Showing 63001 words to 66000 words out of 91747 words

Chapter 22 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

801

ajiye tarihin da zan tuna na ɗana rayuwa kafin aure, na kuma ji daɗin rayuwata da macen bayan fage kafin tawa.
  Zuciyata sai ta ɓaci a lokacin, na fara faɗa akan "Me yasa suka gayyace ni tunda kun san ra'ayina?" Sun bani haƙuri a lokacin muka ci gaba da gudanar da fatinmu.
Anan suka kawo min baƙin loman da nafi sau, rashin sa'a yasa nasha shi, tun da nasha naji jikina ya sauya ba abun da nafi buƙata a lokacin face mace.
Ban san ya akayi ba, naji 'Yan mata biyu sun kewaye ni suna shirin mun Lalata, hakan yasa na fusata na bar wajen, gaba ɗaya na bar wajen fatin na shiga motata nabar garin.
  Ban taɓa shiga tashin hankali irin na ranar ba, kamar yanda ban taɓa jin abun da nake ji ba sai a lokacin, daga ƙarshe da nazo hanyar garin nan, kasa ci gaba nayi da tafiya saboda yanda naji cikina na min ciwo kamar zan mutu, burina ɗaya na sauƙe nauyin da ke ƙasan marata.
  A cikin wanan yanayin na hango yarinyar da bazan iya tan-tance kamanninta ba sai naji abun da ya nake ji ya ƙaru akan na da. Hakan yasa na fito a cikin mota ɗaukanta nayi na shige da ita kangon...." Kuka ne yaci ƙarfinsa ya kasa ci gaba da maganar, sai da yayi mai isarsa sanan ya ci gaba "Ta na roƙona tana min magiya akan kada na cuceta, amma bana jin a lokacin burina ɗaya na sauƙe nauyin da ke kaina.
  Duk da tace min ita marainiya ce amma ban saurareta ba haka na haiƙe mata, na cuci rayuwarta tun tana numfashi har sai da numfashinta ya ɗauke amma hakan bai sa na ƙyaleta ba har sai da naji na daina jin abun da nake ji sanan na ƙyaleta.

  Daga nan na tsallake ta ban ƙara waiwayarta ba, na manta da komi da ya faru a lokacin na koma Legos mahaifata. Sai yanzu da aka mai-maita abun da na mata akan yarinyata 'yar shekara Shida wani ya mata fyaɗe ya gudu shima.
  Yanzu bamu da tabbacin ɗiyata xata ci gaba da rayuwarta kamar ko wacce yarinya, likita yace ba lallai ne ta ci gaba da rayuwaba saboda abin da ya mata ya ƙone mata ƙwayoyin halittarta sanan ƙwayar cuta ta shiga cikinta kamar yanda mahaifarta ta fito waje." Kuka ne yaci ƙarfinsa hakan yasa mutanen garin rafka salati suna kuka suma.

  "Wanan masifar ta kai masifa, yarinya 'yar shekara shida aka yima fyaɗe! Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un." Abun da Mai gari ya faɗa kenan yana matse hawayen fuskarsa, jikinsa sai faman rawa yake  kamar zai faɗo ƙasa.

   "Allahu Akbar! Haƙiƙa rayuwar duniya 'yar ƙarama ce, duk inda akaje aka dawo dole hakki ya bibiyi mai shi.
  Kaga ƙarfin ikon Allah ko? Tun kafin aje ko ina Allah ya bi mata hakkinta dai-dai da zalincin da ka aikata mata. Sanan kamar yanda ka tarwatsa mata rayuwarta ita da ɗan uwanta kaima sai gashi farin cikinka ya gama tarwatsewa cikin ɗan lokaci. Lallai kana da sa'a da akayi saurin an karar da kai tun kafin lokaci ya ƙure maka, amma ko yanzu ma bani da tabbaci akan baka makara ba." Malam Liman ya faɗa yana jujjuya kansa.

  "Dan Allah kada ku ƙi haɗa ni da ita, ku kirata na roƙeta na nemi yafiyarta."
  "Ai bata garin nan Yaro! Sanadin abun da ka mata sun haɗu da iyayenta! Kasan waye Ubanta kuwa?"
  Kai ya girgiza cikin sanyi jiki, shi ina ruwansa da sanin babanta, yarinyar da take rayuwa a ƙaramin ƙauye irin wanan yana da tabbacin babanta ba wani ba ne face manomin da ya gaji da kartar ƙasa da kuma fige ciyawa.

