iya komin ta ba, gwara Ni zan ɗan fi iyawa".
"Haka ne kuma".
Tana Moping ɗin yana taya ta da hira har ta gama, ta wuce ɗakin su don ta gyara can ɗin.
*MAIMUNA NASEER*
Maimuna ɗiya ce ga ƙanwar Mamy, _Ameera (Adama Yunusa Ubale),_ yanzu suna kiran ta da Ummu, Maimuna ita ce ƴa ta huɗu wajen Ummu. Yanzu haka shekarun ta 16years da haihuwa, ta dawo wajen Mamy ne tun sanda ta gama J.I.S 3 ɗin ta, yanzu haka school ɗin su ɗaya da Batool, kuma ajin su ɗaya tunda Sa'anni ne
Ta dawo wajen Mamy ne saboda wani dalili na iyayen su. Wanda za mu ji shi nan gaba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Da dare suna zaune gaba ɗayan su a tsakar Parlour, abinci suke ci, dayake hakan suke yi sau tari ba sa zaman kan dainning, sai su shimfiɗa ledan cin abinci a tsakiyar parlour'n su ci a nan.
Sai da suka gama, Batool da Maimuna suka kwashe komi suka kai kichen sannan suka dawo.
Abba dake shan ruwa, yayi wa ABUL KHAIRI alamun ya dawo ya zauna, ganin ya tashi da ninyan shigewa ɗakin sa
Shi be ma kula ba, sai da Baby tayi masa magana
"Yaya, Abba yana maka alamu da hannu ka dawo".
Kallon ta yayi, sai kuma ya maida kallon nasa ga Abban
Time ɗin ya cire Cup ɗin daga bakin sa yana shirin ajiye wa yace, "Dawo nan mu yi magana".
Babu musu ya dawo ya zauna
"Yauwa wai me ke hana ka leƙa su Momy ne?" (yana nufin iyayen sa, wato kakannin su ABUL KHAIRI)
Mamy ta amshe maganar da cewa, "Nima dai abinda nake ta son mishi magana akai kenan, Mama ma har ta gaji itama tana min ƙorafi". (Kakar su ta wajen uwa)
Sosa Kai ABUL KHAIRI yayi yace, "Abba wlh time ne ba na samu, but insha Allahu zan ƙoƙarta in ga na je".
"Da dai ya fiye maka, kasan halin tsofaffin nan da naci, kuma babu ruwana idan suka sako ka gaba".
Murmushi Mamy tayi tace, "kai Abban su, har da kai?"
Shima murmushin yayi yana ɗaukan tufan da Batool ke yanka wa, yace, "to ai gaskiya na faɗa".
Murmushi Mamy kawai tayi, tana mayar da idanun ta kan ABUL KHAIRI tace, "babu wani uzuri da zaka ba mu Baba na, ka tabbatar ka samu time wannan weekend ɗin, sai ku tafi da ƙannin ka su ma su je su gaishe su".
Jin abinda Mamy tace ne, Batool da Maimuna suka kalli juna suna murmushi cike da murna
Shi dai ABUL KHAIRI amsa mata kawai yayi ya tashi ya wuce ɗaki, Allah-Allah yake yi ya keɓe don kiran sanyin idaniyan sa, sai dai duk saurin da yake yi wajen ya ga ya kira ta, amma har yanzu wayan ta a kashe ne, duk ya rasa sukuni, sai faman kira yake yi duk da kuwa ana faɗa masa a kashe layin yake, but be fasa ba, sai da ya gaji don kansa kafin yaja dogon tsaki cike da takaici ya ajiye wayan, tashi yayi ya shiga wanka
Be ɗau lokaci ba ya fito, ya shirya cikin brown ɗin jallabiya da gajeren wando fari, fitowa yayi Parlour don ya samu ruwa ya sha
Babu kowa sai Baby dake kwance tana gyan-gyaɗi
Ƙarisawa yayi gaban Fridge ɗin ya buɗe ya ɗauki goran ruwa Robber biyu, ajiye wa yayi saman Fridge ɗin sannan ya sake buɗe wa ya ɗauko Glasses Cup, zuba ruwan yayi ya sha sannan ya rufe sauran, sai da ya ɗauki ɗaya goran da raguwan ya tako wajen Baby, hannu ya saka ya ɗan ja mata hanci
Buɗe ido tayi tana kallon sa
Yace, "Autana barci kike yi rabin jikin ki a ƙasa? Tashi ki je ɗaki ki kwanta".
