Showing 72001 words to 75000 words out of 88313 words

Chapter 25 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

nan ya fita wai ya zo a kan haɗa auren Azeeza da Baba na, Ni wlh ban ma san me zance mishi ba".

Shima Abban dariya yayi yace, "lallai kam. To mu ina ruwan mu a ciki? Ai wajen ABUL KHAIRIN ya kamata ya je ya tambaye shi idan har zai iya auren ɗiyar sa tunda ba mu ne zamu zauna masa da ita ba, don Allah ma kar ki saka damuwa a wannan zancen kar ma ki sanar wa da ABUL KHAIRIN. idan shi Sanin ya dawo ki faɗa masa ya je can ya tambayi ABUL KHAIRIN idan zai iya auren ta, mu ina ruwan mu ai akwai rufin asirin da zai iya riƙe mata biyun ko? Maimuna da Azeeza duk ɗaya suke a wurin mu babu bambanci."

"Haka ne Abban su, amma ba ka ganin akwai matsala?"

"Babu wata matsala ki sanar masa haka idan ya sake dawowa, ki nuna masa ke kin amince amma ya je wajen ABUL KHAIRIN ya ji ta bakin sa, ta hakan ne kawai zaku samu zaman lafiya dashi".

"To shikenan Allah ya rufa mana asiri".

"Amin Amin". Duk suka amsa gaba ɗayan su. Kana kuma suka sauya hiran cikin nishaɗi bayan da Mamy ta kawo ma Abban abincin sa nan yana ci.




▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

            *AFTER TWO WEEKS*

        A wannan kwanakin abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da ɗinkewar ABUL KHAIRI da Rahina, domin tuni ya bi shawaran zuciyar sa ya amshi soyayyar ta, sun fara gudanar da soyayyar su cike da so da ƙauna, saboda tuni Rahina ta kama zuciyar ABUL KHAIRIN sosai kuma yana jin ta a ranshi

Kuma har yanzu zaman su da Maimuna bata sauya zani ba, kullum jiya-iyau haka suke zaune, tamkar dai ba mata da miji ba babu abinda ke haɗa su

Izuwa yanzu ita har ta saba da wannan zaman nasu, domin yanzu ta saki jikin ta sosai, daɗin ta ɗaya Baby na ɗebe mata kewa ko yaushe suna tare. Duk da har yanzu shi ke kai su school kuma ya dawo da su idan ya tashi daga aiki.

       Zuwa yanzu ya yanke shawarar tunkarar iyayen sa da maganar auren sa tunda a halin yanzu ya kai inda bazai iya haƙura ba, yana buƙatar mata matuƙa kuma ya kasa ya baiwa kansa damar da zai tunkari Maimuna da buƙatar sa, gani yake yi kawai raini ne zai shiga tsakanin su duk sanda hakan ya kasance, sannan ma shi har yanzu ganin ta yake yi yarinya, sai dai ko gaba yake sa ran idan ta sake girma zuwa ta shiga babban makaranta sai ya haɗa su da Rahina yayi ta manage idan zai iya, idan kuma bazai iya ba a lokacin sai ya sawwaƙe mata auren sa ya ji da Rahina tunda yanzu ita yake ji a zuciyar sa.




                    *******

       Yau ma suna zaune dawowar su kenan Maimuna tayi musu girki suka ci, sai ta wuce ɗaki ta bar su a parlour'n suna kallo

Wayan sa tayi ƙara ya ɗauka yana amsa wa ganin sunan Mamy, gaishe ta yayi

Ta amsa shi tana tambayar lafiyan Maimuna

"Ƙalau take Mamy". Yace da ita cikin sanyin murya

"Ok Masha Allah haka ake so, wai Ni kam yaushe zaka dawo min da Auta na tunda kun ƙi kawo ta na gaji nayi magana? Abban ku ma yanzu ya gama maganar ya kamata a dawo da ita".

"Mamy duka-duka yaushe ta zo? A bar ta a nan mana ko One month ta ƙarisa mana".

