Showing 33001 words to 36000 words out of 88313 words
Chapter 12 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
wai mutuwar Ziyadan shi abar ƙaunar shi? kuma wai shi ake zargi? wannan abun da me yayi kama?
To abun ya haɗe masa biyu, ga dukan da yake sha, lokaci ɗaya suka nemi numfashin sa suka rasa, sun zuba masa ruwa ko zai farfaɗo, amma ina ya ƙi farfaɗo wa, gaba ɗaya jikin sa sai da suka yi masa ruɗu-ruɗu da duka, dole suka wuce dashi Hospital don bashi taimakon gaggawa
Zuwa lokacin dama tuni Abba da Abokanan sa, tare da Mijin Umma Salamatu, sun ta sintiri a bar su su ganshi amma abun ya faskara, suna tafiya aka kawo shi asibiti cikin mawuyacin hali, ai shima sai Abba ya yanke jiki ya faɗi tsaban tashin hankali. Wannan abu dame yayi kama? wai ɗan su ake zargin yayi kisan kai?
◾◾◾
Haka zalika iyayen Ziyada su ma suna can a tashin hankalin, itama Mom sume wa gau tayi har yanzu bata farfaɗo ba, Dady ne kawai yake da ƙarfin hali, amma fa kuka kashirɓan yake yi yana faɗin, "a bar sa ya je ya kashe ABUL KHAIRI, domin duk wanda ya kashe masa tilon ƴar sa, to, sai ya ga bayan sa". Daƙyar su Dadyn Sagir suka hana sa zuwa.
Duk wani bincike sai da likitoci suka yi, kafin suka ba da gawan ta domin ayi mata Sallah. tunda aka kai gawan ta gida mutane suka cika gidan, sai koke-koke ake yi, zuwa lokacin Mom ta farfaɗo har an mayar da ita gida, ta sha kuka sosai musamman sanda ake shirin kai Ziyada makoncin ta, ko addu'a ta kasa mata, sai ma ta ƙara sume wa, sai da aka zuba mata ruwa ta farfaɗo, ana yin sallan magriba aka sallaci gawan ta aka kai ta gidan ta na gaskiya. Sai mu ce Allah ya jiƙan ki ZIYADA, Allah yasa mu yi kyakykyawar ƙarshe Amin.
◾◽◾◽◾
Abba hawan jinin sa ne ya tashi, dole aka ba shi gado
Ita kuwa Mamy dogon suma tayi, sai bayan isha'i ta farfaɗo, sai dai tunda ta farka take kuka. Su Umma Hassana da Umma Husaina ne suke ta faman rarrashin ta, amma ina Mamy sosai take kuka. Ji take yi tamkar a mafarki, wai ɗan ta shi ne yayi kisan kai? Kisan kai? Abun sosai ya girgiza ta
Sai da su Hajiya Falmata da Alh. Sunusi suka taho, su ne suka yi mata nasiha sosai a kan, "yarda da ƙaddara". Daƙyar suka samu suka rarrashe ta. Har ta samu tayi sallan da suka wuce ta, ta duƙufa roƙon Allah a kan, "ya kawo ma ɗanta mafita, domin ta san bazai taɓa yin kisan kai ba, tabbas ɗan ta ya taka sahun ɓarawo ne".
A taƙaice dai duka asibitin suka kwana, inda su Batool da Maimuna suka koma gida tare da Umma Salamatu, tunda dama sun dawo asibitin duba su Mamy. Su kuma su Hajiya Falmata suka wuce da Amir da Baby Gidan su.
A ranan Mamy kwana tayi kai kukan ta wajen Allah, haka ma su Hajiya Falmata, da sauran masoyan su. Hajiya Mama ma ta kasa zuwa sabida tashin hankali, sai dai addu'a da ta duƙufa yi babu ji babu gani.
