Showing 15001 words to 18000 words out of 91747 words

Chapter 6 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

797

cin karo da wanda ya amsa sunan maza sama da kai ba.
  Tabbas ko a Sojojin ma kai Hamshaƙin Soja ne."

  Murmushin gefen baki ya yi kana ya shafa fuskarta har zuwa kan laɓɓanta, anan ya shiga kewaya hannunsa akan laɓɓan nata, kamar mai koyon magana ya fara magana "Ina son wanan!" Ya faɗa yana kai bakinsa cikin nasa.
  Sai da ya tsotseshi son ransa kana ya miƙe a hankali, ya ɗauketa kamar 'yar baby ya shigarta Toilet, da kansa ya yi mata wanka ya naɗota a cikin tawul, ya fito da ita.
  Zama yayi ya shafeta da mai sanan ya ɗauko ƙananun kaya ya sa mata.
"Kin fi kyau a lokacin da ba kwalliya a fuskanki. Ina ji kamar na shafe rayuwata ina kallon kyawawan idanuwan nan naki My Amrah!"

Hannayenta ta sanya ta rufe fuskarta da shi, ɗaukanta ya sake yi ya futo da ita har wajen daining sanan zaunarta shima ya zauna, da kansa ya ciyar da ita abincin sanan ya ci nasa, duk da ƙoƙarin son bashi da tayi, amma ya dakatar da ita.
  "Akwai lokaci, zan zauna ki bani, amma yau ni zanyi wanan aikin."

  "Ina sonka Hubbinah!"

"Na sani!" Ya faɗa yana kai loma bakinsa, harara ta aika masa wanda ya sashi yin murmushi.
  "Kai ko yaushe ba'a faɗa maka kalma ka ce kaji daɗi sai dai kace ma ka san da ita."

Tsayar da cin abincin da yake ya yi yace "Tun kafin ki faɗi magana idanuwanki na sanar dani, shima kafin ya zo zuciyarki ta sanar da tawa.
  Nifa dace akayi na zama soja amma ni asali fasihi ne." Ya faɗa yana gwalonta, cokali ta ɗauka zata ƙwala masa gayi saurin tashi yabar wajen, a haka ta bishi suna zagaye falon.
  Daga ƙarshe dai ya faɗi ta haye kan cikinsa tana masa cakulkuli "Zaka ƙara?"

  Kai ya girgiza mata yana dariya sosai abun da ya shagalar da ita kenan sa kallonsa, sanin bata taɓa ganin dariyarsa ba sai murmushi ko yaushe.
  A hankali ta kai bakinta kan nasa daga nan salon wasan na su ya sauya zuwa duniyar sama.

🌷🌷🌷🌷

#IG
#Dabanne
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨

®NWA

©OUM-NASS

WATPAD @Oum_Nass

Ga masu son cigaba zasu iya samun shi ta kan Prize haka

Ya koma Na kuɗi
idan ta bank Ne #200
300₦ katin mtn
Zaku iya biya ta nan,
Acct: 0472282105
Ramlat Abdul Rahman Manga
GT BANK

SHA ƊAYA

KADUNA, NIGERIA

"Abdul lokaci ya tafi da yawa, idan muka tsaya jiran ra'ayin Imran na tabbata mu ne zamu sha kunya akan wanan lamarin." Anty Aisha ta faɗa bayan barin Ummie daga falon.

"To yanzu me kike ganin ya kamata mu yi?" Abdul ya faɗa yana kallon Anty Aisha ɗin.
"A madadinsa zaka je ka yi bikon Fatima, ka bama iyayenta haƙuri akan abun da ya faru."

Shuru yayi na ɗan lokaci, daga bisani ya ɗago da kallonsa gareta "Anya kuwa za su amince Anty Aisha? Musamman idan kikayi duba ba wanan ne karo na farko da matsalarsa ke korar Fatima daga gidan nan ba.
Kusan a yanzu ma haƙurinta ne ya gaza har ta iya taka ƙafa ta bar gidan nan."

"Ka dai jeka ɗin, koma me zai faru za su sanar da kai yiyuwar dawowarta ta ko kuma zamanta a gidansu. Amma nasan babu wasu iyayen da za su so zaman ɗiyarsu a gidansu bayan an aurar da ita."

Kai ya jinjina sanan ya tashi "Shikenan zan je na shirya ko zuwa magrib ne sai na je gidan in sha Allah."
"Allah ya yarda."
Daga nan ta juyar da kallonta kan sauran 'yan uwanta "Ku baku da abun magana halan?"
Murmushi sukayi duka a tare, wanda yake nuna tsantsar kamarsu "Me zamu ce tunda babbar yaya ta gama maganarta?"
"Baku da ƙorafi kenan akan halayyar Imran?"

