Showing 18001 words to 21000 words out of 91747 words

Chapter 7 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

788

a matsayin Mallakinsa. Kasancewar su masu ƙaramin ƙarfi gidan kuma ba wani babba ba ne. Asalima duka a haɗe suke a waje guda sai 'yar tazarar tsakar gidan da ke tsakanin ɓangaran Abban nasu da na matan gidan.

   Bai daɗe da fita ba sai ga Fatiman ta shigo bakinta ɗauke da sallama. A shekaru ba zata haura ashirun da biyar ba, sai dai yanayinta da kyakkyawan jikin da ke gareta, zai sa ka ɗauka 'yar shekara Ashirin ce.
  Fara ce ba sosai ba, tana da manyan idanuwa da ɗan ƙaramin hancinta da bai da tsayi sosai, dan baza'a sata a rukunin masu dogon hanci ba ko kuma gajeru, kamar yanda bakinta ke da faɗi.
   Har ƙasa ta rusuna tana gaida Abdul wanda wanan ɗabi'ar Fatima ce, ko da wasa bata taɓa gaida shi a tsaye ba.
"Kina lafiya Fatima?"

"Alhamdulillahi lafiya lau Yaya. Ya su Anty Khairat da Ummie?"
"Suma suna lafiya."
Shuru ne ya biyo baya na ɗan lokaci kafin ya yi gyaran murya ya fara magana "Na zo ne akan batun bikonki gidan Imran. Sai dai Abbanki yace ba zaki koma ba har sai shi Imran ɗin ya zo da kansa.
  Ban san me ya faru tsakaninku ba Fatima, bani da masaniya akan matsalar da ta ke ta kai kawo tsakaninki da shi. Kamar yanda Ummie ma bata sani ba.
Abu ɗaya muka sani shine zaman haƙurin da kike da Imran tun bayan aurenku, duk mai ido ya san kina jure zama da shi."

  Shuru ya yi yana ciza kalmar da yake son faɗa mata "Sai dai bayan ke bani da tabbacin wata zata sake shigowa rayuwar Imran har tayi nisan zango haka.  Ƙaddara ta daɗe da sabunta labari, ta kuma yi kutse a cikin rayuwa da duniyar Imran, ta yanda ya zama mutum guda ɗaya da ke fafutukar yin rayuwa a bigiren da ba ya iya tankawa. Da kanki kin san ya zama kurman da bai ji, baya son jiyarwa.
Ban da sani akan gobe amma bana so ki bar aikin ladan da kika daɗe da sanya hannunki ciki. Duka akanki muka sanya burukanmu, muna kuma fatan ki dawo mana da asalin Imran ɗinmu."

  Yana gama faɗar haka ya tashi ya fuce yabar gidan gaba ɗaya. Da kallo Fatima ta bishi hawaye na sauƙa akan idanuwanta, tambaya take da ita mai yawa a tare da ita, tambayar da har yau babu wani mutum guda da ya taɓa tsayawa ya amsa mata ita.
  Ko yaushe a lulluɓe take a cikinta "Me yasa ko yaushe Imran ke nasara akanta? Me yasa har yanzu bata jin tsanarsa a tare da ita? Tabbas soyayyar Imran ce zata hallaka ta." Da kanta tasan ba zata iya barin Imran ta rayu a ƙarƙashin kulawar iyayenta ba, kamar yanda take so da burin ci gaba da kallonsa koda ace baya tanka mata da kalma guda ɗaya ne.

  "Ya Allah ka dubi marainiyar zuciyata mai cike da rauni, Ka kawo min sauƙin akan lamarina da Imran."Ta faɗa tana kifa kanta akan kujerar da ke kusa da ita.

    🌷🌷🌷

 
INUWAR GAJIMARE na kuɗi ne, dan Allah ku kimanta abun da ke gareku da kyakkyawar tausasawa, idan har tsautsayi ya fidda labarin kuyi adalci a tsakani, ku nemi mallakin halaliyar labarin idan har kuna buƙatarsa ba tare da son zuciya ba 08030990232.

  Girmamawa.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

Oum_Nass

0013

ƘAUYEN TONI.