*WASHE GARI*
Kai tsaye Dadyn Sa'ima da Uncle Abbas da ya dawo tun daren jiya jin mummunan labarin, dayake ba ya gari, Hospital ɗin da aka kai ABUL KHAIRI suka wuce, sai dai nan ma an hana su ganin sa. Sun sha wahala matuƙa kafin suka samu ganin sa, dayake DPO ɗin da case ɗin ke hannun sa akwai tsauri, dole sai da suka bi ta hanyoyi kafin suka samu shiga ɗakin da aka kwantar dashi, don ma su manya ne da wahalan sai tafi haka.
A safiyar Ummu da Mijin ta Alh. Naseer duk suka iso, babu daɗe wa itama Aunty Fatima ta iso, duk can asibitin suka wuce kai tsaye, inda Zee da su Safiyya matar Uncle Abbas tare da su Umma Hassana duk suna ɗakin da aka kwantar da Mamy, tunda shi Abba an hana kowa shiga wajen sa, saboda ana son ya huta ne sosai, wataƙil jinin sa zai sauka
Zee Kuka sosai take ta yi, ga ciki da take fama dashi, daƙyar Umma Salamatu ta rarrashe ta, amma duk da haka ta ƙi yin shiru
Ummu na zuwa sabon kuka ya ɓarke, domin rungume Mamy tayi suka fashe da wani sabon kukan. Aunty Fatima na gefe tana taya su.
Lokacin ne su Dadyn Sa'ima suka shigo ɗakin, tare da Alh. Naseer (Mahaifin Maimuna, da suke kiran sa da Baba), tunda shi dama kai tsaye asibitin da aka kwantar da ABUL KHAIRI ya wuce, saboda sai da ya kira Uncle Abbas yayi masa bayanin suna can, sai yanzu suka shigo tare. Su ne suka rarrashi su Mamy tare da musu nasiha, suna faɗa musu, "ba kuka ya kamata su yi yanzu ba, addu'a da kai wa Allah kukan su ya kamata".
Hakan yasa su Ummu suka dakata da kukan, sai hawaye da suke ta faman share wa.
Fita suka yi suka sake koma wa wajen Doctorn da yake duba Abba, sun jima a can har suka nemi ganin sa, a lokacin ma ya farka sai ƙarin ruwa da ake masa, nan suka zauna a wajen sa suna ta mishi nasiha tare da nuna masa, "wannan ƙaddaran su ce, kuma da sannu idan har yana da gaskiya zai fito".
Hankalin Abba sosai ya ɗan kwanta, sai dai da suka sanar masa ABUL KHAIRI na a mawuyacin hali sai hankalin sa ya sake tashi, dole suka ci gaba da ba shi baki.
Haka gaba ɗaya ahalin biyu suka kasance a cikin mawuyacin hali, babu me jin daɗin rayuwar sa a tsakankanin kwana biyun nan da suka shuɗe, sai dai jikin Abba da ɗan sauƙi, haka ma itama Mamy, dole aka ba su sallama suka koma gida.
**********
Inda a gefe ɗaya ABUL KHAIRI yana can shima a mawuyacin halin a asibiti, kwanan sa biyu ya farfaɗo, sabida shima har da alluran barci aka yi masa, yanda gaba ɗaya suka kasa gane kansa, gaba ɗaya tamkar dai ya samu taɓuwa haka ya koma, dole suka yi masa allura har sanda ya sake farfaɗo wa a kwana na uku da kai shi, a nan ne ya dawo hayyacin sa, sai dai kuka sosai yake yi, duk yanda likitocin suka so ya kwantar da hankalin sa sabida halin da yake ciki amma ina, bazai yiwu ba. Dole suka ƙyale sa, idan sun ga ya cika matsawa kansa sai su sake mishi alluran Barci. A haka kwana biyar suka shuɗe yana amsar treating hannun likitoci, da aka ga jikin nasa da ɗan sauƙi sai ƴan sandan suka matsa a sallame shi domin a mayar da shi station su ci gaba da bincike, domin gaba ɗaya Dadyn Ziyada ya tasa su gaba da, "sai sun aika su kotu an amsar mishi haƙƙin ɗiyar sa". Dole aka sallami ABUL suka wuce Station aka ci gaba da bincike.
