Showing 33001 words to 36000 words out of 91747 words

Chapter 12 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

795

yaushe ya ɗaga wayar sai ya tambayi waye? Ko kuma yace 'Ta wata hanya zan taimaka ma?' tun yana jin haushi har ya zo ya daina ji, musamman da ya fahimci hakan halayyarsa ce da ba zai ita dainata ba.

    Bayan Mintuna goma Nurse's suka zo suka ɗauki Khadijatu zuwa ɗakin da za'a mata aikin. Hankalin su duka ya tashi musamman Ishaƙ da ya ke binsu yana riƙe da hannun Khadijatunsa.
  Ina tunanin kamar wanan shine lokaci na ƙarshe da zai sake ganinta, aiki za'a mata aikin da bai san ta ina ake yinsa ba.
   Kansa ya dafe a jikin bango bayan Nurse's ɗin sun dakatar da shi daga bin bayansu da yake.

     Addu'a ce fal bakinsa sai ya kamo wanan sai ya saki ya kamo wancan. A hankali suka fara jiyo taku na kusantowa garesu da kuma wani sassanyan ƙamshin da basu taɓa jin irinsa ba.
  Jin shurun da yayi na salatin da Ammu take shi ya sashi saurin juyowa dan ganin abun da ya sashi wanan salatin.
  Gabansa ne yayi mummunan faɗuwa ganin wata ɓoyayyiyar fuska a jikin wani mutum da ke kusantowa garesu, yana tafiya kamar baya son yi,  idanuwansa sarƙafe a jikin farin gilashi.
   Har ya zo ya gifta su ya shige ɗakin da aka kai Khadijatu, Kansa yaji yana sara masa da ƙarfi kamar zai ɓalle daga maɗaukarsa. Yayin da idanuwansa suka shiga tariyo masa inda ya taɓa ganin mamallakin wanan fuskar.

    🌷🌷🌷🌷

   Inuwar gajimare na Kuɗi ne idan kunyi karo da shi ku kimanta martabar da ke gareku. Kafin ka kira abu namu dole sai ya zama naka kai ɗaya.
Ina baku haƙuri dai idan kunga error's da yawa bana samun damar yi muku editing ne.

  
idan ta bank Ne #200
300₦ katin mtn
Zaku iya biya ta nan,
Acct: 0472282105
Ramlat Abdul Rahman Manga
GT BANK

GIRMAMAWA[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

   0000023000000

Kansa ya riƙe da hannuyensa saboda tsananin zafin da yake masa da sarawar da yake yi masa.
   Duhu ke ratsa hasken da ya cika idanuwansa yana ganin mutanen da ke wajen suna ninkuwa daga bibbiyun da suke zuwa wasu adadin da bai san yawansu ba.

   Iska yaja da ƙarfi yana zamewa daga tsayuwar da yake yana zama, idanuwansa kuma duka ya rintsesu da dukkanin ƙarfinsa.
  Da sauri su Ammu suka iyo kansa suna kiran sunansa amma baya jin ko kalma ɗaya dake fitowa a bakinsu, sai motsawar da bakunansu yake yi kaɗai yake gani.

    "Likita! Likita!" Baban Indo ya shiga xurma musu kira kamar zai tada asibitin gaba ɗayanta.
  Da sauri wasu likitoci guda uku suka zo da gado suka ɗauki Ishaƙ suka shigar da shi wani ɗakin da ke kusa da wanda aka kai Khadijatu.

   "Ya Allah ka sassauta mana." Ammu ta faɗa tana matse hawayenta.

   "Ameen" suka amsa a tare. Daga nan babu wanda ya sake yi musu magana.
 
    ****
Bayan Awanni biyu.
 
   Da ɗai-ɗai Likitocin da suka shiga yima Khadijatu aiki suka fara fitowa anan su Baba da Ammu suka tare su suna tambayar "Ya aikin? Tana lafiya dai?" 
  Fuskokin Likitocin da fara'a sosai a cikinsu "Ku jira Dr. Imran." Suka faɗa suna matsawa daga gefen da suke.
  Shine fitowar ƙarshe a cikin ɗakin shi da wata Nurse da ke bin bayansa riƙe da fayil ɗin aikin nata.
   Yanzu kam ya rufe fuskarsa da mask   idanuwansa har lokacin sanye suke cikin farin hilashi, sai safar hannun dake maƙale a cikin hannunsa yana ƙoƙarin cireta.
  