Suna zaune a wajen har duhu ya shigo, hayaniyar mutanen ta ragu a wajen. Ajiyar zucicya ya sauƙe a hankali, yana kai kallonsa ga Khadijatu da har a lokacin bata san inda kanta ya ke ba.

Tashi ya yi ya taɓa tulun yaji akwai sauran ruwa kaɗan a cikinsa, alola yayi kana ya samu wararren waje duk a bayan gidan ya fara gabatar da sallolin da ke kansa. Tabbas ba zai ce ga sallahr da ya yiba a yau, tun bayan sallar asuba da yayi.
Wata ƙila wanan tashin hankalin yana da nasaba da rashin ibadar da bai yi ba a yau, komi na rayuwarsu ya dawo babu. Amma a hakama sunyi arziƙi da suka tsira da numfashinsu.

Saida ya iddar da sallolin da ke kansa sanan ya ɗaga hannayensa sama addu'a yake son yi amma kuma bakinsa ya yi masa nauyi, zuciyarsa ta karaya bai san me zai roƙa ba. Kuka ne ya ci ƙarfinsa haka ya ɗaga hannu sama yana kuka da ƙyar ya iya buɗa baki ya ambaci "Allah kai ka hallicemu kafi mu sanin abun da ke faruwa da mu. Ya Allah ka kawo mana ɗauki a cikin rayuwarmu, kamar yanda ka tseratar da mu a yau."
shafa hannayensa ya yi akan fuskarsa yana ci gaba da kuka, kukan da bai san na me ye yake ba a yanzu, sai dai abubuwan da suka faru na rayuwarsu da ya ce ba zai ƙara kuka akansu ba zuciyarsa ta gaza jurewa, dole ta koka saboda rashin sanin tabbacin inda za su.

Yana zaune a wajen har dare ya tsala sosai, ya daina jiyo alamun takun mutane. Tashi ya yi da hanzari ya ɗauki Khadijatu ya saɓata a kafaɗarsa kana ya futo daga gidan, sai da ya wai-waya ko ina yaga babu alamun mutane sanan ya fuce yabar gidan.
Gudu-gudu sauri-sauri ya ke tafiya yana waiwayen bayansa, cikin sa'a har ya bar garin bai haɗu da mutane ba.
Ci gaba ya yi da kutsawa ta cikin daji yana tafiya, ƙafafuwansa na huda ƙayoyi amma bai damu ba da ya tsaya, saboda zuciyarsa ta gama bushewa.

Sai da ya tabbatar da ya bar garin sosai ya kuma bashi tazara mai yawa kana ya samu ya rage saurin da yake. Jikinsa ya cike tsarkaf da zuffa.
Bakin titin da ya futo ya sashi sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Kwantar da Khadijatun ya yi a gefen titu shima ya zauna yana maida numfashi, kansa ya ɗaga sama yana ga yanda taurari suka yi ƙawata sararin samaniya, musamman da farin wata ya yi nisa babu wadatar haske a wajen.

A zahiri ne yake kallon saman amma a baɗini ya shiga wata duniyar ne daban, bai san ina yake ba.
Hannun da yaji an ɗora masa akansa ne ya sashi saurin dawowa hayyacinsa, yana bin hannayen da kallo a cikin duhun da ke wajen.
"Khadijatu nah kin farka!" Ya faɗa cikin rawar murya yana ɗagota da ɗorata akan cinyarsa.
"Yayanah ruwa!" Ta faɗa cikin sanyin muryarta.
Idanuwa ya fara bazawa yana tunanin inda zai samu ruwa, dan shi a tsawon yinin da yayi a yau ya manta da kalmar ruwa, tunaninsa bai bashi cewar ya adana shi saboda gaba ba. Ya dai san yawun da ke bakinsa ma ya bushe amma bai kawo a ransa ya tsaya ya nemi ruwan da zai sha ya tada masa da shi ba.

Shuru yayi yana kallon bakin Khadijatun da ke ƙara ambatar kalmar ruwa, yana baza idanuwansa da neman inda zai samo mata shi.
Babu alamun mutane a wajen da yake, yasan ba abu ne mai sauƙi ya iya samun ruwa a kusa ba, ta ina zai fara nema mata ruwan da zata sha?