Tashi tayi ba tare da tayi magana ba ta wuce, don barci ne a idanun ta sosai
Shima ɗakin sa ya nufa ba tare da ya kashe t.vn dake aiki ba, don ya san mutanen gidan ba kwanciya suka yi ba zasu fito.
Washe gari ƙarfe 06:30am. Su Batool suka tashi daga barcin safen da suka koma, nan suka fito suka sami Mamy na haɗa Breakfast a kichen, gaishe ta suka yi su ma suka kama aiyukan da suke yi, sai da suka yi shara suka yi Moping ko ina kafin suka koma ɗaki don so ma shirin school
Itama time ɗin Mamy ta gama haɗa musu Breakfast ɗin, dayake Koko da ƙosai tayi musu, sai dankali da ƙwai da ta soya musu, ga wanda be son cin ƙosai sai yaci tunda ta san wasu ba sa so a cikin su, sai da ta jera komi a kan dainning kafin ta wuce ɗaki, time ɗin ma Abba shima ya gama shirin sa, sai ya fito Parlour don yin breakfast ɗin sa ya wuce, ita kuma ta shiga Toilet yin wanka.
Maimuna ita tayi wa Baby wanka ta shirya ta a kayan school ɗin ta, sannan itama ta shiga tayi lokacin har Batool tayi nata, sai da suka gama shiryawa suka fito yin breakfast
Lokacin Abba da ABUL KHAIRI tuni har sun wuce wajen aiki su.
Sai da school Bus ɗin su Batool ya zo sannan suka fice, Mamy kaɗai aka bari daga baya, itama tana gama shiryawa ta wuce nata wajen aikin.
▪️▪️▪️
Yau ma su Batool sun riga kowa dawowa, can suka baro Amir da Baby tunda dama Pepper ɗaya suke yi a rana
Koda suka dawo girkin rana suka ɗaura kamar yanda suka saba, suna cikin yi ne Zee tazo gidan, rungume ta suka yi suna murnan ganin ta, ita kuma sai tsokanar su take yi da ƴan biyun Mamy, dayake hakan take yawan ce musu, kasancewar suna kama da juna ainun, saboda duk kan su iyayen su mata suka biyo, kuma dama Mamy da Ummu suna tsananin kama basu da wani banbanci.
Tare suka gama girkin da Zee, sannan ta ɗaura faten tsaki nata don tasha, duk da cikin ta ya ɗan girma har yanzu bata dena kwaɗayi ba.
Wajen ƙarfe 01:00pm. Itama Mamy ta dawo, a tare suka shigo gidan da su Amir, su ma dawowan su kenan.
Zuwan Zee gidan, dama ta zo ne kawo wa Mamy kuɗin lefe da Uncle Abbas ya aiko ta dashi, (shine autan ɗakin su Mamy) yanzu haka ya kusa aure nan da wata ɗaya, shine zasu je haɗo masa kayan lefen, kasancewar Mamy ce babba dole ita ce zata ɗau ragaman komi.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Zuwa Ƙarfe 02:30pm. Shima ABUL KHAIRI ya dawo daga aikin sa, sanda ya shigo parlour'n Zee ce kaɗai zaune tana yanka ganye zata yi kwaɗon shi
Sallaman sa ta amsa tana kallon sa
Ƙarisa shigowa yayi shima idanun sa a kan ta
"Yaya sannu da zuwa".
A gaban ta ya tsaya yana amsa mata tare da ƙara wa da faɗin, "yau Uwar ƴan uku ce a gidan namu?"
Murmushi tayi tana ajiye wuƙan hannun ta tace, "kai Yaya don Allah ka dena min wannan fatan, ina Ni ina haihuwan Triple's?".
"Ok ba kya so kenan? Shin baki ji daɗi ba ma nayi miki fata na gari? A lokaci ɗaya kin haifo uku".
"A'a Ni yaya bana so wlh, kai baka san wahalan haihuwa bane tunda ba ku ke haifan ba, amma Ni dai gwara in haifi ɗai-ɗayan".
Hararan ta yayi yace, "dalla ji be ta sai kace ta san zafin haihuwar? Sai ki bari idan kin haihu kya yi maganar".
Dariya Zee tayi tace, "uhm Yaya me ya rage mana yanzu? ai lokaci kawai ake jira".
"Yarinyan nan baki da kunya, Ni kike faɗa wa haka ko?" Yayi maganar yana saka ƙafa ya biga nata, sannan ya kai hannu kanta zai ranƙwashe ta
Saurin kawar da kanta tayi tana turo baki tace, "kai yaya, kai yaya! Wai meye laifi na ne? Na girma fa yanzu na wuce duka".
