Showing 1 words to 3000 words out of 91747 words
INUWAR GAJIMARE⛅
Nagarta Writer's Association
Oum-Nass 🏇
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI
ƊAYA
Gudu yake iya ƙarfin sa, idanuwan sa na fidda ambaliyar ruwa, bai damu da ƙayoyin da yake takawa a ƙafafuwan sa ba, balle mutanen da suke binsa da kallo, suna masa kallon mahaukaci sabon kamu.
Sai da ya kusa fita a cikin garin kana ya hango wani kangon ginin da ya ke kewaye da ciyayi a cikin sa. Kutsa kai ya yi, yana zagawa, yana wara idanuwansa, da har zuwa lokacin basu daina zubar da hawaye ba.
Can ya hango wata yarinya da ba zata wuce shekara goma sha uku ba, kwance ko motsi bata yi, ƙarasawa wajanta ya yi da mugun sauri yana girgizata da dukkanin ƙarfinsa.
Amma ko gezau bata yi ba, ƙara ya saki mai ƙarfi, wanda amonsa ya cika kangon da ya ke "KHADIJATU!" Ya faɗa yana ƙara girgizata cikin tashin hankali.
Ɗagata ya yi da niyar ɗaukanta, nan yaji damshi ya mamaye hannunsa, saurin janye hannunsa ya yi, yana mai fuskantar hannun nasa "JINI!" Ya faɗa, yana ƙara wara idanuwansa a fili wanda suka cika da hawaye.
Ƙirjinsa ne ya ci gaba da bugawa da tsananin ƙarfi, saitin zuciyarsa na fat-fat kamar zata yi tsalle ta fito.
A hankali ya sulale a wajen ya zauna, yana riƙe da zuciyarsa da yake ji tana barazanar fasa ƙirjinsa ta fito. Cike da tsoro yake ƙara kallon yarinyar.
_'Mutum baya tara sani akan gaibu da kuma hasashen rayuwar da zata gifto masa anan gaba. Amma ni ina da yaƙini akanka ISHAQ! Ko da ace duniya da mutane cikinta za su sauya, ina da tabbacin kai ba zaka sauya ba._
_A tare da kai Uba nake gani jigo kuma INUWAR GAJIMAREN da ke samar da iska ko bai bada ruwa ba. Bana so KHADIJATU ta tashi a matsayin marainiya! Bana son jin sautin kukanta! Bana son damuwarta! Ka min alƙawalin zaka kula da ita fiye da rayuwarka!"'_
Kansa ya dafe da yake ji kamar zai ɓalle daga maɗaukarsa, magan-ganun mahaifiyarsu na masa amsa kuwwa a ciki kunnuwansa, kamar a yanzu ne ta ke faɗa masa.
Kamar wanda aka fizga haka ya sake tashi ya ɗagata, ba tare da lura da yanda jinin ke zuba yana ɓata shi ba, hawayen fuskarsa na ƙara ambaliyar sauƙa a kan fuskarsa.
"Kada ki tafi ki barni Khadijatu! Na yima Ummi Alƙawarin zan kula da ke fiye da rayuwata, zanyi dariya a lokacin da kike taki dariyar, zan shimfiɗa rayuwata na baki kariya da dukka nin ƙarfina!
Amma me yasa kika tafi ke ɗaya baki jira ni? Me yasa baki tsaya ni ba? Bayan nace ki jira bazan daɗe ba?"
Shi kaɗai yake sambatu, yana gudu da ita a jikinsa, ƙayoyi duk sun huda masa ƙafafuwansa.
Kai tsaye asibitin ƙauyen nasu ya nufa "Likita! Likita!!" Yake faɗa cikin ruɗewa da neman agajin likitan. Wanda muryarsa ta riga data dusashe.
A hanzarce likitocin suka nufeshi, ganin yana ɗauke da yarinya ba numfashi, ga kuma jini duk ya ɓata su , suka ɗorata akan gadon marasa lafiya.
"Me ya faru da ita?" Likitan ya watsa masa tambaya.
Kai ya girgiza yana riƙe da ƙirjinsa da har lokacin bai daina zafi da bugawa ba.
"Ban sani ba likita! Nima a haka na sameta cikin jini. Dan Allah karka bari ta mutu likita, ka ceto rayuwar 'yar uwata."
Kai likitan ya girgiza cikin tausaya masa, ya shige ɗakin da aka kaita. Tashin hankali ne sosai ya ziyarce shi, kafin ya shiga sharce gumi akai-akai, "Nurse" Ya kira su, nan suka dafa masa, suna ƙoƙarin tsayar da jinin da ke zuba ta ƙasanta.