Su Abba sun sake zuwa, daƙyar suka samu suka gansa, gaba ɗaya ya Gama fita hayyacin sa, har baƙin dole ya yi, duk jikin sa shatin bulala ne, dole ka zubar masa da hawaye, idanun sa sun yi luhu-luhu, bakin sa ya bushe duk ya rame, domin ko abinci ba ya ci, tun yana amsa wa ƴan sandan, "ba shi ne yayi kisan ba" har ma ya dena, sai hawaye da kullum yaƙi ƙafe wa a idanun sa
Sanda ya ga mahaifin sa da Uncle Abbas kuwa, kuka ya fashe dashi me tsuma rai, domin tunda wannan iftila'in nan ya faɗa masa be yi tozali da wani jinin sa ba, shiyasa yayi matuƙar kewar su
Rungume sa Abba yayi yana share hawaye, yayinda shima Uncle Abbas Yana gefe yana share nasa. Sai da suka saki juna kafin shima Uncle Abbas ya rungume sa, sun daɗe a haka yana bubbuga bayan sa, kafin suka saki juna, ya kama sa ya zaunar dashi suka saka shi a tsakiya, babu wanda ya iya magana cikin su, domin ba ƙaramin tashin hankali suke ciki ba, musamman da suka yi tozali da ABUL ɗin
Sai Shi ABUL KHAIRIN ne ma ya soma magana, "Abba Mamy fa?"
Kallon sa Abba yayi, sai ya kawar da kansa yace, "tana nan lafiya.. itama zata zo ta duba ka".
Lumshe idanu kawai yayi yana tsiyayar da hawaye
"Ka kwantar da hankalin ka, mun san cewa ba kai ne kayi kisan nan ba duk da ba mu san me ya faru ba, amma ka daure kayi mana bayanin komai, domin kotu ake son tura mu". Cewar Uncle Abbas Yana me riƙe masa hannu
Buɗe idon sa ABUL yayi ya aza a kansa, sai ya gyaɗa masa kai yana me shashsheƙan kuka. Nan ya soma faɗa musu abinda ya faru a ranan.
"Amma mene ne alaƙar ka da yarinyan da har ta zo maka gida?" Uncle Abbas yayi masa wannan tambayar
Shiru ABUL KHAIRI yayi yana share hawayen fuskar sa da ya ƙi tsaya wa, "me zai ce musu? Shin zai faɗa musu alaƙar su komi da komi ne? Ko kuma kawai zai ce musu ita ce yarinyan da suke soyayya? Kuma a kanta ne ya bijire wa iyayen sa zaɓin da suka yi masa. Amma kuma ya san cewa dole ne asirin sa zai tonu, dole ne duniya ta san mene ne ainihin alaƙar shi da ita na ɓoye. Sabida ya san bincike dole ne ya binciko hakan. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. wannan musiba da me yayi kama? Allah na tuba! Allah ka yafe min.. na San saɓon ka ne ya ja min shiga wannan mummunan ƙaddaran. Ya Allah na tuba! Ka cece Ni!"