   "Likita ya ɗiyarmu take ciki?"

  Bai yi magana ba ya karɓi fayin ɗin da ke hannun Nurse ɗin ya yi ɗan rubuce-rubuce a cikinsa "Ki kai su wajen Dr. Saleem ya musu bayani." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa ba tare da ya ɗago kai ya kalle su ba.

    Raɓawa yayi ta kusa da su zai wuce, amma kuma sai yaga an sa hannu an kare shi, hannun yabi da kallo kafin ya ɗago da idanuwansa yaga wanda ya datse masa hannunsa "Me yasa wani ne zai mana bayani, bayan kai ne ka yima ɗiyarmu aiki."
   Dattijuwar muryar Ammu ta bigi kunnuwansa, a hankali ya ɗago da kansa ya ɗorashi akan fuskarta. Gabansa ne yayi mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Hakan ya sashi saurin matsawa daga kusa da ita ya fuce a wajen cikin tsananin sauri ba tare da yayi magana ba.

     Baki buɗe suke bin bayansa da kallo, wasu likitocin ne suka fito da Khadijatu  daga ɗakin da aka mata aiki, zuwa wani da ke gefe ɗaya. Yayin da su Mairama suka bi bayansu har zuwa ɗakin da suka kaita, wanda ke matsayin nata ne wararre kuma, komi akwai a ɗakin tun daga kan na'urar sanyaya ɗaki da kuma gado, sai fararen kujeru guda biyu a gefe, da 'yar ƙaramar loka.
  Daga gefe guda kuma banɗakine a cikin ɗakin.
  "Nan shine ɗakinta da zata xauna har zuwa lokacin da zata samu lafiya. Ku zo muje wajen Dr. Saleem ya muku sauran bayanin." Nurse ɗin ta faɗa bayan sun kwantar da Khadijatu da take barci, hannunta sanye da drip ɗin ruwa, sai wata roba da aka jona mata a ƙasanta (*catheter*)

  "Sai kuna lura da wanan robar ta jikinta, saboda kada ta zame a jikinta." Nurse ɗin ta sake faɗa tana nuna musu robar da hannunta.
  "In sha Allah." Suka faɗa a tare.

  Futa suka yi su biyu Ammu da Baban Indo sun bar Mairama da Indo tana kula da motsin Khadijatu za su je suga likitan da zai musu jawabi.
     Office ɗin Likitan da ya fara duba su suka koma anan Nurse ɗin ta miƙa masa fayil ɗin tana risinawa "Dr. Imran yace ka musu sauran bayanin, shi ya riga da ya tafi."

   "Ok! Ku zauna." Ya musu nuni da ɗaya daga cikin kujerun da suke zagaye a ɗakin.
  Zama suka yi suna fuskantar sa ya buɗe fayil ɗin ya na duba abun da Imran ya rubuta.
Gyara farin gilashin da ke kan fuskarsa "Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara, yanzu abun da ya rage shine bin ƙa'idodim aikin da aka mata domin gujewa komawa gidan jiya.
Daga yanzu idan zata tashi tsaye dole ku kula kada ta miƙe gaba ɗaya, sanan kada ku bata abinci mai nauyi, saboda ba'a so taci abin da zai sata yin nishi mai ƙarfi yayin tsugunno. Shi kuma nishi mai ƙarfi zai iya warware aikin da aka mata saboda kusancin da ke wajen da inda aka mata aikin.
Abincin cinta zai zama mai ruwa-ruwa haka, sai kuma ɗanyen kifin da za'a dafa maya.
Waɗan nan sune dokokin da ya kamata ku kula da su."

"In sha Allah Likita, mun gode sosai." Daga haka suka fice a ɗakin suka barshi. Yana binsu da Addu'ar Allah ya sauwaƙe.

