Showing 21001 words to 24000 words out of 91747 words

Chapter 8 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

800

sai yaji kamar babu wanda ya kai shi sa'a a wanan duniyar.
Ita ɗinma haka ta ke ji, ta san tuni ta ɗara sa'a ta samu ta haye da ɗaya tamkar dubu a rayuwarta, Aabidullah ɗin da maza ke tsoron giftawarsa a gareta kuma ya zame mata sanyin da kan sanyaya murya, lokuta masu yawa takan yi mamakin yanda soja kamarsa ke kashe lokacinsa da tattalinta a tare da shi.

"Ina sonka Aabidullah!"
"Na sani." Da sauri ta juyo tana kallonsa domin a tunaninta a zuci ta faɗi maganar, ido ɗaya ya kanne mata yana murmushi, rungumesa ta yi tana jin soyayyarsa na huɗa sassan jikina.
"Na sani ba zaka sauya ba!"

******
Malam Madori.

🌷🌷🌷
DAN Allah kuyi malejin wannan, yau munyi rashin wutar nepa.
in sha Allah da safe Zaku ga na barka sa sallah.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

OUM-NASS

0015

Bayan kwana biyu.

   Shugowar likita ya sashi saurin tashi daga kwanciyar da yake "Likita dan Allah ka zo ka cire min wanan jonin da ka min, ka kaini naga ƙanwata!"
   
  Tausayinsa ne ya kama Likitan ganin yanda yake magana a fuzge kamar yana ƙwatota daga bakinsa.
  "Ka yi haƙuri ka bari ka samu sauƙi, itama tana nan ana kula da ita sosai."

   Kai ya girgiza yana kai hannunsa jikin kanular da ke hannunsa, ja yayi ya fuzge da ƙarfi nan take jini ya zubo hannun nasa ya wargaɓar yana ƙoƙarin tashi akan gadon.
  Ido Likitan ya fiddo waje cikin mamakin mutumin, da sauri ya ƙarasa kusa da shi yana ruƙo hannunsa "Haba mana ƙanina! Kamar wanda bai san zafin jikinsa ba!  Ka ga fa yanda jini ke zuba a jikinka?"

  Ƙwace hannunsa yayi daga ruƙon Likitan yana tashi akan ƙafafuwansa "Ai na faɗa maka ka kaini wajen ƙanwata kaƙi. Na maka roƙo da magiya amma kaƙi kaini. Ni a yanzu rayuwar ƙanwata tafi min komi a duniya, ban san zafin jikina ba sai zafin zuciyar da ke bugawa da sunan ƙanwata.
  Na tabbata duk inda take itama yanzu bata cikin jin daɗi."

   Kai kawai Likitan yake gyaɗawa cikin sanyin jiki "Zo mu je na kaika wajenta."

  Gaba Likitan yayi yana bin bayansa har suka fuce a ɗakin, ɗakin kusa da nasa yaga likitan ya shiga a ransa yana mamakin dama ashe kusa suke ake ɓata masa lokaci? Shi da ya san suna kusa yaushe zai ɓata lokacinsa wajen roƙon su kai shi, lallai rashin sani ya fi dare duhu!
   Yana zura ƙafarsa a ɗakin ya fara jiyo shassheƙar kukanta hakan ya sashi saurin shiga ɗakin. Hangota yayi a ƙarshen gadon ta haɗe kai da gwuiwa tana ta kuka, ta takure jikinta a waje ɗaya sai ajiyar zuciya ta ke sauƙewa.
  "Khadijatu!" Ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita, ɗago kanta ta yi fuskarta duk tayi jage-jage da hawaye da majina.  
  Ƙarasawa yayi kusa da ita yana riƙe hannunta, dan ko har yanzu bata gane shi ba, ganin yanda ta kafe shi da idanuwa tana ƙara ci gaba da sabon hawayen da ke zuba akan idanuwanta.
"Khadijatul Ishaƙ!" Ya faɗa cikin sanyin murya yana matse hannayenta.

  Ajiyar zuciya ta saki tana ɗaga hannunta da nuna masa ma'aikatan lafiyar da ke ɗakin, hannunta ya riƙe ya sauƙe ƙasa yana rungumeta a jikinsa "Ba abun da za su miki. Ina tare da ke ƙanwata!"