"Ya Allah! Wani rashin imani ne haka?" Ya faɗa cikin tsoron ganin halin da yarinyar ta ke ciki.
Fitowa ya yi bayan sunyi nasar tsayar mata da jinin da ke zuba a jikinta, ya kuma basu umarni da suyi mata ɗinki a jikinta.
A hautsine ya miƙe yana tunkararsa "Likita ƙanwata tana raye? Me ya sameta?"
Numfashi likitan ya ja, a hankali ya zare gilashin da ke idonsa "Ta zubar da jini mai yawa jikinta, akwai yiyuwar sai an ƙara mata jinin."
"Muje a gwada nawa zai mata, ko leda nawa ne a zuƙa a sa mata, dan Allah likita kada ta tafi ta barni. Idan ta mutu nima mutuwa zanyi." Ya faɗa hawaye na ƙara ambaliya akan fuskarsa.
Sosai likitan ya ƙara ji tausayinsa, da kuma ƙaunarsa na shigarsa a lokacin, duka a shekaru ba zai haura sha takwas ba, amma hakan bai hana nuna tsantsar ƙaunar da yake ma ƙanwar tasa ba.
"Muje a gwada to."
Da hanzari ya bi bayan likitan suka shiga aka gwada, jinin nasa yazo ɗaya da nata, haka suka ja leda ɗaya, yace sai an ƙara, da ƙyar likitan ya lallasheshi akan shi zai bada nasa, dan ba zai iyu a ɗauki leda biyu a jikinsa ba.
Godiya ya yima likitan hawaye na bin kwarmin idonsa, ba zai ce ga rana guda da wani ya nuna musu kwatan-kwacin wanan ƙaunar ba, ba zai kuma iya tuna ga ranar da wani ya musu magana da tausasawa ba, tun bayan mutuwar ahalinsu.
Sai da aka sa mata jinin sanan Likita ya ja shi zuwa ofishinsa, cikin sanyin murya ya fara masa magana "Ka san abin da ya sami ƙanwarka kuwa?"
Kai ya girgiza ba tare da ya yi magana ba, dan yawun bakinsa ya riga da ya ƙafe.
Numfashi likitan ya ja yana fuzgar da iska mai ƙarfi a bakinsa "An yi mata FYAƊE ne! An ji mata raunin da ya haddasa ƙasanta haɗewa, wanda ya zama dalilin zubar jini a tare da ita, kasancewar shekarunta sunyi ƙanƙanta. Wanda ya haiƙe mata ba da wasa ya je mata ba, a tunanina kisan kai ya so ya yi!"
Tun bayan da ya ambaci kalmar Fyaɗe bai sake jin wani abu ba, sai sautin da ke amsa amo a kunnuwansa, dafe kansa ya yi hannu bibbiyu yana ganin komi da ke ɗakin yana juya masa, a hankali ganinsa yayi rauni, idanuwansa suka rufe ruf, nan ya sulale ya faɗi ƙasa.
A firgice likita ya ƙara ƙwala ƙara yana kiran "NURSE."
*****
Kai take juyawa tana fizge-fizge idanuwanta a runtse wanda hakan zai tabbatar maka da mafarki ta ke yi, sai dai bige-bigen da take da kuma shura ƙafar da take shi zai nuna ma cewar mugun mafarki ta ke yi.
Can kuma ta fara magana da sautin muryarta, wanda ke nuna furgicinta da kuma raunin maganarta wanda bata fita a dai-dai.
"Me ye na maka? Ka yi haƙuri dan Allah! Ban sanka ba karka min mugunta!
Banda kowa sai Yayana, bamu da Baba da Mama sai mu kaɗai! Ka tausaya mana kada ka min mugunta, Yayana zai rama min!
Kaga kai ɗan gayu ne, har turare kake sawa, kayanka masu kyau ne, baka kama da masu mugunta, kada ka min mugunta."
Can kuma maganar tata ta tsaya saboda numfashinta da ke fita da sauri-sauri haka maganar ta sarƙe mata duk a lokaci ɗaya "Yayanahhhh!" Ta faɗa da wata raunanniyar murya cak numfashinta ya sake ɗauke.
"Ya ilahi!" Nurse ɗin ta faɗa lokacin da taga numfashin yarinyar ya sake ɗaukewa a karo na huɗu tun bayan wanzuwarsu a cikin asibitin, haka kuma ba zata iya ƙididdige adadin hawayen tausayawa yarinyar da ta goge ba.
