Showing 27001 words to 30000 words out of 91747 words
igiyar ladan da nake ta saƙawa a duka shekarun da suka wuce ni."
"Fatima zuciyata ce ta gaza samun nutsuwa da komawar gidan da ba'a ƙaunarki. Ko wata uwa tana son ganin yaranta cikin farin ciki da nutsuwa a gidajensu, amma duk lokacin da na ganki sai naji karaya da rauni sun daki zuciyata. Ina gani kamar ban kyauta miki ba."
"A'a Mama ban taɓa kallon zaman da nake a gidan Imran a matsayin ƙunci ba, asalima na ɗauki hakan a matsayin ƙaddarata, ko wata mace akan jarrabeta a gidan mijinta ne. kamar yanda ko wacce take haƙuri a cikin gidan aurenta.
Dan Allah Mama ki barni na koma gidan Imran! Ki barni na ƙarasa rayuwata a ƙarƙashin ikonsa."
"Fatima amm...."
"Ya Isa haka Hauwa'u!" Abban Fatima ya faɗa yana ɗaga mata hannunsa.
"Tunda har ta dage ki barta ta koma ɗakinta. Idan ta zauna anan ma sabon labari ne zai buɗe, a yanzu abu guda zaki mata shine ki bita da addu'a da kyakkyawan fata akan zamansu ya ɗore."
"Shikenan Allah ya kiyaye ya kaɗai fitina, ya haɗa kanku da alkhairi."
"Ameen" Abba ya faɗa yana Juyo da kallonsa zuwa ga Fatima "KE kuma ki kula, ki ƙara haƙuri akan wanda kika yi a baya. Duk daɗin rayuwar gidanku ba zata kai ta ɗakinki ba, sai dai ba'a jin wanan daɗin har sai an haɗa da haƙuri.
Ki guji kawo suka da ƙaran mijinki ga mahaifiyarki, domin ke zaki iya mantawa amma ita abun zai ci gaba da caccakar ruhinta."
Kai ta gyaɗa "In sha Allahu Abba."
"Allah ya yi miki albarka. Sai ki tashi ki shirya kafin ya zo."
A hankali ta miƙe ta bar su anan. Bayan fitarta Abba ya ci gaba da bama Mama haƙuri wanda basu tashi anan ba sai suka tsinkayi sallamar Imran.
Fuska a sake suka karɓeshi suna sake sabuwar gaisuwa daga nan Mama ta tashi dan kira masa Fatima. Ko ba komi yau ɗaya Imran ya girmamata, ya kuma nuna damuwarsa a kan Fatimanta. Wanda a baya bashi da wanan lokacin, kenan wanan dalilin ne yasa fatima nacewa akansa da hango sauyi a tare da shi.
Itama tana shiga ta tuso ƙeyar Fatima da dama ta shirya kayanta tsaf, ta fesa wanka da ado, ɗakin sai maraba yake da ƙamshi kamar sabuwar amarya.
Murmushi Mama tayi tana jijjiga kai, lallai lamarin yaran yanzu sai kurum.
Har ƙofar gida ta rakota tana musu Allah ya kiyaye ita da Abba da fatan farin ciki ya ɗore a rayuwar tilon 'yar tasu da suke sonta kamar rai.
***
A hankali yake tuƙa motar yana yi yana kallon gefen Fatima, zuciyarsa cike da wani yanayin da bai gane kansa ba.
Ruƙo hannunta yayi wanda sai da suka ji shokin dukka ya kamasu, ido ya lumshe ya buɗe a hankali ya kalli Fatiman da idonta ke kallon hannayensu.
"Babu gaisuwa Madam!" Ya faɗa cikin sanyin murya kamar yana raɗa.
Kai ta ƙara sunkuyarwa ƙasa "Ina yini!"
"Ban amsawa."
Dago da kai tayi ta kalle shi cikin sanyin jiki, tana karyar da kanta "Me yasa?"
Bakinsa ya ɗan taɓe kaɗan yana kallon titin, yana ƙara murza hannunta da take jinsa har tsakiyar kanta "Sai da na roƙa! Kuma naga ba haka ake gaida miji ba."
"Yi haƙuri Amintaccena! Faɗa min yanda zan gaida ka."
Kallota yayi yana ƙara rage tafiyar motar, matsowa yayi kusa da ita ya sumbaci kumatunta. Hakan yasa ta ɗauke numfashinta gaba ɗaya, dan bazata taji sumbatar da yayi mata.
"Haka ake gaisuwar, ba sai kin wahalar da bakinki wajen magana ba."
