Showing 9001 words to 12000 words out of 91747 words
zanin da sauri ya ɗaura mata zanin akan doguwar rigar da ke jikinta.
"To Likita mu zamu tafi sai kuma wata rana idan da kwana. Mun gode sosai da kulawar da kika nunama 'yar uwata, har abada ba zamu manta alkhairinku garemu ba da kuma karamcinku."
Yana gama faɗar haka ya riƙo hannun Khadijatu suka fara tafiya, Nurse Ramla na biye da su tana maida ƙafufuwanta a inda suka ɗauke ta su.
Har sai da ta rako su harabar asibitin, wanda shima Dr. Anwar ke wajen yana kallonsu.
"Khadijatu!" Ta faɗa wanda hakan yasa su tsayawa daga tafiyar da take.
A hankali ta ƙaraso kusa da ita ta rungumeta gam daga bisani ta saketa.
"Ina jinku kamar wasu halittu da suka kasance sashi na rayuwata tun bayan wanzuwarku a wanan asibitin, kamar yanda bani da ilimi akan abun da ya zama silar jin ƙaunarku a raina.
Amma na bar hakan a matsayin iko na Allah da kuma buwayarsa na sanya soyayya a zuciyar bayinsa.
Khadijatu! Abun da ya faru da ke a baya ba kome bane akan abun da zaki fuskanta a gaba, sai dai ina roƙonki kada ki gaza akan hakan, kada ki bari imaninki yayi rauni akan ƙaddarar da ta sameki.
Duk wani abu da ya faru a rayuwa yana da ƙarshensa, ki ɗaula larurarki tana da ƙarshe, ki ɗauka kamar ba kome ne ke faruwa da ke ba. Akwai mutane da yawa da matsalolin rayuwarsu suka tsallake naki, kamar yanda mutane da yawa suke son taka koda matsayi irin naki ne muddum za su rabu da raɗaɗin da ke tare da zuciyoyinsu.
Ki ɗauka wanan ba ko me ba ne! Ki ɗauka kina tare da garkuwar Yayanki! Duk lokacin da xaki shiga ƙunci ki duba halin da Yayanki zai shiga! Ina da sa rai a tare da shi.
Karki karaya Khadijatu, kada ki ji tsoron sabbin shafukan rayuwarki da suke shirin buɗewa. Duk bawan da ke raye a wanan duniyar akwai kalar jarrabawar rayuwar da ake masa. Ki ɗauka wanan ce kalar taki jarrabawar.
Allah ya baki lafiya ya ƙaddara haɗuwarmu da alkhairinsa."
Daga haka ta saki hannun Khadijatu ta matsa, dan ta basu damar tafiya da ita.
Kallonta Khadijatu ta yi hawaye na zuba akan fuskarta, tana son samun wani muhallin da zata ajiye maganarta, wanda ba ta san inda suka nufa ba.
Kalmar da tafi bata mamaki da tsoro itace wadda tace 'Bata ga komi ba a yanzu.' Idan a kintata dai-dai duk wahalar nan da tasha ba ko me bace kenan.
Bin hannunta da kallo tayi wanda ke cikin riƙon Ishaƙ, tana ji kamar babu komi da yayi saura na daga halittarta. Iskar da ke kaɗawa tana ratsa har cikin ɓargonta.
Wannan ke nuna mata babu wani abu da yayi saura a jikinta wanda ke rufe, ƙofar da ke killace ta buɗe.
🌷🌷🌷
_Wanan ba kome ba ne! Har yanxu ba'a ɗauki kaso ɗaya daga cikin goman matsalolin Khadijatu ba! Wanan kawai shimfiɗa ne!_
*Ko waye zai zama Inuwar gajimare ga rayuwar KHADIJATUL ISHAƘ? Ku dai ku ƙara matsowa da mutuntakarku, ku kuma tanadi furan Nagartarku, ni kuma zan ajiye muku GIRMAMAWATA a ko wani layi na tafiyar.*
#InuwarGajimare
#Dabanne🙌[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
NAGARTA WRI. ASSOCIATION
©OUM-NASS 🏇
BAKWAI
Tafiya suke irin ta makaho da ɗan jagoransa, a tsakaninsu babu wanda ke da kuzarin yiwa ɗan uwansa magana.
