Showing 84001 words to 87000 words out of 91747 words
"Eh na sani Yallaɓai! Ina son doka tayi aiki a kaina dai-dai da laifin da na aikata, kamar yanda Allah s.w.a ya faɗa a cikin alƙur'aninsa "Mazunaci da mazunaciya budurwa ko kuma saurayi a musu bulala tamanin, idan kuma sun kasance masu aure a jefesu har sai sun mutu."
Kai Alƙalin ya gyaɗa har a lokacin mamaki ne shumfuɗe akan fuskarsa "A yayin da duniya ta cika da mutane masu aikata laifi suna ɓoyewa, kai kuma sai ka bayyana kanka dan a maka hukunci dai-dai da abun da ka aikata.
Ban san waye kai ba yaro, amma naji a zuciyata duk yanda akayi kai mutumin kirki ne, bani labarin yanda ka aikata wanan kuskuren a rayuwarka."
Kamar ba zai yi magana ba can kuma ya basu labarin abin da ya faru har xuwa yau da ya kawo kansa.
"Allahu Akbar! Allah al-hakimu." Shine abun da Alƙalin ya ke ta nanatawa.
"Duk da ta yafe min Yallaɓai ina jin tsoron kada wani abun ya sake biyo baya, kada zunubin da na aikata ya sake waiwayar rayuwata a karo na biyu."
"Tabbas kayi gaskiya yaro. Yanzu tun a duniya Allah ke sakawa mutanen da aka cuta kafin aje lahira. Lallai kai kayi sa'a kana kuma da babban rabo da har ka samu suka yafe maka."
Kallon Yaronsa yayi "Maza ka sanar da sarkin bulala ya shirya, zamu shafe wani dattin da ke manne da fata."
Da sauri Yaron nasa ya futa duk da jikinsa babu ƙwari, jin tausayin Aabid yake na taɓa zuciyarsa. Ya daɗe baiga wanda yayi tuba mai kyau irin na wanan matashin ba.
Bayan wasu lokaci suka zo shi da wani kakkauran mutum baƙiƙƙirin da shi fuskarsa babu wanzuwar fara'a a cikinta. Ko ina a jikinsa a murɗe yake, ga kuma wata murɗaɗɗiyar dorunar da ta sha mai tana walƙi a hannunsa.
Kallo ɗaya Aabid ya masa bai ƙara sha'awar sake kallonsa ba.
Da hannu alƙali ya nuna masa Aabid "Ka masa bulala tamanin." Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga Aabid ɗin.
"KWANTA!" Murɗaɗɗen mutumin ya faɗa da muryarsa mai shirin fasa kunnuwa.
Ba musu Aabid ya kwanta ya runtse idanuwansa yana jiran sauƙar bulalar a fatar jikinsa.
Idonsa ya wara da ƙarfi saboda jin bulalar da yayi a jikinsa, a hankali ya sake lumshe idanuwansa, saboda ji yayi tun daga tsakiyar kansa har zuwa yatsan ƙafarsa bulalar ke ratsawa.
A haka maɗaukin bulalar ya ci gaba da zuba masa ita a jikinsa da dukkanin ƙarfinsa, kafin a gama sai da rigarsa ta rine da launin jini, yayin da wajen da aka fiya dukansa ya yayyage.
Ya ɗauki tsawon lokaci kwance a wajen kafin ya iya tashi, yana jin bayansa kamar ba nasa ba, raɗaɗin da ke sauƙa a jikinsa yana huda ko wata ƙofa ta jikinsa.
"Nagode Yallaɓai." Ya faɗa da sautin muryarsa marar amo yana murmushi akan fuskarsa.
Kai Alƙalin ya gyaɗa yana girmama juriya irin ta mutumin, da aka gama dukansa amma babu ƙwalla ko kaɗan a idonsa balle yayi ihu.
"Allah ya kiyaye gaba, ya amshi tubanka yaro, ya baka zuri'a mai albarka da tsafta."
"Ameen Jazakallu khairan." Ya faɗa yana ficewa a ofishin alƙalin.
Ƙarfinsa da kuzarinsa yayi ƙasa sosai amma haka yake ƙoƙarin yafa dauriya a zuciyarsa. Musamman da idanuwansa suka yi masa karo da mutanen da ke binsa da rakiyar ido.
Motarsa ya shiga ya mata key ya fice a harabar kotun bai tsaya ko ina ba sai gida.