"Wanan hakkin har ina? Ina mutumin da ya lalatawa yarinyar nan rayuwa zai kai hakkinta? Wa zai samu da zai taya shi sauƙe masa tarin zunuban da ya yi dakon ɗauka nata?"
Maganar da ta faɗa tana share hawayen idanuwanta "Tabbas akwai hisabi! Akwai kuma hakki mai bibbiyar rayuwa ya datse igiyar jin daɗin duk wani azzalumi."
Ƙoƙarin ceto rayuwarta take amma ina gani take kamar numfashinta yayi tafiyar da ba zai dawo ba ne.
Da gudu ta fice a ɗakin, can sai gasu da babban likitan, da kuma wasu Nurse's ɗin sun ƙara wanzuwa a ɗakin.
Kanta suka nufa suna kawo mata ɗauki ta ko wani sashi na jikinta.
Amma har zuwa lokacin babu alamun numfashi a tare da ita, babu kuma alamun cewar numfashinta zai iya dawowa dai-dai.
"Ya Allah!" abun da likitan ya faɗa yana dafe da kansa da yake ji kamar zai rabe biyu saboda zafi da sarawar da yake masa.
Kallon Nurse ɗin da ke kula da ita ya yi, yaga hawaye nata tsere akan fuskarta kamar ba likita ba.
"Shima Yayan nata har yanzu bai farka ba Ramla! Kaina ya kulle da yawa, ban san mi zan iya yiba a yanzu!" Ya faɗa da muryarsa da ke fita da rauni shima.
Da ƙyar ta cira ƙafarta ta isa bakin gadon da yarinyar ke kwance, kanta ta ke shafawa tana ganin yanda fiskarta tayi fayau ta rame, tana kuma ganin yanda bakinta ya ƙara tsukewa a lokaci guda, kamar bai taɓa wanzuwa a buɗe ba. Bugun zuciyarta ne ya ƙara nunkuwa lokacin da taga dogon karan hancinta da ya miƙe ya ɗan lomatsa ta tsakiyarsa, dumful ɗin da ke kan kumatunta sun lotsa kamar da ta ke magana.
Hawayen da bata tsammaci zubarsu ba su suka ɓalle da gudu suka zuba akan goshinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauƙe lokacin da hawayen ya zuba akan goshinta, da sauri suka sake rufuwa akanta dan sake dai-daita mata numfashinta, kana ya mata allurar barcin da zata samar mata da hutu da kuma nutsuwa.
Kusan a tare suka sauƙe ajiyar zuciya dukkansu, sanan suka fice a ɗakin aka bar Nurse Ramla ita ɗaya a wajanta, tana ƙara kallonta tana kuma son tuna inda ta san wanan fuskar .....
🌷🌷🌷🌷
#InuwarGajimare
#Dabanne[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
NAGARTA WRI. ASSOCIATION
OUM-NASS
BIYU
"Anyi mata fyaɗe ne!"
Kalmar da ya ke ji tana ƙara amsa kuwa a cikin kunnuwansa, tun bayan farkawarsa a dogon suman da ya yi. Yana ji ita kaɗe ce kalmar da ta rage a kansa, wadda ta ke ɗawainiya a majiyar isar da sautinsa.
Hawaye ke sauƙa akan idanuwansa kamar an ɓalle famfo, kansa kuwa ji yake kamar zai rabe masa gida biyu saboda ciwon da ya ke masa, zuciyarsa na ƙara cika da nauyin da bai taɓa jin irinsa ba.
"Ki yi haƙuri Ummi! Na gaza cika alƙawarin da na ɗaukar miki! Na gaza zama INUWAR GAJIMARE a tare da KHADIJATU! Na gaza kare mata martabarta Ummi!" Maganar da yake faɗa bayan farkawarsa daga suman da ya yi, yana bubbuga kansa akan fulon gadon asibitin.
Tashi ya yi daga kan gadon da yake yana cire kanular ruwan da ke jikinsa.
Fitowa ya yi daga ɗakin da aka kwantar da shi, yana takawa da ƙyar, saboda ƙarancin kuzarin da ke tare da shi. Gefe guda kuma yana jin abin da ya tokare masa a maƙoshi har a lokacin bai faɗa ba.
Karo suka yi da Likita wanda yake shirin shiga ɗakin da aka kwantar da shi, baki buɗe ya ke kallonsa "Kai da baka da lafiya ina kuma zaka je a haka?"
