Showing 57001 words to 60000 words out of 91747 words
GANE SAI MU BAR TAFIYAR A HAKA.
RUƘo hannayensa Khadjatu da Ishaƙ sukayi "Mun daɗe da yafe maka Babba, domin duk wanda ya samu matsayi irin naka abun da zai yi kenan." Suka faɗa a tare.
Anan Malam Liman yayi gyaran murya yana kallon Ishaƙ "Haƙiƙa al'amarin Allah ya wuce abun a misaltashi, da naso taimaka muku sai ƙaddararku ta sabunta daga gareni, kamar dai yadda kace ba ni zan zama silar share muku hawayenku ba, amma na iya zama dalilin ambaton son taimaka muku baya.
Tabbas na tayaku murnar haɗuwa da iyayenku, ina kuma roƙon Allah ya bi muku hakkinku dai-dai yanda aka cuceku."
"Ameen." Duka mutanen wajen suka amsa. Daga nan suka ajiyema Mai garin kuɗaɗe masu yaawa, akan ya rarrabama mutanensa. Baki ya buɗe yana kallon tilin kuɗin da bai taɓa ruƙe irinsu ba a shekarunsa na duniya, sai dai ya ji labarinsu a duniya.
Daga nan suka tashi suka bar fadar mutane na faman ɗaga musu hannu da godiya mai yawa kamar za su musu sujjada. Yayin da zuciyoyinsu ya cika da nadama wasu kuma na ɗaukarma kansu alƙawarin gyara rayuwarsu, zaa su taimaki mutumin da ba su saniba muddum ransu.
***
Bayan dawowarsu aka samarma Khadijatu maakaranta mai kyau, kasancewar a lokacin tana matakin junior ne, basu dawo da ita baya ba, kasancewar suna da dama a hannunsu, Imran da kansa ya kaita makaranta.
Daga bisani kuma ya nemo ƙwararrun malamai ya ajiye maata guda uku, ita da Indo komi nasu ɗaya ne, wata ƙauna take yima Indo wadda bata san adadinta ba.
Tabbas rayuwa sai yanzu take gara musu, kamar yanda zuciyoyinsu suka cika da kulawa da kyautatawa daga iyayen nasu, ba zasu iya ware sashe ɗaya suce shine sashen da yafi sonsu ba.
Lokuta masu yawa Khadijatu sukan keɓe da Ishaƙ musamman a waya suna hira da labaran halin da suke ciki a cikin hirarsu Ishaƙ ke faɗin "Khadijatu kinga yanda duniya take ko? Ashe muna da sauran kwanakin da zamu ba soyayya da kulawa daga wasunmu bayan mu? Ban san me zai faru a gaba ba, amma ko yanzu na mutu nasan burina ya cika. Duk da ban sauƙe nauyin da Mami ta ɗora min a kaina ba, amma na samu ƙwarin gwuiwa na samun masu tayani."
Duk lokacin da yayi mata wanan maganar sai ta kashe wayar tayi ta kuka, gani take kamar wasiyya yake bata, kamar zai iya mutuwa ne ya barta.
Duk duniya bata da uban da take gani kamar Ishaƙ, har yanzu bin mutane take da kallo tana amsa kiran sunan ɗiyarsu da suke mata, sai dai a fuskarta yaƙe take, bata yarda akwai wanan soyayyar ba.
****
LAGOS, Nigeria
BAYAN SHEKARA ƊAYA!
"Nurieyyah hasken idaniyata! Farin cikin ruhina! Wa zai taɓa min ƙalbina ya ga wuta?" Waƙar da Aabid yake ma Khadijatu tana faman dariya, kasancewar yanzu tayi wayo sosai, har ta fara tafiya.
Lokuta masu yawa Amrah sai dai ta kalleshi, dan tun tana ƙarama da yaji kukanta sai ya rufeta da faɗa, yana cewa da saninta ta bar masa yarinya ita ɗaya tana kuka.
Akwai lokacin da take kuka taƙi shan nono, ya karɓeta ya na masifa, ƙarshe a ranar sai da ya mari Amrah saboda a cewarsa itace ta zama silar kukan yarinyar, saboda ta hanata nono.
Amrah tayi kuka har ta gode Allah amma ba wanda yabi bayanta, hatta surukanta haushinta suka ji akan itace ta mata laifi ta barta tana kuka har tayi zuciya taqi shan nonon.