Ido ta rufe da tafukan hannunta, tana jin kunyar da bata taɓa jin irinta ba. Abun da ya bata mamaki shine anya wanan Imran ɗinta ne? Idan shine ya akayi ya sauya lokaci ɗaya? Dan ta san Imran ɗin da ta sani magana wahala ta ke masa, ko yaushe sai dai yayi nuni da hannu ko ido, a yayi magana ya yi sau biyu ko ɗaya.
Bata ankara ba taji ta a sama, hakan ya sata dawowa a hayyacinta, sai dai ta makara domin tana ciki ruƙon Imran ɗin ne.
"Lokacin da kika fita ban da masaniya, amma kuma yanzu da na dawo da ke zan shigar da ke ne da ƙafafuwana da suka gaza ɗaukana wajen binki na tsawon lokaci."
Ido ta lumshe tana jin zuciyarta na yin rauni, tana jin soyayyar Imran na ƙara fallatsuwa a cikin ruhinta.
"Dan Allah ka ajiye ni na tafi da ƙafata." Ta faɗa cikin rawar murya tana jin hawaye na barazanar sauƙa akan idanuwanta.
"Me yasa?"
Kai ta girgiza masa hawayen da take ƙoƙarin riƙewa ya gangaro ƙasa "Bana so makauniyar zuciyata ta amince akan ko yaushe zan samu wanan tausasawar. Dan Allah ka barni na ci gaba da yin rayuwar da nake cikin yarda da kai na. Kada ka ruɗar min da tunani da zuciya da sabbin abubuwan da ba zasu ɗore ba."
Kafin ta ƙarasa taji ta kwanci a cikin abun da ya nutsar da ita, hakan ya sata buɗe idonta dan ganin inda ta ke, sai dai rumfar da yayi mata da dukkanin jikinta ya hanata samun tabbacin ganin wajen da take, duk da hasken da ke akwai a ɗakin, wanda bashi da yawan da zaka ga komi ya bayyana.
Bakinsa ya ɗora akan nata ba tare da yayi magana ba, hakan ya sata jan zuciya mai ƙarfi, ko wata ƙofa ta jikinta na buɗewa tana amsawa da ƙarfin ikon da ya samar a tare da ita.
A hankali yake tafiyar da ruhinta da tunaninta har sai da ta manta wani ƙunci ya taɓa riskarta a rayuwarta, duniyar da Imran ya kaita bata yi tsammanin zuwanta a tare da shi ba.
Ashe a baya rayuwa take cikin duhu da gidadanci? Me yasa ya ɓoye kansa ya barta take ta lalume cikin duhu?
Yau ɗaya dai ta fahimci darasin rayuwar da ko wata mace mai ji da kanta take bada labarinsa, yau taji dalilin da yasa maza kan kira kansu jarumai a duniya. Tayi kukan da ba zara tan-tance ko na miye ba, ta kira sunan Imran fiye da adadin lissafi, kalmar Amintaccen da ta ambata masa ya zanu a cikin zuciyarta da mafi tsadar alƙalami.
Sai dai bata da tabbacin shi zai zana nata sunan a zuciyarsa, domin kalma ɗaya yake nanatawa a kunnuwanta "Ki yi haƙuri yau ɗaya na sauƙe nauyin da ke kaina! Na gaza cika miki alƙawalin da na ɗauka! KIYI HAƘURI!"
Hawayen da ke sauƙa akan idanuwansa ya haɗu da nata ya cika raunataccen idanuwanta.
Kalmar haƙuri da gaza cika alƙawarin da yake ta nanatawa ta ankarar da ita hasken da ya cika zuciyarta yana tafe da ratsin duhu a cikinsa.
Kenan hakan na nufin duhu ne zai ci gaba da tasirantuwa a cikin duniyarta.
Anya bata yi gan-ganci da ta kira Imran da sunan Amintaccenta ba?
******
Lagos, Nigeria.
A hankali ya shiga sauƙowa daga kan matattakalan benin, hannayensa sarƙafe a cikin aljihunsa, kamar ko wani lokaci fuskarsa babu walwala a ɗaure take gam.
Sai dai ganin hasken ransa da yayi yasa shi saurin sakin fuskarsa, yana ƙarasawa kusa da ita.
"Barka da safiya Rabin raina!" Amrah ta faɗa tana risinawa daga tsayen da take.
Ɗan murmushin gefen baki yayi yana ƙarasawa kusa da ita, sumbatar goshinta yayi sanan ya amsa mata gaisuwarta "Kin tashi lafiya Habibaty!"