"A'a gaskiya ka dawo min da ɗiya ta ai mu ma muna son jin ɗumin ta, hakan ma ya isa wlh mun gode da ɗawainiya".

"To shikenan zan kawo ta anjima".

Mamy tace, "yauwa to ai gwara haka,". Daga haka ta kashe wayan bayan sun yi sallama

Ajiye wayan yayi yana kallon Babyn yace, "wai kin ji Mamy tace a mayar dake gida."

A tunanin sa ko baza tayi murna bane sai ta hau tsalle tana faɗin, "Yeeeeee zan koma gida inga su Mamy".

Riƙo ta yayi yana ɗaura ta a kan cinyan sa da murmushi a face ɗin sa yace, "ok wato ba kya son zama dani dama ko?"

Girgiza masa kai tayi da faɗin, "a'a yaya ina so, amma ina so in je in ga su Mamy ne".

"Hmm ba wani nan Ni zaki yiwa wayau, yanzu har Auntyn ki ba kya son zama da ita ko? Shikenan tashi ki je ki faɗa mata ta haɗa miki kayan ki zuwa anjima zan kai ki".

Da gudu ta sauka a jikin sa ta wuce ɗakin Maimuna don ta sanar mata

Murmushi kawai yayi yana mayar da hankalin sa kan kallon sa ya ci gaba da yi.



         Ita kuma tana shiga ta sanar wa Maimuna abinda yace

Da sauri Maimuna ta tashi daga kwancen da take tana riƙe mata hannu tace, "yauwa Auta na nima ki je ki ce mishi in shirya zan bi ku."

"Eh Aunty tare zamu je ma, bari in faɗa masa". Tafaɗa tana juya wa da gudu ta fice

Murmushi Maimuna tayi a ranta tana addu'ar, "Allah yasa ya amince". Tayi kewar gida tunda tayi auren bata taɓa zuwa ba ga shi watan ta ɗaya kenan.

        Tana zaune Baby ta dawo tace mata yace, "A'a".

Shiru Maimuna tayi bata iya cewa komi ba, ji take yi tamkar ta kurma ihu sabida baƙin ciki amma sai ta daure ta miƙe ta soma haɗa wa Baby duk wani kayan ta da babu shi cikin akwatin ta

Ita kuwa Baby murna ya rufe ta zata je ta ga iyayen ta, tuni ta tuɓe kayan ta tana faɗin, "Aunty kiyi min wanka sai in sanja Kaya".

"To bari in gama".

           Bayan ta gama wankan tayi mata ta shirya ta cikin kaya har da mata kwalliya

Tana gama mata ta fice da gudu parlour don ta sanar masa ta shirya. Ganin ba shi a Parlour sai ta nufi ɗakin sa suka ci karo a bakin ƙofa

"Wow my angel kin Yi matuƙar kyau, wa yayi miki kwalliyan?"

Tana washe baki ta bashi amsa da, "Aunty ne tayi min, ka gani ma har da jan-baki ta saka min".

"Inyee kin yi kyau Auta na, amma bari in je in Yi sallah sai in zo mu tafi ko?"

Gyaɗa masa kai tayi

"Yauwa good Girl". Ya shafa kanta yana wuce wa don alwalan ya kai shi ɗaki dama.


     Ita kuma ɗakin Maimuna ta koma ta tarar da ita tana sallah, sai itama tayi join ɗin ta ko alwala babu bare Hijab a jikin ta, saboda gani take yi tayi kwalliya baza ta goge ba. A haka suka yi sallah suka gama suka zauna zaman lazimi.

         Lokacin da ABUL KHAIRI ya dawo sai ya kwaɗa mata kira daga Parlour

Da gudu ta fice har tana tuntuɓe

Itama Maimuna tashi tayi ta ja mata kayan zuwa parlour'n

Yana riƙe da hannun Baby za su fita. Kallo ɗaya kawai yayi mata ya janye idanun sa suka fice

Hakan yasa taja akwatin tabi bayan su, har bakin mota ta kai ta buɗe baya ta saka

Su kuma tuni sun shige ciki Baby nata ɗaga mata hannu tana ɓangale baki

Itama murmushin take mata tana me ɗaga mata hannu zuciyar ta na cike da kewar ta, har suka fice tana a wurin don ta kasa yin magana. Sai da me gadi ya ja gate ya rufe kafin ta juya tana share hawayen da suka sauko mata ta koma ciki.






