Showing 78001 words to 81000 words out of 91747 words

Chapter 27 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

814

ya lotsa "Ba wanan sauƙin nake tambayarka ba. So nake naji kace min zuciyarka ta ƙarfafa tun lokacin da ka fahimci ɗan ƙaramin hakkin da ka raina ya baka wuya."
Kallonta yayi cikin rashin fahimtar abun da take faɗa "Me kike son faɗa min?"
Kallon su Mom tayi "Dan Allah ko zaku iya bamu waje muyi magana da shi?"
"Me zai hana 'yata." Suka faɗa suna ficewar har da Imran ɗin shima da zuciyarsa bata kwanta da hakanba.

Shi dai Aabid kallonta yake cikin tsananin soyayya. Murmushi ta masa sanan ta fara magana.
"Zan baka wani labari ne akaina, lokacin da na je asibiti wani likita ya nuna kulawarsa a kaina, duk da cewa ba ɗan ƙasar bane, asalima aikin da yake baya wuce sau biyu a wata, amma a dalilina ya koma rayuwa a asibitin gaba ɗaya.
Ya rufe ko wani abu da zai taso masa da zai sa shi barina a lokacin. Duk wata kulawa da ake kira da sunan kulawa ya bani ita, ciki harda lokacinsa, farin cikin. Ya zamar da matsalata tashi, daga baya kuma bai duba ɓarnar da ka minba, bai damu da tawayar da ka saniba, a hakan dai ya gabatar da ni a gaban iyayensa suma sun nuna min soyayya kamar ɗiyar da suka haifa ta cikinsu.
Wanan ya sa na manta da cutar dani da kayi, na rufi babinki a cikin shafukan labarina. Musamman da nake sonsa kamar raina! Nake girmama duk wani abu da ya zo min da shi."
Ido ya lumshe yana jin wani ɗaci na tasowa tun daga zuciyarsa har zuwa bakinsa, jin kalmarta ta ƙarshe na tana sonsa.
Maganarta ce tasa ya sake buɗe idanuwansa "Aabid abun da ka min a rayuwata ya riga da ya wuce, na yafe maka tun kafin ka gabatar da fuskarka a gabana. Abun da kawai na kasa cirewa a raina shine me yasa bayan ka aijata min mugunta ka tsallake ni ka tafi duk da kasan ka barni bana numfashi? Me yasa baka sake waiwayar rayuwata kaga ina raye ko na mutu ba? Wani laifi na aikata maka da ka min haka? Shin wani ne ya turoka ko kuwa dan kanka kazo gareni? Waɗan nan sune tambayoyin da suka kasa ɓacewa akaina."
Kai ya girgiza a lokacin hawaye na zuba akan fuskarsa, shi kansa ba zaice ga dalili guda ɗaya da yasa ya tafi ya barta ba, kamar yanda bashi da uzuri akan dalilinsa na ƙin dawowa wajenta asalima ya manta da babin rayuwarta.
"Kaga wanan zafin da kake ji a zuciyarka, namu ya danne shi nida yayanah! Amma a haka muka danne muka ci gaba da fafutuka da rayuwa duk da ba mu san ina zamu je ba? Bamu san kuma ina zata kaimu ba."
Hawayen da ya taru akan fuskarta ta share da hannunta "Idan har ni a matsayina na mace zan iya danne wannan ciwon da ɗacin, inaga kaima mai sauƙi ne a gareka ka cire soyayyata a zuciyarka, kasancewar ba alkhairi ne ya haɗamu da kai ba tun a haɗuwarmu ta farko. Ina kuma da yaƙini akan wanan karonba ba alkhairin ne zai sake haɗamu ba duk da cewa kalmar aure ta shiga maganar.
Kai namiji ne da kake ɗauke da nauyin mutane uku a kafaɗunka, mamanka babanka da kuma matarka. Kai ne kake da babbar zuciyar da zaka ƙwararata dan ka baasu kulawa, kamar dai yanda yardarsu take a kanka.
Ni na ƙarfafa zuciyata na rayu dan yayana me zai hana kaima ba zaka manta dani ba ka rungumi ƙaddararka. Domin ƙaddararmu bata a tare da kai Aabid.
Dan Allah ka manta dani, kada ka bari Zuciyarka ta rinjayi tunaninka. Na maka abun da ka kasa bani, ka kashe min ƙaramin hasken da ke rayuwata, yayin da ni na kunna maka hasken da ya ɗauke a taka rayuwar.
Dan Allah ka dawo min da hasken da ka karɓe a gareni, ta yanda zaka ɗauke alhakin mutuwarka akan soyayyata." Ta ƙarasa maganar tana haɗe hannayenta biyu a waje ɗaya.