Dariya sukayi mai sauti wanda ta ƙara fito da kamarsu a zahiri, duk da cewa itama Aishan na ɗiban kama da su, amma ta su daban ce, wanda idan ba saninsu kayi ba bazaka tan-tance kamarsu ba.
"Ƙorafi akan Imran wani abu ne da ya daɗe da xama wucecce, musamman idan mukayi la'akari da abun da ya sameshi a baya.
Sanin kanki ne dama can ba damuwa yayi da halayyar mutane ba balle kuma a yanzu da yake jin zamansa shi ɗaya yafi masa komi jin daɗi.
Kinaga dai hatta kasuwancinsa ma a gida yake tafiyar da shi."

"Duk da haka dole sai mun tsaya mun taro shi kana ya dawo hayyacinsa.
Kun dai san Ummie ba komi zata nuna ya sosa mata rai ba, musamman akan abun da ya shafi Imran da ko yaushe take masa kallon soyayya da tausayawa.

"Anty Fatima me zamu iya yi masa a yanzu? Bayan ya dakatar da aikinsa mafi soyuwa a gareshi! Ko kin manta har gida hukumar lafiya ta biyo shi akan ya koma aikinsa na Likita, wanda duk faɗin garin nan shine babban likita a ɓangaran mata da kuma dashen zuciya.
Amma duk da haka yace bai da ra'ayin wanan. Kina ganin a yanzu akwai wani abu da zai so?"

Shuru suka yi na ɗan lokaci, bata ƙara magana ba ta tashi ta haura sama inda ɗakin Ummie ta ke.
Kamar yanda ta yi tsammani samunta ta yi a zaune ta haɗa tagumi, idanuwanta na zubar hawaye, ƙarasawa tayi cikin sanyin jiki, ganin mahaifiyarsu a cikin wanan yanayin.

Dafa ta tayi hakan yasa Ummie ɗagowa ta yi saurin goge fuskarta tana maye wajen damuwarta da murmushin yaƙe "Aisha tafiya za ku yi ne?"

Kai ya girgiza tana zama kusa da mahaifiyar tasu "Ummie har sai yaushe ne zaki daina ɓoyewa kina kuka aka matsalar Imran? Ni a ganina wanan ba itace hanyar da zata ɓulle da mu ba.
Ke ya kamata ki sauya masa rayuwa a matsayinki na mahaifiya a gareshi."

Fuskarta ta sauya tana fuskantar Aisha cikin sanyin murya ta fara magana "Aisha a matsayina na uwa ina jin ƙuna da raɗaɗin yanda rayuwar Imran ta tarwatse a sanadin ɗan ƙaramin kuskuren da nayi.
Ko wata uwa takan tsayu ta zama bango jinga ga rayuwar yaranta, amma kuma ni sai na zama uwar da ta yi silar tarwatsa wanan bangon.
Ki faɗa min ta wata hanya ne zan iya taimakawa Imran? Bayan da kaina na ruguza masa ko wani sa rai da ya ke da shi.
Ta ina hawaye zai bar zuba a kwarmin idanuwana, bayan na zama silar zubar hawayen mutane da yawa.
Sam ba zan iya ba." Ta faɗa tana girgiza kanta, hawaye na ci gaba da sauƙowa a idanuwanta.

"Ki daina faɗar ke ce sila Ummie! Duk abun da ya faru da rayuwar Imran dama can Allah ya ƙaddara masa zai same shi ne.
Ke gyara kika so yi ba wai wargaza musu rayuwa ba. Ki daina damun kanki Ummie, ki manta da abun da ya riga ya faru, mu gyara gabon da take kusantowa garemu."

"Idan na manta da goben ya zanyi da FATIMA? Ko kina so ki ce min itama ta zama cikin labaran JIYA?"

Ɗagowa Anty Aisha ta yi tana kallon Ummie itama kallonta take cikin salon jiran amsar da zata bada.....

*********

ƘAUYEN TONI.

Burum aka turo ƙofar ɗakin da suke ciki, wanda ya sa Khadijatu ƙara ƙanƙame Ishaƙ, jikinta ya ƙara tsananta daga rawar da yake yi.
Shi kansa ya tsorata daga yanda yaji an turo musu ƙofar ɗakin, hakan ya tabbatar masa da wanda ya turo ba ƙalau ya ke ba.

