Showing 42001 words to 45000 words out of 91747 words

Chapter 15 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

802

sa takun-kumi ga kowa.
Ranar da kuka Hajara ta sameni akan sai na faɗa mata asalinta, domin har lokacin ta kasa tuno kanta, duk da kalar neman maganin da muke da binciken da muke, ƙarshe sai cewa akayi sai irin hatsarin ya sake faruwa ko zata tuno kanta.
A lokacin ban faɗa mata ba, domin ina tsoron abun da zata iya yi. sai da ta bari na bar gidan sanan ta dawo ɗakina ta min filla-filla da takardun ɗakin hotonta ta gani da na wasu mutane masu kama da ita, sai kuma sunan garin malam-madori a jiki.
Su ta ɗauka ta fice a ɗakin, babu wanda yasan sun bar gidan, sai direban dana wakilta akan ɗaukansu zuwa unguwa, shima sai da yayi da gaske da mata alƙawarin bazai faɗa minba sanan ta shiga cikin motar ya kaita.
Labarin rasuwar direban ne da yayi hatsari ya same mu amma har yau ban samu labari akan gawar Hajara da ta yara na ba."

Kuka ya ƙara sawa da tsanani yana ware hannayensa duka biyun yana kallo "Na girbe sakamakon ƙaryar da nayi, na butulcema yardar da kuka min, ko wata rana tana zuwar min da ƙunci da ɗaci a cikin zuciyata, babu matar da nake so babu yaran da nake gani a matsayin yarana.
Ban saniba suna raye ne ko sun mutu? Ban samu damar neman yafiyar Hajara ba, ban nemi yafiyar iyayenta na haɗa hannayensu da itaba, nasan idan nace ku yafe min na so kaina da yawa. Shi yasa har yau na gagara zuwa inda kuke."
Kowa a palon kuka yake idan aka ɗauke Ammu da take ta jijjiga kai.
Hawayen fuskarta ta share ta miƙe tsaye "Ado tashi mu tafi." Ta faɗa cikin kakkausar muryarta.

Tashi yayi jiki a sanyaye yana kallon Abdallah da ya juye ya zama Imrana a gabansa, shi yasha ammaki duk yawonsa a duniya da ganin hotunansa bai taɓa kawowa shine Abdallah da ya auri ƙanwarsa ba. Hakan kuma na da nasaba da sakankancewar da yayi a matsayin ABdallahnsa talaka ne kuma maraya wanda labarin mutuwarsu ya riskesu.

"Dan Allah ku yafe mana, kada ku tafi ku barmu da nauyin zunubanku a ranmu!" Ummi ta faɗa tana riƙe ƙafafuwan Ammu.
Kallonta Ammu ta yi ta kalli mutanen da ke palon sanan ta tauna laɓɓanta na ƙasa, ɗacin da ke taso mata a zuciya take son maida shi.
"Me yasa lokacin da kike aikata abubuwan baki tuna cewa akwai nauyi da zunubi a cikinsa ba! Kun siyar da yardar da muka baku, kun musauya mana ita da butulci da ha'inci ke da ɗanki.
Baku taɓa kawowa aranku Hajara nada gata ba a duniya? Bai taɓa baki labarin zinariyar zuciyar da ke garemu ba ta kyautatawa duk wanda suke tare da mu?
Bana jin koda ace Hajara zata dawo duniya zata yafe miki ke da ɗanki, domin ku mayar mata da ƙunci akan fuskar dariyar da take da ita.
Dama ganganci ne duk bayan wanan abun da ya faru ka tsugunna a gabanmu kace mu yafe maka Abdallah! Kuskurene bayan ka sabauta mana rayuwar ɗiyarmu da jikokinmu kace mu yafe maka! Dama tun a lokacin da hatsarin ya faru ka sanar da mu da munzo tun akan lokaci.
Ba Umminka kaɗai ce ta sabauta mun rayuwar ɗiyaba, har da kai da sakacinka, da tun lokacin ka dawo min da ɗiyata da na amsheta cikin farin ciki na kula da rayuwarta koda ace baba namijin da zai sake neman aurenta."

Hawayen da ya sauƙa akan fuskarta ta goge tana yin murmushin da yafi kuka ciwo "Ko wasu iyaye suna fatan binne yaransu ne suyi musu addu'a amma mu bamu samu koda ganin tokar gawar tamu 'yar ba.
Ku kunyi abun da zaku iya, sauran kuma mun barku da wanda ya haliccemu.
Mu tafi Ado!"