Murmushi yayi fuskarsa ya fahimci Khadijatu ta masa nisa, nisa na har abada, amma duk da haka ta martaba soyayyarsa a gareta.
"Shikenan Khadijatu! Kija kiyi rayuwarki ta farin ciki da wanda kike so. In sha Allah zan ƙarfafa zuciyata wajen kawar da tuhumarki a matsayin silar ciwona.
Amma dan Allah kada kice zaki rabu dani gaba ɗaya, ki bani damar yin zumunci da ke da ahalinki koda ta fuskar gaisuwa ne."
Kai ta gyaɗa masa tana murmushi sannan ta miƙa masa hannunta "Abota kawai!" Shima hannunsa ya miƙa mata ya haɗu waje ɗaya.
"Abota kawai!" Shima ya faɗa yana murmushi.
Sakar mata hannu yayi "Zan sake zuwa mu dubaka ni da yayanah!" Ta faɗa tana tashi akan ƙafafuwanta.

"Nagode sosai Khadijatu." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

Murmushi ta masa itama "Kai dai ka tabbatar ka rayu kafin mu dawo."
Ido ya lumshe mata yana buɗesu daga haka ta fice tabar ɗakin ya bita da rakiyar ido.....


🌷🌷🌷🌷

Jiya ban baku ba yau ga breakfst nan idan Allah yasa na samu lokci anjima za ku sake jina, amma fa hakan ba yana nufin zan muku ba ne. Ya danganta da lokacin da na samu da yawaitar chag a wayana.


GIRMAMAWA
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG....

54000

"Umhmm ke nake sauraro madam!"

"Mu zauna!" Ta faɗa tana nuna masa kujerar da ke tsakiyar palon.
  Kallon Kujerar yayi kamar ba zai zaunaba sai kuma ya je ya zauna ba tare da yayi magana ba sai kafeta da idanuwa da yake yi.

  Murmushi tayi sanan ta kawar da kallonta daga gareshi "Musulunci ya bamu tambari mai kyau da kyakkyawar nagarta ta yanda zamu kira duk wani musulmi da ɗan uwanmu.
Sanan Annabinmu ya koyar da mu ribar haƙuri da kuma fifikon daraja dake cikin yafiya a duk lokacin da aka cutar da kai.
  Habibey naje wajensa ne saboda kare kimar aikin mahaifina na tsawon shekaru, naje ba tare da neman shawara ba saboda aikin Allah ba ya buƙatar tattaunawa.
  Hakan ba yana nufin zan yarde ma buƙatarsa ba ne. Asalima duk duniya inda za su taru akan kalmar soyayya bazan ji ba, saboda kunnuwana sun riga da sun toshe da jin kalmar tun daga bakinka.
  Zuciyata kuma ta cika da ƙayoyi da karmami ta yanda babu wanda zai ƙarasa gareta balle ta amsa muradinsa bayan kai.
  Mahaifina mai ceton rayukan mutane! mijin da zan aure mai kawar da matsalolin mutane. Taya zaka tsammaci zan so mutumin da ke kashe rayuka, ya datse jijiyon kyautatawa, wanda ke tsaye a bakin iyaka. Ban shirya rayuwar furgici ba, ban da zaɓi akan duniyar fargaba."
  Tunda ta fara maganar yake kallonta har zuwa yanxu da ta kai ƙarshen maganarta. Zafin da yake ji a ƙirjinsa ya koma yayi sanyi, lokaci mai yawa yana mamakin yanda baya iya yin fushi da Khadijatu, domin koda ace yayi fushi kalma ɗaya take faɗa ta daƙusar da ƙumajin da ke gareshi.
  "Me kike son faɗa min?"
Idonta ta lumshe ta buɗe sanan tayi murmushi "Kai kaɗai ne kake sarrafa zuciyata."

  Murmushi yayi shima cikin jin daɗi ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, sanan ya sosa sumar da ke kansa "Wayo kike so ki min?"