   Juyowa yayi yana kallon Likitan "Kaga ni ba! Gaba ki ɗaya a wanan duniyar nine rayuwarta, kamar yanda take rayuwata itama. Duk yanda na matsa a kusa da ita gani take za'a iya cutar da ita.
  Ni ban san zafin dake kan fata da tsokar jikiba kamar yanda na san zafin zuciyar da ta cika da ƙuna a cikinta.
  Duniya ta cika da ababen mamakin da yafi mamaki zama abun al'ajabi, mutanen da suka kewayeta kuma sun rayu da son kansu da kafa kansu ne kawai ba tare da sun tsaya sun duba su waye suke da rauni a kusansu ba.
  Shi yasa na sha mamaki da naji wani ya kawo mu ya taimaka mana ba dan ya amfana da wani abu daga garemu ba, na san ba lallai mu ƙara haɗuwa da shi ba, amma idan wata rana ka haɗu da shi ka miƙa godiyar mu a gareshi da addu'ar samun aminci da kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa."

   Yana gama faɗar haka ya tashi tsaye yana riƙe da Khadijatu da itama ta sauƙo akan gadon, yana nufar ƙofar waje.
  Da ƙyar Likitan yayi ƙarfin halin yin magana, saboda tausayinsu da ya gama ratsa zuciyarsa, daɗin daɗawa kalaman da ya faɗa masa da ke nuna suna cikin ƙuncin rayuwa, tun bayan kawosu asibitin.  Ga kuma ƙanwarsa da ta ke cikin yoyon futsari da alamun taɓun hankali a tare da ita.

   "Yanzu ina zaku je ba'a sallameku ba? Ba ku gama warkewa ba kai da ƙanwarka."

   Kallon Likitan yayi yana murmushi da iyakarsa fatar bakinsa "Duniya da faɗi Likita, baku da magani da kayan aikin da zaku warkar da ƙanwata. Idan na miƙe ƙafa nace lallai sai na jira warkewata ya zanyi da ta-ta larurar da tafi tawa?
  Zamu ci gaba da zama ne da ku kuna shiga kuna fita aduk lokacin da kuka so, amma ita ko nan da nan bata iya matsawa, saboda furgicin da ke gareta ba zai bata wanan damar ba."

    Daga haka ya ruƙeta suka fita a cikin ɗakin, yana jin bayansa na riƙewa da kuma ƙafarsa da har yanzu bata da ƙarfi.  A ranar da abun ya faru bai ji zafin ciwon ba, sai yanzu da yake ji ko ina a jikinsa a ɗaure ya ke, hakan na nuna masa ya samu raunuka da yawa a jikinsa.
  Sai dai babbar sa'arsa ɗaya da Khadijatu ba ta samu ko ƙwarzane ɗaya ba.

   Sai da suka kusan barin harabar asibitin yaji an ce "Yayan Khadijatu!"
Tsayawa yayi cak daga tafiyar da yake yi yana juyowa da son ganin wanda ya kirashi da wanan sunan.

   Likitan yaga ya biyo su yana ta sauri har ya cimmasu, baƙar leda ya miƙa masa "Wanan sauran maganin ka ne. Akwai na Khadijatu shima yana cikin wata leda fara."
  Hannunsa ya sa a aljihunsa ya miƙa fiddo kuɗi "Wanan sauran sanjin kuɗin gadonku ne da aka biya, tunda kun tashi ba amfanin na riƙe muku shi."

   Kallon kuɗin yake da mamaki kamar yaga abun tsoro a hannunsa "Ka karɓa naku ne, ka je ka nema ma Khadijatu magani, ka siya mata kaya saboda larurarta na buƙatar wadataccen kaya."

  Hannu biyu ya saka ya karɓi kuɗin, yana kallon Likitan hawaye na zuba akan fuskarsa, wanan shine karo na biyu da yaga tausayawa a fuskar likitoci.
  "Nagode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi, ya ji ƙan mahaifa. Kaine mutum na uku da naga tausayawa a tare da shi a wanan duniyar tamu. Ina fatan Allah ya tausaya maka kamar yanda ka tausayama rayuwarmu, ka dawo mana da abun da bamu san da zamansa ba a matsayin mallakinmu.
  Allah ya dawo maka da dukkanin kyawawan mafarkanka su zame maka gaskiya."

   "Ameen nagode sosai. Khadijatu ba sallama?" Ya faɗa cikin sigar tsokana.
  Cakume Ishaƙ tayi tana cusa kanta a ƙirjinsa.
  "Yi haƙuri Likita larurarta bata  ba ta damar yin magana da kowa ba, asalima tana tsoron mutu."
 