"Wash! Yayanah na gaji da tafiya." Khadijatu ta faɗa tana tsayawa daga tafiyar da ta ke.
Hango tazarar tafiyar da ke gabansu yayi, gashi ba wani ci gaban abun hawa ne da su ba a garin, ko da ma ace akwai a yanda suke ɗin nan babu wanda zai ɗauke su.
Bayansa ya juyo mata "Hau na goyaki sai mu tafi."
Tausayinta ne ya kamata, hakan ya sata girgiza mata kansa "A'a Yayanah, muje zan iya tafiya a ƙafar." Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga ƙafarta, amma kamar abun tsafi ƙafar taƙi ɗaguwa, ga ciwon da ke jikinta kamar an taɓa shi.
"Wayyo Allah!" Ta faɗa a hankali saboda azabar da take ji ba zata iya ɗaga muryarta ba.
Ɗaukanta yayi ba tare da yayi wani tunaninba, idanuwansa cike da ƙwallah "Sannu Khadijatu nah! In sha Allah wani abun ba zai ƙara samuki ba. Zaki warke! Zaki samu rayuwa kamar kowa a wanan duniyar." Ya faɗa yana tafiya da ita a hannu kamar jaririya.
"Kayi haƙuri Yayanah na ƙara zame maka nauyi a tare da kai! Ji nake inama ace mutuwa ta ɗauke ni ko na samu sauƙin raɗaɗin da nake ji a tare da ni! Inama ace zan dawo da jiya yau da banyi kuskuren tsallake umarninka ba! Da na jiraka koda ace zan kwana a tsaye ne."
Kai ya ke girgiza mata tun da ta fara magana, hawayen da ya taru a idanuwansa suka samu damar gangarowa "A'a Khadijatu ke ba nauyi ba ce a gareni. Asalima ke wata futula ce a cikin rayuwata da idan babu ke zan kasance cikin duhu.
Ki daina fatama kanki mutuwa, domin hakan butulcewa ni'imar da Ubangiji ya sauƙar a gareki ne, da ace mutum na iya ganin abun da ke zuciyar wani mutum ɗin, da kin fahimci naki raɗaɗin mai sanyi ne Khadijatu.
Duk abun da kike gani ya sameki ba kome bane idan aka danganta da wanda ya samu wasunki. Akwai da yawa daga cikin mutanen da rayuwarsu tafi taki hautsinewa, na tabbata Allah yana tare damu, ba zai ɗora mana abun da yafi ƙarfinmu ba.
Ki daina tuna jiyan da ta tafi ta barmu da mugun miki, muyi addu'a akan samun kyakkyawar goben da ke ɗago mana hannu."
"Yayanah...!"
"A'a Khadijatu kina buƙatar hutawa, kiyi shuru kawai."
Ido ta lumshe wanda ya bama hawayen fuskarta damar sauƙowa, ta san yayanta na mutuƙar sonta, amma bata taɓa tsammanin zai mayar da rayuwarsa cikin nata su zama abu ɗaya ba, tabbas zata iya cewa jikinta ne ke da ciwo, amma a fuskar Yayanta raɗaɗin zafin ciwon ta ke gani. Yana daurewa ne kawai a matsayinsa na namiji, jigo, kuma garkuwa a gareta, wanda ba zai bada koda 'yar ƙaramar ɓular da zata ƙara hautsina mata rayuwarta ba.
Jikinta ne ya shiga karkarwa kamar wanda zazzafan zazzaɓi ya ritsata, hatta bakinta rawa ya ɗauka haƙoranta na dukan junansu.