  "IMRAN YASIR NASAR shine mahaifinta." Kunnuwansa yaji kamar sun masa gizo.
  "Wani Imran ɗin Baba?"
"Dakta Imran Yasir Nasar, fitaccen ɗan kasuwa wanda yayi shuhura wajen aiyukan alkhairi, mazaunin Kaduna. Shine mahaifinta, yanzu haka ma suna can ita da yayanta da sauran danginsu."

   Kamar sauƙar aradu haka yaji maganar tasa indai Imran ɗin da ya sani ne to shikam tasa ta ƙare, amma kuma ko zai yi guduwa-gunduwa da shi sai yaje ya roƙeta gafara, zai durƙusa su taka shi indai har zasu barshi ya ga Khadijatu ya roƙeta gafarar abun da ya mata.

  Tashi yayi tsaye yana haɗe hannayensa biyu waje ɗaya "Nagode sosai! Dan Allah ku yafe min kuma, zan je itama na roƙi yafiyarta!" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

   "Mu baka mana komi ba, asalima abun da ka mana shumfuɗar hanya ka mana saboda gyara mu'amularmu da mutane, sai dai ka sani ka cutar da su cutarwa mafi muni da tsanani, ka tafi ka bar baya da ƙura domin ƙalubalen da suka fuskanta irin abun da ko a cikin labari bamu ci karo da shi ba. Allah ne ya ƙaddara musu sauran rayuwa a gaba shi yasa har yanzu suke raye." Nan suka faɗa masa abun da ya faru da su tun tafiyarsa har zuwa ƙona sun da akayi, da kuma labarin da suka basu bayan barinsa garin su.

   Kuka yake kamar ransa zai fita, yana jin tarin zalincin da ya aikata akansu "Ni ne silar komi! Ni ne azzalumin da ya wanzar da zalunci a cikin duniyarsu. Ya Allah ta ina zan fara neman wanan sauƙin? Ta ina zan nemi yafiyarsu?" Ya faɗa cikin kuka jikinsa na rawa kamar zai faɗi.

    "Ba abun da zai gagara. In sha Allah zata yafe maka, kaje kada lokaci ya ƙara ƙure maka." Malam Liman ya faɗa, cikin sanyin jiki ya shiga mota suna ɗago masa hannu har ya fice a garin.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

GIRMAMAWa.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

   440000

Tunda ya shiga motar hawaye ke sauƙa akan fuskarsa, yana ji kamar ba za su yafe masa ba, duk da ƙarfin gwuiwar da mutanen garin suka bashi.
  Gudun da yake yasa ya isa garin ana sallahr azahar, wannan dalilin yasa ya samu wani masallaci ya tsayar da motarsa.
Alwala yayi a lokacin ya kalli yanda jikinsa ya yi duƙun-duƙun, jini ya bushe duk ya ɓata masa kayansa, tabbas yana jin gaɓɓan jikinsa suna masa ciwo, amma kuma tashin hankalin da yake ciki ya mantar da shi dalilin da yasa ciwon.
  Gidan wanka ya nema ya biya yayi wanka sanan ya sauya wani kayan a jikinsa, a lokacin wata ƙaramar waya take ta faman ƙara a  cikin motar.
  Ɗauka yayi yaga dai wayarsa ce da yake amfani da ita wajen kiran mutanen gida, shi ya manta da barunsu da yayi cikin tashin hankali, domin abun da ke gareshi ya girmi nasu tashin hankalin.
   Wayarce ta ƙara yin ƙara hakan yasa shi kallon allon wayar, sunan Dad yaga yana ta yawo a jiki, cikin sanyin jiki ya ɗauki wayar "Kana ina Aabid?" Ya tambaye shi muryarsa da tashin hankali.
  Yawu ya haɗiye mai ɗaci a  bakinsa "Kaduna!"
Cikin mamaki ya sake jin muryarsa "Me kaje yi Kaduna Aabid? Me ka tafi yi babu masu tsaro a tare da kai kabar  mu cikin tashin hankali?"
  "Zan dawo ne Dad, ina ƙoƙarin sauƙe nauyin da na ɗaukarma kaina ne!"
  "Akwai wani nauyi da ka ɗauka akanka bayan na iyalinka? Duk wani nauyin da zaka sauƙe a duniya bayan na kula da iyalinka ne Aabid! Ka dawo ka kula da yarinyarka wanda take tsananin son kulawa a yanzu."
 
