Showing 51001 words to 54000 words out of 88313 words

Chapter 18 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

sosai, domin ba kaɗan ba hankalin ta ya tashi da jin Sagir ɗin ta ne wanda yayi kisan, shikenan ita kuma baza ta taɓa cika burin ta ba? Wanda take matuƙar ƙauna tun tasowan ta shi ne ya aikata wannan mummunan aika-aikan, shikenan ta rasa shi har abada, taya zata iya rarrashin zuciyar ta Bayan ta gama sallama ta gare shi? Shiyasa ta kasa jure wa ta gudu ɗaki take wannan uban kukan tana toshe bakin ta da filo

Maimuna ce ta shigo ɗakin domin tuɓe uniform ɗin ta ta koma cikin ƴan uwa, don bata san ma Batool ɗin ta taso a wurin ba tunda bata lura ba, tana shigowa ta ganta a haka tana kuka, da sauri ta ƙarisa wajen ta ta zauna cike da tashin hankali take tambayar ta, "abinda ke damun ta take kuka?" Gaba ɗaya ta gama ɗaga hankalin ta ganin Batool ɗin a haka

Ita kuma Batool tashi tayi tana share hawayen ta amma wasu suna zubo wa, zuciyar ta na ƙuna daƙyar tace, "ban san ya zaki kalli zancen nawa ba Maimuna, ban san wani irin fassara zaki yi min ba. Wanda aka kama da kisan kai ya laƙaba wa Yayan mu shi ne yau nake kuka domin shi, ina kuka ne domin na rasa shi gaba ɗaya a rayuwa ta Maimuna". Ta ƙare maganar tana me sake fashe wa da kuka

Da sauri Maimunan ta saka hannu ta janyo ta jikin ta wanda har nata idanun sun soma tsiyayar da hawayen tausayin Batool ɗin, kasancewar ta me tausayi da damuwa da damuwar wani, bubbuga bayan ta ta hau yi kafin tace, "idan na fahimce ki Batool kina nufin kina son Yaya Sagir ne?"

Gyaɗa mata kai tayi tana ci gaba da kukan ta

"Kiyi haƙuri haka ƙaddaran ki take, Allah zai musanya miki da wanda ya fi shi, don Allah ki dena kuka kinji kar wani yazo ya ganki a haka?" Sai ta ɗago ta kuma tana share mata hawayen yayinda nata kuma suke zuba. Bata barta haka ba sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali wajen bata baki kafin suka tashi suka cire kayan su, sannan ita Maimunan ta fice don kar aji su shiru, daga nan ta duba idan an gama abinci ta zubo musu.

              Sai yamma kowa ya watse a gidan, har su Ummu duk sun koma gida a yau ɗin, inda saura mutanen gidan ne kaɗai

Sai a time ɗin ne ma su Maimuna suka ga ABUL KHAIRI da ya fito za su yi sallama da su Ummu, shi ne ya zauna a dainning yake cin abinci, inda su kuma gaba ɗaya mutanen gidan suke Parlour suna ɗan taɓa hira

Sai da ya gama ne Abba yace mishi, "yazo ya zauna akwai maganar da za su yi".

Zama yayi a ƙasa yana duƙar da kanshi




Kowa tsit yayi suka mayar da hankalin su kan Abban da ya soma magana.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 28*

*________* Da faɗa Abban ya soma mishi, bayan ya gama ya ɗaura mishi da nasiha kafin kuma ya ƙara da faɗin, "daga yanzu an tsayar da ranan auren su shi da Maimuna nan da wata biyu me zuwa, tunda ya ga alaman aure yake so abinda yake aikata wa kenan, to, za su yi masa can ya ƙarata, abunda ya faru dashi sai ya zamar mishi izna, tunda a ganin shi yana saɓon Allah ne a ɓoye, sai ga shi da ya tashi kama shi ya tona mishi asiri ta inda ba ya zato".

Mamy itama sai da ta ƙara da nata Nasihan

Kafin Abba ya sallame shi

Haka ya tashi jiki babu ƙwari ya shige ɗakin sa

Su ma su Batool ɗin ce musu yayi, "su wuce su je su kwanta tunda suna da makaranta".

Haka suka tashi suka wuce ɗaki, ran Maimuna duk babu daɗi, shikenan ita kuma nata ya ƙare, dole dai sai ta auri ABUL KHAIRI, mutumin da ya tsane ta, shin ya zaman nasu zai kaya, gaba ɗaya ta kasa sukuni har sai da ta zubar da hawaye

Batool da ta kula da yanayin ta tun shigowar su ɗakin, ita ta matsa kusa da ita tana ta rarrashin ta, ta san haka ƙaddaran su yake, ita ga shi an haɗa ta da wanda ba ta so, ita kuma ga shi tana fama da son wanda be ma san tana yi ba, babu halin auren shi tunda yayi mata nisa, sai duk tausayin kansu ya kamata, amma kuma ta san Maimuna ta fi ta buƙatar a tausaya mata, dole ta ɓoye nata damuwar tana rarrashin ta.