****

A hankali ya buɗe idanuwansa yana kallon silin ɗin dake jikin ɗakin, tashi yayi zaune ransa duk ba daɗi, a hankali tunanin abun da ya faru da shi ya dawo masa sabo. Fuskar mutumin ce ta ƙara dawo masa akan idanuwansa.
Tabbas ya san mutumin, kuma duk inda ya sanshi ba wai ƙaramin sani ya masa ba, yana ji kamar ya ɓata wasu lokuta masu tsawo ne a tare da wanan mutumin.
Tashi yayi ganin babu kowa a ɗakin ya fito waje, anan yaga Baban Indo na tahowa, da sauri ya ƙarasa kusa da shi "Assha! Kai da baka da lafiya me ya fito da kai Ishaƙ?"
"Na warke Baba. Ina Khadijatu?"
"Tana ɗaki na musamman ne! Dama nazo na dubaka ne naga ko ka farka, ashe ka tashi har ka fito. Taho muje." Ya faɗa yana riƙe da hannun Ishaƙ.
A hankali yake sake kallon wajen da ya ga tahowar mutumin yana ji kamar zai sake ganinsa ne, sai dai har suka shiga ɗakin baiga alamunsa ba, ko mai yanayin tafiyarsa babu.

Da sallama suka shiga ɗakin, Indo ce kaɗai ta samu zarafin amsa musu sallamar amma banda Ammu da ta rafka tagumi.
Kusa da ita Ishaƙ ya ƙarasa ya zauna, sai ya ɗan tureta wanda hakan ya sata saurin zabura "Ya dai tsohuwa? Kina tunanin zan tafi na barki ba masoyi a duniya ko? To gani nan na dawo da sauran lokaci."
Harara ta buga masa sanan ta yi tsaki, tana juyar da kallonta ga Baban Indo "Ado nikam idanuwana sun fara gane-gane ne ko kuwa mugun gamo nayi?"
Kallonta yayi cikin rashin fahimta "Me kika gani Ammu?"

"Abdallah na gani yanzu Ado! Abdallah na gani ya shiga ɗakin tiyatar Khadijatu."

Hular kansa ya cire da yaji ta jiƙe sharkaf da gumi "Kema kin ganshi kenan Ammu."
"Ƙwarai da gaske na ganshi da fararen kaya ya shige ɗakin da aka yima Khadijatu aiki. Da na fara tunanin idona ke min gizo amma da yazo giftawa sai naga hatta tafiyarsa iri ɗaya ce sak da ta Abdallah."

"Amma kuma bamu ga fitowarsa ba ai Ammu har muka bar wajen. Wanan ne ya bani mamaki ya ɗaure min kai."

Shuru ne ya cika ɗakin na ɗan lokaci ba wanda ya sake magana, can suka tsinkayi muryar Indo "Nifa Yunwa nake ji Baba, kana biya gane-ganen wanan tsohuwar ƙila wani aljanin ne ma tayi gamo da shi."
"Ungo nan Indo! Uwar tawa kikema wanan shaƙiyancin haka?" Baban Indo ya faɗa yana aikama Indo daƙuwa.
Dariya Ishaƙ ya tuntsire da ita ganin yanda Ammu ta gwamutsa fuska ba tare da ta kula Indo ɗin ba.
"Kai nima dai nafi yarda Ammu ta yi gamo yau, ka duba kaga yanda ta sauya lokaci ɗaya, har ana mata magana tana ƙin bada amsa."

Bakinsa yaji an buge wanda ya sashi saurin ruƙe bakin "Ka fita a idanuwa na rufe Isiyaku! Yau ban son ɓuruntu da yasasshen zance ne, idan kuma so kuke nayi yanzu zanyi maganinku anan."
Tashi yayi daga kusa da ita ya koma can kusa da Mairama "Inna saifa kuna haɗa mata da Addu'a yau naga ta sauya da yawa."
Ya faɗa cikin sigar raɗa, murmushi Inna ta yi tana kallon gefen da Khadijatu ke kwance, har a lokacin barci take, fuskarta tayi fayau ta rame sai dogon hancinta ya fito ya ƙara tsayi, gashin idonta yayi zara-zara a cikin zagayayyun idanuwanta masu yalwar girma. Shima kallonta yayi nan take gabansa ya faɗi, yayi saurin juyowa ya kalli Ammu da har lokacin bata janye hannunta daga tagumin da ta buga ba.