Taɓe baki yayi yace, "don kinyi auren shi ne kika wuce duka? To Ni a waje na baki wuce ba, har yanzu kallon ki nake yi tamkar Auta na, kuma tsaf zan saka tsumagiya in zane miki jiki babu ruwana".
Ita dai Zee kumbura fuska tayi tana faɗin, "caf ɗi".
Ƙura mata ido yayi yana ci je leɓe, kafin yace, "me kika ce? Ban ji ba".
"Yaya Ni ban ce komi ba".
Kafaɗa ya ɗage yana nufan hanyan ɗakin Mamy yace, "ki ce Batool ta kawo min abinci ɗaki na".
"Tom". Ta'amsa mishi tana ci gaba da yankan latas ɗin ta
Sai kuma ta ɗaga murya tana kwaɗa wa Batool kira
Fitowa tayi da gudu tana amsa mata
"Ki je ki haɗo wa Ya ABUL abincin sa ya dawo".
Batool amsa mata tayi ta wuce kichen da sauri.
Lokacin shima ABUL KHAIRI ya fito daga ɗakin Mamy ya wuce ɗakin sa, yana shiga rage kayan jikin sa ya hau yi, ya rage daga shi sai Singlet da dogon wandon shaddar jikin sa, zama yayi gefen gado ya ɗau wayan sa ya soma kiran Ziyada, duk da be sa ran zai same ta ba, tunda tun jiya taƙi ta kunna wayan nata, da zaran ya kira Switch off. Sai dai yanzu ɗin ya yi Sa'a wayan a kunne take, but har ta katse ba'a ɗauka ba, sake kira yayi idanun sa ƙyam akan wayan.
Batool ce ta shigo da sallama
Ya ɗago kansa yana kallon ta, ciki-ciki ya amsa mata sallaman bayan ya maida idanun sa kan wayan sa
Ƙarisowa tayi ta ajiye abincin saman Centre table, sannan tayi masa sannu
Amma be amsa ta ba, don shi hankalin sa na ga wayan sa
Kamar yanda ta san halin sa, dole ne idan ka kawo masa abinci sai ka zuba masa, don haka bata tsaya tambayan sa ba ta hau buɗe coolarn don ta zuba masa.
Time ɗin ne Ziyada tayi peacking Call ɗin, don haka yayi saurin haye wa kan gadon sosai don yaji daɗin yin wayan, ya kalli Batool dake ƙoƙarin zuba abincin, ganin ba ta kallon sa sai yace, "tashi ki wuce".
Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa
Shi kuma ya sake yin mata alama da hannu a kan ta fice, at the same time yana yiwa Ziyada sallama
Tashi Batool ɗin tayi ta fice abun ta.
Kwanciya yayi yana lumshe idanun sa jin zazzaƙan muryan Ziyada ta bugi kunnen sa, har wani ajiyan zuciya ya sauke sabida jin sanyin da ya ratsa shi, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta yanda zai narkar mata da zuciya ya kira sunan ta
"ZIYA.. LOVE".
Daga can Ziyada itama gyara kwanciyar ta tayi kan makeken gadon ta, a ranta tana jin wani daɗi na ziyartan ta jin muryan mafi soyuwa a gare ta, sai dai kuma jan aji ya saka taƙi amsa mishi, tayi shiru abunta tana sake sauke numfashi, wanda ke dukan kunnen ABUL KHAIRI yana saukar masa da kasala tare da ƙara mishi wutan ƙaunar ta, ji yake yi kamar ya buɗe ido ya ganta a kusa dashi ya rungume ta ya nuna mata how much he missed her; and how much he love her, sai dai babu hali, don haka ya janyo pilow ya matse yana sake kiran sunan ta cikin wani irin murya da sai da ya saka ta amsa mishi babu shiri, don sosai wannan karon muryan nasa ya tsarga mata har cikin jini da ɓargo
"Wai ba na baki haƙuri ba, meyasaka kike fushi dani?"
Shiru tayi bata amsa shi ba, sai ma mutsu-mutsu da take faman yi
"ZIYAAA.. LOVE".
"Umm.." tafaɗa a hankali
"I say you are silent".
"Ba kai ne ba.." tayi maganar cikin shagwaɓan da ya sake zautar dashi
Domin abinda yafi ƙauna wajen ta yaji tana masa shagwaɓa
"Me nayi Ziya.. Love?". Ya tambaye ta a hankali
Shiru tayi masa
Sai ya sauke numfashi kafin yace, "Ziya.. Love kin san mene ne?"