Kansa ya dafe da hannunsa kana ya saki yana miƙewa tsaye da ita akan kafaɗinsa "Khadijatu babu ruwa anan wajen, bana jin zamu samu ruwa a kurkusa. Ki ƙara haƙuri na ɗauke ki mu yi gaba, in sha Allah sai mu samu ko a hanya ne."
Kai ta gyaɗa cikin raunin murya ta ce "To Yayana!" Tafiya ya fara yi yana gyara mata zamanta, sam a yanzu bai buƙatar ƙara yin kutse a cikin dajikan da ke tsallakensu, amma kuma tafiya a titi a ina zai samu ruwa?
"Babu." Ya faɗa a fili kamar yana yin magana da wani ne.

Suna tafiya a cikin talatainin daren da ko wani mahaluƙi yake kwance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Sai dai nasu labarin ya sha ban-ban da na mutanen da ke da galihu, a yau ya tabbatar da almajiri ya fisu gata da samun kyakkyawan muhalli, tunda shi yana ƙarƙashin kulawar malaminsa ne.

Tuntuɓe ya ji yayi da wani abu wanda hakan ya sashi kifawa zai faɗi, cikin zafin nama ya tare Khadijatu yana taga-taga da ita kamar za su zube a tare.
Cikin ikon Allah ya tsaya cak kamar da aka ruƙe shi.
Kansa ya kai ƙasa dan ganin abun da ya yi tuntuɓe da shi har ya kusan kada shi. Da mamaki yake ganin wani ɗan ƙaramin dutsene a wajen "Ikon Allah!" Ya faɗa yana ɗaukan dutsen a hannunsa dan ya kawar da shi a gefen hanyar, har ya ɗaga zai cillashi sai kuma ya ji tsoron dare ne, gara ya kai shi gefen a hankali ya ajiye shi.

Gangarawa ya yi daga bakin titin ya sauƙa gefen da zai shigar da shi wani dajin da ban "Bismillahi!" Ya faɗa yana ajiye dutsen a ƙasa, abun mamaki yaji hannunsa ya shiga cikin ruwa.
Ido ya fuddo waje cikin tsananin farin ciki ya fara kiran "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka kawo mana sauƙi."

Da sauri ya sauƙar da Khadijatu ya fara ɗebo ruwan a hannunsa yana bata, cikin sauri ta shiga shansa akai-akai da ya ɗebo sai ta shanye, a haka har sai da ta ƙoshi sanan ta girgiza masa kai.
Ɗebowa ya yi shima ya sha ruwan sosai, kana ya wanke jikinsa, itama Khadijatu ya wanke mata nata jikin da ta gama jiƙe shi sharkaf da fitsari.
Sai dai rashin wasu kayan yasa ya barta da kayanta, ya sake goyata suka bar wajen, yana jin zuciyarsa wasai, ta samu nutsuwa, haka kuma gangar jikinsa ta samu ƙarfin ɗaukan Khadijatun.

Tafiyar da bata wuce mintuna biyar ba, suka hango hasken wani gari da kuma futulun da suka ƙawata garin, "Alhamdulillah!" Ya faɗa yana ƙara sauri dan ya samu damar shiga garin da ya ke cike da hasken futulu.

Sai dai duk yanda ya kai da saurin ji yayi ƙafafuwansa sun gaji, ba zai iya ci gaba da tafiyar ba, abun har mamaki ya bashi ganin yanda ƙafarsa taƙi ɗaguwa, kamar da aka riƙe masa ita.
"Ya Allah! Me ke shirin faruwa da ni ne?" Ya faɗa cikin tsoron halin da ya tsinci kansa a ciki.

Ganin lokaci na tafiya kuma ba zai iya ci gaba da tafiya ba, ya sa shi ya zauna a wajen yana kwantar da Khadijatu akan cinyarsa, wani haske yaga ya shige idonsa, wanda ya ɗauke ganinsa da jinsa, bai ƙara sanin inda kansa ya ke ba...


*******

KADUNA, NIGERIA.

"Ummie Fatima ai Ƙaddarar Imran ce, idan har nace itama tana cikin labarinsa da ya kamata ki tursasa masa zama da ita.
Ke kaɗai ce zaki sake wanan abun ki gyara wancan kuskuren da kika riga kikayi."