          Daƙyar dai a ranan suka samu barci ya sure su

Inda ita Maimuna ma har mafarkin ABUL KHAIRIN tayi, haka ta farka a firgice duk jikin ta ya jiƙe, barcin da bata koma ba kenan ta ɗauro alwala tana neman zaɓin Allah, a nan ta ƙarisa daren nata har zuwa kiran sallan asuba, sai da ta tashi Batool kafin ta tayar da Sallan.



           Bayan sun gama suka sake kwanta wa na ɗan mintoci, sannan suka tashi suka fara aikin gida

Suna cikin yi ne itama Mamy ta fito ta soma taya su

Sun gama komi inda suka yi wanka suka shirya cikin uniform ɗin su, sannan suka karya suka fito suka tafi.



         Shima Abba shirya wa yayi ya tafi wajen aikin sa

Ita Mamy dayake ta ɗau hutu, sai zuwa gobe zata je, shiyasa ta shige ɗaki ta kwanta don ta sake huta wa, bata yi yinƙurin tashin ABUL KHAIRI ba tunda ta san yana buƙatar hutu shima.



           Bata sani ba ma shi ya rigada ya tashi tunda ya kasa barcin ma, damuwa ce cinkushe a ranshi, komi ya jagule mishi, ji yake yi kamar yayi ta kurma ihu sabida tsaban damuwar dake addabar shi, daga ƙarshe dai tashi yayi ya shiga Toilet yayi wanka, sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya fito Parlour, jin shiru gidan sai ya wuce kanshi tsaye saman dainning, haka ya haɗa tea kaɗai ya ɗan kurɓa sannan ya koma Parlour, kanshi ya ɗaura a jikin kujeran yana me lumshe idanun sa, shiru yayi kawai yana ƙara nutso a cikin tunanin da ya addabi ruhin sa. Motsin da yaji shi yasa ya ɗago kansa yana me sauke kyawawan idanun sa da suka sake girma suka sanja kala saboda tsaban damuwa da rashin barci, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ba ya cikin mood ɗin sa

Mamy da ta ƙariso ta zauna gefen shi, ta kalle shi tace, "Baba na lafiya kuwa? Me ke damun ka?"

Sai da ya ɗan saki numfashi kaɗan fuskar shi babu walwala yace da ita, "babu Mamy, ina kwana?".

Murmushi tayi tana shafa kanshi tace, "lafiya lau. Ya ka tashi?"

"Alhmadulillah".

"Kana saka damuwa a ranka ko? Me ke damun ka?"

Shiru yayi

Sai tace, "don Allah ka cire komi a ranka kaji? Duk abinda ya faru a rayuwar ka ƙaddaran ka ce, kuma ka ɗau komi cikin sauƙi don Allah ba na son kana saka damuwa a ranka, komi zai wuce ka manta komi, sannan maganar ka da Maimuna na san har yanzu ba son ta kake yi ba, amma da sannu zaka fahimci wace ce ita, zaka san cewa ita kaɗai tafi dace wa da kai, ita kaɗai ce zaka ji daɗin zama da ita, har yanzu baka fahimce ta bane, ka zauna kayi tunanin magana ta sannan ka koya wa kanka zama da ita, da sannu kaima zaka ƙaunace ta, Maimuna me sauƙin kai ce, duk yanda ka juya ta ta hakan ne zaku zauna".

Ɗan ɗago idanun sa yayi da suke cike da hawaye yana kallon ta, be iya cewa komi ba illa gyaɗa mata kai da yayi, duk da bakin sa yana son furta wa

Murmushi tayi tace, "Allah ya maka albarka, ka je kayi Breakfast Kar ka zauna da yunwa".

"Nayi". Ya faɗa a hankali

"Anya Baba na?"

"Allah kuwa". Yayi maganar cikin shagwaɓa

Dariya tayi tana jan kumatun sa tace, "har yanzu baka girma ba, ga shi har kana shirin ajiye iyali ko".

Shima murmushin yayi kaɗan yana ɗaura kansa a kafaɗan ta yace, "Mamy ai Ni a wajen ki yaro ne Ni har yanzu, kuma bazan taɓa girma ba".

"To ai na kusa huta wa tunda ga Maimuna zata amshe min wannan nauyin, sai dai ka riƙa mata".

Shiru yayi kawai be amsa ta ba

Itama sai ta sauya hiran nata don dai kawai ya saki jiki sosai yayi fara'a, haka tayi ta jan shi da surutu

Shima ɗin sai ya biye mata. Koda ta tashi ma shiga kichen raka ta yayi yana taya ta da ɗauko wannan da wancan, hakan sai ya mantar dashi kaso arba'in daga cikin damuwar sa.