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:_
_"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
_Allah yasa mu dace._
*________________________________*
*PAGE 21*
*________* "Kai lokacin ku ya cika ku fito haka nan, daga yau babu me sake ganin sa sai lauyan sa, don haka ku nemi lauya kafin a shiga court". Cewar wani tsagerar ɗan sanda dake kula da ABUL KHAIRIN
Kallon juna suka yi, sai suka miƙe kuma. ABUL KHAIRI na ji yana gani suka yi masa sallama suka tafi babu yanda zai iya, sai kawai ya kifa kai ya soma kuka, abinda yake yi kenan ko da yaushe, babu abinda ke damun sa sai kewan gida, tare da kewar Ziyadan shi, har yanzu ya kasa yarda cewa Ziyadan shi ta mutu, gani yake yi mafarki ne kuma zai farka, ko kaɗan halin da yake ciki ba ya damun sa, mutuwar Ziyada ya fi komi ɗaga masa hankali, shi ke saka shi fita hayyacin sa lokaci ɗaya. "Wai Ziyadan shi ce ta mutu?" Tambayan da kullum yake wa kansa kenan, kuma ya rasa me ba shi amsa, domin zuciyar sa ta ƙi yarda da hakan duk da azaban da yake fuskanta.
Su Abba suna koma wa gida, suka tarar da su Mamy na jiran su, daga Mamy sai su Maimuna, sannan sai Ummu da Safiyya matar Uncle Abbas, dayake su Umma Salamatu zuwa suke yi su koma kullum, yau kuma babu wacce ta zo a cikin su, ƙila sai anjima, ita kuma Ummu tun ranan tana gidan, Baba shi ya koma Kaduna. su Aunty Naana da Aunty Rufaida ma duk jiya suka zo da mazajen su, itama Aunty Fatima ta koma jiya, amma zata dawo.
Da sallama suka shigo, inda su Ummu suka amsa musu suna bin su da kallo. Zama suka yi su Maimuna suna musu, "sannu da zuwa" suka amsa su da, "yauwa"
Ummu tace, "Yaya kun samu ganin nashi kuwa?"
Sai da Abba yaja numfashi kafin yace, "eh mun ganshi amma daƙyar, kuma sun ce daga yau ba wanda zai sake ganin sa sai dai a samu lauya, domin court za'a je".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Cewar Ummu cike da tsananin damuwa
Itama dai Safiyya salatin tayi tana me zuba tagumi da hannu biyu
While Mamy hawaye ta soma yi tana me riƙe da kanta
Hakan da su Batool suka gani ne yasa su ma suke nasu hawayen, har ta Baby da take ƙaramar su kuka take yi, duk da bata gama fahimtar ma abinda ke faruwa da Yayan nata ba, sai dai ta san an kama shi.
Uncle Abbas yace, "haƙuri za ku yi Adda, Ni hakan ma yafi wlh, gwara a tura Court ɗin ayi-ayi ko zai samu ya fito".
"Amma taya kake tunanin zai fito bayan ba mu da ƙwaƙƙwaran sheda? Yarinyan nan a gidan sa ta mutu, ina jiye mana shiga kotun nan a yanke masa hukunci". Cewar Ummu kenan cike da tsananin damuwa
Abba yace, "ya zamu yi? Allah zai fitar dashi insha Allahu, dole zamu dage da addu'a domin nasan ɗan mu be aikata ba". Sai ya kalli Mamy da ke ta faman hawaye bata ce komi ba yace, "ki dena kuka don Allah, hakan na ƙara min tashin hankali, sai in rasa me ke min daɗi".
Ɗago kai tayi ta kalle sa da hawaye a fuskar ta tace, "Abban su dole nayi kuka, yanzu wai Baba na ne ake zargin yayi kisan kai? Wannan abun da me yayi kama? wlh ji nake yi kamar na haukace tsaban baƙin cikin wannan lokacin.."
"Subhanallah.. kar ki sake faɗar hakan kin ji ko? Ke musulma ce fa, sannan na san ki da yarda da ƙaddara, Khadijah kina da haƙuri sosai, don haka kar wannan ƙaddaran ya sanya ki ki kauce hanya". Abba ya faɗa yana kallon ta
Gaba ɗaya parlour'n shiru aka yi in ban da shashsheƙan kukan su Batool da suka kasa dena wa
Uncle Abbas yace, "yanzu to ya za ayi? Wani lauya zamu samu? Ni shi ne damuwa na".