Tashi tsaye Ummie ta yi tana ƙara kallon Anty Aisha da take kafeta da idanuwa "Bana so na sake shiga rayuwar Imran a karo na biyu Aisha. Kamar yanda bana so na sake yin kuskuren tirsasama Fatima zama da shi.
Itama ɗiyace da aka haifeta, dole tana buƙatar samun 'yanci a gidan mijinta. Ba wai ta ƙare rayuwarta wajen kula da shi ba."

Tashi Anty Aisha ta yi tana rataya jakarta a kafaɗarta "Ummie wanan zaɓin naki ne fa. Idan kika ci gaba da yin haka to kamar kin ɗauki wuƙa kin ƙara daddatsa zuciyarsu ne.
Ko babu daɗi ki shiga cikin lamarin kamar yanda kika zama silar wargaza komi da ke gidan nan."

Tana gama faɗar haka ta fuce ta bar mata ɗakin, rakiyar ido ta bita da shi cikin mutuwar jiki, ita kanta tasan gaskiya ne ta faɗa mata, amma kuma a yanzu bata buƙatar ƙara shiga rayuwar yaranta, musamman Imran da take jin soyayyarsa fiye da ko wani ɗa da ta haifa a cikinta, amma kuma son zuciyarta ya ɓoye soyayyar da take masa.

Daga ɗakin Ummie ɓangaran Imran ta shiga ba tare da ta jira ya mata iso ba, samunsa ta yi yana ruƙe da kansa, idanuwansa a lumshe.

Tausayinsa ne ya kamata sosai, amma kuma bata da yanda zata iya, dole ta yi abun da Ummie ta gaza yi. Imran ƙaninta ne da take jin sonsa a zuciyarta, asalima itace ta sha wahalar rainonsa fiye da Umminsa, wanda take masa kallon ɗa ba wai ƙani ba, kamar yanda shima yake mata.
Sai dai abun da ya faru da shi ya sauya duniyarsa da tunaninsa, ya zama bahagon mutumin da bai jurar magana da kowa.

Zama ta yi kusa da shi tana kallonsa, idonsa ya buɗe ya kalleta sanan ya sake rufe shi, ta san ba magana zai mata ba, kamar yanda ta sanshi da shariya.

Murmushi ta yi tana kallonsa "Imran wanan ƙuncin da kake ciki ba shine zai dawo maka da jiya ta dawo yau ba. Duk abun da ya kuskurema ya riga da ya kuskure maka ba zai dawo gareka ba.
Shekaru sun ja, lokaci ya tura da yawa, me zai hana ka rungumi ƙaddararka hannu bibbiyu, ka ɗauki Fatima a matsayin matar rufin asirinka wadda zata cike maka gurbin da ka rasa."

Ido ya buɗe ya kalleta daga bisani ya ɗanyi murmushi marar sauti "Anty Aisha kina ga zan iya mantawa da sauri haka? Abun da ya faru da ni ba mai saurin mantawa ba ne."

Dafa kafaɗarsa ta yi cikin tausayawa "Na sani ba mai sauri ba ne, amma ai anja lokaci da yawa. Irin wanan kan faru da mutane masu yawa, kuma su yi rayuwarsu kamar ba abun da ya same su, saboda sun riga da sun bunne ciwon a zuciyarsu sai lokaci zuwa lokaci suke tona shi.
A matsayinka na musulmi kana buƙatar wanan kyakkyawar zuciyar, kana buƙatar hamdala ga Allah dan ya baka ladan haƙurinka.
Idan ka yarda da ƙaddara sai ya musauya maka da mafi alkairin abun da ka rasa."

"Ta Ina zan fara Anty?"

"Ka je ka yi bikon Fatima, ka koma bakin aikinka na asibiti. Hakan kaɗai ne zai sa ka dawo da rayuwarka, koda ba kayi farin ciki ba, zaka sanya mutane da yawa a cikin farin ciki."

"Aikina yana buƙatar nutsuwa Anty. Ni kuma bani da wanan nutsuwar!"

"Kana da akwai tunda baka zauce ka shiga bola tsince-tsince ba. Baka cire kayan jikinka kana yawo ana kamoka ba."