          Sai da suka gama ya wuce ɗakin sa ya kwanta tunda a lokacin barci sosai yake ji, dayake be yi ishashshe jiya ba, sai ya kwanta zuwa kafin a kira sallan azahar.







◾◾◾◾◾◾◾◾◾

           Gadan-gadan aka tayar da ginin gidan da ABUL KHAIRI zai zauna, a cikin anguwan su filin yake, sai dai akwai ɗan tafiya sosai da gidan su, tafiyan mintuna goma sha biyar ne a mota zai kai ka

Abba shi ya ɗau nauyin komi yake mishi, dayake da kuɗi shiyasa komi yake tafiya cikin sauri

Gefe ɗaya kuma biki na ta ƙarato wa. Har yanzu Maimuna ko kallon arziƙi ba ta samu daga wurin ABUL KHAIRIN, shi manta wa ma yake yi ita ce wacce za'a haɗa su aure, sai idan ya ganta tunanin sa yake zuwa gare ta, sai ya dinga bin ta da kallo yana aiyana ta yanda zai iya zama da ita, sam bata dace da shi ba a ganin shi, kwata-kwata ba irin kalan matar da yake so bace ita, ba wai don kyau ba, tunda tana da kyan ta, kuma suna kama ma dashi sosai tunda duk kan su su Mamy suka biyo, dayake itama ta biyo Ummu ne, kuma Ummu da Mamy sak kamannin su ɗaya, tamkar tagwaye haka suke, shi dai ya fi son mace wayayyiya me shekaru kamar wacce ta shiga jami'a, Ziyada ce kawai dai tayi dai-dai da ra'ayin shi, har yanzu ya kasa manta ta, idan yana tunanin ta har zubar da hawaye yake yi, Allah be ƙaddara zai mallake ta ba, soyayyar ta ta rigada ta bi jini da tsokan shi, manta ta kuwa zai mishi wahala tsantsa, domin ya daɗe da mallaka mata zuciyar shi, be jin zai sake son wata bayan ita, ya ɗau auren nan ne tamkar ƙaddara wanda bazai iya guje mata ba, amma ba wai don jin daɗin ruhin sa ba.







            ◾◾◾◾◾

      Ana saura sati Uku bikin ne Zee ta haihu ɗiya mace, inda aka yi sunan yarinyan aka sanya mata A'isha sunan mahaifiyar mijin ta, suna kiran ta da Iman

      Su Batool can suka tare gidan ta saboda taya ta aikace-aikace, duk da akwai umma Salamatu dake zaune da ita tana mata wankan jego

A can ne ma Zee ɗin take yiwa Maimunan gyaran jiki, ita take koya mata duk wani kissa da zata janyo hankalin ABUL KHAIRI, tunda sun san ba ta gaban sa, zaman su sai an shirya

Duk kunyan Maimuna haka ta zage tana koyan komi da ake koya mata, tunda ta ɗau alƙawarin faranta ran mijin ta har ta dawo da hankalin sa gare ta, duk da har yanzu ba wai son shi take yi ba itama, amma kuma zuciyar ta ko kaɗan ba ta ƙinsa, ABUL KHAIRI yana ɗaya daga cikin mazajen da suke matuƙar burge ta, wanda tana jin zata iya zama dashi a matsayin mijin ta idan har za su zauna lafiya, shiyasa take ƙoƙarin ta ga ta karkato hankalin sa itama, har tana jin a ranta tana matuƙar ƙaunar auren, amma gefe ɗaya kuma tana tausaya wa kanta, tana ga kamar baza ta iya ba, sai dai yanda kowa ke ƙarfafa mata gwiwa ne yasa take dagewa, a ganin ta ai itama mace ce, zata iya jawo hankalin sa wata rana ya so ta.




            Sai da satin bikin ya shiga kafin suka koma gida, inda gidan har ya soma cika da jama'a Masha Allah. Ana ta shagulgulan biki.



     Har ranan auren da aka ɗaura musu aure, aka shaida ɗaurin auren Yunusa Hayat Sunusi (ABUL KHAIRI) da Amaryan sa Maimuna Naseer.

       Dare na yi aka miƙa ta gidan mijin ta

Su Batool su ne amara ƙirjin biki, su da sauran ƙawayen su na school suke zaune da ita har sanda su ABUL KHAIRIN suka zo shi da Sulaiman Yayan Maimunan da shima ya zo bikin, sai dai zai zauna a gidan su Batool ne saboda burin iyayen su, tunda har an gaya mishi ana son haɗa su da Batool, shi kuma dama ra'ayin shi yana son ta, shiyasa yayi na'am da maganar nasu ya dawo gidan da zama tunda ya gama service ɗin sa, a nan zai zauna har ya jawo hankalin ta ya sami soyayyar ta.