   "Dad ku ai kuna nan, zaku kula da Nurie fiye da yanda zan kula da ita. Amma kuma hakkin da na ɗauka a kaina dole ni zan nemi sassaucinsa ga wanda na ɗorawa shi.
Ka tayani addu'a Dad, ka tayani roƙon Allah ya yafe min zunubin da na aikata!" Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya.
"Me ke faruwa da kai Aabid? Akwai wani abu da kake ɓoye mana ko?"
"Hakki Dad! Hakki ne ke bibiyata. Dan Allah ka tayani addu'a kada ka bincike ni a yanzu." Ya ƙarasa maganar yana kashe kiran, wayar gaba ɗaya ya kashe yana sakata a aljihunnsa.
Yayin da Dad yayi ta kiransa amma yake jin wayar a kashe, hankalinsa ya tashe ƙwarai dan bai taɓa ganin Aabid a cikin yanayi irin wanan ba, sai dai koma me yake faruwa da shi yana addu'ar Allah ya kawo masa sauƙi kamar yanda ya roƙi addu'a daga gareshi.

Bayan ya yi sallah ya nemi adireshin gidan Imran Yasir Nasar, kasancewarsa babban mutum wanda mutane suka sanshi yaasa bai sha wahalar samun gidan ba.
Tun daga yanayin unguwar da ya shiga jikin Aabid yayi sanyi, duk yawan barikin da yake a ƙasar nan bai taɓa ganin yanayin unguwa nitsatsiya irin wanan ba, ta ko ina matakan tsaro ne suke caje wanda ke shigarta. Hakan ya kawo masa tsaiko har sai da ya fidda takardar shedarsa ta aiki sanan suka shiga sara masa suna bashi hanya, wani a cikin jami'an tsaron ya masa jagora zuwa gidan Dr. Imran.

Gidan da yafi ko wani gida girma a unguwar da tsari nan jami'in 'yan sandar ya nuna masa, kai ya jinjina yana danna ƙararrawar motarsa, wanda yasa masu gadin gidan leƙowa, sai dai ganin motar da basu sani ba yasa basu buɗe get ɗin ba.
Har sai da ɗan sandar ya fita ya musu bayani sanan ya suka buɗe wangalelen get ɗin gidan.
"Ya Rabb!" Aabid ya faɗa lokacin da yake cusa hancin motarsa zuwa gidan, yana ganin ƙurewar ƙasa da dukiyar da aka gama narkarwa a gidan.
Daga nan idanuwansa ya sauƙa akan wasu 'yan mata guda biyu kyawawa kamar yaran larabawa, sai dai ɗaya a ciki ta ninka ɗayar kyau, amma kuma duk da haka za'a kirasu yaya da ƙannawa.
Bugun zuciyarsa ne ya ƙaru lokacin da idonsa ya sauƙa akan mafi kyau a cikinsu. Ya daɗe da tsayar da motar amma kuma ya gaza motsawa daga cikin motar, ƙaryata idanuwansa yake da ganin kyan da babu irinsa a duk yawonsa na duniya. Bugun da zuciyarsa ta ke kuma yana ƙara hauhawa fiye da ko wani lokaci.

Da ƙyar ya iya shahada ya fito daga motar, yana ji kamar iska zata ɗauke shi saboda rashin ƙarfin da ke tare da shi.
A hankali ya fara ajiye takunsa yana nufar inda 'yan matan suke zaune akan fararen kujeru da kuma kofuna a gabansu, sai yanzu ya tuna rabon da ya sha ruwa ya manta balle kuma abinci.
"Assalama alaikum!" Ya faɗa cikin muryarsa da ta gama dashewa da bushewa.
Ɗaya ce ta amsa a cikinsu ya yin da kyakkyawar ta ke duba wani ɗan ƙaramin littafi a gabansa "Dan Allah Khadijatu ƙanwar Ishaƙ nake nema."