A hanya ya sake samun kiran ogansu akan neman da ake masa a wajen aikinsa, haƙuri ya bashi ya sheda masa rashin lafiyar da ke tare da shi tun bayan rasuwar 'yarsa.
Ya tausaya masa sosai ya kuma ƙara masa makwanni uku akan wanda yayi ada amma bayansu ba'a buƙatar wani uzuri daga gareshi.
Godiya ya masa yana jin daɗin halaccin da suka masa, aikin soja aiki ne da basa samun hutu a rayuwarsa, wanda tsananin hutunsu baya wuce sati biyu a shekara, amma shi ya samu fiye da watanni ɗaya.
A hankali ya futo a motarsa bayan mai gadi ya wangale masa get ɗin shiga gidan, bai wani yi mata fakin mai kyauba haka ya fito ya nufi ɓangaransu, a hanya yaci karo da MOM ta rako Dad saboda bakin aikinsa da zai fara fita a ranar.
Da mamaki suka kallonsa cikin ruɗewa suka iyo kansa "Aabid me ya sameka? Me ye wanan a bayanka?"
Murmushi yayi yana kallon bayan nasa da ya gama jiƙewa da jini, ga kuma rigarsa da ta fatattake saboda tsabar duka "Ba komi fa ku kwantar da hankalinku."
"Kamar ya zaka ce mana ba komi bayan ga shatin bulala nan raɗo-raɗo a bayanka. Wani marar imanin ne ya maka wanan dukan Aabid?" Dad ya faɗa idanuwansa na taruwa da hawaye, ko ina a jikinsa rawa yake saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Mom kam tuni har ta fara kuka, tana ƙara juyo da bayan Aabid ɗin.
Hannunta ya kawar yana share mata fuskarsa "Ba komifa Mom ki kwantar da hankalinki, naje an kaɗai min dattin da ke jikina ne, an kankare min ƙurar da ta manne a jikina. Kotu na kai kaina aka min hukuncin da akema duk wanda ya aikata zina saurayi! Kawaifa bulala tamanin aka min ba wani abu mai zafi ba."
Dafe ƙirjinsu sukayi a tare suna wara idanuwansu kafin su fara salati da hailala a fili.
"Aabid me yasa ka yanke wanan ɗanyen aikin ba tare da ka yi shawara da mu ba? Khadijatu ta riga da ta yafe maka ba buƙatar ka je ka kai kanka a jima wanan ciwon." Dad ya faɗa cikin tsananin tashin hankali hawayen da ya taru akan fuskarsa ya samu damar sauƙowa.
"Khadijatu ta yafe min Dad na sani. Amma bani da tabbacin Allah ya yafe min, ina tsoron kada abun da ya faru da Noorie ya sake faruwa da wani daga cikin ahalina ko dangina Dad." Yana gama faɗar haka ya ratsa ta gefensu ya wuce ya barsu, baki buɗe.
Zama Dad yayi ya dafe kansa yayin da yayi jifa da hularsa, a cikin rayuwarsa bai taɓa ganin tashin hankali kamar na yau ba, me yasa saboda ɗan ƙaramin kuskuren da ɗansa yayi yake ta shan wahala a kansa.
Anya kuwa ba ƙwaƙwaluwarsa ta samu matsala ba? Ta ya mutum da hankalinsa zai kai kansa ga halaka yana sane?
Kansa ya jingina a jikin kujera hawaye na silala akan fuskarsa, da alamu ciwon ne a jikin Aabid amma kuma zafin na jikinsa ne.
"Alhaji me kake yi haka ne?"
"Ki barni na huta Hajiya. Ki barni na samu nutsuwa ko na bar jin abun da nake ji."
"To amma futar office ɗin fa?"
"Na fasa." Ya faɗa yana wurgi da 'yar jakarsa a ƙasa.
"Allah ya kyauta." Ta faɗa tana bar masa filin palon.
****
Lokacin da Aabid ya shiga ɓangarensa kai tsaye toilet ya shige ya haɗama kansa ruwan ɗumi ya yi wanka, sosai yake jin raɗaɗi da zugi na ratsa shi, bayan futowarsa ya ga Amrah a ɗakin nasa ta ɗaga rigarsa tana jujjuyawa.
"Me ya faru da wanan rigar Aabid?"