Kai ta girgiza cikin sigar shagwaɓa "A'a dai!"
Ido ya fiddo waje cikin sanyin muryar da yake mata magana "Me ya sameki? Zo mu je asibiti a duba min ke!"
Murmushi ta yi ganin ya rikice a lokaci ɗaya, nan ta fara dariya mai sauti "Lafiyata lau Hubbi! Na daɗe ban ganka a ruɗe ba ne kawai! Sanan yau naga fuskarka ba walwala. Hakan bai min ba!" Ta ƙarasa maganar tana langare kai, wanda ya sashi sauƙe ajiyar zuciya.
Ɗaukanta yayi ya zaunarta akan cinyarsa bayan ya zauna a kujerar da ke zagaye da falon "Kiran gaggawa aka min office. gashi ban gama gani kwalliyar da kika min ba, shine naji zuciyata ta ɓaci da yawa."
Wuyansa ta saƙalo da hannunsa tana kai bakinta saitin nasa, sai da ta tsotseshi son ranta sanan ta sake shi.
A hankali ta sauƙe ajiyar zuciya tana shafa bakinsa da hannunta "Me kuma yayi saura? Ka riga da ka tsotse kwalliyar, idan ka dawo wata sabuwa daban zaka tadda."
Fuskarta ya shafa ba tare da yayi magana ba, sanan ya sauƙeta akan cinyarsa, yana ɗaukan jakarsa ya rataya a kafaɗarsa.
Hannayensa kawai ya iya ɗaga mata alamar bye-bye. Wanda ta fahimci bai buƙatar rakiyar ta, dan ta riga data kunno shi da yawa.
🌷🌷🌷
Assalama alaikum, ya kuke ya ƙoƙari? Kuyi haƙuri da tsaikon da aka samu na post, in sha Allah zaku na samunsa ko a lokaci irin wanan ne, har zuwa lokacin da yarona zai samu lfy, kafin nan komi zai dai-daita, ban so na barku cikin jirana, ina ƙoƙarin sauƙe nauyinku da ke kaina. Nagode sosai da addu'arku Allah yabar zumunci.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
00002000
Malam Madori.
Tun shigowarsu garin Ishaƙ ke wara idanuwa yana kallon mutane da suke hada-hadarsu a cikin garin. Mutanen da basu damu da rayuwar wasu ba balle su taimaka musu.
Sai dai ya kawar tunaninsa da ya tuna mutanen garin dai guda biyu da suka musu hallaci suka basu dariyarsu da kuma kyautata musu da aikinsu. Baban Indo da kuma Likitan da ya amshi jinyarsa.
Sai dai rashin azanci da gidadancin da ke kansa bai barshi ya tambayi koda sunansa ba.
Sai da suka futa daga garin suka gangara wata unguwar da bata da cikowar mutane sanan Baban Indo ya tsayar da motarsa, a ƙofar wani ɗan matsakaicin gida.
Tun da motar ta tsaya ɗai-ɗaikun yara suka fara tsalle suna kiran "Ga Baba! Ga Baba!" Murmushi Baban Indo yayi kana ya fito a cikin motar, hannunsa ya zura a aljihu ya shiga raba musu alawa. Wanan yana ɗaya daga cikin al'adar Baban Indo duk lokacin da zai zo gida sai ya rabama yara alawa, dalilin da yasa da sun ganshi ya za su rugo su tare shi.
Sai da ya sallame su sanan ya koma ya buɗema su Ishaƙ motar "Ku zo muje ko?"
Fitowa suka yi a tare Khadijatu na riƙe gam da rigar Ishaƙ a hannunta, duk inda ya ɗauke ƙafarsa nan take mayar da tata ƙafar.
Da sallama Baban Indo ya shiga gidan suna biye da shi.
"Maraba lale!" Wata mata ta faɗa tana shimfiɗa musu tabarma a tsakar gidan.
Zama Baban Indo yayi yana faɗaɗa fara'arsa "Yauwa sannu da gida Mairama."
Juyar da kallonsa yayi ga su Ishaƙ da suke tsaye "Ku zauna mana Ishaƙ."
Kai ya girgiza yana kallon Khadijatu da take riƙe da shi gam-gam "A'a Baba kada mu ɓata mata tabarma, naga mai kyau ce kuma sabuwa."
Fuska Baban Indo ya tsuke kafin yayi magana Mairama ta rigashi yi "Haba yaro ku zauna mana! Me ne a ciki idan kun ɓata? Ai sai a wanke."