"Lahaula wala ƙuwwata illa billah! Kun ga irin abun da nake faɗa muku ko? Ku zo ku gane min abun da idanuwa na yake gani?"

Muryar da ya ji yasan mamallakiyarsa, ko ba'a faɗa masaba yasan Babba ne.

Ido ya runtse yana ƙara buɗeshi, ko ba'a faɗa masa ba yasan abun da ya kawo su, da kuma dalilin da yasa shi rafka wanan sallatin.

"Ni dama nasan tunda maganar nan ta ke zagaye tana dawowa nasan akwai ƙamshin gaskiya a cikinta. Ƙarin daɗawama da ya zo yake batun barunsu garin nan a yau. Jama'a ku tayani ganin abun da ke faruwa da idanuwanku, kun dai ga ba sai an sanar da ku ba." Babba ya faɗa yana ƙara kutso kansa cikin ɗakin dan bawa mutanensa damar ganin abun da ya ke faɗa.

"La'ilaha illahu lahhu, muhammadur rasulillahi! Kai jama'a wanan duniya ina zaki damu haka?" Mutanen sa suka faɗa suna shigewa ɗakin da ba zai iya ɗaukansu duka ba.

Jin ihun maza da salatin da suke yi yasa Khadijatu ƙara damƙe Ishaƙ "Na shiga uku Yayana za su kasheni!" Ta faɗa cikin rawar murya.

Shima ƙara damƙeta ya yi yana ji kamar ana shirin ƙwace masa ita "Ba za su kasheki ba khadijatu! Dan rayuwarki ba'a hannunsu ta ke ba.
Ni na tabbata Allah yana tare da mai gaskiya."

MUryarsa da AMO mai ƙarfi take futa, yana ji ko wani tsaro da ke zuciyarsa na fucewa a cikin zuciyarsa.

"Da kyau! Gar da ka tabbatarwa da duniya cewa kai tantirin ɗan iska ne. Kamar yanda itama ƙanwarka ta miƙa wuya da abun da kake bata.
Yanzu ba sai an jimaba za mu fudda mugun iri a cikinmu.
Mu futa ku cunnawa ɗakin nasu wuta ku ƙone harda su....." mAI GAri ya faɗa yana fucewa a ɗaki.
Nan take matasan da suke jiran takife suka futa da sauri suka ɗauko kanazil suka fara sawa a jikin ɗakin har da jikin su ISHAƘ da suke dunƙule a waje ɗaya, ba abun da ke futa a idanuwansu banda kuka da hawaye, a zuciyarsu suna ambaton Allah Yayin da warin kanazil ɗin ya bugi Khadijatu, nan take numfashinta yake futa sama-sama.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Alhmdulillah!
Tofa anan na kawo ƙarshen Free page.
Karku manta yanzu ne aka fara labarin Inuwar Gajimare, har yanzu bamu da tabbacin waye yama khadijatu fyaɗe? Wa zai ceci rayuwarsu a lokacin da ake gaf da cinna musu wuta? Me yasa Khadijatu ta suma? Me ne Labarin Imran da Mahaifiyarsa? Ya labarin soyayyar Amrah da angonta Aabid? Tukunna ma me yasa labarin ya zama INUWAR GAJIMARE??

Duka zaku samu amsoshinku a tare da ni, babu tsada #200 ɗinki ta wadace mallakarsa. akwai tsagwaran girmamawa a tare da ni.

Za kuyi screen short Ku tura ta wanan number 08030990232 WhatsApp only

#IG
#DABANNE

OUM-NASS
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: IG

Oum-Nass

0012

   Hankalin Ishaƙ ne ya ƙara tashi ganin yanda numfashin Khadijatu ke sarƙewa, sai wani gunji take tana fuzgarshi, jikinta kuma ya fara saki daga ruƙon da ta masa.
 
   "A'a Khadijatu! Kada kiyi saurin tafiya ki barni! Ba abun da zai same mu!Ba abun da za su iya yi mana! Dan Allah Khadijatu ki dawo ki bari mu tafi tare, kada ki karaya! Karki tafi ki barni."

   Numfashi ta ja da ƙarfi, nan take jikinta ya saki, a dai-dai lokacin da Mai gari ke cewa "Kuyi sauri ku cinnama ɗakin wuta."
  Wutar suka wulla akan ɗakin nan take wuta ta kama ci kamar da gayya take hayaƙi ya mamaye ɗakin, baka jin sautun kome sai na tashin wutar. Su kansu mutanen da ke wajen sun tsorota da yanda wutar ke tashi sama, hakan ya sa suka yi saurin barin gidan harda mai gari da yake ji kamar zafin na ƙona fatar jikinsa.

