Showing 57001 words to 60000 words out of 88313 words
Chapter 20 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ka gan ni ba?"
Dariya yayi yace, "to ban da ke da abun ki jiya fa aka kawo ki ko?"
"To yaushe zaka zo Yaya?".
"Yanzu ma zan zo, dama kiran Batool nayi in ji ko zata tafi ne sai in zo in ɗauke ta".
"To Yaya amma dai tare da Yaya Aliyu zaku taho ko?"
"A'a Aliyu na gidan Hajiya Mama, amma ai shima zai zo ya duba ki na san bazai koma be zo ba".
"To Yaya".
"Yauwa ki ba wa Batool ɗin wayan idan tana kusa".
Sai da ta kalli Batool ɗin ta ɗan yi dariya kafin ta amsa mishi, sannan ta miƙa mata wayan
Ita kuma ta amsa wayan tana ajiye cup ɗin hannun ta. "Ina kwana Yaya, na tashi ai ban ganka ba".
"Ai baki damu dani ba tunda baki kira Ni ba, Ni kuwa kin ga na damu dake har na tambayi Mamy tace min kin taho nan ne".
"Ayya Yaya wlh ba haka bane, ka ga muna sauri ne shiyasa ban kira ka ba".
"To ai babu komi, yanzu yaushe zaki tafi in zo in ɗauke ki?"
"Sai yamma Yaya".
"Ah ah har yamma ƙanwata? Anya baza ki takura wa ma'auratan nan ba? kin san fa jiya aka yi auren nan be kamata ki zauna musu a gida ba, Ko kema kina son ayi miki haka ne?"
Dariya tayi cike da kunyan sa tace, "Ni kuma Yaya Sulaiman?"
"Eh mana kefa, gaskiya ba na son kema ayi miki haka, don haka yanzu zan zo in ɗauke ki".
Murmushi tayi kawai tace, "to".
"Baki ce Allah ya kawo Ni lafiya ba, haka ake yi babu addu'a?"
Batool dai duk jinta tayi wani iri, sai kace wasu masoya, amma a ranta sosai take jin farin ciki tsantsa, shiyasa tayi masa addu'ar kamar yanda ya buƙata, daga nan suka yi sallama tana ajiye wayan fuskar ta yalwace da murmushi
Maimuna da ta kafa mata ido tace, "wai Ni ban gane ba, meke shirin faruwa ne?"
"Aina kenan?" Batool ta tambaye ta a rashin fahimta
Ɗage mata gira tayi tace, "ke da Yaya Sulaiman mana, Anya ba soyayya kuke yi ba?"
Zaro ido tayi kafin tace, "soyayya kuma? Haba ke kuma idan soyayya ne ai zaki fi kowa sani, kema kin san wanda nake so".
"Yes I know. Amma tunda yanzu babu halin soyayya dashi Ni ina ma yaya na kamu, I'm serious wlh".
Jinjina kai Batool tayi kafin ta ɗauki Tea Cup ɗin tana cewa, "kanki ake ji dai, kin san dai Yaya Sulaiman baza a rasa shi da budurwa ba, so karma ki Yi wannan zancen ya ji ki".
"Ni yanzu da nayi tunanin nan har na ga kun fi dace wa, na san Yaya Sulaiman ustazu ne babu ruwan sa da ƴan mata".
Sai kawai Batool ta hau mata dariya
Ita kuma ta saki baki tana kallon ta. "Me kike wa dariya ne?"
"Babu. Bar zancen nan".
🔵🔵🔵🔵🔵
Sanda Sulaiman yazo suna nan zaune a parlour'n
Da murna Maimuna ta tare shi tana mishi sannu da zuwa
Sai da ya zauna kafin ya amsa ta shima yana murmushi yace, "yauwa ƙanwa ta Amarya".
Dariya tayi kawai
Itama Batool tayi masa nata sannu da zuwan
Yace, "ban amsa naki ba".
Sai ta langaɓe kai tace, "to Yaya Ni me nayi?"
"Dawo kusa dani sai in faɗa miki".