                    ******

           Suna zuwa gidan bayan yayi parking suka fito, ya ɗaukar mata jakan ta suka tasar wa shiga cikin gidan

Ita Baby tuni ta ruga a guje ta shige ta bar shi a baya

A lokacin da ya shiga da sallama su Mamy na zaune a parlour'n gaba ɗayan su ban da Sulaiman da ya fita. Baby na Kan jikin Mamy suna murnan dawowar ta, yayinda ita kuma sai rattaba musu zance take yi suna mata dariya

Gaishe su yayi yana murmushi da kallon Baby

Suka amsa Abba da Mamy suna tambayar shi Maimuna?

Kafin ma yayi magana Baby tayi tsagal ɗin cewa, "ai ta ce zata biyo mu yace mata baza ta zo ba".

Kama haɓa Mamy tayi

Shi kuma Abba na dariya yace, "ki ce shi ya hana ta zuwa?"

"Eh mana Abba".

Shi dai ABUL KHAIRI shiru yayi yana faman shafa kai yana hararan Babyn

Sai a lokacin su Batool suka sami damar gaishe shi

Ya amsa su yana faɗin, "Amir samo mun ruwa in sha".

Tashi yayi ya kawo mishi

Batool kuma miƙe wa tayi tabar parlour'n tana amsa Call

Shima Amir yana ajiye ruwan ya wuce ɗakin sa

While su kuma suka ɗan soma taɓa hira.


       Kamar shuɗewar mintuna sai kuma ABUL KHAIRIN yace, "Dama ina son mu Yi wata magana ne".

"To Baba na muna sauraron ka ai".

Sai da ya ɗan ja numfashi kamar bazai yi maganar ba don ya rasa ta ina zai fara

Jin yayi shiru sai Abba dake kallon sa yace, "ba magana kace zamu yi ba ko ka fasa ne?"

Girgiza kansa yayi kafin yace, "Dama a kan ina son zan sake aure ne.." shiru yayi domin ya kasa ci gaba sabida jin maganar tayi masa nauyi da ya furta

Su kuma saboda jin maganar a bazata sai duk suka kasa magana suna me bin shi da kallo

Abba ne ma ya samu ƙwarin gwiwan furta, "aure kuma? Aure kamar ya?"

Sauke kansa ƙasa yayi yana faman shafa ƙeya, cike da kunya yace, "aure nake so na ƙara Abba, sabida.."

"Ka buɗe baki kayi mana magana saboda me? Duka-duka auren naka yaushe aka yi shi ne da zaka zo mana da maganar sake wani? Kanka ɗaya kuwa?" Cewar Abban a zafafe jin kamar ma rainin hankali ne irin na ABUL KHAIRIN

"Abba na ga Maimuna tayi ƙarama da aure yanzu, shiyasa nake son sake wani auren sabida kada na shiga haƙƙin ta da yawa, kuma.."

Katse sa Abba yayi da faɗin, "in ji uban wa yace maka tayi ƙanƙanta da aure? Kawai dai kace kana son ka sake aure amma ba sai kace tayi ƙanƙanta ba, Maimunan yarinya ce da zaka ce tayi ƙanƙanta?"

Mamy tace, "Ban da abun ka Baba na Ni kaina lokacin da aka yi min auren fari ai kamar Maimunan nake, sannan ita kanta mahaifiyar Maimunan sanda tayi aure shekarun ta sha biyar ne a duniya, bata kai ma Maimunan ba a time ɗin, kuma tana da shekara 16 ta haifi Naana me ya same ta? Idan ma wani abun kake tunani gwara ka dena, ko wacce mace da haka ta saba kaji ko? Batun aure yanzu ma ba zai yiwu ba duk da dai ba hana ka yi zamu yi ba, amma yanzu duka-duka wata ɗaya ne da kwanaki da auren ku, ka bari sai sanda ta cika shekara ko fiye da hakan sai ka sake tunda kana da ra'ayi, mu baza mu hana ka ba tunda mun san ita ba zaɓin ka bane ba sai ka tunatar mana ba".