"Khadijatu me ya faru!" Ishaƙ ya faɗa cikin ruɗewa ganin yanda take ƙoƙarin zamewa daga ruƙon da ya yi mata.
Bata Iya bashi amsa ba sai ƙara runtse idanuwanta da tayi, jikinta na ƙara tsanannata rawar da yake.
"Inna... Jin... Nn.. Tsoro Yaya nah! Zuu... Zuciyata na bugawa da ƙarfi Yaya."
Ruɗewa yayi ya kalli inda suke, majalissar da matasan garin ke zama ne suna kashe lokacinsu a wajen, kasancewar ba wani aikin yi gare su ba.
Takun tafiyarsa ya ƙara yi kamar wanda zai tashi sama, wanda hakan ya sa matasan tuntsurewa da dariya.
"Su Isiyaku ina aka shiga ne kwana da yawa? Babu kai babu masoyiyar ƙanwarka."
Wani a cikin matasan ya faɗa cikin shaƙiyanci da sigar tsokana, ko tari bai musu ba saima ƙara saurinsa da yake yi.
"Kai ni dai wanan Ƙaunar taku na bani mamaki, yanzu tafiyar ma ba zaka bari tayi ba sai ka ɗauketa kamar jaririya?"
Dariya duka suka kwashe "Abunka da wanda ke kwasar romon garaɓasa, ai idan da akwai abun da yafi ɗauka to na tabbata zai mata."
"Kumafa haka ne Aƙilu, kaima ka hasko jirgin nasu."
Tsayawa ya yi yana kallon su hawaye na zuba akan fuskarsa, jikinsa ya ɗauki rawa sosai, yana jin zafin da ke cikin zuciyarsa na ƙaruwa fiye da na baya.
"Mu tafi Yayanah, bana son jin muryar su." Khadijatu ta faɗa tana ƙanƙame shi daga riƙon da ya yi mata.
Hakan ya sashi ɗaga ƙafafuwansa ya bar wajen da su ke "Kunji ashe itama ta zama 'yar hannu." Nan suka ƙara bushewa da dariya abunsu.
Haka ya ci gaba da wuce mutane ko ina ya keta sai dai maganar banza da izgilancin da ake musu, ko da sau ɗaya babu wani mutumin da ya tambaye shi abun da ya faru da ƙanwarsa.
To wa suke da shi ma da zai damu da lafiyarsu? Wa ni mutum ɗaya ne zai ɓata lokacinsa wajen tambayarsu abun da ya faru da shi.
Bayan duk garin babu wani mutum ɗaya da zai ce nasa ne, babu wani da zai kira da abokinsa, kamar yanda babu wani da ke damuwa da lammuransa shi da Khadijatunsa.
Su dai suna zaune ne cikin rashin sanin dalili da amfaninsu, suna kuma rayuwa ne a matsayin yaran da basu da galihu, wanda suke cikin kulawar MAI GARI a matsayinsa na shugaba a garin da kowa ke zama nasa.
Sai dai nasu ya fi na kowa muni, su baƙuncinsu a matsayin nauyi ne da kuma larura, wanda suke fafutukar nemawa kansu abun da za su kai bakinsu tun kafin su mallaki hankalinsu.
Zai iya ƙidaya adadin lokacin da aka dangwara musu abinci a gidan na mai gari, duk da cewa ya bada lasisin ciyar da su na tsawon rayuwarsu a garin.
Sai dai maganar a iya fatar kunnuwan matayensa ta tsaya, musamman Gamandi uwar gidansa da ke jagoranta ko mi na gidan, take kuma shimfiɗa mulkinta cikin izza da zalinci dai-dai nata.
Bayan yaranta babu wani yara da take kallo a matsayin yara a gidan.