Ajiyan zuciya Abba ya sauke, ba tare da yace komi ba illa tunanin mafita da yake yi a ransa
Mamy tace, "Ni zan tsaya masa, zan tsaya wa ɗana".
Gaba ɗaya kallon ta suka yi
Inda Abba yace, "taya zaki tsaya masa bayan ga halin da kike ciki? A'a baza ai haka ba, wani lauyan za mu samo".
"Meye amfani na idan har ban tsaya masa ba? Kar ka manta nima lauya ce. Don Allah Abban su ka bar Ni in tsaya masa don Allah". Ta ƙare maganar da rawan murya tana me ci gaba da hawayen ta
"Yaya ka bar ta kawai tunda zata iya, hakan ma ya fi wlh". Cewar Uncle Abbas
Ummu tace, "Adda don Allah ki bari a samu wani yayi aikin nan, baza ki iya ba".
"Nima haka nake gani". Abba yace hakan
"Zan iya, zan iya, Ni zan tsaya wa ɗana, babu wanda zai fi Ni ƙoƙarin ƙwato wa ɗana haƙƙi, domin babu wanda ya san me nake ji". Ta ƙare maganar da kuka tana me miƙewa ta shige ɗakin ta
Shiru suka yi duk kan su suna me bin ta da kallo, inda Ummu kuma ta tashi ta bi bayan ta
Shi kuma Uncle Abbas yace, "ka bar ta tayi don Allah Yaya, aikin ta ne fa, na san Adda ta tana da ƙware wa a aikin ta, memakon ma a samo wani gwara ita tayi hakan zai fi".
"To shikenan Allah ya shige mana gaba". Abinda Abban ya faɗa kenan
Sosai Uncle Abbas yaji daɗi, inda ya miƙe yana cewa Abban, "za su tafi, ko zuwa gobe ko jibi za su dawo, idan kuma da matsala za su yi waya".
Itama Safiyya miƙe wa tayi tana gyara mayafin ta, kafin ta kalli Uncle Abbas tana cewa, "bari in shiga in Yi musu sallama". Wuce wa tayi ta shiga ɗakin Mamy, nan ta tarar da su suna tattaunawa wa, domin har Ummu ta rarrashi Mamyn tayi shiru, sallama tayi masu a kan, "zata tafi," sai kuma tace, "Aunty ko dai in wuce da su Amir da Baby ne? in ya so su zauna a wajen mu, na ga su ma suna shiga damuwa da halin da ake ciki, gwara su je can ko sa samu sukuni".
Ummu tace, "nima haka na gani, ku wuce kawai tare ɗin".
"To shikenan, sai mun dawo goben, Allah ya bayyana gaskiya, Allah ya ba mu haƙuri da juriya".
"Amin Amin". Suka amsa daga Ummu har Mamyn
Sai da suka fito suka yi sallama da Uncle Abbas
Maimuna kuma taje ta haɗo wa Baby kayan ta ɗan kala biyar haka cikin jaka, shima Amir ya haɗo nasa. suna fito wa suka wuce
While Batool da Maimuna suka shiga kichen ɗaura girkin dare. Suka bar su Ummu suna tattaunawa a Parlour.
***** ****** ***** ***** ******
*TWO DAYS*
Yau Mamy ta shirya ta wuce police station don gana wa da ABUL KHAIRI, tana isa ta nemi iso wajen DPO, bayan ya bata iznin shiga, sai ta shiga suka gaisa, sannan ta faɗa masa, "ita ce mahaifiyar ABUL KHAIRI, ta zo ganin sa ne".
DPO yace, "Madam ai an rufe ganin sa har zuwa ranan da za'a gurfanar dashi Court, shawaran dai da muka ba ku ku nemi lauya, domin Monday na sama Mahaifin yarinyan yace za'a shiga court".
Kallon sa tayi fuska babu walwala tace, "DPO Ni dama ba na zo nan bane a matsayin wacce zata gan shi, a matsayin