Ammu ta ƙwace ƙafarta daga ruƙon Ummi suka fice suka bar gidan, a ciki babu wanda ya ƙara yunƙurin binsu balle su nemi yafiyarsu.
Sai da suka zo fice a gidan sanan Ammu ta kalli Baba "Da kuɗi a hannunka Ado?"

"Eh Ammu!" Adai-daita ta tsayar musu suka tafi tasha motar kano suka hau har lokacin babu wanda ya ƙara magana a cikinsu, zuciyoyinsu sun tsinke sun gama karaya da sha'anin rayuwar mutane........


🌷🌷🌷🌷🌷

GIRMAMAWA...
Kuyi haƙuri idan kun samu errors bana samun damar yi muku editing.[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

    000002900000


  LAGOS, NIGERIA.

A cikin kwanaki biyun nan da suka zo Amrah ta fice a kamaninta ta rame ƙware saboda tsangamar da Aabid ke mata akan ta samar masa ciki.
  Tun tana kuka tana roƙonsa har ta zo ta gagara roƙonsa, ta koma kamar sunduƙin da aka sassaƙa shi. Ya zame mata asalin sojanta da ta sani a baya, abun har ya fara bata tsoro.
  A cikin satin kuma ta fara jin sanji a jikinta, duk lokacin da ya zo da niyyar kusantarta sai taji zuciyarta na tashi, tana jin ba daɗi a haɗuwar jikinsu, shi kansa ƙyan-ƙyaminsa ta ke yi.
  Da ya ɗauka abun wasa ne ko kuma saboda ta gaji sai da ya mata da iya ƙarfinsa anan ta wanke shi da amai,ta fara jan numfashinta da ƙyar numfashinta na ta barazanar ɗaukewa, jini ya fara biyo ƙafafuwanta.
    Ba shiri ya ɗagata ya sunkuceta zuwa toilet ya mata wanka doguwar riga ya zira mata a jikinta ya ɗauketa zuwa asibiti, duk ya gama ruɗewa ya fuce a kamaninsa, ko sojojin da suke gadinsa bai sauraraba sai su ne suka biyo bayansa har zuwa asibitin, da ƙaran jiniyar da ya gama cika asibiti.

   A guje likitoci suka tareshi da gado suka ɗora Amrah zuwa wani ɗaki. Har yayi zai biyo su suka dakatar da shi suka barshi yana ta kaiwa da kawowa, tsoronsa ɗaya kada ya rasa Amrah saboda son zuciyarsa. Yana mahaukacin sonta ba zai iya jure rayuwa babu itaba.
   Hawaye ne ya sulalo akan kumatunansa yayi saurin sharewa gudun kada mutane sugan shi yana kuka.
  
  Bayan wani ɗan lokaci, likitocin suka  fito da sauri ya tari Babban likitan yana tambayarsa lafiyar matarsa.
  "Alhamdulillah tana cikin ƙoshin lafiya, ka biyo ni office na maka bayani."
  Ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi jin Amrah tana lafiya, daga nan yabi bayan Likitan har office ɗinsa.
  "Bismillah zauna!" Likitan ya faɗa masa yana masa nuni da kujerar da ke gabansa.
  Zama yayi yana fuskantar Likitan da yake ta rubutu a jikin wasu takardu, sai da ya gama sanan ya miƙa masa hannu suka gaisa.
  "Ya akayi kake wahalar da matarka bayan kasan akwai shigar ƙaramin ciki a jikinta? Saura ƙiris cikin ya ɓare Allah ya taƙaita muka tsayar da jinin da ke zuba."
  Ido Aabid ya wara waje yana kallon likitan kamar bai san abun da yake faɗa ba "Mi kace yana damunta likita? Sake faɗa naji ko kunnuwana ne suke min gizo."
  Murmushi likitan yayi sanin bai san abun da ke faruwa ba "Matarka na ɗauke da cikin sati biyu. Amma sanadin yawan saduwar da kake da ita cikin na barazanar fita a jikinta, kasancewar bai yi ƙwarin da zai iya ɗaukan abunka ba ga kuma mahaifarta bata da ƙwarin riƙe ku kai da yaron cikinta.
  Idan har baka bata hutu ka ɗaga ƙafaba to tabbas nan gaba ba zamu iya tsayar da cikinba."