"Adalci." Ya faɗa yana tsane gashin kansa da ɗaya tawul ɗin da ke cikin ruƙonsa.
"Adalci?" Ta faɗa cikin sigar tambaya.
A hankali ta ɗaga ƙafarta zuwa wajensa, bayansa ta duba taga shatin bulala ya faffasa masa fatar jikinsa. Gashin jikinta ne ya miƙe yayin da zuciyarta ta buga da ƙarfi "Na shiga uku me ne wanan a bayanka Aabid? Kamar duka fa."
"Ba kama ba ne dukane."
Kanta ne ya kule ta rasa abun da zata faɗa kafin ta yi magana ya tareta "Na kai kaina kotu Amrah na amshi sakamako dai-dai da laifina. Ki taya ni roƙon Allah akan ya yafe min ya amshi tubana." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa da ta fara rawa.
Kuka ne ya kufce mata nan take ta rungumeshi tana ƙara sautin kukanta, bayan ta ya shiga bubbugawa yana jin jikinsa kamar ana datsa shi sanadin zazzafin da ya rufe shi.
"Jikinka zafi Aabid!"
Kai ya gyaɗa mata yana ƙoƙarin zamewa daga ruƙon da ta masa, kwanciyar rubda ciki yayi akan gadon nan take jikinsa ya tsananta "Lulluɓe ni Amrah." Ya faɗa muryarsa na rawa..
Da sauri ta ɗauko ƙaton bargo ta lulluɓa masa kuka na cin ƙarfinta, a guje ta sauƙa ƙasa ta shedama Mom Aabid ba lafiya, Likitan family ɗinsu ta kira bai fi muntuna ashirinba ya zo da kayan aikinsa, yasha mamaki ganin yanda bayan Aabid yayi har ya fara faɗan wane ya masa wanan dukan.
Shuru sukayi basu bashi amsa ba sai Dad da yayi magana "Kayi aikinka kawai."
Shuru yayi bai sake magana ba ya duba shi ya jona masa ƙarin ruwa sanan ya bashi maganunnuwa da kuma wani da za'a na shafa masa a bayan nasa.
Ya tafi yana mai musu fatan samun sauƙi.
Sai da yayi sati guda yana fama da rashin lafiya sanan ya samu ya warke shatin bulalarma ya bar zugi sai tabonsa a jikinsa, a cikin kwanakin sunga tashin hankali sosai a gidan, domin kowa baya barci akansa suka kwana saboda gani suke kamar shima zasu iya rasa su.
A cikin kwanakin kuma Iyayen Amrah suka kawo musu ziyara kamar yanda suka alƙawarta mata, sosai suka yi murna ta rasa ina zata sa kanta saboda farin ciki.
Gaba ɗayansu suka zo harda Nabil. Anan yake basu labarin an yanke aurensa da Khadijatu nan da wata ɗaya za'ayi.
Ihun murna Amrah tayi ta ƙanƙame yayan nata, "Wow masha Allah ashe muna da raƙashewa. Har naji inama na janyo kwanakin nan wallahi."
"Yanzu ne ai ƙanwata, duk abun da aka sa masa rana saurin zuwa gare shi." Ya faɗa yana shafa kanta.
Hannayen Aabid ta riƙe tana kallonsa da ya yi shuru kamar an dasa shi a wajen zuciyarsa banda bugawa ba abun da ta ke "Da gaske dai Khadijatu ta kuskure masa?"
"Ya kamata naje naga Khadijatu mu saba kafin lokacin Yaya."
Murmshi yayi yana kallon Aabid da ya futa a hayyacinsa kamar bai san me suke tattaunawa.
"Ya kamata dai kam, dan kinsan ni ba zan kawo miki ita nan garinba, ya mata nisa zata wahala. Idan kun matsu kuje har gida ku ganta."
Kallon Aabid tayi da bai yi magana ba har lokacin asalima kamar bai san akan me suke magana ba "Kace wani abu mana Aabid." Ta faɗa tana girgiza shi.
Furgigi yayi ya kalli su Abbu da suke kallonsa sai ya ƙaƙalo murmushi "Zamu je mu ganta ai dole. Ko banza tayi nasarar raba abokina da titi da gangar gwauraye." Ya faɗa cikin sigar dariya da kuma ƙoƙarin danne ciwon da ke cikin zuciyarsa.
Dariya duka mutanen palon suka sa, idan aka ɗauke Nabil da ya cika ya batse.