Waro idanu kawai tayi ta kasa tashi
Sai yayi murmushi kawai yana amsan ruwan da Maimuna ta zuba mishi a Cup ya sha, kafin yace da ita, "kin ga ke ya kamata ki tarbe Ni ba Amarya ba, amma ke kin zauna kin bar ta da aiki".
Da sauri Batool ɗin ta tashi tace, "ayya Yaya ai dama Ni zan ɗauko maka ta riga Ni".
Dariya suka yi su biyun
Ya ƙara da faɗin, "kin ji wasa nake miki dawo ki zauna. Ina Angon ne wai? Kar dai ace na zo ba ya nan?"
"Yana nan Yaya, amma yana ciki". Cewar Maimuna tana neman wuri ta zauna
"Ok Kira shi mu gaisa to, baki faɗa mishi zan zo bane?"
Kamar zata yi kuka tace, "Eh. Amma yaya.." sai kuma tayi shiru don bata san me zata ce mishi ba
"Mene ne?" Yayi maganar yana kallon ta
"Wai da zance ne ka kira shi a waya".
Jimm yayi kawai yana kallon ta, sai kuma be ce komi ba dai ya ɗauki wayan sa ya nemo Numban sa ya kira sa. Yana Ring ɗaya biyu ya ɗauki wayan. "Hello ɗan uwa gani a gidan ka fa"... "Ok." Sai ya cire wayan daga kunnen sa ya kashe tare da ajiye wa.
Two minutes ago sai ga ABUL KHAIRI ya buɗo ƙofa ya fito, daga shi sai dogon wando da Singlet har a lokacin be sanja ba, fuskar sa babu walwala haka ya iso wajen
While Maimuna da Batool ƙyam suka yi wuri ɗaya suna zare idanu
Sai da ya zauna kafin Batool tayi saurin gaishe sa
Be kalle ta ba ya amsa ta yana mayar da idanun sa kan Sulaiman, kaɗan ya saki fuskar sa yace, "zuwan yaushe?"
"Yanzu na zo. Amma haka ake yi zaka shige ɗaki ka bar Amaryan taka ita kaɗai?"
Murmushi kawai yayi be ce komi ba, don ya san halin Sulaiman idan ya biye mishi surutu zai saka shi, shi kuma kansa ciwo yake masa yanzu
"Am.. dama Ina so muyi maganar nan da muka yi da kai kwanakin baya".
Sai da ABUL KHAIRIN ya kalli su Maimuna suka haɗa ido kafin ya janye nashi idanun yana sake haɗe rai, "ka bari zamu yi maganar a waya".
Sulaiman yace, "ok mu ma ba zama zamu yi ba yanzu zamu tafi, Batool tashi ki ɗauko gyalen ki mu wuce".
"Nima zaka sauke Ni a gida zan ɗauko mota ta, bari in saka kaya". ABUL KHAIRI yayi maganar yana tashi ya wuce nashi ɗakin. Be jima ba ya fito cikin shirin sa na ɗanyen shadda me ruwan ƙasa, ɗinkin tazarce ne amma tayi masa mugun kyau sosai, dai-dai jikin sa ga shi ya kafa hula kalan kayan ƙube, takalmin ƙafafun sa cover ne baƙi ya saka da agogon hannun sa
Yana fito wa suka fice da Sulaiman don a lokacin su Maimuna sun koma ɗaki
Batool ɗaukan jakan ta da gyalen ta tayi ta yafa suka fito tare, sai tsokanar Maimunan take yi wadda kamar tayi kuka da tafiyan Batool ɗin
A bakin ƙofa ta tsaya tana ɗaga mata hannu har suka bar gidan, ta saka hannu ta share ƙwallan ta kafin ta shige ciki, a kan kujera ta kwanta tare da rufe idanun ta, tana tunani a haka barci ya ɗauke ta. Bata tashi ba har sai da aka kira sallan azahar, har a lokacin kuma ABUL KHAIRI be dawo ba, sallah tayi a ɗaki ta sake kishingiɗa a saman gadon ta taci gaba da tunanin ta, dayake ko kaɗan ba ta jin yunwa shiyasa bata yi tunanin nema wa kanta abinci ba.