Wani rusasshen gida ya shiga da ya ke zagaye da katangewar karare, ba zaka ɗauka cewar za'a samu abu mai amfani a cikin gidan ba, balle a yi tunanin mutane za su iya rayuwa a cikin gidan.
Ɗaki ɗaya ne tal a cikin gidan, wanda yayi ƙasa sosai ƙofarsa ma sai an tsugunna ake shigarsa.
A haka ya shigar da Khadijatu cikin ɗakin, ya zaunarta a gefe, sanan ya karkaɗe muta shinfuɗar tabarmar da akayi, wadda ta samu ƙari da fallen zani guda.
Ɗaukanta ya yi ya kwantar da ita, yana mata fulo da ƙullin kayansu.
"Kwanta ina zuwa, zan samo miki abincin da zaki ci."
Hannunsa ta riƙe "Ina jin tsoro Yayanah!"
"Ba abun da zai faru da ke Khadijatu, yanzu zan dawo da yardar Allah."
Kai ta shiga girgiza masa kafin wani lokaci hawaye ya shiga zuba a idanuwanta.
"Bazan iya zama ba Yayanah!" Ta faɗa cikin sanyin murya jikinta duk ya ɗauki rawa kamar da aka sa mata wutar lantarki.
Kansa ya dafe da hannunsa yana ganin yanda ta futa a kamanninta, duk ta furgice, tun bayan shigowarsu cikin gari.
"Ya Allah!" Ya faɗa yana zama a kusa da ita.
******
KADUNA, NIGERIA
A hankali ya ke juya kofin madarar da ke hannunsa, idanuwansa na sarƙafe a cikin na'ura mai ƙwaƙwalwa, lokaci zuwa lokaci yake dannata.
Fuskarsa ko kaɗan babu walwala, wanda hakan ke nuna cewar yana cikin damuwa.
Wayarsa ce ta yi ƙara, ya ke kallonsa kan allon wayar, *Ummie nah* sunan da yaga yana yawo akan allon wayar.
Ajiye kofin madarar ya yi daga hannunsa, sanan ya ɗauki wayar ya kara a kunnensa "Assalama Alaikum!" Ya faɗa cikin sanyin murya, wadda ba zaka tsammaceta daga gareshi ba.
Shuru ya yi na ɗan lokaci, kafin ya amsa da "Toh!" Yana miƙewa akan ƙafafuwansa.
Daga ɗakin ya fita yana takawa cikin nutsuwa, da kamalar da ke gareshi. Sai da ya futa daga ɓangaran nasa sanan ya shiga wani kyakkyawan sashen da ya fi nasa ƙawatuwa, duk da bai kai nasa girma ba, amma yanda aka tsara wajen ya fi nasa kyau nesa ba kusa ba.
Da sallama ya shiga palon da aka cika shi da kayan alatu na burgewa, yanayin da yaga mutanen falon da kuma kallonsa da suke shi ya tabbatar masa da zaman da suke ba na daɗi ba ne.
Kujera ya samu ya zauna kafin ya rusuna a hankali "Barka da hutawa Ummie!"
Kallonsa ta yi tana nazartar Tilon ɗan nata, da take jin soyayyarsa fiye da sauran yaran nata "Yauwa Imran."
Daga haka ya yi shuru bai sake cewa kowa ko mai ba, ta san ba zai ƙara magana ba tunda ya tsuke bakinsa, ya kuma gyara gilashin da ke idonsa.
Wanan wata halayyace da ta sanshi da ita tun ƙuruciyarsa, har zuwa yanzu ba abun da ya sauya a gare shi.
"Baka ga 'Yan uwanka ba ne? Su ba zaka gaida su ba?"
Sai a lokacin ya sake kallon mutanen wajen, yayyunsa ne guda uku mata sai kuma Yayansa da yake bi ma.
"Sannunku!" Ya faɗa yana maida kansa ƙasa.
"Ciwo mu ke da zaka ce mana sannu! Ummie Imran ba zai taɓa sauya halinsa ba wallahi.