   Tun da likitan ya faɗi kalmar ciki a jikin Amrah bakinsa yaƙi rufuwa ji yake kamar ba gaske, kamar dai har lokacin kunnunwansa ke masa gizo.
  "Likita kana so kace min Amrah na ɗauke da cikina?"
  "Tabbas tana ɗauke da cikinka, tsawon sati biyu."
  Miƙewa yayi daga kan kujerar da yake ya yi sujjada a ƙasa yana ɗaga hannayensa sama "Allah nagode maka!"  Shine abun da yake faɗa yana mai-maitawa.
  Daga nan ya zura hannunsa a cikin aljihunsa ya rarimo duka kuɗin da ke aljihunsa ya miƙawa likitan wanda shi kansa bai san adadinsu ba.
   "Wanan tukuicinka ne." Ya faɗa yana barin ɗakin, sai kuma ya sake dawowa "Likita zan iya ganin matata?"
  "So... So.. sSosai kuwa yallaɓai!" Likitan ya faɗa cikin rawar murya saboda kuɗaɗen da ke riƙe a hannunsa.
  Tashi yayi ya raka shi har ɗakin Amrah sanan ya fito ya barshi, hawa gadon yayi ya ƙan-ƙameta gam yana jijjigata "Nagode Amra! Nagode da bani farin cikin raina." Mutsu-mutsun ƙwace kanta take daga jikinsa amma ya gagara sakinta.
  Cikinta ya shiga shafawa "Amrah duba nan ki gani, nan ajiyata ce a cikinsa, kina ɗauke da gudan jinina Amrah." Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta.
  "Da gaske ina da ciki a jikina Zumar?"
  Dariya yayi yana ƙara ƙanƙameta wanda ya sata sakin ƙara "Da gaske mun kusa zama Dady muka." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da wani yalwataccen farin ciki.
  Wayarsa ya ɗauke ya kira Dadynsa, yana ɗagawa bai bari yayi magana ba ya rigashi "Dady na kusa zama Baba nima! Amrah na ɗauke da cikina Dady."
  Daga can ɓangaren Alh. Mai tama ya tashi zaune daga kishingiɗen da yake "Da gaske kake son!"
"Muna ma asibiti Dady ka zo tare da Momy ta ga ɗana."
"To son ai nima dole na zo na ganku."

Ba'a ɗauki wani lokacin mai tsawo ba asibitin ta cika da mutane da bushe-bushen algaita, ranar likitoci sun sheda da ranar sa'arsu ne saboda bajinta da kyautar girman da Alh. Maitama yayima ma'aikatan asibitin, shi kansa likitan da ya bada labarin haihuwar ba ƙaramar kyauta ya samu ba, ciki kuwa harda kyautar kujerar makka.

Daga nan dai Momy tace gidansu za su tafi da ita ta huta, shima Aabid cewa yayi binsu zai yi baiga ta zama ba.
Amrah dai kunya ta hanata magana dan bata taɓa tsammanin haka daga Aabid da iyayensu ba, cikin sati biyun ne ake ta ma yamiɗiɗi da cin-cirindo haka? Lamarin bai ƙara tsinke mataba sai da taga yayanta da 'yan gidansu sunzo, ita dai bata san me suka ɗauki ɗaba haka, da suka nuna masa soyayya tun kafin ya zo duniya.

*****
Kano Nigeria.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

   00000030000000

KANO, NIGERIA.
 
   Kamar kurame haka suka koma tun bayan shigarsu asibitin, duk da cewa su Inna da Ishaƙ sunyi mamakin ganin sun dawo a kan lokaci.
  "Baban Indo ina Hajaran? Kun sameta kuwa?" Inna ta faɗa tana kallon bayansu da bata hango wani mutum a bayansu ba.
  "Ko dai ba shi bane Abdallah da ya auri Hajara ba? Ko kuma dai kamannine dai?" Ta sake aika musu da tambaya ganin babu wanda yayi magana a cikinsu.

   Zama Ammu ta yi akan gadon tana kallon fuskar Khadijatu da ta samu barci "Har yanzu bata farka ba ne?" Ammu ta tambayesu tana share tarin tambayoyin da Mairama ta ke musu.
  Jiki a sanyaye Mairama ta yi magana "Ta tashi amma kuma tana yawan zabura da ihu, kamar dai yanda ta saba, sai dai na yau ɗin yafi na kullum." Ta ƙarasa maganar tana kallon Baban Indo da wara masa hannu na son ya mata ƙarin bayani.