Matsawa yayi kusa da jikin gadon Khadijatu ya shafa fuskarta, anan yaga kamar idonta na juyawa da alamun son buɗe su.
"Ta farka Inna!" Ya faɗa ciki fara'a.
"Ko dai ka tasheta ba jarababen yaro! Annan ɗinma tashinta zaka nayi a barci kamar yanda kake mata angida ko? Ni wanan masifa da me tayi kama ni Hasiya?"
Ammu ta faɗa cikin masifa wanda yasa Ishaƙ ƙumewa, dariyar Indo ce ta sa shi ƙara jin haushin abun da Ammu ta masa.

"Wallahifa Ammu, anan ɗinma sai ya nuna mana halinsa."
"Innah kina jin yarinyar nan ko? Zan bige mata bakinta." Ishaƙ ya faɗa cikin fushi da zafin rai.
"Ki fita idona na rufe Indo, ina ruwanki da shi?"
"Babu tsakina ma Innah, amma ƙato dashi yana hana yarinya barci ai abun a duba ne shima." Ta ƙarasa maganar tana rufe bakinta.
A fusace ya taho da niyar dukanta ta shige bayan Ammu "Ammu kina ganifa yanda ya tashi Khadijatu, amma dan bai son gaskiya shine zai zo ya dakeni."

"A kul ɗinka Isiyaka da dukar min jika. Yo wani ja'irin ne yace ka tasheta tana barci bayan likita mai fararen kaya yace abarta ta huta. Ni banga ma amfanin biyomu ba da an barka kaje ka ci gaba da sara ƙasa da tsince ciyawa ai."

Nunfashinsa ne ya fara sama saboda ɓacin ran da yake damunsa, sai jan numfashi yake yana fuzgar da iska. Wannan dama halayyarsa ne duk lokacin da ransa ya ɓaci sai numfashinsa ya riƙe, sai yana jan iska da ƙarfi.
A da sai ya daɗe baiji ɓacin raiba da haushin mutum, amma yanzu kuma da ya san zafin jikinsa da mu'amalantar mutane ba wuya zuciyarsa ta hassala. Ashe a bayanma dan bai damu da mutane ba ne shi yasa ransa baya ɓaci da su.

Tashi Baba Yayi ya shiga shafa bayansa yana bubbuga kafaɗar "Ka silace maza, ka huce yayan Khadijatu da Aishatu, angon Ammu ko bata so. Allah bar maza ko dan mata su rayu kamar tsuntsaye!"
Dariyace ta kamashi jin kirarin da Baba yake masa " Ja'irin bawa!" Inna ta faɗa cikin dariya itama.
Dariyar da suke gaba ɗaya ita ta haddasa tashin Khadijatu a tsorace nan ta kurma wani razanannen Ihu wanda yasa dukansu suka iyo kanta suna kiran "Khadijatu!"



******

Tun da ya dawo daga asibitin zuciyarsa ba daɗi, matar da ya gani a gabansa yake ta gani a yanzu.
Tashi yayi tsaye cikin sauri ya shige ɗakinsa nan ya dinga jifa da komi da ke cikin ɗakin, yana zazzage tarin takaddun da suke ɗakin yana ɗaukansu yana dubawa yana jifa da su.
Ko ina a ɗakin ya haukace, wani abu yake son dubawa amma bai ganshiba bai kuma san inda ya kai shi ba.
Gajiya yayi ya zauna a cikin ɗakin anan ya haɗe kai da gwuiwa a waje ɗaya.
Shurun da taji babu alamunsa tun bayan shigowarsa gidan shi ya bata damar tashi ta duba ɗakin. Ganin yanda ya shigo gidana a hargitse bai amsa mata ko da sannu da zuwan da take masa ba.
Wanan wani abu ne da ta manta rabon da ta ganshi a tare da Al'ameen ɗinta, tun bayan dawowarta gida rayuwar aurensu ta gyaru suke yinta cikin kulawa duk da har zuwa yau bata taɓa jin kalmar so a bakinsa ba amma kuma babu ƙiyayya a idanuwansa.
Tana tura ƙofar ɗakin taga ɗakin kaca-kaca, ko ina ta duba takardune a ciki.
Gabanta ne yayi mummunan bugawa "Al'ameen!" Ta kira sunansa da ƙarfi dan ko alamun inda yake bata gani ba.


🌷🌷🌷🌷


IG na kuɗi ne, idan tsautsayi ya riskeki samunsa ki killace Kimantawarki, ki martaba kanki a matsayinki na mai aji, ki guji kallon abun da ba mallakinki ba ne hakan ya zama rauni a gareki da kuma tawaya.

