Showing 87001 words to 88313 words out of 88313 words
Chapter 30 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ko a gefen hulan sa, ta matar sa yake yi domin yanzu soyayya sosai suke sha, ga cikin su yanzu da ya soma girma tunda tuni sun san tana da ciki, tun wani zazzaɓi da tayi na kwana ɗaya har suma tayi domin shi ya ɗauka ta mutu ma, hauka ne kawai be yi ba a lokacin. Sai da aka kaita asibiti tayi kwana biyu tana fama da zazzaɓi me zafi wanda yake saka surutai sabida zafin sa aga mutum kamar ya haukace
Su Ummu duk sai da suka zo gaishe ta sabida wannan rashin lafiyan da tayi
To ta dalilin hakan ne yasan tana da ciki tun sanda aka bincika ta aka gane musabbabin ciwon yana da alaƙa da cikin. Satin ta ɗaya a asibitin kafin ta warke. Tun daga lokacin kuma tattali ya sake sauya wa, babu Irin son da be nuna mata. Itama tuni ta gane ƙaunar sa yayi mata baƙe-baƙe a rai, gaba ɗayan su sun mayar da hankali kan junan su suna tattalin junan su. Har zuwa sanda ta haifu ta sami ƴa mace. Ranan suna yarinya taci sunan Ummu. Wato ADAMA za su na kiran ta da Ihsan.
A lokacin ne aka saka ranan auren Batool da Sulaiman tunda a time ɗin ne suka gama secondary School ɗin su, tuni soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su. Zuwa watanni uku aka yi auren suka wuce Kaduna don a can yayi gidan sa.
*******
Sai da Maimuna tayi shekara ɗaya da haihuwa kafin ABUL KHAIRI ya nema mata addmition ta soma zuwa B.U.K. a yanzu dai komi ya ci gaba a wurin ta, domin dai-dai gwargwado ta zama wayayyiyar mace yanda Mijin nata yake so, baza kace ita bace saboda mugun sauyawan da tayi
A kullum ABUL KHAIRI alfahari yake yi da ita saboda samun ta da yayi a matsayin matar sa. Sai a yanzu yake sake godiya ga Allah da ya basa iyaye masu tsananin ƙaunar sa, waɗanda suka iya hangen nesa kuma suka gano masa nasa future ɗin, ga shi yanzu komi sai dai ya ce alhamdulillah sabida samun Maimuna a matsayin matar sa, mace ta gari me kunya da sanin ya kamata, a iya tsawon rayuwar su na aure bata taɓa ɓata masa a sanin ta ba sai dai a rashin sani, wanda dama aka ce zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa, duk da a yanzu ta zama mace kamar yanda yake fata ya samu mata su yi rayuwa na ban birge wa, hutu da jin daɗi da kuma waye wa, duk ya samu but har a yanzu ɗin tana nuna kunyan ta gare shi, a kullum nuna wa take yi kamar yanzu suka soma sanin juna saboda tsananin kunyan ta, tabbas ya gane kunya a wurin mace wani babban jari ne da ƙawa da burge wa a wurin ta, duk macen da bata da kunya tabbas bata zama mace ba, mace me kunya ita ce mace, macen da duk abinda mijin ta yake buƙata zata yi masa amma ta cikin salo da jan aji da nuna kunyar ta ta ɗiya mace. shiyasa a koda yaushe yake sake jin ƙaunar ta na ƙara mamaye zuciyar sa, yana jin tamkar a yanzu ne ya fara son ta, kullum soyayyar ta sake zama sabo take yi a zuciyar sa, sabida iya mu'amalan ta da iya zaman ta, shiyasa a ko yaushe addu'ar sa Allah ya ƙara musu ƙaunar juna.
A yanzu haka shekara huɗu da ɗan watanni kenan da auren su, kuma a yanzu haka final exams suke rubuta wa a school, bata jima da sake haihuwar ɗiyar ta mace ba da Allah ya ba su don ko arba'in ma basu gama yi ba, yarinyan ta ci sunan Mamy Khadeejah, za suna kiran ta da Noor.