Fisabilillahi da girmansa da kome amma ace har yanzu bai san ya zai gaida mu ba? A gabanki yake kira mana Sannu kamar wasu kasu fama da ciwo.
Ni dama tunda naji ance Fatima ta bar gidan nasan matsalar nan tasa ce, shine har yanzu yake fama da baƙin muskilancinsa kamar kansa farau.
Na rasa wani irin mutum ne shi da bai san Ƙaddara ba, sama da shekara goma amma har yanzu ba abun da ya sauya zani na halayyarsa."
Kai ya ɗago ya kalleta, bai ce komi ba sai lumshe idanuwansa da yayi "Bakya gajiya da hayaniya Aunty Aisha."
"Bazan gaji ba, kamar yanda bakya gajiya da baƙin ƙulafuncinka."
"Aisha!" Ummie ta faɗa da ƙarfi sanin yanzu zai iya tashi yabar wajen ba tare da an kammala maganar abun da ya tara su a wajenba.
Murmushi ya yi kana ya tashi "Imran Zauna!" Ummie ta Faɗa da cikin sigar bada Umarni.
Zama ya yi yana kallon agogon da ke hannunsa.
"Me ya haɗaka da Fatima ta bar gidan nan ba tare da sanina ba."
Kansa ya nuna "Ni kuma ya zan sani!"
"Ku ji min maganar banza ko? Ta ya mutum da matarsa zata bar gida amma ace bai sani ba." Aisha ta ƙara faɗa cikin hassala kasancewarta mace mai zafin rai da zuciya.
"Ban sani ba Anty Aisha! Ki je ki tambayeta ƙila ta gaji ne." Yana gama faɗar haka ya miƙe yabar musu palon ba tare da ya sake tsayawa jin me za su ce ba.
"Taɓɗijam! Wallahi Ummie sai kin dagema ɗanki, al'amarinsa ƙara haukacewa ya ke." Aisha ta faɗa cikin ƙufula.
Wanda hakan ya sa sauran 'yan uwanta yin dariya.
"Akwai abun da ke damunsa wanda mu bamu sani ba. Ke kuma baki iya bin abun duniya a hankali ba Aisha komi sai kin yi zafi-zafi kamar cin ƙwan makauniya." Yayansu ya faɗa cikin tausayawa ɗan uwansa.
"ALLAH ka kawo haske a cikin rayuwar ɗana." Ummie ta faɗa tana tashi daga wajen, saboda sanin abun da ya sauya masa rayuwa daga walwala zuwa ƙunci.
🌷🌷🌷🌷🌷
#InuwarGajimare
#Dabanne
Wattpad @Oum_Nass
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
®NWA
©OUM-NASS 🏇
TAKWASS
ƘAUYEN TONI.
Zama yayi a kusa da ita, yana kallon yanda jikinta ke rawa har a lokacin "Me kike jin tsoro anan Khadijatu? Gidanmu ne fa da muke rayuwa a cikinsa tun wanzuwarmu a garin nan? Ba abun da zai faru da ke a cikinsa, ba abun da zai sameki. Yanzu zanje na dawo, zan nemi aikin da zan Kula da ke ne, na nemo mana abincin da zamu ci."
Kai ta shiga girgizawa tana ƙara damƙe hannunsa da dukkanin ƙarfinta "Ba zan iya zama anan babu kai ba Yaya! Duniya da mutanen cikinta duka sun sauya! Kafin yau Yarda ce mai yawa da sa rai ga mutanen da suke kewaye da ni.
Amma a yau tsoro ne da kuma furgici akansu, gani nake a ko wani lokaci wani zai sake farmakar rayuwata."
Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, shima hawaye ne ya ɓalle a idonsa yayin da ya kwantar da ita akan kafaɗarsa yana bubbuga mata bayansa.
'Me yasa rayuwa ta fiya ƙuntatawa na?' Tambayar da yake wa zuciyarsa wanda bashi da amsarta.