      "Ka kula min da Khadijatu! Kada ka bari ta yi kuka maraici Ishaƙ!" Wanan kalmar yake ji tana masa amsa kuwwa a ɗakin Kamar a lokacin ake faɗa masa ita.
  Ido ya runtse yana jin zafin wutar na ratsa ko wani sassa na jikinsa, ga wutar da ta gama cinye rufin ɗakin tana shaftowa tana faɗowa tsakar ɗakin.
  Wawurar zanin Khadijatu ya yi da ya mata shumfuɗa ya lulluɓeta da dukka Zannuwan, kayan jikinsa da suka jiƙe da kanazil wuta na wawuro shi, duk yanda ya duba a ɗakin babu hanyar da zai futa, ko ina wuta ta gama kewaye shi.
  
  Idanuwansa ya kai ga tagar da ke ɗakin, itama a kewaye ta ke da wuta dalilin Kanazil ɗin da ke jikinta.
  "Wanan ce kawai damata! Dole ki rayu Khadijatu ko da ace ni zan rasa tawa rayuwar." Ya faɗa yana cicciɓar kaɗijatu da iya ƙarfinsa ya ɗorata akan kafaɗarsa, yana riƙe da ita da hannunsa ɗaya.
  Buga windon ɗakin yayi da hannunsa, nan take katakon ya ɓalle wuta kuma ta biyo hannunsa, yatfe hannun nasa ya shiga yi amma cikin rashin sa'a wutar ta kama fatarsa, wata sabuwar azaba ya ji ta sauƙa tun daga tsakiyar kansa har zuwa ɗan yatsan ƙafarsa.
  Saurin ratsawa ya yi ya wundon yana shigar da Khadijatu wanda har lokacin bata fudda numfashi, shi kansa ya riga da ya sare da rayuwa, burinsa ɗaya a yanzu ya ceci rayuwar Khadijatu, ko bai rayuba to yana buƙatar Khadijatunsa ta rayu.

    Da ƙyar ya iya shigar da ita, wutar da take ci ta kama zannuwan da ya rufeta, amma duk da haka bai fasa kiciniyar fiddata ba, a hankali ya zurata waje, yayin da shima ya futo da iya ƙarfinsa, bayan gidan ya kewaye da su, cikin zafin nama ya yaye zanin da yake ci da wuta, ya warɓar da bokitin waje, kana ya tafi wajen tulun da suke zuba ruwa ɗauko, cikin sa'a akwai ruwa a cike a cikinsa, ajiye shi yayi da yaji akwai ruwa a cikinsa, kwanciya yayi a ƙasa ya fara burgima a cikin rerayin da yake gidan, yana kaiwa yana kawowa, har sai da wutar jikinsa ta mutu.
 
  Daga nan ya ɗaga ruwan tulun ya kwara a kansa tun daga tsakiyar kansa a hankali yake jin sanyinsa na ratsa fatarsa yana jin zafin dake fatarsa na raguwa.
  Rage ruwan ya yi kusan rabi ya kwarama Khadijatu a jikinta, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauƙe ba tare da ta buɗe idanuwanta ba.
  Shima ajiyar zuciyar ya saki yana matsowa kusa da Khadijatun ya rungumeta ƙam, sai a lokacin Kuka ya zo masa.

  "Kaico! Kaicon rayuwar da babu iyaye a cikinta! Kaicon rayuwar da ta cika da zargi da son zuciya! Me yasa mutane suke da gaggawa? Me yasa babu wanda ya tsaya yaji labarin gaskiyar da ke tare da mu? Dan Allah Khadijatu kada ki mutu ki barni kema! Kada ki barni ni ɗaya maraya a wanan duniyar! Ina buƙatar rayuwarki Khadijatu! Ina ƙwarara numfashina a yau saboda ke Khadijatu! Dan Allah kema ki daure ki rayu ko saboda ni ne!" Ya ƙarasa maganar yana ƙan-ƙameta ko ina a jikinsa ya yi fata-fata, kayan jikinsa sun gama yin duƙun-duƙun, sun yayyafe sakamakon wutar da ta gama cinsu ta cinye.

   Babu komi da ya yi saura a tare da shi, idan aka ɗauke Numfashin da ke gareshi, wanda yake ta ƙoƙarin sai-saita shi dan kada ya tafi ya barshi.
Sai Khadijatun da ya sanya a gaba yake fatan ta farka, duk da yaji numfashin da ta ja, amma har a lokacin bai ƙara yarda cewar tana numfashinba, zuciyarsa ta daɗe da gama tsinkewa, duk sa ran da yake da shi a rayuwarsa ya gama yanke tsammani akansa.