Sai yamma taji shigowar motar sa gidan, ko bata duba ba jikin ta ya bata shi ne, shiyasa ta sake lafe wa a kan gadon tana kallon ƙofa kamar wacce zata ganshi a wurin
Sai kuwa ga shi ya murɗo ƙofan ya shigo, ciki-ciki yayi sallaman idanun sa ƙirr a kanta
Da sauri ta tashi zaune kanta a ƙasa tunda tayi masa kallo ɗaya, ji take yi kamar ta nitse sabida ta cire hijabin jikin ta, duk tayi tsimu a wurin ta kasa jirga wa don bata san me zata yi ba
A hankali ya tako fuskar sa a matuƙar haɗe amma idanun sa a kanta don ya kasa ɗauke wa, ajiye mata ledan hannun sa yayi a saman gadon kusa da ita, be ce komi ba ya juya ya fice
Ita kuma kamar jira take yi sai ta saki wani gwauron numfashi har da dafe ƙirjin ta tana me lumshe idanu, haka ƙirjin ta ke faman buga wa kamar zai faso sakamakon yanda ta ɗauke numfashi tun zuwan shi kusa da ita shi ya jawo mata hakan, ta ɗan jima a haka tana mayar da numfarfashi kafin ta ware idanun ta tana kallon ledan da ya ajiye mata, ɗauka tayi ta soma buɗe wa don taga abinda ke ciki.
********
Shi kuwa yana shiga ɗakin sa Direct Kan gadon sa ya samu ya zauna tare da kame kansa yana me rufe idanun sa, sai kuma ya gyara ya kishingiɗa yana ɗago ƙafafuwan sa ya aza Kan gadon bayan ya cire takalman nasa, ya sanya hannayen sa yayi matashi da su yana me ƙure wa ƙofa idanu kasancewar nan side ɗin yake kallo, duk bayan sakon yana me lumshe idanun sa yana buɗe wa, yanda zuciyar sa ke son matsa masa da tunanin ta ne sai ya ja tsaki yana sake juya kwanciyar sa, da zaran ya rufe ido ita yake gani shiyasa duk second ya buɗe ya rufe ya kasa barin idon waje ɗaya, ya san be taɓa ganin ta a haka ba shiyasa zuciyar sa ta kwaɗaitu da son ganin ta, amma bayan haka ba ya tunanin akwai abinda ke birge sa a game da ita, be taɓa tunanin haka take ba sai a yau ɗin, dole ne ma ya hana ta saka wannan kayan in ba haka ba komi zai iya faruwa, sai ya sake jan dogon tsaki yana tashi zaune ya jawo wayan sa, don dai ya kawar da tunanin banzan nashi shiyasa yake ta latse-latsen wayan sa har sanda aka kira sallan magriba, ya tashi yayi alwala ya fito ya nufi masallaci, da nisa sosai da gidan sa, amma a haka ya taka ya nufi masallacin, be dawo ba sai da aka yi sallan isha'i
Yana shigo wa yaji wani ƙamshi me daɗi ya mamaye hancin sa, da sauri ya lumshe idanun sa yana sake ware wa a parlour'n, sai da ya gama ƙare ma ko ina kallo kafin ya kai duban sa ga wajen dainning, a nan yaga an jera cololi da alamu girki ne tayi, ɗauke kai kawai yayi ya wuce ɗaki har yana saka keey.