Bata da bakin magana haka ta shige ɗaki tayi kukanta ta more, babu wanda ya ƙara kulata.
To yauma kamar kullum ya sanyata agaba yana mata waƙa tana ta dariya, ga kakaninta a gabansu suna tayashi da mata tafi.
Wani maƙoƙon takaici ne ya cika Amrah, tana ga kamar wanan mafarin sangarta yaro ne. Ƙarin daɗawa kuma yarinyar Allah ya wadata da hanzari da ɗan banzan ta'adi, idan kuma tayi magana suce ubanta ke siya.
Wanan yasa ta ɗaukarma kanta alƙawarin ko harara ba zata ƙara haɗata da Nurieeyah ba.
"Dad nifa na fara tunanin makarntar da zan kai Nurieeyy nah!" Aabid ya faɗa yana haɗa hancinsa da na Nurieeyyah.
Washe baki Dad yayi yana shafa kan Nuriee ɗin "Wacce zaka kaita?"
"ONE MILLIONS IN TOWN!"
"Wow kamar ka shiga zuciyata. Ni kaina makarantar tana ƙayatar dani, babu makarnatar da zata dace da Habibaty kamar ita.
Ina alfahari da kai ɗana." Ya ƙarasa maganar yana jinjina hannunsa.
Dariya mom tayi itama tana yaba zaɓin ɗannata.
Amrah kasa jurewa tayi saboda sanin da tayi ana kashe miliyoyin kuɗi a ko wani zango na karatu "Amma dai ba nursery zaka kai ta tayi acan ba, sai ta girma ta san kanta?"
"Kina da damuwa akan hakan idan na kaita ta fara daga nursery ɗin?"
"Gasky abun yayi tsauri da yawa Aabid! Kuɗin da za'a kashe ya isa ka samarwa wasu aikinyi, kayi haƙuri ka bari ta ƙara girma, dan gaskiy gani nake hakan albozaranci ne!"
"Kajiba Dad! Idan nace muku Amrah tana kishi da Nuriee sai kuce ba haka ba! Yanzu na fara tunanin abunta ya wuce kishima ya koma baƙin ciki.
Amrah ina fatan kuɗin da za'a kashe ba naki ba ne ko?"
Kai ta gyaɗa cikin sanyi jiki "Nagode Allah da ni ke nema da gumi na! Idan kina adawa akan hakan zamu samu matsala da ke."
"Allah ya baka haƙuri!"
Ta faɗa tana barin wajen ya bita da harara da tsuka.
Su dai iyayen sai haƙuri suke ba shi.
Tun aranar ma ya je ya cikema Nuriee komi na makarnt, da yace sai ta shekara biyu, amma dan ya ƙular da Amrah ya kaita tun yanzu a fara da rainonta acan idan ya so sai ta mutu dan baƙin ciki.
Hakan kuwa ya ƙona mata rai, yarinya 'yar shekara ɗaya xa'a bawa ƙaton gardi rainonta, da tayi magana anan ta sha baƙar magana ya ƙara da vata raddi akan ai ba gardin Nigeria ba ne, asalima balarabe ne da bai damu da mata ba balle yara ƙanana.
Shuru tayi bata ƙara magana ba, haka rayuwar gidan taci gaba da kasancewa, idan har kana son ganin walwala a cikin gidan to ka so Nurieeyah ka tattalata tattali mai kyau.
Anan zaka ga dariyar kowa da kowa.
******
BAYAN SHEKARA BIYAR!
Gudu yake sosai tun ƙarfinsa, ƙafafuwansa babu takalma, haka ya shige motar iyayensa na tambayar lafiya.
ganin ba zai basu amsa ba yasa suka ɗuru a cikin motar suka bishi, Amrah ma ta shiga motar cikin rashin sanin inda za su tafi.
Mamki ne ya kama su ganin ya kawo su makarantar su Nurieeyyah.Sai dai cincirindon mutanen da suke gani zagaye a waje ɗaya ya haddasa musu fuwar gaba.
Wawan birkin da yaja, yasa hankalin mutane ya juyo kansa. Tun kafin motar ta tsaya ya ɓalleta ya fito, wanda yasa Dad da Mom rafka salati.