Shiru ABUL KHAIRI yayi kansa a ƙasa yana sauraron ta

"Yanzu kai idan ma aka ce kazo da maganar aure yanzu zaka zo mana dashi? Tukunna ma wace ce yarinyan da zaka aura ɗin?" Abban yayi masa wannan tambayar

Daƙyar ya iya furta, "Rahina".

"Rahina". Duk suka maimaita sunan a tare

Kana kuma Mamy ta ƙara da faɗin, "ba dai Rahina ƙawar Ziyada ba?".

"Eh ita".

"Ka rasa wacce zaka aura sai wannan yarinyan mara tarbiyya Baba na? Yarinyan da ta sanadiyyar ta ƙawar ta ta afka harkan zina shi ne har kake tunanin auren ta wato? Yanzu fisabilillahi kai baka ji kunya ba da har kake soyayya da ita?"

Abba yace, "ai bazai ji kunya ba tunda na ga alamun ba kunya ya cika ba. To tun wuri ka rabu da ita wlh tun kafin mu saka ƙafan wando ɗaya da kai kaji ko? Kuma batun aure idan ma auren zaka yi sai dai ka auri ƴar uwan ka Azeeza tunda itama tana son ka, ai gwara ita da wadda ka kawo mana, ko ba komi zumuncin Mamyn ku da dangin ta zai ƙarfafa. Kuma wlh ina faɗa maka duk ranan da ka biye wa son zuciyar ka itama ka je kuka aikata the same abinda kuka yi da wancan kai da Allah, tunda aure ne dai ga mata nan mun maka baka da hurumin da zaka bibiyi wata mace, gwara tun wuri ka rungumi matar ka ku zauna lafiya. Tashi dalla ka wuce mana a nan kana wani sim-sim da kai sai kace mutumin kirki".




Miƙe wa yayi ba tare da ya furta kanzil ba ya fice, motan sa ya shiga ya fice a gidan. Direct wani pharmacy ya wuce, sai da ya daɗe a cikin motan be fito ba sai saƙa da warwara yake yi, kafin kuma ya buɗe motan ya shiga cikin shagon. Ya jima kafin ya fito ya ja motan zuwa gida zuciyar sa kamar zata ƙone sabida baƙin ciki.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️





*________________________________*

              *PAGE 37*

*________* horn yayi a bakin Gate ɗin gidan sa, ana buɗe masa ya kutsa hancin motan cikin gidan, kai tsaye parcking space ya wuce ya tsayar da motan, be fi minti uku ba ya fito riƙe da leda a hannun sa, wuce wa yayi cikin gidan ya saka keey ya buɗe ya shiga

Babu kowa Parlour don lokacin Maimuna na ɗaki tana karatun school

Dakin sa ya wuce ya buɗe ya shiga ya rufe har da murza keey. Saman gadon sa ya nufa ya zauna ya soma zare cover shoes ɗin ƙafafuwan sa, bayan ya gama ya buɗe lockern gadon sa ya ajiye ledan da ya taho da shi, kwanciya yayi kansa na kallon silling ɗin ɗakin yana me lumshe idanun sa. Shiru yayi kawai yana sauraron bugun zuciyar sa da kuma tunanin da ya hau masa kai. Sosai ya burma cikin tunani har be san sanda aka yi kiran sallan magriba ba, sai a lokacin sannan ya buɗe idanun nasa yana me tashi ya shiga Toilet, alwala yayi ya fito daga ɗakin zai fice

A lokacin ne itama Maimuna ta fito daga kichen riƙe da coolar a hannun ta zata Kai saman dainning, haɗa idon da suka yi yasa tayi saurin sauke kai ƙasa tana ci gaba da taho wa