  Bakinta ta rufe da hannunta "Ni na isa? Wayo da kansa idan ya ganka guduwa yake Habibey. Kaga kenan Khadijatu ta gaza ace ta maka wayo."
  "Yaushe bakinki ya buɗe haka?"
Kanta ta kawar tana kallon sashen da Ishaƙ yake ashe tuni yabar musu palon, shima juyawa yayi yaga baya nan "Yaushe wanan ya tafi?"
"Lokacin da kake tuhumar ƙanwarsa."

   Dariya yayi sanan ya tashi akan ƙafafuwansa yana kallon agogon da ke saƙale a jikin hannunsa "Gashi ban gaji da ganinki ba, lokaci ya min tafiyar angulu da yawa."
  Fuskarta ta sauya itama cikin yanayin damuwa "Sai nake ji kamar rayuwata ke shirin kuskurewa daga gareni."
    Hannayensa ya harɗe a ƙirjinsa yana kallon kyakkyawar fuskarta da baya gajiya da kallonta tsawon rayuwarsa.
  Lokuta masu yawa yana mamakin irin soyayyar da yake yiwa Khadijatu, yayin da yake ganin baikin mutanen da suke kiran soyayya na raguwa a duk lokacin da kuka daɗe da mutum. Amma kuma shi a nasa ɓangaren ko wata rana yana jin soyayyar Khadijatu na nunkuwa a zuciyarsa, yana jin bugawar zuciyarsa na tafiya da soyayyarta.
  "Ban san me yasa nake jin babu daɗiba a duk lokacin da na zo kuma zaan tafi na barki! Hakan na tunasar da ni jinkirin da nayi akan kasa mallakarki a ɗan ƙan-ƙanin lokaci, ta yanda zan maidake futular dubawa ta.
  Ina sonki Khadijatu fiye da yanda nake jin futar kalmar a bakina! Dan Allah Khadijatu koda ace hali yayi na sabunta rayuwa da duniya kada ki guje ni! Kada ki juya min baya."

  Duk wata kalmar da ya faɗa yana ƙara narkar mata da zuciya, tana jin saƙon da ke futa daga laɓɓansa yana hudda ƙirjinta, yayin da take jin ƙofofin kwanyarta na bitar karatun da yake bata.
  A hankali ta ƙarasa kusa da shi tana kallon idanuwansa "Har abada Khadijatu ba xata guje ka ba Nabil! Sai dai ni ke da tan-tama akan me ya kaini soyayya da balaraben miji wanda mata suke rubibinsa, kada na killace kaina wata kuma ta kallar min kyakkyawan saurayina."

  Dariya yayi mai sauti itama tana tayashi dariyar "Kabar dariyafa Habibey ina ga zan amso ma Niƙaf a gida ka sanya kana yawo! Ko naje kasuwa na siyoma dozin."

  Ido ya fiddo waje daga haka ya janye daga kusa da ita ya nufi hanyar waje "Na lura so kike 'yan hisbah su kama ni! Sai munyi waya Azizaty." Ya faɗa yana ɗaga mata hannunsa.

  Itama hannu ta ɗaga masa tana murmushi dan tasan idan har ba haka ta masa ba bazai tafi ba, duk da cewa itama ba son tafiyarsa ta ke ba, amma kuma akwai wani nauyi da ke kanta da ya kamata ta sauƙe, shine alƙawarin da ta ɗauka ma Aabid.

   A gurguje ta shiga ɗaki tayi wanka ta sauya kaya daga doguwar riga zuwa atamfa da siket. Ta yane kanta da gyale ta fito palo, wanan yana daga cikin ɗabi'arta da wuya ta futo koda palo ne babu gyale a jikinta.

   Ɓangaran Ammu ta shiga anan ta tararta a zaune ita da Aisha da Nabil sai Inna suna hira, wanan yana daga cikin al'adarsu duk yammaci a ɗakin Ammu suke zama suna hira.
  " 'Yar agaji an dawo ashe?" Ammu ta faɗa tana aika mata da harara.

  Murmushi tayi ya kalli Inna "Barka da Yamm Innah!" Ta faɗa tana zama kusa da Ishaƙ.
  "Barka dai 'Yatah. ya gajiya?"
Kai ta girgiza kawai ba tare da tayi magana ba "Ni naga tunku ma ƙarewar dunkumewa. Aikin banza kawai." Ammu ta faɗa kamar zata make Khadijatu.
  Dariyarta take ƙoƙarin dannewa sanan ta yima Aisha alama da ido "Sahiba zamu koma asibiti ki shirya mu fita tare."
  Miƙewa Aishan ta yi da sauri "Yanzu kuwa 'yar uwata."
   "Asibitin uwar wa xaku je? Me zaku ɗauko acan.Kinga Khadijatu ki kiyaye ni, ki fita idona na rufe." Ammu ta faɗa tana ajiye kofin da ke hannunta.