Tace, "Um.. um".
"Meyasa kike son saka Ni abinda Allah ya hana ne? Ko kin manta cewa Allah ya hana mu aikata Zina? To meyasa kike son muyi?"
Shiru tayi don bata da abin cewa
Don haka yaci gaba da faɗin, "Ziya.. love Ni ina guje miki wulaƙanci ne, idan na rigada na san ki a waje babu ta yadda za'a yi na daraja ki in mun yi aure, duk da ina matuƙar ƙaunar ki Love, but duk idan aka ce na gama sanin ki sannan muka yi aure, dole zaki fuskanci wulaƙanci a wuri na, kuma bazan yi ɗokin ki ba tunda mun rigada mun gama sheƙe ayar mu a waje, Ni kuma wannan abun ne nake guje miki, wlh Ziya ina son ki, ina matuƙar ƙaunar ki, ƙaunar da nake miki ne yasa bazan taɓa cutar dake ba, bazan wulakanta ki ba, sannan nafi son idan na aure ki in riƙa ganin ki da ƙima da daraja kamar ko wace mace ta ƙwarai, Please Ziya ki danne duk wani abu da kike ji har mu kai ga Aure, tunda Dady yace sai nan da Two years mu bari zuwa lokacin, kamar yanzu ne zaki ga ya zo kinji? Kinga nima Ina cikin wani hali sosai a kan buƙatar ki, amma babu yanda zan iya, tunda muna rage zafi shikenan mu bar shi a haka".
Numfashi Ziyada taja kafin tace, "to naji Bie, bazan sake maka maganan ba na bari".
"Yauwa ko ke fa ƴanmata na uhm, har kin sa naji sanyi a raina, kar ki damu ai muna tare, kuma kamar yau ne zaki ga an kawo ki gida na sai yanda muka yi da juna ko?"
Murmushi me sauti ta saki tace, "uhm Bie kenan".
Dariya shi kuma yayi yace, "ko dai kunya na kike ji ne? Ki faɗa abinda ke ranki don nasan Ziya.. love ba ta rasa abun faɗa".
"Bie ina kewar ka ne fa kawai".
"Da gaske Love?"
"Umm".
Sake matse pilown hannun sa yayi yana faɗin, "nima haka Love, ina matuƙar kewar ki a kwana biyun nan da kika taso Ni gaba, ji nake yi tamkar mun shekara bamu ji ɗumin juna ba, kin san jiya wlh daƙyar na iya daure wa ban fisgoki jiki na ba a lokacin da na tashi na ganki kusa dani".
Dariya ta ƙyalƙyale dashi tana cewa, "kai Bie amma sai ka nuna kamar baka damu dani ba, har da ture ni". Taƙarishe maganar cikin sigan shagwaɓa
Datse leɓen sa na ƙasa yayi kafin yace, "sorry dear bazan sake ba, yanzu ina buƙatar jin ɗumin mata ta in fito mu haɗu?".
"A'a".
"Why Loveeee?" Yayi maganar da jan sa a hankali
Daga can numfashi kawai Ziyada take sauke wa, cikin tsantsan sha'awa tace, "Ni nayi fushi ba yanzu zan sauko ba, sai dai ka bari sai gobe".
Mamakin maganar ta yayi, musamman yanda yaji muryan ta yasan itama tana buƙatar sa, amma kuma sai yayi shiru be ce mata komi ba
Ita kuma ta sake cewa, "Byee Bie zuwa gobe zamu haɗu". Bata jira yayi magana ba ma, ta tsinke wayan
Kifar da wayan yayi yana rufe idanun sa tare da sake ƙanƙame jikin sa yana fid da numfashi a hankali.
▪️▪️▪️
Ziyada tana tsinke wayan ta soma neman layin Saleem, sai dai kafin ma ta kira sai gashi ya kira ta, da sauri tayi peacking jikin ta na rawa, nan suka soma hira me tada junan su hankali, daga ƙarshe ta buƙaci zuwa wajen sa
Dama yana gidan sa ne, don haka cikin zumuɗi ya amsa mata
Babu ɓata lokaci ta miƙe ta sauya kayan ta zuwa doguwar rigan abaya, baƙa me kwalliya sosai, yane kanta tayi da gyalen rigan; ta zari HangBag ɗin ta da keey ɗin mota ta fice
Ko ɗakin Momyn ta bata leƙa ta faɗa mata zata fita ba ta fice abin ta, motan ta taja ta miƙa gidan Saleem.
.
_Mu je zuwa, more Comments more typing._
_kar ku manta Vote and share please._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