Bai saurara ba ya shiga kutsa kansa wajen taron mutanen su Mom ba biye da shi.
Wata kyakkyawar yarinya mai zubin yaran larabawa, gashinta ya kwanto har fuskarta, tana kwance a kan wani farin ƙyalle idanuwanta a rufe fiskarta tayi fayau da ita. sai idanuwanta da suke da alamun bushewar hawaye.
Bugun zuciyarsa ne ya ƙaru daga inda yake, ya kwasa da gudu ya ƙarasa kusa da yarinyar "Nurieey!" Ya faɗa yana ɗagota daga kwancen da take yana ɗorata a jikinsa.
Lemar da yaji a jikinsa ya sashi duba hannun nasa "JINI!" Ya faɗa cikin rawar murya "Dan Allah ki tashi Nuriee! Ki tashi kiga Papanki!"
Su kansu su Dad kasa ƙarasawa sukayi suka tsaya kamar wanda aka dasa su a wajen.
Jiniyar Motar asibitin da suka fara ji ya sasu juyowa, da buɗa mata haanya.
Cikin zafin nama likitoci suka ɗauketa suka sata a motar, shima bin bayansu yayi ya shiga motar. Su Dad kuma suka bisu a motar da suka zo.
Asibiti mafi tsada suka kaita, sannan suka shige da ita ɗakin hatsari da gaggawa.
Tashin hankalin da Aabid ke cike ba zai iya faɗuwa ba, banda hawaye ba abun da ke zuba akan fuskarsa.
Su kansu iyayensa suma hawayen suke, basu san me ya faru da Nuriiee ba kamar yanda shima bai san me ya sameta ba.
An kirashi a waya dai an sanar da shi anga Nurieeyah a tsakiyar makaranta a yashe! Hawayen fuskarsa ya share "Ya Allah kada ka jarrabe ni da mutuwar Nurieeyah."
Ya faɗa yana shafe fuskarsa da hawaye ya gama wanketa.
"In sha Allah ba abun da zai sameta! Ka zo ka zauna Aabid."Mom ta faɗa cikin tausayama yaron nata.
Kai ya girgiza "Ba zan iya zama ba Mom! Ina jin kamar rayuwata ke shirin barina."
Kuka ya sake saki kamar ƙaramin yaro ba general na soja ba.
Ƙofar ɗakin da aka buɗe ya sashi sauri tare likitan "Dakta ya yarinyata take?"
Kallonsa likitan yayi kana yace "Ku biyoni ofishina."
Cikin sauri suka bi likitan, da yake ta faman zirga-zirga a offishin nasa.
"Ku zauna!" Ya ce musu cikin raunanniyar muryarsa da bata fita.
Zama sukayi, likatan ya zare farin gilashin da ke idonsa, kana ya goge gumin da ya jiƙa fuskarsa zuwa idonsa da ya taru da ruwa.
"Tun da nake aiki ban taɓa ganin abun da ya ɗaga min hankaliba irin na yau! A shekaruna goma na aikin asibiti ban taɓa jin tsoro da tausayin rayuwar duniya ba sai yau! Ina jin tausayin kaina da yarana da suke rayuwa ba tare da masu kula da su ba." Likitan ya faɗa yana share hawayen da ke gangarowa akan fuskarsa.
"Me ya faru da ɗiyata Likita?"
Shuru likitan yayi kamar b zaiyi magana ba, can ya nisa ya sauƙe ajiyar zuciya "Mahaifar yarinyarku ta zazzago sanadiyyar Fyaɗen da aka mata! Ƙwayoyin halittarta sun ƙone saboda ƙarfin da akasa aka farmata! Kuyi haƙuri bana jin koda yarinyarku ta rayu zata yi rayuwa mai tsayi da kyau!"[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
00041000
Kamar sauƙar guduma haka sukaji maganar ta Dakta, kunnuwansu sun ɗoɗe kamar basa ji "Dakta kace mi ne?" Amrah ta tambaya bakinta na rawa, gani take kamar gizo kunnuwanta suke mata.
Kai Dakta ya girgiza "Kiyi haƙuri Hajiya!" Shine abun da ya faɗa, amma kuma bakinsa ya masa nauyin da ba zai iya mai-maita matsalar da ta samu yarinyar ba.
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Dad da Mom suka shiga mai-maitawa.