Ajiye littafin ɗayar tayi a hankali ta ɗago da fararen idanuwanta masu girma ta ɗorasu akan fuskarsa, wanda shima a lokacin hankalinsa ya koma kanta, a tare gabansu ya buga da ƙarfi sanadin haɗuwar idanuwansa.
Ko da zata shekara dubu a duniya ba zata taɓa manta wanan fuskar ba, fuskar da ta kassara rayuwarta ta yagalgala mata burukanta a duniya.
Jikinta ne ya ɗauki rawa tana dafe kanta dake shirin barazanar ɓallewa saboda sara matan da yayi a lokaci guda "Khadijatu me ya faru?" Ɗaya budurwar ya faɗa, sai dai ina bata san me take cewa ba.
Idanuwanta ne suka shiga yawatawa a cikin baƙin kundin da ya shafe dukkanin farin cikin rayuwarta. Tsohon hoton da ta ke ƙoƙarin rufewa da buɗewa ne ya shiga dawo mata akan fuskarta kamar a lokacin yake faruwa.

"Ya Allah! Aisha kaina zai fashe!" Ta faɗa da ƙaramar muryarta numfashinta na fita sama-sama.
Ƙarasawa kusa da ita Aisha tayi tana ruƙeta, gami da jijjigata da dukkanin Ƙarfinta "Khadijatu ki me ya faru dan Allah?" Shine maganar da take cikin tashin hankali, amma bata iya bata amsa ba, a hankali numfashin da take ta faman ruƙewa ya ƙara yawan futa, hotunan da take gani a idonta suka ɗauke duhu ta mamaye wajen ganin nata.

"Wayyo Allah ku taimaka mana! Khadijatunah!" Aisha ta faɗa da dukkanin ƙarfinta hakan ya ja hankalin mutanen gidan suka fito a guje.

Ganin halin da take ciki yasa suka shige ciki da ita, kasancewar Imran yana gida, shi da Anwar, suka fara ƙoƙarin ceto rayuwarta.

Yayin da mutanen gidan suke ta kai kawo, banda Aisha da ta cika musu kunne da ihu, har sai da Baba ya daka mata tsawa sanan tayi shuru. Shidai Aabid jikinsa ya ƙara yin sanyi musamman da yaga yanda gidan ya cika da dangi duk saboda ta suma, ga hankalinsu da ya tsananta tashi. Babu wanda ya san da zuwansa balle ya nuna damuwarsa akansa.

****
Bayan wani lokaci duk suna zaune a babban falon sun tusa Khadijatu da tambaya "Me ya faru ya haddasa miki suma?"
Shuru tayi ba tayi magana ba, saboda ba zata iya faɗar ko waye ta gani ba. "Ke Indo me ya tsorata har ta yi irin wanan suman?" Baba ya tambayeta yana kafeta da idanuwanta.

Idanuwa ta fara yawatawa a cikin falon sai ta ga duk mutanen wajen sun zura mata ido suna jiran ji daga gareta, idonta ne ya sauƙa akan Aabid da shima kallonta ya ke a lokacin, hannunta ta ɗaga ta nuna Aabid "Wanan mutumin ne yazo yana nemanta, bayan ta ganshi ne kuma ta riƙe kanta, daga nan ta suma."

Sai a lokacin hankalinsu ya koma kansa, da mamaki suke kallonsa dan duk zamansa basu san da wanzuwarsa a gidanba "Yaro waye kai? A ina ka santa har ka zo nemanta?"

Kansa ya sunkuyar ƙasa yana jin zuciyarsa kamar ana caccakarta da allura 'Ta ina ma zai fara faɗar waye shi? Ce musu zai yi shine ya lalata musu rayuwa yarinyarsu ya tarwatsa mata duniyarta, ko kuwa ce musu zai yi shine azzalumin mutumin da ya keta martabarta? Bai taɓa sanin a rayuwa akwai irin wanan kunyar ba! Bai taɓa tunanin zai ji tsoro kamar yanda yake ji a yanzu ba!'
"Ya Allah!" Ya faɗa da sautin da bai futa da ƙarfi sai a iya kunnensa kawai ya jiyar.
"Kai muke sauraro duka!" Abbu Yasir ya faɗa bayan ya gama nazarta yanayin yaron.

Fuskarsa ya shafe da tafukan hannunsa, yana jin gumi na sartu a jikinsa, duk da sanyin na'urar sanyaya ɗakin da ke wajen.
"Ammm... Ummmm.. Ni abokinta ne "

"Aboki kuma?" Suka faɗa a tare suna kallon fuskarsa. Kai ya gyaɗa musu dan basu tabbacin maganarsa.