  Kai ya girgiza mata kawai yana ɗaga mata hannu alamun ta jira.
  "Ammu ƙwaƙwalwar Khadijatu ta samu matsala sanadin fyaɗen da aka mata! Duk wanan lokacin ashe ta riga da ta zauce bamu ankare ba."  Ishaƙ ya faɗa hawaye na sauƙa akan fuskarsa.
   Maganar Ishaƙ ya haddasa bugawar zuciyar Ammu da ƙarfi.     'Ƙwaƙwalwar Hajara samu matsala ta manta komi da ya shafi rayuwarta ta baya!' Kalaman Imran suka daki kunnuwan Ammu kamar a lokacin yake faɗa mata su.
 
   Hawaye ne ya silalo akan kumatun Ammu na tausayama rayuwar Khadijatu, lallai tsautsayi sila gareshi yayin da ƙaddara ke da saurin zuwa.
   "Ya Allah ka kawo mana ɗauki." Ammu ta faɗa hawaye na sauƙa akan fuskarta.
  Ƙofar ɗakin aka turo wanda ya sasu saurin kallon ƙofar Ummi ce ta fara shigowa fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye, bayanta kuma Imran ne shima ya shigo ɗakin daga nan sai su Anty Aisha da Abdul, Hassana da Hussaina.
"Me kuka biyoni nan ku yi min? Ko kun zo ne nima ku hallaka ni kamar yanda kuka hallakar min da ɗiyata?" Ammu ta faɗa cikin masifa da zafin rai. Zafin da ke zuciyarta na ƙara ninkuwa daga matakin da yake a baya.
  Tsugunnawa Ummi ta yi wanda suma yaran nata suka yi a gaban Ammu ɗin  "Dan Allah Ammu ki tsaya ki saurareni, koda sau ɗaya ne ki tsaya ki saurari ni."
  "Me zan saurara daga bakinki? Wata kalma ce ta rage daga bakinki? Ai duk wani abun da zaki faɗeshi a yanzu kin daɗe da faɗama Hajara shi. A yanzu kuma babu wani abun da yayi saura tsakanin mu da ku! Komi ya riga da ya ƙare."
   "Har yanzu akwai abun da yayi saura tsakaninmu, domin jinin da ya gauraya ya tsaga ya kuma yi male-male a cikin tafiyar.
Idan har na aikata zalinci a cikin rayuwar Hajara to nice na girbe abin da na shuka da zalincina, na kwashe kaso mai yawa na wanan zalincin." Ummi ta faɗa tana kuka wanda yasa jikinsu duka ya yi sanyi idan har aka ɗauku Ammu da har lokacin jininta ke tafasa.
"Abdallah da na sani maraya ne wanda ke neman halak cikin ko wani hali, shi na ɗauki ɗiyata na damƙama a hannunsa. Amma wanan!" Ta faɗa tana nuna shi da hannunta.

Kafin ta ƙara magana Ishaƙ ya tare "Dan Allah Ammu ki sauraresu! Duk abun da suka miki ki tsaya ki ji abun da ya ke tafe da su!" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa da take ɗauke da rawa.
Ido Ummi ta wara tana kallon matashin yaron da ke magana a gabansu, hankalinta ya dugunzuma ta yanda bata tsaya ta ƙarewa mutanen da ke ɗakin kalloba.
Miƙewa tayi akan ƙafafuwanta ta isa kusa da shi tana shafa fuskarsa, wanda hakan yaja hankalin duk mutanen da suke ɗakin suke binta da kallo.
Gefen fuskarsa ta juyar zuwa bayan kunnensa anan wani dogon tabo ya fito da yake ɗauke da alamun anyi ɗinki a wajen.
Sakin fuskarsa tayi ta riƙe hannunsa tana duba yatsun hannunsa anan taga ainihin shidannin da aka yanke na hannunsa, sakinsa ta yi ta ƙarasa gaban Khadijatun da take kwance, fuskarta tayi suwal karan hancinta ya ƙara fitowa idanuwanta sun fito duk da arufe suke.
"Idan har Hajara bata zo hannunku ba ya akayi yaranta suke wajenku?" Ta aika tambayar saitin Ammu da take cika tana batsewa.
Ba zata taji maganar hakan ya sata miƙewa tsaye "Me kika ce?"
"Ya akayi naga yaran Hajara a wajenku? Ina nufin waɗan nan yaran na Imran da Hajara ne. Ta ya akayi suka zo wajenku bayan kunce baku da labarin Hajara?"