Shima ɗauke nasa idon yayi ya ƙarisa ya fice abin sa

Numfashi kawai ta ja taci gaba da abinda take yi har ta gama kana ta wuce ɗaki itama tayo alwala ta gabatar da sallan ta, bata tashi a wurin ba illa Kur'ani da ta ɗauka ta soma tilawa har sai da aka kira sallan isha'i, ta tashi ta gabatar sannan tayi wanka tayi shirin ta kamar yadda ta saba, rigan barci ta sanya doguwa me ruwan toka, yanayin rigan ya sanya ta ɗauka Hijab Wanda ta kawo mata iya ƙasan gwiwan ta ta saka, sannan ta fito Parlour

ABUL KHAIRI na zaune ya tasa t.v a gaba yana kallo, sai dai a baɗini tunani yake yi jefi-jefi kuma yana kai kallon sa ɗakin Maimuna. Ganin fitowar ta be san sanda ya sauke ajiyan zuciya me nauyi ba yana me sake bin ta da kallo ganin ta da Hijab yau kuma. Lumshe idanuwan sa yayi sabida ƙamshin turaren ta da ya hautsina masa kai sanda ta gibta shi ta wuce ta gaban sa. Buɗe su yayi yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a kan dainning ɗin

Ita kuma duk ta gama tsarguwa saboda ji take yi kamar yana kallon ta, amma bata ɗago kai ba har sanda ta dangana ga wajen dainning ɗin ta samu wuri ta zauna, abincin ta soma zuba wa kamar yanda ta saba, ta gama zuba nata kuma sai ta tsaya tana tunanin ta zuba masa ko ya? Kasancewar ganin be taso ba, kuma baza ta iya ce mishi, "ya taso ga abinci ba". Sai kawai ta soma cin nata ba tare da ta kalli inda yake ba.



       Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ABUL KHAIRI ya tashi ya nufi wajen Fridge ya ɗauko fresh milk ɗaya, kai tsaye wajen dainning ɗin ya nufa yana me jan kujera ya zauna. Be kalle ta ba yace, "zuba min kaɗan".

Da sauri ta ajiye cokalin hannun ta ta miƙe ta soma yunƙurin zuba masa

Da kallo yake bin ta kawai ganin yanda take ta ɓarin jiki, be san sanda ya ja tsaki ba yana sake haɗe rai, ji yake yi kamar ya make ta sabida shi kwata-kwata ya tsani idan yana wurin ta riƙa ɓare-ɓaren jiki, sai kace ta mayar dashi dodon ta

While duk ta rasa nutsuwar ta sabida jin yayi tsaki, a tunanin ta ko tayi laifi ne shiyasa har tana ɗago wa ta kalle sa. Kallon da ya sakar mata ne yasa tayi saurin mayar da kanta ƙasa lokaci ɗaya ta sake tsure wa. Daƙyar ta iya gama zuba abincin ta zauna sai dai ta kasa ci gaba da cin nata illa juya cokali da take yi

Shi kuwa tuni ya mayar da hankalin sa ga nasa yana ta faman kaiwa baki, sai dai fuskar nan nasa duk ta gama sauya wa sabida damuwan dake ran sa. Sai da ya ji motsin tashin ta ne ma ya dawo duniyar tunanin da yake yi yana bin ta da kallo. "Ina zaki je?"

Maimuna da har ta kusa sauka a wurin sai ta juyo tana kallon sa, yanda idanun su suka shige na juna hakan yasa ta janye nata cikin wani irin yanayi da ya same ta lokaci ɗaya. Bata iya magana ba sabida yanda bakin ta ya kasa buɗe wa bare ta ba shi amsa

"Dawo ki zauna".

Babu musu ta dawo ta zauna tana haɗe hannayen ta wuri ɗaya

Umarni ya sake bata a kan, "ta ɗauki Fresh milk ɗin ta shanye".

Jin abinda yace har sai da ta ɗago kai ta kalle sa da mamaki a cikin ranta, ganin dai ba ita yake kallo ba yasa ta sanya hannun ta na rawa ta ɗauka, buɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login