  "Yayana harda kai! Kai ne zaka kaimu kaji?" Ta faɗa yana langare masa kai.
  Kansa ya kara a kunnenta "Ko baki ce ba dole na biku! Dan yanxu ina ƙoƙarin Cimma nasara ta ne." Ya faɗa yana tashi a kan ƙafafuwansa ya fice a ɗakin.

  Salati Ammu ta ke tana kallon Innah da take ta danne dariyarta "Kina jin za su haukata ni amma ba zaki musu magana ba."

   "Bari naje na kawo miki turaren da nake  baki labarinsa." Ta faɗa tana danne dariyarta da tashi a wajen 'Ni na isa shiga maganar nan ƙarshe ki barni a cikinta.' Ta faɗa a zuciyarta tana barin wajen.
   "Ammu kema idan zaki ki shirya muje."

  "Allah ya ɓoyi kurwata ba inda zani. Ku dai da xaku iya ku sauƙa ƙalau."

  Tashi tayi bayan su Ishaƙ sun futo cikin shirinsu, "Bye Ammu!"
  Ko kallo basu isheta ba haka suka fice suka barta.

  Bayan sun futa suka yiwa su Fatima sallama anan tace taje ta karɓi saƙonta a wajen mai aikin abincinsu.
  Tana zuwa ta tadda kulolin abinci ne  guda uku ashe taji lkcn da ta ce zasu je asibitin, shine tasa aka musu farfesun ɗanyen kifi da kuma jalof ɗin kuskus, sai ɗayan da aka yayyanka kayan frut a cikinsa aka jefa ƙanƙara.
Ido ta lumshe tana girmama lamarin Antyn nasu, bata ɗauka zata mata wanan karramarwa ba duk da a zaman da sukayi da ita harara bata taɓa shiga tsakaninsu ba, asalima soyayya take nuna musu suna kawar da kai.
Futa tayi tama ma'aikatan alama da su biyota da shi.
Suma su Ishaƙ sunyi mamakin ganinta da wanan kayan "Anty Fatima!" Kawai ta faɗa suka gane abun da take nufi.
Bayan motar ta shiga da sauri ta rufe anan Aisha ta yi narai-narai da ido, murmushi Ishaƙ yayi ya zagaya ya buɗe mata gidan gaba "Shiga madam." Ya faɗa yana sunkuyar da kai.
Murmushi ne ya suɓucema Aisha hakan yasa ta shiga cikin motar, sanan ya rufe ya zagaya mazaunin direba ya tada motar.
A hanya suna tafiya yana kallon Aishan "Har yanzu banji amsar saƙona ba Madam! Idan horani ake ya kamata a faɗa min na bada haƙuri." Kai ta kawar gefen glass ɗin tana kallon yanda motoci suke wucewa.
"Ko maganar sai na siya ne?" Nanma ya sake tambayarta.
"Ya Ishaƙ mana!" Ta faɗa tana masa nuni da Khadijatu da take bayan motar.
Dariya yayi ya kalli Khadijatu "Ƙanwata kinji wai ba zata min magana a gabanki ba."
Ɗago da kanta tayi ta kalli Aishan sai ta tuntsure da dariya "OH Allah kace yau an ƙara min daraja ana jin kunyata.
Nagode Anty Aisha. Yayana baka tambaye nima ya akayi a asibitinba da kuma abin da zai mayar da ni?"

Murmushi yayi yana kallon Aishan da ta turo baki tana harararsa ta gefen ido "Ai nasan zaki faɗa min ne ƙanwata da mun zauna."

"To duk ku kawar da batun soyayyarku na baku labari."
"A'a dai kam ƙanwata. Ke kin siyu ki bari nima na taya ko a siyar min, idan munje gida sai ki bani labarin duka."
Dariya ta yi ta jingina da jikin kujera ta fara danna wayarta "Fatan alkhairi Yayanah!" Daga haka tasa headphone a kunenta.