Dariya ya yi mai sauti wanda ya sata itama dariyar "Kina so kice sai na haukace ne na zama marar nutsuwa?"

"Ka gwada tuɓe kayanka da kaina zan maka sasari." Ta bashi amsa cikin tabbatarwa.

"Anty baki sauyaba, ina tunanin yanda surukanki suke da ke!"
"Kamar dai yanda kake yi da ni haka." Ta bashi amsa tana bige ƙeyarsa.

Shafawa yayi yana murmushi a hankali ya jinginar da kansa a jikinta "Shikenan zan je na dawo da Fatima, zan kuma koma bakin aikina.
Inaga daga wanan kuma babu wani sauran ƙorafin da zaki sake zuwa ki min."
Fuskarsa ta shafa cikin jin daɗin amincewarsa, wanda kusan kowa ya gaji da halinsa.
"Allah ya maka albarka, ya kareka da kariyarka, ya kawo maka sauƙin damuwarka."
Murmushi ya yi yana kallonta ba tare da yayi magana ba.
"Kano zan koma da aiki Anty!"

"Kano kuma?"
Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya ƙara magana ba.


🌷🌷🌷🌷🌷


IG
DABANNE

OUM-NASS
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

OUM-NASS

0014 B

LAGOS, NIGERIA.


Tunda ya shiga palon yake jin ƙamshi ya cika masa hancinsa, idonsa ya lumshe ya fara bin inda ƙamshin yake.
Abinci ne reras akan daining table ɗin, buɗe kulolin abincin ya yi, yana lumshe idanuwansa da kuma haɗiyar yawu.
Cikin hanzari ya shige ɗakin Amrah ganin bata palon, kamar yanda ya yi zato haka ne, tana zaune ta haɗa kai a jikin mudubin da ke ɗakin, hannayenta biyu ta zuba tagumi, bata san da shigowarsa ɗakinba.

Ƙarasawa ya yi cikin sinɗa a hankali ya rungumota cikinsa, ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallonsa ta mudubin dake gabanta. shima kallonta yake yana ƙara rungumeta a jikinsa, fuska ta ɓata tana turo ɗan ƙaramin bakinta.
Juyo da ita yayi gabansa ya na kallon idonta da taƙi yarda su haɗu da nasa.
Risinawa ya yi yana kai bakinsa saitin nata, kawar da kai ta yi tana ture shi daga kusa da shi.

Marairaice murya yayi yana langware kai cikin sanyin muryarsa da ya saba yi mata magana "Yi haƙuri Rabin raina! Kada ki min wanan horon!"
Ido ta ɗago tana kallonsa tuni hawaye sun zubo akan idanuwan nata "Ya rabb!" Ya faɗa yana ɗaukanta ciɗak daga kan kujerar da dake zaune.
A kan gado ya kwantar da ita yana binta zuwa wajen, bakinsa ya sa yana lashe hawayen da yake zuba akan fuskarta, har zuwa saman idonta, da harshensa ya ke zagaye saman idon yana lasawa, hakan ya sa tsikar jikinta zubawa tana sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Ganin hakan yasa ya gangaro da harshensa saitin bakinta ya zura shi akai, ya shiga sarrafata tun tana mutsu-mutsun ƙwacewa har ta gaza ta sakar masa lago.
Haka ya shiga fidda kayan jikinta duka daga nan ya sauya salon labarin nasu daga rarrashi zuwa sabuwar duniya da ban, wanda ta mantar da su komi da ke a tare da su na ɓacin rai.

***
Bayan awanni biyu.

Kamar 'yar baby ya ɗaukota daga ɗakin ya ajiyeta akan cinyarsa, abincin ya fara bata, tana ci kamar ranta baya so.
"Ki daure kici ko na samu nutsuwar ruhina!" ya faɗa yana kai mata abincin a bakinta, kamar ba zata karɓa ba, can ta buɗe bakinta a hankali ya sa mata, taunawa ta ks cikin yanga kamar ranta baya so, shi kuma sai riritata yake kamar ƙwai.
Yana jin soyayyarta na ƙara caccakar ruhinsa, da ko wani salo idan ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login