******
Ita kuma a lokacin har ta fito daga wanka ta shirya cikin riga da skert na atamfa, ɗinkin ya kama ta cib a jikin ta kamar wata ƴar baby, ga shi yarintan ta ya sake fito wa ainun, bata shafa komi a fuskarta ba haka ta gama gyara wa ta fito kanta tsaye ta nufi ƙofan ɗakin ABUL KHAIRI tunda ta ga ba ya parlour'n, ta san ya dawo tunda ta ji motsin sa shiyasa ta nufi ɗakin ta faɗa masa "ga abinci idan zai ci," duk da wani sashi na zuciyar ta na cike da fargaba don bata san me zata tarar ba, a haƙiƙanin gaskiya Allah ya dasa mata tsoron ABUL KHAIRI saboda kwata-kwata be taɓa mata wasa ba, be taɓa kallon ta da idon rahama ba, shiyasa take matuƙar shakkan sa domin be da mutunci a yanda yake nuna musu, amma sai ga shi ƙaddara ta haɗa su wuri ɗaya, ta haɗa su zaman aure, abun da bata taɓa tunanin zai iya kasancewa ba ko da a mafarki ne, wai yau ita ce igiyar aure ya haɗa su da ABUL KHAIRI.
*Whatsapp number don't calling*
07065334256
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 31*
*________* Nocking take ta Yi amma shiru, shiyasa ta saka hannu ta tura nan ta ji a kulle ne. A lokacin taji muryan sa yana faɗin
"Idan kika bari na buɗe ƙofan nan na cid da ke a wurin nan; wlh sai na haɗa miki jini da majina".
Kamar ƙiftawar ido sai gata a ɗakin ta har da saka keey tana rufe wa, a baƙin ƙofan ta tsaya tana mayar da numfashi, bata manta dukan da yayi musu ba ita da Batool wanda ya ja kwanciyar ta a gadon asibiti, idan kuwa ya kama ta yanzu ai me ƙwatan ta sai Allah, gwara ta shafa wa kanta lafiya ta fita a harkan sa, "ai ɗan ba ƙara wlh". Tafaɗa a fili tana nufan kan gadon ta ta zauna.
Ta shafe mintoci a haka tana faman tunani kafin ta tashi tayi shirin kwanciya ta kwanta abin ta, da haka barci ya ɗauke ta cike da mafarkai kala-kala.
Tun daga ranan kuwa ta fita a harkan shi, idan ta tashi da safe zata yi musu Breakfast ta Kai saman dainning, haka ma na rana da na dare kullum tana yi, amma be taɓa ci ba, be ma taɓa zuwa ya duba abinda take girka wa ba, ita kuma tsoro ya hana ta sake mishi magana, iyakanta da shi idan suka haɗu a Parlour ta gaishe shi, wani zubin ya amsa ta a ciki-ciki, wani zubin kuma yayi banza da ita, a haka suke rayuwar tasu tamkar basu san juna ba, amma abun mamaki da zaran ƴan uwa sun zo zai saki jikin sa har ya nuna musu kamar suna zaune lafiya
Shiyasa itama ta fita harkan sa ta saba da wannan halin nasa, dayake ko yaushe suna waya da su Mamy shiyasa take rage kewa, har Ummu tana kiran ta ta tambaye ta, "ko akwai matsala?" Amma sai tace mata, "a'a". Bata taɓa faɗa musu wani abu game da zaman su ba duk da ko yaushe sai sun tambaya, idan Mamy bata tambaya ba Ummu zata tambaye ta, ita Ummu ma har tsiya take mata a cewar ta, "idan ma tana ɓoye wa ne ita ta sani, dama ta san halin ta shegen zurfin ciki ne da ita". Ita dai duk faɗan da zata mata ba ta iya ko tari ne, haka zata ƙyale ta ta kashe wayan da faɗan, "ita ta sani baza ta sake tambayan ta ba," amma kuma gobe bazai hana ta sake ɗin ba
Ummu tana matuƙar son Maimuna sabida ta san halin ta ita ce kaɗai daban da ƴaƴan ta, shiyasa take bata tausayi, bare kuma ta san yanda ABUL KHAIRI ba ƙaunar ta yake yi ba, shiyasa take lallaɓa ta ta sanar mata halin da suke ciki tunda ta san ita ce a wahala, amma kuma duk rarrashin da faɗan amsar ta ɗaya ne, "wlh babu komi". Shiyasa ta ƙyale ta kawai tunda haka ta zaɓa.