Har suka je asibitin bata san me suka tattauna ba, wanan karonkam sun tadda shi zaune a kan kujera idanuwansa na kallon bakin ƙofa.. Yana ganinsu ya sauƙe ajiyar zuciya, yayin da Mom dA Dad suka shiga wasa baki na ganin Khadijatu .. .


🌷🌷🌷🌷🌷

Wash yau na ɗan futa ne, kuyi hqr da rashin update da wuri.[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG....
 

  5500000.....


  Gaida su Mom suka yi dukkansu kana suka tambaye su mai jiki. Da sauƙi suka amsa musu fuskarsu a sake. Daga nan suka gabatar musu da kayan abincin da suka kawo musu, godiya suka ƙara musu a karo na ba iyaka, domin ko kaɗan basu ɗauka za su samu wanan karamcin da kulawa daga garesu ba.
   Shi dai Aabid sai binsu yake da kallo yana girmama cika alƙawarin Khadijatu da kuma karamcinta gareshi.
   "Na ɗauka kin manta ba zaki dawo ba." Ya faɗa da sakakkiyar muryarsa yana kallonta.
  "Idan Khadijatu tayi alƙawari bata saɓawa Aabid. Musamman wanda ya kasance na aboki ne." Ta faɗa tana murmushi.
  "Nagode da karamcinki." Ya faɗa yana sunkuyar da kansa, wani nauyi da kunyarta na shigarsa, yayin da yake ƙara girmama duk wani abun da ke gareta.

   Sun daɗe a asibitin har sai da suka ga yaci abinci sanan suka bar asibitin,  a lokacin jin zuciyarsa yake saƙayau kamar ya samu wasu dangin da yake nema, kasancewar Ishaƙ ya ware shima yayi wasa da dariya da shi.
   Yaron da ya dake shi shine yake jansa a jikinsa kamar ƙaninsa zuciyarsa ta kasa jure hakan  "Ishaƙ kaima ka yafe mun?"
  Murmushi Ishaƙ ɗin yayi yana kallon Khadijatu "Ina yafewa duk mutumin da ƙanwata ta yafema, kamar yanda nake girmama duk wanda ke da kusanci da ita.
  A duniyata ƙanwata ce abu na farko da nake dubawa, shi yasa idan ta kawo min fari tace baƙi ne sai nima na masa kallon baƙin."
  "Ban taɓa ganin soyayyar yaya da ƙanwa kamar taku ba Ishaƙ. Nagode sosai."
  "Yawonka ne kaɗan a duniya, na tabbata da kana zagayata da kaga waɗanda suka fimu." Ya faɗa yana ruƙo hannun Khadijatu.
  Hannu ta ɗaga masa suka bar ɗakin yana binsu da rakiyar ido, shi dai duk zagayensa a duniya bai taɓa cin karo da soyayyar yaya da ƙanwa kamar Ishaƙ da Khadijatu ba, duk da yace yawonsa kaɗan ne, amma kuma ba ta yanda zai kasance an samu wanda suka fusu, koda akwai to 'yan kaɗan ne a wanan duniyar.

   ****
Bayan kwana biyu.

  A cikin kwanaki biyun nan shaƙuwa ta shiga tsakanin Aabid da ahalin gidan su Khadijatu, kamar yanda su Mom suka ɗauki mutanen gidan a matsayin danginsu.
  A kwanaki biyun da sukayi a asibitn sun samu kulawa sosai a garesu, dan kullum sai an samu wanda zai zo duba Aabid daga gidan, yayin da Khadijatu da Ishaƙ ya zame musu jiki wajen zuwa kullum.
  A lokacin kuma Aabid ya fahimci Nabil ne masoyin da Khadijatun take so, tabbas ko da ace Khadijatu bata masa magana ya janye akan buƙatarsa ba dole ya janye ya haƙura ya bar ma Nabil ita. Domin ta ko wata fuska Nabil ya dame shi ya shanye, mafi girma a ciki shi mutumin kirki ne mai haba-haba da mutane, bai taɓa jin Nabil yayi maganar soyayya ga 'yar kowa ba, kamar yanda bai taɓa jin labarin budurwarsa ba.
  Amma kuma tun bayan haɗuwarsa da Khadijatu labarinta ya cika dodon kunnuwansa, ba wayar da za su yi su gama bai bashi labarin Khadijatunsa ba, tun yana jin haushin abun har ya mayar da shi jiki.

   "Lallai kinyi dace, kin samu farin zinaren da ba kowa ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login