"Haba abokina me ne na damuwa bayan ka kusa samun 'yanci." Aabid ya sake faɗa cikin sigar tsokana, hakan ya sa shi yin dariya.
"Ba komi ka faɗi duk abun da kake son faɗa lokacinka ne."
Anan su Dad suka sake yin dariya.
Sun sha hira sosai wadda mafiya yawan hirar tasu akan bikin Nabil ɗinne, da kuma yanda ya kamata tsarin bikin nasu ya kasance.
Shi dai Aabid ji yayi duk zaman ya isheshi gashi ba damar ya tashi a gane abun da ke damunsa, dole ya danne zuciyarsa ya zauna aka ci gaba da tattaunawa da shi.
Yanda suke labarin bikin sai ka ɗauka gobe ne za'ayi auren. Wata ƙila kuma saboda shine biki na ƙarshe da za'ayi a gidan nasu.
Kwanansu ɗaya suka yi shirin tafiya har airport su Mom suka rakosu sai da suka ga tashinsu sanan suka dawo gida, Amrah ta damu Aabid akan ya kaita taga matar yayanta, Duk da ta ganta a hoto amma tana son ganin fuskarta, tunda Yaya Nabil yace mata yasanta har gidansu ma ya sani.
"Ki shirya gobe sai muje. Amma kwana ɗaya kawai za muyi mu dawo." Tsallen murna ta shiga yi masa tana raguza jikinsa, ɗan kuzarin da ke gareshi ta so kadawa.
Abun da ya manta tashinsa ya miƙe a gabansa, shi har ya manta yaushe ma rabon da yaji sha'awar mace, duk da xasu kwanta su tashi da Amrah a waje ɗaya.
Lallai ya yarda ba abun da ya kai tashin hankali a duniya, abun da yake tunanin ba zai iya kwana guda bai yi shi ba, sai gashi ya yi watanni bai yi ba. Lokacin da jikinsa ya haɗu dana Amrah sai da yayi kuka, kuka mai yawa yana ƙara roƙonta yafiyarsa. Yana ji a zuciyarsa Khadijatu ta masa nisa, gara ya riƙe abun da ke gareshi tun kafin shima ya kuskure masa.
Itama ɗin kuka take domin gani take kamar an sauya mata Aabid ɗinta, duk wani karsashin da ke gareshi ya gudu ya barshi.
"Lallai Allah mai hikima ne akan komi."
Washe gari zuciyarsu fes suka tashi, kamar yanda ya mata alƙawalin zuwa ganin Khadijatu, sun shirya tsaf direba ta kai su airport suka ɗauki hanyar Kaduna.
Zuciyarsa na buga kamar zata yi tsalle ta faɗo, yayin da Amrah ta cika kunnuwansa da labarin Khadijatu tana siffanta yanda kamar matar Yayanta xata kasance "Nabil mai kyau ne, nasan matarsa zata zama ta musamman. A yanda naga hotonta nasan ganinta zai fi hotonta ƙawatuwa."
Idonsa ya lumshe yana kokawa da zuciyarsa, yi yayi kamar barci ya ɗauke shi. Har jirginsu ya sauƙa bai nuna ma Amrah wata alamar da ke nuna idanuwansa biyu ba. Ganin idonsa a rufe yasa itama ta tsuke bakinta ta kwantar da kanta akan kafaɗarsa take barci ya ɗauketa dama ta gaji da yawa.
Lokacin da jirginsu ya sauƙa yasha mamaki ganin Ishaƙ ya zo ɗaukansu "Abun mamaki ya akayi kasan da zuwanmu?" Aabid ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Nabil ne ya sanar da ni zaku zo kai da ƙanwarsa ganin Khadijatu."
Juyo da kallonsa yayi ga Amrah, kai ta gyaɗa masa tana dariya "Ai na zata ita zata zo ɗaukanmu da kanta." Kafin ta yi shuru kuma ta hango wata kyakkyawar budurwa na futowa a motar "Ya rabbi wanan ce matar Yayanah?" Amrah ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita.
"A'a madam kin saɓa lamba wanan tawa ce." Ishaƙ ya faɗa cikin barkwanci yana kallon Aisha da ta ke hararsa.
"Sannunku da zuwa." Ta faɗa tana buɗe musu bayan motar.