  Kai Likitan ya girgiza cikin tausayinta "Allah ya bata lafiya, yanzu ina zaku kaita."

  "Acan ƙauye dai Likita ya rubuta mana katin sauya asibiti ya tura mu kano, amma yanzu bamu da takardar sanadin gobarar da mukayi a ɗakinmu."

  Kai Likitan ya jinjina cikin tausaya musu "Bari na rubuta muku takardar idan yaso idan kunje ku ce akaiku asibitin malam aminu kano."
  Risinawa yayi har ƙasa "Mun gode sosai Likita, Allah ya saka da alkhairi."

   "Ameen ba godiya ai duk yiwa kai ne."

  Da sauri ya koma office ɗinsa bai jimaba ya sake futowa ya miƙa musu takardar "Wanan itace shedar kun zauna a wani asibitin, an mata aiki, in sha Allah komi zai dai-daita. Allah ya bata lafiya."
  "Ameen likita nagode sosai." Daga nan sukayi sallama da likitan yana ɗago musu hannu har suka bar asibitin.
  A ƙofar asibitin yaga masu sayar da abinci ya siya musu suka ci, duk da cewa ba sosai suka ci ba amma sun rage tarin yunwar da suka kwasa, duk da sinadarin ƙarin kuzarin da aka sanya musu.

  Daga nan suka yi tambaya aka kwatanta musu kasuwar garin, kamar yanda Likitan ya bashi shawarar siyama khadijatu kaya, a cikin kuɗin da ya bashi dubu goma sai da ya kashe mata dubu biyar da siyayyar kaya dinkakkun da ya samu har kala biyar, kasancewar rayuwa bata yi tsada mai yawa ba.
   Daga nan tasha suka nufa anan ne suka sha wahala saboda duk masu motar da suka gansu ƙin yarda suka yi su ɗauke su, asalima ƙyamar su suka ringayi suna korarsu da cewar ba za su iya ɗaukansu haka jiki gaje-gaje da fitsari ba.
  Har ƙasa ishaƙ ya risina yana roƙonsu akan su taimaka su ɗauke su ko nawa ne za su biya shi idan suka kai shi.
  Da suka gaji da magiya korarsu suka yi, wani ma bulala ya ɗauka ya fara zane su "Ubanwa zai ɗauke ku da mummunan jikin nan naku, ku lalatawa mutane kujeru da za'a shekara ana tara kuɗinsa."

   Tashi Ishaƙ yayi yana tare dukan da yake kaiwa Khadijatu "Kada ka daki ƙanwata! Inda baka taimaka mana da kuɗinmu ba kada ka cutar da mu da muguwar zuciyarka."
Ido mutumin ya fiddo waje yana kallon ƙaramin yaron da ke gabansa yana faɗa masa magana, a fusace ya ɗaga bulalar ya zubama Ishaƙ a jikinsa, wanda ya sa idauwan ishaƙ ɗin suka yi ja saboda zafin dukan.

   "Allah ya isar min akan zalluncinka!" Ya faɗa yana shirin barin wajen, Khadijatu ta ƙwalla ƙara ganin yanda mutumin ya shiga zubama Ishaƙ bulala ta ko ina kamar Allah ne ya aiko shi.
  "Kai ɗan gidan uban waye a garin nan da zaka tsaya a gabana kana zagina da faɗa min magana.
  Dan Ubanka wa yace kaje a lalata ƙanwarka kazo nan kana cewa a kaita asibiti, a shegen gidadancinku da auren jahilcin da kuke ya janyo mata. Wani shegen ne ya aike ku yi."

   Zuwa yanzu kam Ishaƙ hawaye ya jiƙa fuskarsa amma duk da haka bakinsa bai mutuba yana kuka yana kiran "Allah zai saka min, ban yafe maka ba wallahi."
  Ɗaga bulalar da ta daɗe da karyewa mutumin yayi zai dake shi, yaji anriƙe bulalar, a fusace ya juyo da niyar yin masifa ga mutumin da ya riƙe masa bulalarsa.
  "A'a Balarabe zalincin yayi yawa gaskiya. Ga duka ga tsinka jaka, kaji tsoron hakkin maraya, kaji tsoron addu'ar wanda aka zalunta."
  Rai Balarabe ya ɓata yana kallon dattijon "Baban Indo gaskiya kana shigar min hanci da ƙundudune, kai baka ga abun da yake min ba ne? Duk wajen nan babu wanda bai ji kalar zagin da yake min ba, saboda mun ce ba zamu ɗauki ƙanwarsa da take fama da yoyon futsari ba.
  Duba kaga wajen da take tsaye inda ya jiƙe jagaf, ta ina zamu iya tafiyar awanni biyu da ita a kan motarmu?"
   KAI Baban Indo ya girgiza cikin sanyin jiki ya ruƙo hannun Ishaƙ da Khadijatu da har lokacin take ihun kuka  "Ni zan kai su a motata. Inaga babu wanda zai yi ƙorafi akai."