Jikin Ammu ne ya shiga rawa tana nuna Ummi da hannu tana kallon Ishaƙ da Khadijatu da shima kansa Ishaƙ ɗin kansa ya masa gingirim.
"Kika ce wannan yaran Imran ne?" Ammu ta faɗa bakinta na rawa.

Juyowa tayi tana kallon mutanen ɗakin da suma suke kallonta kowa bakinsa a buɗe. bata iya magana ba, ta ɗauki wayar salular da ke hannunta ta danna madannai "Yasir ka shigo room 0013."
Ta kashe wayar sanan ta ƙara danna wayar hannunta "Anwar ka zo da kayan aikin da zaka ɗauki jini." Ta kashe wayar ta zauna har lokacin bata yi magana ba.


Ɗakin da aka turo shi ya sa hankalinsu juyowa kan wanda ya shigo ɗakin, gaba ɗayansu miƙewa sukayi a tsaye suna kallon wanda ya shigo ɗin, suna ƙara kallon Ishaƙ da ya ƙame kamar saƙaƙo yana kallon mutumin.


🌷🌷🌷
DAN Allah kuyi malejin wanan, in sha Allah zuwa anjima zan muku wani post ɗin, muna fama da rashin wutar nepa.
Girmamawa.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

B00000310000T


Duk a cikinmu mun ƙame da kallon mutumin da ke ɗauke da zagayayyir dattijuwar fuskar Ishaƙ, badan shekarun da suka fito a jikinta ba da babu abun da zai hana a kirashi da sunan Ishaƙ.
Sai dai ban-bancin dake garesu bai wuce na yanayin hasken fata da shekarun da mutumin zai faɗa masa ba.
Cikin takun ƙasaita ya shiga ɗakin fuskarsa babu yabo babu fallasa yana kallon mutanen da suke ɗakin har idanuwansa ya sauƙa akan fuskar Ishaƙ ɗin.
Ƙarasawa yayi har gabansa yana kallonsa tun daga sama har ƙasa, mamakin da ke kan fuskarsa ya gaza ɓoyuwa, asalima shafa fuskar Ishaƙ ɗin yake, yana ƙare masa kallo tun daga samansa har zuwa ƙasansa.

"Allah Al-hakimu!" Ya faɗa da sautin muryarsa mai cike da nagarta.
Yana ƙara kallon mutanen da suke ɗakin "Nasha ji ana magana akan masu kamanni iri ɗaya a duniya, amma jin labarin nake kamar hikaya, musamman idan nayi la'akari da yaran cikina basu ɗauki kamannina haka ba.
Idanuwana sun kalli fuskata a jikin wanina ba wai madubin da nake dubawa ba. Ko ba'a faɗa minba wanan yaron Imran ne! Ko da ba'a tan-tanceba naji a jikina jinina ne shi."
Ya faɗa cikin taushin muryarsa yana ƙara damƙe hannun Ishaƙ da ke jikin nasa. Yalwataccen murmushin da ke kan fuskarsa kuma ya gaza ɗaukewa.
Su kansu su Ammu mamakin wanan kamannin suke, idan aka ɗauke su Abdul da suka ƙame a waje guda.
"Nifa kun ruɗani da yawa! Dan Allah kada kusa kaina ya buga da hautsinanniyar maganarku! Har yanzu na gaza yarda waɗan nan yaran Abdallah da Hajara ne. JI nake kamar kun shigo cikin labarin dan ku ruɗar da gajiyayyun shekaruna."

"Ammu ko makaho ya shafa wanan mutane biyun yasan akwai alaƙa ta jini a tsakaninsu, ki kalla da kyau hatta tsayuwarsu da komi nasu iri ɗaya ne da Yasir. Babu abun da Ishaƙ ya bari na kakansa komi nasa ne.
Ammu kada ki ɓoye mana gaskiyar da ta bayyana ɓaro-ɓaro, kada ki ruɗa kanki da son tanadin ɗaukan fansa a kaina, ki haramtama yara kusanci da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login