Yayin da Aabid ya zama kamar wani mutum-mutumi, kallonsa duka sukayi suka ga ya ƙame a wajen baya koda ƙifta idanuwa.
Zungurinsa Dad yayi nan ya ɓingire a wajen, salati suka sake rafkawa nan take suka iyo kansa "Aabidullah!" Suke ta faman kiran sunansa, shi kansa Dakta ya tsorata da yanayinsa, take ya kira wasu likitocin aka kaishi sashen taimakon gaggwa.
"Wata irin ƙaddara ce wanan ni Amrah! Ya Allah kana gani, kana ji, kai ne masanin abun da ke ɓoye a fili da kuma zuciya.
Ya Allah kada ka jarrabe ni da rashin abubuwa guda biyu a lokaci ɗaya! YA ALLAH!!" Kukan da yaci ƙarfinta ne ya tsaya, ta kasa ci gana da maganar da take, su kansu iyayen Aabid ɗin kuka suke babu wanda ke lallashin kowa.
Bayan wani lokaci Likitocin suka fito, take suka rufe Dakta ɗin "Ya ɗanmu yake Dakta?" Suka faɗa cikin haɗuwar baki.
"Alhmdlh munyi nasarar dai-daita numfashinsa, ya farfaɗo yanzu dama furgici ne ya sashi suman zaune. Mun masa allurar samun hutu nan da awa guda zai iya farkawa."
"Mun gode Allah!" Suka faɗa cikin haɗuwar baki daga bisani suka shige ɗakin. Yana kwance fuskars tayi fayau da ita, idanuwansa duk sun faɗa wanda ke nuna tashin hankalin da yake ciki.
Zama sukayi dukkansu suna share hawaye akan fuskarsu. "Ina Nuriee take?" Mom ta tambaya tana baza idanuwanta a ɗakin, daga can nesa da Aabid ta hangota kwance an sa mata bututun iska a bakinta da hancinta. Ƙaarasawa suka yi kusa da ita, take jikinsu yayi sanyi saboda tashin hankalin da suka hango a tare da ita.
"Wanan wani rashin imani ne naka? Wanan ƙaramar yarinyar me ta sani da za'a haiƙe mata? Wani dakon zunubi ne haka mutum ya aza a kansa?" Dad ya faɗa cikin rawar murya yana shafa kan Nuriee.
"Ya Allah ka bi min hakkina! Ka ɗora nauyin ikonka ga wanda ya zalinci ɗiyatA!" Amrah ta faɗa hawaye na biyo kuncinta.
"Ko baki faɗa ba Zina bashi ce Amrah! Tana biyo lokaci ta karɓa daga abun da aka karɓa daga gareta. Yayin da sharri kan zama ɗan aike, ya bi sahun wanda aka zalunta ya masa hisabi dai-dai da zalincinsa.
Allah kana gani, ban cutama ɗan kowa ba, ban harari ɗan kowa ba! Ya Allah ka mana hisabi dai-dai da zalincin da aka mana!" Mom ta faɗa hawaye na kwaranya akan fuskarta.
Cikin rawar jiki Dad ya ɗauki wayarsa ya shiga kira "Ina son a kama duk ma'aikatan da suke cikin makarntar ONE MILLION IN TOWN tun daga kan leburorinsu har zuwa malamansu.
Ina kuma son a ƙwacewa makarantar lasisin aikinta!" Dad ya faɗa cikin rawar murya.
Cikin abun da baifi mintuna talatinba aka kama duk masu ruwa da tsaki na makarantar kamar yanda Dad ya bada umarni.
Bayan Awa guda Aabid ya farka bai tsaya ba ya fincike jonin ruwan da ke hannunsa, ya nufi gadon da Khadijatu take kwance.
Kuka ya ɓarke da shi yana jijjigata, da ko alamun numfashi ba ta yi "Na rantse da Allah! Na rantse da ubangijin da ke busa numfashi sai na ɗaukar miki fansa, duk wanda ke da alhaki akan wanan sai ya fuskanci hukunci dai-dai da abun da ya aikata miki" Aabid ya faɗa hawaye na bin kwarmin idonsa.