   "Motarka kace ai, ina ruwan wani da wani mahaukaciya ta yi baƙo." Balarabe ya faɗa yana aikama da Ishaƙ da muguwar harara.

  Babu wanda ya tanka masa har suka tafi motar da Baban Indo ya kaisu, shinfiɗar leda yayi akan kujerar sanan ya ɗora wani bargo mai kauri cikin tausayawa yace "Ku shiga mu tafi na kaiku Kano ɗin."

  Risinawa ISHAƘ yayi yana masa godiya, kayan hannunsa ya karɓa ya saka a bayan motar daga nan shima ya zagayo ya shiga ya kunna motar suka bar tashar, ya ɗauki hanyar KANO....

🌷🌷🌷🌷🌷

Karku manta Book ɗin nan na kuɗi ne Idan ta Bank ne #200
Idan kuma katin waya ne 300
Zaku iya biya ta nan,
Acct: 0472282105
Ramlat Abdul Rahman Manga
GT BANK
A yi screen short ɗinsa a turo ta wanan no 08030990232[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

OUM-NASS

0016

  KADUNA, NIGERIA.

    "Saƙona ya sameka ashe?"  Mahaifin Fatima ya faɗa bayan sun gama gaisawa da Imran a mutunce.

  Kai ya gyaɗa masa cikin sanyin muryarsa yace "Eh Abba!"

"Masha Allah! Naji daɗi da ka amsa min ka zo. Me yake faruwa tsakaninka da Fatima ne?"

   Ɗago da kansa yayi ya kalli Abban Fatima da shima yake kallonsa da idanuwansa "Ta faɗa muku wani labari ne akan zamanmu?"
   Murmushi Abban Fatima yayi yana ƙara kallon Imran ɗin da shima kallonsa yake "Ba sai ta faɗa min ba ai, yanayinta kaɗai ya isa a gane ba ƙalau kuke zaune ba."

   "Ni dai ƙalau nake zaune da ita Abba amma ban sani ba ko ita ba hakan ba ne a wajenta."
"Imran kalamanka suna nuna min cewar kamar a zuciyarka babu soyayyar Fatima. Amma ni ban tursasa maka zama da ita ba, tun farko da nasan baka buƙatarta da bazan fara bada auren fatima da kai ba.
   Imran babu dole a cikin rayuwar aure abu ne da yake zaɓinka kuma igiyar sarrafashi take hannunka. Duk abun da ka zarta a tsakani bani da ƙorafi akansa, asalima zan sa hannu bibbiyu na amsheta a matsayin ƙaddarata, haka kuma ba zan riƙe ka a raina ba asalima sai dai na gode maka da ka dawo min da abun da na baka a mutunce."

   Kai Imran ya shafa yana jin nauyin kalaman Surukan nasa, duk da bai futo kai tsaye yayi masa magana ba amma ai shi ba mahaukaci ba ne yasan jurwaye yake masa.
   "Kayi haƙuri Abba, in sha Allah makamancin hakan ba zai sake faruwa ba. Duk da zuciyata ta ginu wajen biyayyar amsar fatima ba dan ina so ba a farko, amma a yanzu na fahimci ita kyauta ce daga Allah a gareni da ya musauya min ita daga mummunan ƙaddarar da ta gifta a gareni.
  A yanzu kuma na sanya hannu biyu na amsheta dan na cika godiyata ga mahallicin da ya ƙaddara min samuwarta a cikin rayuwata.
  Idan har akace a yau na rabu da Fatima na tabbata ni ke da hasara babba."

   Tashi Abba ya yi yana ɗaukar hularsa da sata akansa "Kana da zaɓi dai Imran, ni ba zan so kaina na ƙuntata ma rayuwarka ba. Zan turo maka Fatiman ku dai-daita da ita."

   "Nagode Abba. Allah ya ƙara girma."
 