Oum-Nass
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG



00000240000

Hango shi tayi ya haɗe kai da gwuiwa sai juya kansa yake a jikin gwuiwarsa.
Da sauri ta ƙarasa kusa da shi tana jijjiga shi da iya ƙarfinta "Al'ameen me ya sameka?" Ta faɗa a ruɗe jikinta har ɓari yake kamar mazari.

Ɗago da kansa yayi anan idanuwansu suka haɗu waje ɗaya, a tsorace ta matsa baya ganin yanda idanuwansa ya sauya kala daga farin da ta sanshi da shi zuwa jajaye.
"Me ya faru Imran?" Ta faɗa cikin rawar murya, bai iya mata magana ba ya fara ƙoƙarin tashi akan ƙafafuwansa.
Wayarsa ce ta shiga ƙara wanda ya sashi kallon saitin inda yake jiyo ƙaran nata, tashi Fatima tayi ta ɗauko masa wayar ta miƙa masa lokacin kiran har ya katse, wani kiran ne ya sake shigowa Dr. Saleem ya gani akan wayar hakan ya sashi faɗuwar gaba mai tsanani.
A hankali ya ɗaga wayar ya kara a kunnensa "Dr. Imran akwai matsala a asibiti! Marar lafiyarka ta farka sai ihu take da fuzge-fuzge ina jin tsoron kada wani abun ya samu aikin da aka mata."

Bai bashi amsa ba ya katse wayar ya fice da saurinsa yabar Fatima na tambayarsa 'me ya ke faruwa?" Amma bai tsaya bi ta kanta ba ya bar gidan zuciyarsa tana tsalle kamar zata faso a ƙirjinsa.
Gudun da yake ya taka muhimmiyar rawa wajen isarsa asibitin akan lokaci, duk da tarin cinkoson da ya tadda a hanya amma hakan bai hana shi zuwa a ɗan ƙaramin lokaci ba.
Tararsa Dr. Saleem yayi da sauran Nurse's a hanya "Mun kasa riƙeta mu yi mata koda allura ne Dakta, tun da ta farka takr ihu tana ƙan-ƙame jikinta a waje ɗaya, ta gaza bamu damar kula da ita yanda ya kamata." Dakta Saleem ya faɗa a lokacin da suke tafiya da Dakta Imran.
"Nan ne ɗakin." Dakta Saleem ya faɗa ganin yana shirin wucewa ɗakin.
Shiga ɗakin yayi a hankali idonsa ne yayi tozali da ita da yanayin da take ciki, ta takure waje ɗaya tana wurwurga idanuwa. Yau babu wanda ta iya saurara banda kuka babu abun da take tun bayan farkawar da tayi.
Ƙarasawa kusa da ita yayi yana musu nuni da hannu akan su matsa daga inda take, matsawa sukayi duk suna kallon fuskarsa kansu duka ya ɗaure da sake ganinsa.

"Baby!" Ya faɗa da sanyin muryarsa, ɗago da kanta tayi tana kallonsa ganinsa kusa da ita sosai, ya sata saurin sakin razanannen ƙara "Dan Allah ka matsa kusa da ni kada ka cuta min!" Ta ƙarasa maganar cikin karkawa da rawar murya.

"Ba abun da zan mikifa zan dubaki ne na gani."
Kai ta shiga girgizawa "A'a ni bana so! Dan Allah kada kaima ka cuta min.
Yayanah!" Ta faɗa da iya ƙarfinta.
Da sauri Ishaƙ ya ƙarasa kusa da ita ya ruƙe hannunta "Gani Ƙanwata ba abun da zai sameki Khadijatul Ishaƙ!"

A razane Dakta Imran ya juyo da kallonsa zuwa kan Ishaƙ ɗin, Ido ya fiddo waje ganin fuskar da ke jikin ta yaron, sanan ya maida kallonsa ga Mararar lafiyar da ke gabansa.
"KHADIJATUL ISHAƘ?" Ya faɗa cikin sigar tambaya wanda bai san ya faɗi tambayar ba.

Kai Ishaƙ ya ɗaga sama "Ƙanwata ce, tun lokacin da ta samu larurar nan ta ke yawan zabura da tsorata, ko wani mutum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login