Itama Batool ta haifi ɗiyar ta mace me sunan Ummu ita suna kiran ta da Khairat, sai cikin na biyu da take ɗauke da shi.
Ko wani fanni Familyn suna a cikin farin ciki Masha Allah sai godiyar Allah.
_*ALHAMDULILLAH.. ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH* Komi yayi farko aka ce zai yi ƙarshe, a yau na kawo ƙarshen littafi na me suna *ABUL KHAIRI* Alhmadulillah ina godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranan, farin ciki na ba ya iya misaltuwa, kuma ina godiya ga duk FAN'S 🤩 ɗina da ta sanadiyyar su ne har na iya kammala wannan littafin, tabbas da ba don ku ba da tuni na ajiye alƙalami na, ina yi ne kawai domin farin cikin ku, Allah yasa hakan na isa gare ku, Allah yasa kuma ina faranta duk kan zuciyoyin ku? Ina fatan ya zame mana darasi da kuma tunatar wa a rayuwar mu. Na gode ga duk masoyana na fili dana baɗini. Love You so Much. 🤩_
Mu haɗu a sabon littafi na da yardan Allah idan Allah ya kai mu rai da lafiya. *MEEMA FAROUK*
*ƊANƊANO daga cikin littafin.
*RIYADH NORTH*
Hannun ta riƙe da bairo tana juya wa a kan book ɗin but ta kasa rubuta komi, tunani ne sosai a ranta wanda ya hana ta saƙat, shin yaushe ne zata kasance cikin farin ciki? Har yaushe ne komi zai wuce a rayuwar ta? Komi ya koma mata kamar baya? Idan ta zauna tana irin waɗannan tunanin sai taji da ace ba'a haife ta ba...
Faɗin da bairon nata yayi ne ya sanya ta dawo cikin hayyacin ta, idanun ta a kan bairon amma ba ta da alamun ɗauka, sai ta tsira mishi Sexy eyes ɗin ta a ɗan soconni kafin ta janye su tana jan ajiyan zuciya, lumshe idanun tayi a lokaci ɗaya tana buɗe su, ko kaɗan fuskar ta babu ɗigon fara'a wanda dama ta jima rabon da ta ganta cikin farin ciki, idan kuwa ka ga tayi murmushi sai dai tana gaban Abee ɗin ta ne, wannan kuma domin farin cikin shi take yi, ba ya ga haka babu wanda ke ganin dariyan ta bare murmushin ta a yanzu, ko yaushe a yanayi ɗaya take, walau farin ciki ko baƙin ciki, abin har ya zame mata jiki
Tashi tayi tana saka room silifers ɗin ta da ta zame su daga ƙafafun ta, sai ta taka a hankali ta nufi bakin windown ɗakin ta, hannayen ta ta sanya ta zuge cootin ɗin wanda haske ya bayyana a cikin ɗakin da ada babu, kanannaɗe hannayen ta tayi a ƙirji tana bin wajen da kallo, yayinda ta faɗa duniyar tunanin da ya zame mata jiki ko yaushe, tana tuna abubuwan dake faruwa a rayuwar ta
Daga ita sai guntun riga me ruwan Powder, dressed sleeping ne, sai gashin ta da ta ɗaure shi a ƙasan ƙeyanta ta sanya baƙin hula me kauri wanda ya fito mata da tuntun gashin nata, har kunnen ta ta rufe a cikin hulan wanda da alamu garin da akwai sanyi ne, duk da haka be sa ta sanya kayan sanyi ba, illa hulan dake kanta na sanyin, kuma ba wai don ba ta jin sanyin ba, sai dai ta saba da yanayin ne.
Ta jima a nan a tsaye kafin ta janye idanun ta tana wuce wa cikin Toilet, wanka tayi ta fito ɗaure da Towel a jikin ta, a lokacin ne ake mata Nocking a bakin ƙofar ta.
_Kar in cika ku da surutu bari in bar ku haka. Sai dai ina muku albishir salon na daban ne. coming soon. *MEEMA FAROUK*_