      Shiyasa da suka tashi tafiya shi ya kwashe su gaba ɗaya, ya mayar da sauran gida sannan suka wuce gida shi da Batool ɗin, tunda ya zo dama yake shige mata ita duk bata san yana yin hakan bane domin ya sami soyayyar ta ba, tunda ta san cewa suna ɗasawa da shi sun saba sosai idan ya zo gidan su, amma ta ga salon na yanzu daban ne, yanda yake nuna mata kula wa da kuma yanda yake shige mata, sai dai bata kawo komi dai a ranta ba.

            










_To ya zaman ABUL KHAIRI da Maimuna zai kaya? Ga dai su a gida ɗaya inda aka kawo mishi matar sa . Sai mu ce Allah ya sanya alheri._


_Afwan na san babu yawa kuyi manage, da babu ne nace gwara kaɗan ɗin._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 29*

*________* Gidan two bedroom ne ko wanne da Toilet ɗin sa, sai babban Parlour da Toilet da wurin dainning table, sannan sai kichen dake da babban store ɗin sa da aka cika mata maƙil da kaya, shi kanshi kichen ɗin abun kallo ne bare akai ga zuwa kyakykyawar parlour'n nata da ya ci kujeru har set biyu, sun yi matuƙar kyau sosai, kuma komi an saka mata kalan ruwan madara ne da coffee shiyasa komi ya bada kala kamar ka sace ka gudu, har ta ɗakin ta kalan ruwan madara da coffee ne, sai abubuwan da baza a rasa ba da suka kasance baƙi

Iyayen ta da su Abba sun yi ƙoƙari wajen sun cika mata kaya ko ta ina, komi sai dai ace Masha Allah tubarakalla.


            Tunda su Batool suka fice a ɗakin take zaune a tsakiyar gadon ta tana jiran next abinda zai faru, duk da a tsorace take a wannan lokacin, shiru-shiru tana zuba idon ganin ABUL KHAIRI ya shigo saboda ta san ƙila zata ganshi, amma tsit kake ji daga ya je raka Sulaiman waje, har gyangyaɗi ya soma ɗiban ta bata motsa a wurin ba domin ba ƙaramin tsoro take ji ba ganin ta ita kaɗai babu kowa, ko ba komai tana son ganin ABUL KHAIRI domin zuciyar ta ta samu sukuni

Daga ƙarshe da barcin yaci ƙarfin ta ta ji shiru be dawo ba, sai ta ƙudundune kanta a saman gadon, da haka tana tunani tana gyangyaɗi har barcin ya sure ta gaba ɗaya.


               *******

      Shi kuwa ABUL KHAIRI tunda ya raka su Sulaiman bakin ƙofa sai ya rufe gidan shi ya wuce ɗakin sa kanshi tsaye, gaba ɗaya fuskar sa babu walwala jin sa yake yi kamar an ɗaure shi, jikin sa har rawa yake yi tsaban yanda yake ji a zuciyar sa

Wannan ranan da ya ci burin zuwan ta shi da masoyiyar sa, ita ce yau ta zo masa a bahagon yanayi, sai dai wata ba ita ba, mutuwa ta ɗauke mishi wacce yake matuƙar so da ƙauna; kuma yake fatan su kasance a inuwa ɗaya cikin rayuwar Aure, be taɓa tunanin ƙaddara irin wannan zata zo masa ba, yau ace ya auri wata ba Ziyada ba, haƙiƙa yau yana cikin baƙin ciki tsantsa, be san ya ya zai iya rayuwa da wata bayan ita ba, be san ta yanda zai ba wa zuciyar sa haƙuri har ta manta ta ba, ita kaɗai yake so a duniya, kuma ita ce kaɗai wacce zai so har ya koma ga mahaliccin sa, ba ya jin ko ɓurɓushin ƙaunar Maimuna a ransa, shiyasa bazai iya rayuwa da ita a matsayin matar sa ba, gwara su zauna a haka har sanda iyayen su za su fahimci zaman nasu su raba auren.


                 Haka ya kwanta a wannan daren a cikin mawuyacin hali, babu abinda yake yi sai mafarkin Ziyadan shi, yana kuma burin ace ko a mafarki ne su riƙa kasance wa tare har abada.



            🔵🔵🔵🔵🔵

         Washe gari da safe Maimuna ta tashi a makare, wuyan ta duk ya sanƙare sabida a yanda tayi barcin, daƙyar ta iya motsa wa har ta sauka a kan gadon, Toilet ta shiga ta soma ɗauro alwala ganin safiya tayi sosai, sai ta fito ta nemi Hijab cikin akwatunan ta da aka jera mata su a ɗakin

Sallah tayi har ta idar, kafin ta zauna nan tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login