Tabbas bai taɓa tsammanin za'a samu wani mahaluƙi a wanan duniyar da rayuwarsa tayi kamancecceniya da tasa rayuwarba.
Da fari sun rayu a yankin da ba nasu ba, mutanen da basu da alaƙa da su, mutanen da suke ware jinsi da jininsu, suke aibanta wanda ba nasu ba.
Amma duk da haka sun rayu da su, basu koresu daga garesu ba, sun samu kulawarsu da tausayawarsu a lokacin da suke gaɓar ƙuruciyarsu, sun hidimta musu wajen basu lomar da za su kai bakinsu.
Sai dai a ganzu yasan ba za su basu wanan kulawarba, a yanzu duniyarsu ta ƙara hautsinewa, sun zama ababen nunawa da yima dariya tun a lokacin da ƙaddarar ƙanwarsa ta sauya.
Babu mutum guda da ya nemesu balle ya ji dalilin ɓacewarsu, ashe haka maraichi ya ke? Yau da mahaifiyarsu na raye da ta rungumesu ta lallashesu, ta kuma shimfiɗa rayuwarta dan ɓoye labarinsu.
Amma kuma a yanzu babu abun da ya rage, domin tun faruwar lamarin labarinsa ya cika gari.
Ido ya lumshe yana jingina kansa a jikin bangon ɗakin, ɗacin da ke maƙogwaransa ya gaza faɗawa, da ƙyar ya tattara yawu mai ɗacin da ke bakinsa ya haɗiye.
A hankali yaji numfashinta na sauƙa akan kafaɗarsa, hakan ya ankarar da shi ta samu barci ne. Gyara mata kwanciyarta yayi daga jinginar da take zuwa kwanciya. Hakan ya sata buɗe idanuwanta tana riƙe hannunsa "Kada ka tafi ka barni Yayanah!" Ta faɗa a hankali tana rufe idanuwanta saboda barcin da ya ci idanuwanta.
Lumshe nasa idon ya yi a hankali saboda tausayin rayuwarsu da kuma makomarsu.
Kafin yau kullum Khadijatu ke ƙarfafa masa gwuiwa akan ya fita ya nemo musu abin da za su ci, wani lokacin har rakiya take masa. Idan aka masa wani abu na ɓatanci wanda zai sa zuciyarsa sosuwa takan zauna ta ƙarfafa masa zuciya da bashi haƙuri akan kada ya yi fushi.
A lokaci irin wanan kuma suna zama ne su ci abinci a tare, ta ɗauko littafin karatunta na makaranta tana koya masa abun da ake musu a makarantar, hakan yasa shima yake iya wasu abubuwan.
Amma kuma sai gashi yau komi ya sauya, rayuwarsu ta hautsine ta yanda labarinsu bai da daɗi.
Ya ɗauki tsawon lokaci a wajen kafin ya iya zameta daga jikinsa ya tashi, cikin sanɗa ya bar ɗakin. A gaggauce ya bar gidan ya nufi gidan Mai gari.
Tun zuwansa mutane suke kallonsa suna haɗa kai suna ƙus-ƙus, bai kawo komai a ransa ba kasancewar wanan ɗabi'arsu ce.
Da sallama a bakinsa ya ƙarasa wajen ciki-ciki suka amsa masa sallamar suna kallonsa suna ƙara haɗe kansu waje ɗaya.
Risinawa yayi ya gaida Mai gari, amsawa yayi fuskarsa ba yabo ba fallasa, sanan ya gaida sauran mutanen da suke wajen.
"Babba an sauyama Khadijatu asibiti zuwa birnin Kano! Shine na zo na sanar da kai."
Gyaran murya Mai gari yayi "Ina Ishaƙ ya ke?"
Risinawa ya yi cikin girmamawa gabansa na tsananta bugawa, dan ya daɗe da