Ajiyar zuciya Amrah ta sauƙe "Amma dai ke ƙanwarta ce ko yayarta? Koma dai tagwaye ne ku? Naga kamarku ta so xuwa ɗaya."
Murmushi Aisha tayi tana gyaɗa mata kai ba tare da tayi magana ba "Kai masha Allah! Lallai yayana ya iya zaɓi."
"Amrah wai ke bakinki baya shuru ne?" Aabid ya faɗa yana haɗe fuskarsa, saboda ji yake zuciyarsa na tafasa, yana jin dama basu zo ba.
"Nayi shuru, amma dai kasan ba zan iya gani na ƙyale ba ko?"
Harara ya buga mata wanda yasa ta ruƙe bakinta tana dariya.
Shima Ishaƙ sai matse dariyarsa yake dan a yanda yake ganin wata wuta na futa a idon Aabid ya fahimci kishi ne ke cinsa. Banda abunsa wanda ke da Mace kamar Amrah ai bazai sha'awar neman wata ba, dan ba ƙarya kyakkyawa ce ita ajin farko a sahun kyawawan.
A hanya suna tafe bata dai yi shuru ba ta ci gaba da tambayar Aisha da Ishaƙ akan Khadijatu sudai sai amsa suke bata da eh ko a'a.
Tun shigarsu gidan Amrah take baza idon ganin Khadijatu amma babu ita babu alamunta.
Har sai da suka shiga palon anan sukaga mutanen gidan, sosai suka samu tarba mai kyau akan fuskarsu. Family ɗin sun ƙayatar da Amrah sosai sai suke mata kama da nata ahalin.
Amma duk da haka ido take bazawa tana son ganin ta inda Khadijatu zata fito.
A hankali suka fara jiyo takun takalmi na kusantowa garesu, hakan yasa suka maida kallonsu ga inda takun yake fitowa, sanye take da atamfa ƙirar kamfanin holland a jikinta da aka mata ɗinki doguwar riga a jikinta, ƙafafuwanta sanye da farin takalmi yayin da ta yane kanta da farin gyale a kanta. Fuskarta babu kwalliya a cikinta sai kwalin da ta sa a idanuwanta, da farin man laɓe. Yana da mutuƙar wahala ta yi kwalliya da ta wuce wanan.
Tunda ta sauƙo Amrah ta miƙe tana buɗe da bakinta, ita kanta tafiyarta ma abun birgewa ce balle ƙirar jikinta, a matsayinta na mace mai aji taji Khadijatu ta tafi da zuciyarta.
"Ya Rabb! Ashe gaskiyar Yayana da ya kusa yi mana hauka." Amrah ta faɗa taana raɗama Aabid da ya kusan yin suman zaune, ƙoƙarin janyo da numfashinsa yake yaji kamar ana ruƙe masa shi.
'Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Ya Allah ka kare ni kada na aikata abun kunya anan!' Aabid ya faɗa a ƙasan zuciyarsa.
Har zuwa lokacin da sassanyan murayr Khadijatun ta ratsa dodon kunnensa, ya nemi komi da ke kansa na shirin ficewa da gudu.
Bai tsinke da lamarinba sai da yaji Amrah ta cika masa dodon kunne da ihu a lokacin da ya ɗaga kansa ya ganta a cikin ruƙon Khadijatu ta ƙanƙameta kamar zata mayar da ita cikinta.
🌷🌷🌷🌿🌿
Assalama alaikum.
Ya kuke ya aiki, haƙiƙa naji daɗin addu'arku, jikin mamana kuma da sauƙi, nagode ƙwarai.
GIRMAMAWA.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG .....
58000
Idanuwansu ne suka sarƙe da na juna a lokacin da ya ɗago da kansa yana ganinta, wani mahaukacin kyau yaga ta ƙara yi masa akan idanuwansa, saɓanin wanda ya santa da shi.
"Ya Allah!" Ya faɗa yana ƙoƙarin jan numfashinsa a lokacin da ta aika masa da kyakkyawan murmushi.
Sun ɗauki lokaci rungume da juna kafin daga bisani Khadijatu ta zame jikinta daga na Amrah.
"Maraba da zuwa ƙanwata." Ta faɗa cikin haɗaɗɗiyar muryarta mai tafe da aji nutsuwa a cikinta.
"Bismillah zauna." Khadijatu ta sake faɗa tana mata nuni da kujerar da ke gabanta.
A tare suka zauna anan