Satin su biyu ABUL KHAIRI ya koma bakin aikin sa, hakan da ta gani ne yasa itama ta same shi da zancen, "zata koma school". A lokacin da ta sanar mishi be ce mata komi ba don yana zaune a Parlour ne, sai ma tashi da yayi ya shige ɗaki abin sa
Ita kuma sai jikin ta yayi sanyi har tana tara ruwan hawaye, gaba ɗaya gani take yi kamar kashi ma ya fi ta daraja a gidan, ko kaɗan be taɓa mata kallon arziƙi ba, kamar ita kaɗai take rayuwa a gidan sabida babu ruwan sa da ita, sai ayi kwana biyu magana ɗaya be haɗa su ba, tabbas idan tace tana jin daɗin zaman nan ta yiwa kanta ƙarya, har ga Allah har zuciyan ta ba son shi itama take yi ba, amma kuma takan damu da rashin nuna mata kulawa da be yi, ya nuna tamkar babu halittan ta a wurin, ita kuma a rayuwa tana me ƙaunar me kulawa da ita, tana matuƙar ƙaunar kulawa, tana son taga mutum ya damu da ita duk da ita ba me son hayaniya bane.
Abun mamaki kuma washe gari tana barci sai ji tayi ana buga mata ƙofa, da sauri ta wartsake jin muryan sa yana cewa, "baza ta buɗe bane?" Ta duro a Kan gadon da sauri ta nufi ƙofan ta buɗe
Shi ne kuwa tsaye a gaban ta yana bin ta da kallo
Duk ta kiɗime lokaci ɗaya ganin ya kafe ta da idanun sa masu saka ta sanyin jiki, har bata san sanda ta duƙa tana gaishe shi ba
Sai kawai dariya ta so kama shi ganin yanda duk ta diririce, be iya ɗauke idanun sa a kanta ba illa tamke fuska da yayi don hana kansa dariyan da ya zo mishi, murya a dishe yace da ita, "me kike yi har yanzu baki shirya ba?"
"Am.. uhm dama.. dama.."
"Na baki ten minutes ki shirya ki same Ni". Ya katse ta da faɗan hakan yana juya wa ya fice
Da sauri ta saki numfashi tana me miƙe wa, sai a lokacin ma ta kalli jikin ta daga ita sai vest da guntun skert, "oh Allah na na shiga uku. Haka nake?" Tafaɗa kamar zata yi kuka. Sai kuma ta juya da sauri tana faɗa wa kan gadon ta, kanta ta lulluɓe tana faɗin, "na shiga uku Ni Maimunatu, haka na fita ya gan ni? wayyo Allah Ni". Sai ga hawaye, da sauri kuma ta tashi tuna maganar sa da tayi, sai kawai ta fashe da kuka tana faɗa wa Toilet da gudu, "wlh idan na wuce lokacin nan kashi na ya bushe a wurin sa, to shi ne be ce min in shirya tun jiya ba sai yanzu, salon kawai mugunta". Da haka take ta surutai har ta gama wankan. Kafin ma ta shirya har mintuna goman da ya ɗiba mata ya wuce, sai ta koma kuka wiwi jikin ta na ta faman rawa, hijabi a hannu haka ma takalman ta ta fita da gudu tana faman share hawaye. A Parlour taci birki ganin sa zaune yana latsa waya
Shima ɗago kai yayi yana kallon ta ganin ta da yayi kamar an jeho ta, da idanu kawai yake bin ta yanda yaga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, sai mamaki ya cika sa amma be iya ce mata komi ba illa sake kafe ta da kallo da yake yi
Ita kuma tana tsaye tana share hawayen ta, sai ta soma saka hijabin ta duk jikin ta rawa yake yi
Tashi yayi kawai ya nufi bakin ƙofa
Har ta bi bayan sa ta tuna bata ɗauki jaka ba, sai ta koma da gudu ta ɗauko ta fita
Lokacin ya shiga mota har ya tayar yana kallon hanya, tunda ta fito yake bin ta