Kallon Likitan ya yi cikin raunin murya irin ta wanda ya gaji da kuka ya fara magana "Ƙanwata likita! Ina so nasan halin da ta ke ciki Likita!"
"Kana buƙatar ka huta kaima, yanzu barci take kaima ka je ka huta saboda..."
"A'a Likita bana buƙatar hutun da kake ta kira! Wani hutu ne ya rage min bayan an lalata min rayuwar ƙanwata? Wani hutu ne ya rage bayan rai guda ɗaya tilo da nake da shi a duniya yana barazanar barina? Wani hutu ne ya rage min a duniyar da ta cika da mutane masu son kansu? Ina hutun da zanyi a yayin da mutane basu duba can-canta balle su kimanta su kyautata? Bani da wanan haɓakon, bani da wanan ƙumajin, bani da wanan jarumtar, dan na riga da nayi saken da wanan hutun ya warware ko wani sa rai da nake da shi.
Ka faɗa min ina Khadijatu ta ke?"
Tunda ya fara magana hawaye ke sauƙa akan fuskar Likitan, bai taɓa cin karo da abun tausayi irin na yaran nan ba, bai taɓa ganin abun da ya tsaye masa a ƙoƙon rai kamar nasu ba.
Hawayen fuskarsa ya goge yana ƙoƙarin ɓoye idanuwansa a cikin farin gilashin da ke idanuwansa, gefe guda kuma yana kawar da ƙwayar idanuwansa daga kallon matashin saurayin da ya ke ganin rauni da gajiyawa a tare da shi, mafi muhimmanci shine ƙaunar ƙanwarsa da yake gani.
Hannunsa ya riƙo ya jashi har zuwa ɗakin da aka kwantar da Khadijatu, har a lokacin barci ta ke, ga Nurse ɗin da ke kula da ita tana faman share hawaye.
"Ga Khadijatu nan." Likitan ya faɗa.
Bai bari ya ba shi dama ba, ya ƙarasa wajanta, yana zama a kusa da ita, kallonta ya ke yana ganin zallar ramar da tayi a yini ɗaya tak.
'Wai wanan Khadijatun sa ce ta dawo haka! Yarinyar da bata san miye damuwa ba, ko yaushe murmushi na shimfiɗe akan fuskarta, bata da damuwa, bata da hayaniya wanda ya wuce wasa da yara sa'anninta, amma itace ta koma haka.'
Kifa kansa ya yi a kanta yana ƙara sautin kukansa "Me yasa sai ke Khadijatu? Waye wannan da ya cuta mana? Laifin me muka yi masa da ya nuna ƙwanjinsa akan ki Khadijatu? A ina zan ganshi? Ko na ganshi ba zan iya karɓo miki da abin da ya ƙwace naki ba, balle na sa rai zaki yi alfahari da dukkanin muryarki a matsayin budurwa. Ban san ta ina zan fara gyara miki wanan rauninba, amma na miki alƙawarin tsaya miki da dukkanin ƙarfina, na yi alƙawarin duk lokacin da nayi karo da shi sai ya shimfiɗa gwuiwoyinsa yana neman yafiyarki, ba zan iya tafiya na barki ba da na shiga duniya nemansa Khadijatu."
Sosai Likita da nurse Ramla suke hawayen tausaya tausayama yaran "Allah ya sani ina jin tausayin waɗan nan yaran Dr Anwar, ina ji zuciyata na caccaka da ƙunci da ɗaci a maƙoshi na."
"Hmm gara ke Anty Ramla. A iya shekaruna na aiki ban taɓa cin karo da abun da ya tsaye min a rai ba kamar wanan. Ko yaushe a wai-wai nake jin irin wanan matsalar na faruwa, ban taɓa tsammani za sameta a nan ba.
Ga ƙaramin ƙarfi, ga maraici na rashin iyaye." Ya ƙarasa faɗa yana goge hawayen da ya silalo a idanuwansa.
"Karka taɓa ni! Bana so! Kada ka cutar min! Yayanah!!" Saurin ihunta da maganarta wanda su suka ankarar da su farkawarta.
Da sauri Suka iyo kanta, Ishaƙ na ƙara riƙe hannunta gam kamar za'a ƙwace masa ita "Khadijatunah! Buɗe idanuwanki ki ganni, ga yayanki ya zo."
Ya faɗa yana ƙara riƙe hannunta, har a lokacin bata bar fizge-fizge da rintse idanuwanta ba, tana shura ƙafafuwanta.
"Yayanah!" itace kalmar da take fita a bakinta.
"Khadijatu!" Shima ya faɗa hawaye na ƙara silalowa a idanuwansa.