   Ɗorata ya yi akan cinyarsa yana kallon ɗakin da suke fito a cikinsa, shi kansa yasan ikon Allah ne ya fidda su a cikinsa, musamman da ɗakin yake ruftawa da kansa yana faɗawa, ginin da dama ya ɗauke shekaru babu gyara a tare da shi, ƙarfinsa ya gama ƙarewa, duk da ginin ƙasa ne hakan bai hanashi kassarewa ba.

  Daga inda yake yana jin hayaniya da ihun mutanen garin, yana jin kalmar aibatawa da suke jifansu da su, da yawa kuma suna yima kansu barka da suka rabu da mugun iri.
  
  Yau kam ya yarda basu da kowa a duniya, ya kuma ƙara yarda duk duniya basu da masoyi, basu da bangon da za su kara su jinga a jikinsa.
  Ya zai yi da Khadijatu a yanzu? Ta ina zai nema mata maganin cutar da take damunta?
  Hannunsa ya kai cikin aljihun da ke wandonsa, babu komi a ciki sai tuttushin da yaji a ciki. Yana kai hannunsa yaga ba burbuɗin kuɗin da ya ajiye, shi kansa aljihun ya riga ya ƙone babu alamunsa an taɓa yinsa a jikinsa.

  Yawu ya haɗiye mai ɗaci yana jin kansa na barazanar rabewa biyu saboda sarawar da ya yi masa.
  "Shikenan ta faru ta ƙare!"Ya faɗa cikin raunin muryarsa, yana haɗe kansa a jikin na Khadijatu da jiran tsammanin yanda rayuwa zata ƙara yi da su.

********
LAGOS, NIGERIA

  ARMY BARECK

Sojojine burjuk ta ko ina sun yi layi suna gudanar da bitarsu ta ƙwarewa, fuskokinsu babu walwala ko kaɗan, ko wanne a fusace yake yana jiran tsammani.

  Daga gabansu kuma Kanal Aabidullah Isma'il ne ke basu horo fuskarsa babu walwala ko kaɗan, asalima yana yi yana duba agogon da ke maƙale a hannunsa.
  Tsaki ya yi mai ƙarfi ganin yanda lokaci ya ja sosai gashi suna da sauran  lokaci kafun su tashi.

   A gaggauce yaci gaba da ba su horon  su kansu sun san ya na da uzuri shi yasa ko ya mutum ya yi kuskure futo da shi yake ya sashi tsallen kwaɗo yana binsu yana musu bulala.
  Wanan dalilin yasa da yawansu suke kokawa tun bayan gabatar musu da Kanal Aabidullah a matsayin mutumin da zai ba su horon aikinsu.

  Wayar hannunsa ce ta yi ƙara, ganin wanda ya kira yasa shi ɗaga musu hannu da alamun kowa ya tafi, a gaggauce ya hau mashin ɗinsa wanda shine abun da yake jin daɗin hawansa  fiye da mota, saboda yana jin iska na ratsa sassan jikinsa.

  Ajiyar zuciya suka saki sanan suma suka bar wajen suna ji kamar an sauƙe musu wani gungume akansu.

  ******
KADUNA, NIGERIA.

 
  "Abdul wanan ba shine karo na farko ba. A matsayina na Uba bazan ci gaba da tauyewa ɗiyata haƙƙinta ba. a farko nayi wanan kasadar, duk da ina da tsammani akan gidan da na kai ɗiyata.
  Sai dai kuma na yi dana sani daga baya, musamman da ya kasance ban ƙaru da komi a lamarinba sai baƙin ciki.
  A yanzu kam ba zan ƙara shiga maganar nan ba, idan har Imran yana son matarsa to ya zo da kansa, ina da tambayoyin da nake so na yi masa. Ina son sanin dalilin abun da ya shiga tsakaninsa da Fatima."

   Kai Abdul ya gyaɗa cikin gamsuwa da maganar Mahaifin Fatiman, shi kansa yasan ya yi ƙoƙari, dan ba ko wani uba ne zai juri ganin ɗiyarsa cikin ƙunci ya ƙyale ba. Ko yanzun ma ya fahimci tura ce ta kai bango yasa ya dakatar da ƙudurinsa.
  "Abba ko zan iya ganin ita Fatiman?"

Shuru ya yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya tashi tsaye "Bari na turo maka ita."

  Ya faɗa yana barin falon da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login