"Ameen." Ya faɗa yana fita daga ɗakin.
  Futarsa ba jimawa Fatiman ta shigo bakinta ɗauke da sallama, amsawa yayi yana kallon kanta a ƙasa, idan ba gizo idonsa ke masa ba gani yayi ta ƙara kyau, wata ƙila dan bai taɓa tsayawa ya ƙare mata kallo haka ba.
  Risinawa ta yi ta gaida shi ya amsa fuskarsa a sake "Kina lafiya Fatima?"

  Kai ta gyaɗa masa ba tare da ta yi magana ba "Kawai kuma sai na samu labari kin bar gida! Wani abun aka miki da ya ɓata miki rai ne?"

  Ɗagowa ta yi ta kalleshi yanda yake magana a nutse cikin sanyin muryarsa, amma kuma maganar irin ta rainin hankali da kuma ƙurewa mutum gudu "Ni kake tambaya wani abun ya faru Al'ameen? Duk da sanin da kayi ni da babu duk ɗaya ne a wajenka, kamar yanda kake min kallon marar amfani a tsawon zamanmu da kai. Amma kuma kai ne zaka zo kana tambayata me ya faru?"
   Ƙafarsa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana kallon yanda idanuwanta suke zubar da hawaye, shi bai san me yasa zuciyarsa taƙi bama Fatima koda ɗan ƙaramin waje ne ba. Ba zai ce ga abun da yake ji agame da itaba kamar yanda ba zai ce yana jin haushinta ba. Abu ɗaya yake ji akanta shine zamowarta wata katanga da ta katage masa duk wani jin daɗinsa, ta hana rayuwarsa walawa kamar yanda yake son yi. Ta datse duk wata igiya ta cikar mafarkansa.

  "Yaushe na taɓa faɗa miki baki da amfani a wajena Fatima?"
  "Ba sai ka faɗa min ba Al'ameen, yanayinka da ɗabi'ar da kake nuna min ita ta tabbatar min da rashin amfanina a wajenka.
  Shekaru goman da suka gifta a tsakani sun gaza baka damar tsayawa ka min koda kallon muntina guda ne. Amma ni da ko wata daƙiƙa da zata buga tana bugawa ne da amsa kuwwar ƙaunarka a zuciyata. Duka yarda ta na gareka wanda har gobe bazan iya ƙasƙantar da kallon da nake maka a matsayin Amintacce a gare ni ba.
  Dan Allah koda sau ɗaya ne ka kalleni a matsayin macen da ke da rauni da kuma gazawa ta ko wata fuska. Koda baka bani tsawon lokacinka ba ka ware koda mintuna ƙalilan ne da zaka yi magana da ni." Ta ƙarasa maganar tana haɗe hannayenta biyu a waje ɗaya, hawaye na zuba akan idanuwanta, duk yanda ta so ta nuna ɓacin ranta akan Imran ta gaza. Asalima idan ta kalleshi sai taji duk wani kuzarinta ya riga da ya ƙare, har yanzu wanan kwarjinin nasa na nan bai ragu ba. kamar yanda bugun zuciyarta bai samu rauniba.

   "Ban san ya zan faɗa miki ki fahimta ba Fatima! Amma a zuciya babu tsanarki kamar yanda babu soyayyarki. Sai dai a raina inaji wanan shine karo na ƙarshe da zamu sake samun saɓanin da zaki barni. Gidan da kika bari ya zama kufen da babu komi a cikinsa, duhu ya riga da ya lulluɓe futulun da suke ƙawata shi. Maƙaƙi ya maye gurbin ƙamshin da kullum ya ke tashi a cikinsa.
  Fatima ba'a gane amfanin abu sai har ya yi maka nisa, kamar yanda naji a zuciyata a yanzu, tafiyarki ta ankarar da ni amfanarwar da ke gareki.
  Sai dai ban saniba ko hakan zai ci gaba da faruwa idan har kika zauna a kusa da ni! Ina so wanan ƙuncin ya tafi ya barni mu rayu a tare da ke."

    Kallonsa take tun farkon fara maganarsa, tana murza idanuwanta da son tabbacin wake gabanta "Dan Allah idan mafarki nake kada ku tashe ni! Kada ku ce min wanan Imran ɗin ne yake ambatar amfanina."

   Tashi yayi daga inda yake ya matsa kusa da ita, tsugunnawa yayi ya ruƙe hannunta da jan karan hancinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login