"Ƙarya kake! Duk duniyar nan Khadijatu bata da abokin da ya wuce ni! A cikin rayuwar Khadijatu babu kalmar ƙawa balle aboki! Waye kai? Me ya kawoka gidnmu har ka shiga rayuwarta da ta suma?" Ishaƙ ya faɗa cikin hargowa yana jin kamar ya make mutumin, jin cewar shine silar suman Khadijatu, duk da a ido ya girme masa amma gani yake tsaf zai kikkifa masa mari.
"Dan Allah ko zan iya magana da Khadijatu ita ɗaya?" Aabid ya faɗa, saboda ko wani kuzarinsa ya riga da ya ƙare, a yanzu ya manta da cewar shi soja ne wanda ke riƙe da akalar manyan sojoji a bayansa. Yayin da yake ganin kansa a matsayin ɗan ƙaramin ɓeran da namun dawa suka zagaye shi suna farautar rayuwarsa.

"Babu wannan damar! Duk abun da zaka faɗa mata ka faɗe shi anan. Bama ɓoyema iyayenmu komi da ya shafi rayuwarmu! Matsalarmu tasu ce tare muke haƙawa mu binne." Ishaƙ ya sake faɗa.

Kallonsa Aabid yayi yaga yanda yake kafe shi da idanuwa, ko ba'a faɗa masa ba yasan wanan shine Ishaƙ yayan Khadijatu! Shine mutumin da yake jin tsoro da kunyar haɗuwarsa da shi fiye da Khadijatun da iyayent.

Sauƙa yayi akan kujerar da yake ya ƙarasa gaban Khadijatu da take binsa da kallo tun bayan fara maganarsa. Gwuiwoyinsa ya zuba a ƙasa yana haɗe hannayensa waje ɗaya, hawayen da bai shirya sauƙarsu ba suka fara zuba akan fuskarsa "Nasan kin gane ni! Nasan kin ruƙe fuskata tunda har ganina ya sa kika suma, wanan ya ankarar dani fuskata bata goge a cikin zuciyarki da kuma kwanyarki ba."
Shuru yayi yana kallon yanayinta da take kallonsa ba tare da tayi magana ba, haka kuma bata motsa ba balle yasa ran zata masa magana.

"Nasan laifin da na miki laifi ne mai girma, wanda ya wuci a kirashi da laifi sai dai zaluncin da na wanzar da shi bisa son zuciyata. A yau gani a gabanki na kawo kaina, ban san ya kika ji a zuciyarki ba, amma tabbas na fara tono haƙon ramin da na gina shi da kaina, gadar zalincin da na haɗa ta rikita ta afka da ni a cikinta.
Dan Allah Khadijatu ki yafe min abun da na miki! Dan Allah ki yafe min kuskuren da na aikata a kanki a shekarun da suka wuce!"

Kallonsu mutanen falon suke, suna mamakin maganar da Aabid ya ke, suna kallon Khadijatu da son jin abun da zata faɗa.
Murmushi tayi wanda ya sa kumatunta lotsawa, wanda hakan ya bama sauran mutanen falon mamaki, abu ne mai wahala Khadijatu tayi murmushi mai tsayi haka, amma sai gashi yanzu tana yi har kumatunta na lotsawa.
Zuciyar Aabid ce ta tsananta bugawa lokacin da Khadijatun ta ke murmushi, zai iya cewa bai taɓa ganin wani mutum a duniya da murmushi ya masa kyauba kamar Khadijatun da ke gabansa, idanuwansa kuma sun shagala da kallon fuskarta.
"Waye kai? Me yasa kake neman yafiyata?" Ta tambaye shi har a lokacin murmushi ne akan fuskarta.

Ƙamewa yayi daga durƙushen da yake, yana kallonta, fuskarsa na sauyawa daga kallon da yake mata zuwa na mamaki, kamar yanda suma mutanen falon suke mata kallon mamaki......



🌷🌷🌷

😀😃Kalma ɗaya tak akan Khadijatu....
Dan Allah kuyi hqr da jinkirin da kuke samu, nagode da addu'arku ga ƙanwata, tana samun sauƙi.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG......


  4600000

    "Kaga ni ba! Kuskure sau ɗaya ake aikata shi a rayuwa, amma sai ya shafe tsawon rayuwarka yana caccakar ruhinka.
  Yanzu ba lokacin kuka ba ne a wajenka, saboda lokacin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login