"Lokaci ya ƙure mana Aabid! Lokaci ya ƙure maka na neman wanda ya aikata mata wanan ɗanyen aikin. Balaraben da ka aza nauyin kula da Nuriee tun yarintarta shine ya aikata mata wanan aikin. Wanan balaraben dai da kace baya sahun gardawan maza 'yan nigeria shi ya aikara rashin imani ga Nuriee daga nan ya watsata tsakar makarnta ya gudu yabar ƙasar. Wanan mutumin da ka sakan-kance akan zai kula maka da Nuriee fiye da ni mahaifiyar da ta kawota duniya! Mutane sunyi gaskiya da sukace idan ka kasa haƙa ramin da zaka tone matsalarka sai ka rarraba masa ƙofar da mutane za su bi ta ciki su ƙara ma ita.
Bani da hakkin kowa akaina! Ban kasance cikin azzaluman mata ba! Iyayena basu taɓa aikata alfasha ba! Amma sai gashi yau an aikatama ɗiyata abun da ko a mafarki ban zata zai faru da wanina bama.
Sai nakega kamar ture ne da ɗaukan fansa ta gayya aka aikata akan 'yata! Ban aikata Zina ba Aabid, kaima ina da yaƙinin baka cikin sahun mazan da suke aikata ta! Akan wanan hujjar nake da yaƙini akan ZINA bashi ce da take tafiya take dawowa dan karɓa.
Ni da kai bamu kasance cikin wanan ba! To waye a danginmu da ya taɓa aikata ZINA? Hakkin wa ke bibiyarmu mu da ɗiyarmu?" Kuka ta fashe da shi tana rungumeshi ta baya.
"ZINA BASHI CE!" Maganar ta shiga amsa kuwwa akan kunnunwansa, hawayen idanuwansa ya ƙafe daga zubar da yake.
Wani sabbin hoto ne ya shiga giftawa akan idanuwansa.
Kamar wanda aka sama wutar lantarki haka jikinsa ya shiga rawa, bai tsayaba har sai da ya zame jikinsa daga ruƙon da Amrah ta ke masa, a guje ya fice yana zarar mukullin motar da ke hannun Dad, ƙafarsa babu taklmi balle a samu ado a jikinsa.
Motar ya shiga ga fice daga asibitin cikin matsananci gudu, yayin da su Dad suke binsa da gudu, sai dai basu tadda shi ba sai ƙurar motarsa da suka gani.
"Ya Allah ya kare min kai Aabid!" Dad ya faɗa cikin tausayama rayuwar yaron nasa da sanin inda za shi.
Gashi duk masu tsaron lafiyarsa yasa suna casa masa ma'aikatan makarntar su Nurie akan sai sun nemo inda Labib ƙasim basar yake. Balaraben da ya keta mutuncin Jikarsa.
🌷🌷🌷🌷
BARKANKU DA SAFIYA 💃🏼
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
00000042000000
Gudun da yake a motar yasa mutane da yawa kaucewa, wasu kuma suna tsayawa suna bin motar da kallo, yayin da bakunansu ke binsa da aibatawa suna Allah tsine wanan mummunan ɗabi'ar ta gudu. Wasu kuma aciki sukan ce "Sune suke haddasa mana hatsari a cikin gari."
Shi dai bai kulaba balle yasan akan abun da suke magana, tashin hankalin da yake ciki ma ya isheshi. Idanuwansa na sauƙar da ambaliyar rayuwa, kawai kalaman Amrah ne yake masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.
"ZINA BASHI CE!" Wanan maganar ita take dukkan kunnuwansa take ratsa zuciyarsa.
"Ya Allah!" Ya faɗa a lokacin da hawaye ke cin ƙarfin idonsa, gani yake kamar ba zai je akan lokaci ba.
Tafiyar da ya kamata ace yayita a kwana ɗaya itace yayita a yini guda, dare ya tsala sosai haka ya kangarar da motarsa a gefen wani kango, duk da dare yayi sosai amma hakan bai hanashi gane wajen da yake tsaye ba. Fitowa yayi daga cikin motar ya ɗauki jarkar ruwa ya ɗaura alwala, anan inda yake ya tsaya yana ƙarema kansa kallo kasamcewar hasken farin watan da ya cika duniya, wata milk ɗin shaddace a jikinsa da jini ya mata ado, ƙafafuwansa sunyi buɗu-buɗu babu takalmi.
"Dama a duniya akwai tashin hankali irin wanan?" Ya tambayi kansa yana