"Kada ka taɓa ni!" Ta faɗa tana buɗe idanuwanta da ƙarfi, dai-dai lokacin kuma da tayi karo da fuskar Dr. Anwar na ƙoƙarin zuwa kusa da ita, ganin tana gaf da cire ƙarin ruwan da ke hannunta.
Sanan kuma a kusa da ita tana ganin hannunta cikin na wani namijin da bata iya tan-tance fuskarsa, hakan ya sa ta saki ƙara da ƙarfin gaske "Shika min hannuna! Kada ka matso kusa da ni!" Ta faɗa tana fizge hannunta da iya ƙarfin da ya rage a jikinta.
Gefe guda tana ƙara kiran "Ka tsaya, kar ka matso kusa da ni, na roƙeka." Bata ƙarasa maganarba taji sauƙar hannu akan nata hannun, hakan ya sata ƙara ƙwalla ƙara mai ƙarfin gaske kafin numfashinta ya sake ɗaukewa idanuwanta su lumshe.
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Kalmar da Dr. Anwar ya faɗa cikin tsoron abin da ya ke tsammanin ya faru da Khadijatu.
"Khadijatu!" Ishaƙ ya faɗa da buɗaɗɗiyar muryarsa yana girgizata iya ƙarfinsa "Shikenan ta mutu Likita! Ki buɗe idanuwanki Khadijatu! Karki ki ce za ki barni ni ɗaya a wannan duniyar!"
Yana gama faɗar haka shima numfashinsa ya fara sama-sama kafin wani lokaci shima ya ɗauke ya faɗa kanta babu numfashi a tare da shi.
"Mun shiga Uku ni Ramlatu!"
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Ku yi maleji plx, nd kuyi hawaye kaɗan.
#InuwarGajimare
#Dabanne
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
©NAGARTA WRI. ASSOCIATION
® OUM-NASS🏇
UKU
Wanan karon ruwa Dr. Anwar ya ɗauko ya tuttule shi a kan Ishaƙ, doguwar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin daga bisani ya buɗe idanuwansa.
"Khadijatu karki mutu ki barni! Ki buɗe idanki dan Allah." Ya faɗa yana girgizata da ƙarfinsa.
Dafa shi Dr. Anwar ya yi kana ya fara masa magana cikin sigar lallashi "Ka nutsu Ishaƙ, ƙanwarka na raye bata mutuba, furgici da tsoro ne ya haddasa mata sake suma a karo na biyu, amma ina tabbatar maka zata farka.
Kai ne kake da alhakin bata kulawa a yanzu, idan ya kasance zuciyarka tayi rauni sosai, ta ina mu za mu yi aikinmu a kanta? Bayan kai ma ka gaza bamu wanan damar. Ka zama Namiji ishaƙ! Ka rayu ko dan ƙanwarka. Ka fara ƙarfafa zuciyarka, ta yanda zaka iya ƙarfafa mata ta ta zuciyar."
Kai ya ke gyaɗa ma Likitan yana share hawayen kan fuskarsa "Na yi shuru Likita. Na daina kuka, ka tasar min ƙanwata, bana so ta mutu ta barni!"
"In sha Allahu za ku rayu tare da ita, ba zata mutu ta barka ba."
Kai Ishaƙ ya iya gyaɗawa kawai, yana jin ɗacin da ke maƙoshinsa ya gaza ɗaukewa, kamar yanda yawun da ke bakinsa ya ɗauke.
Gefe guda kuma yana Addu'a akan ƙanwarsa ta farka.
Sosai Dr. Anwar da Nurse Ramla suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar Khadijatu, duk wani abun da ya kamata su mata sun yi mata, amma hakan ya ci tura, kamar ba komi su ke mata ba.
Kallonsa Ishaƙ yake cikin sarewa da fargabar abun da zai je ya zo, ya kifa kansa a jikin bangon ɗakin, hawaye na ta tsere akan idanuwansa.
'Ban shiryama wanan baƙar ranar ba ko kaɗan, ban taɓa hasashen zuwan rana irin wanan mai cike da ƙunci da ɗaci a rayuwarmu ba. Ya Allah ka kawo mana ɗauki, ka dubi maraichin mu, kada ka jarrabe ni da abun da zuciyata ba zata iya ɗauka ba.'
Maganar da Ishaƙ ya ke a zuciyarsa kenan yana ƙara jin bugun zuciyarsa na tsananta fiye da lokacin da take bugawa.
'Ta ina zan fara gwada rayuwa