Zama yayi yana kallonta gami da girmamata. Gaidata yayi sanan ga zunguri Khadijatu da take maƙale da shi har lokacin.
"Malam ina ka samo baƙi haka masu alkunya?" Mairama ta tambaye shi tana kallonsu.
Shuru yayi na ɗan lokaci kafin daga bisani ya bata labarin abun da ya faru da su tun farkon haɗuwarsu "Wallahi na daɗe banji tausayin wani mutum ba a duniya sai wanan yaron! Ban taɓa ganin abun da ya bani tausayi da tsoron rayuwaba sai dalilin haɗuwata da waɗan nan yaran.
Yana kuka yana roƙon a kaisu asibiti da kuɗinsu amma suka ƙi ƙarshe suka bishi da duka. Wanan rashin adalcin har ina Mairama? Ta ina mutane za su ga ci gaba a rayuwarsu bayan sun cika zuciyarsu da rashin tausayi da imani? Ta ya zamu ga rayuwarmu ta dai-daita bayan kullum muna ƙoƙarin ganin bayan rayuwar wasu?"
Ido Mairama ta shiga matsewa da bakin zaninta sanan ta face hancinta da majina ta ƙi tsayawa.
"Lallai duniya ta cika da abubuwan mamaki da ban tsoro. Yaro bamu labarinku."
Ido ya runtsa ya shiga basu labarin rayuwarsu tun farko har zuwa yau, da dalilin zuwansu garin.
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Yanzu dan ɗaukan alhaki na ɗan Adam wanan tatsitsiyar yarinyar aka farɗa aka mata wanan lalatar! Ya Allah kada ka jarrabe mu da abun da yafi ƙarfinmu." Mairama ta faɗa bakinta na rawa irin na wanda yaci kuka ta ƙoshi.
"Zo nan ɗiyata!" Ta faɗa tana tashi daga mazauninta.
Ƙanƙame Ishaƙ Khadijatu tayi tana girgiza kanta da maƙe kafaɗarta "Ba zata zo ba ai Inna. Tunda wanan matsalar ta faru kullum cikin tsorata da tsoron mutane ta ke."
"Ai dole ta ji tsoron mutane! Duk wanda fuskanci mummunan ƙalubale irin wanan dole ya yi fiye da abun da wanan yarinyar ta yi."
Zama tayi kusa da ita tana dafa jikinta da kuma ƙoƙarin janyeta a jikinsa "Kiyi haƙuri Khadijatu, ruwan da ya jiƙa maƙoshi shi ke ƙonashi. Ko yaushe rayuwa takan zo da sabbin darrusan da ba'a tsammanin zuwansu, a hankali suke buɗewa suna cika bango.
Duka abun da ya samu rayuwarki a baya yana cikin shafin rayuwarki, idan kika rungumi ƙaddarar da ta riskeki sai kiga shafukan rayuwarki sun girmama.
Daga wanan ranar ku ɗauke ni a matsayin uwa a gareku! Duk abun da ya shafi rayuwarku ni zan tsaya muku kamar yanda zan tsayama Indo. Duk wanda ya tambayeku akan labarin iyayenku to ku nuna ni a matsayin uwar da ta wanzar da ku."
"Ba ke kaɗai ba, ni kaina daga yanzu na koma matsayin uba a garesu. Jigo kuma garkuwar a gareku."
Hawaye ne ya shiga sauƙa akan idonsa yana ji ko wata ƙofa ta jikinsa na miƙewa tana tashi, sanyin da yake ji a jikinsa ya samar da wata sassanyar iska ga zuciyarsa.
Hannayensa ya haɗa waje ɗaya yana so yayi magana amma bakinsa ya kasa, sai rawa yake yana karkarwa. Duk da wanan butulcin da yayi musu na ƙin auren 'yarsu amma su sun ɗauke shi ɗa, ba shi ɗayaba harda ƙanwarsa da mutane suke kyara suke gudun tsayuwa da su inuwa ɗaya.
Ruƙe hannayensa da suke rawa Khadijatu tayi, tana faman girgiza kai itama.
"Duk da larurar da ke damunmu shine kuka ɗauke mu a matsayin yaranku? Duk da na gujema haɗa jini da ku amma ku kun maida ni ɗaya daga cikinku. Wasu irin mutanene ku? Wata zuciya gareku haka?" Yaa ƙarasa maganar hawaye na ƙara ambaliya akan fuskarsa, yana jin kunya na ƙara lulluɓe idanuwansa da gangar jikinsa.
"Iyayen da suka damu da damuwar yaransu, suke kuma ɓata tsawon rayuwarsu dan ganin yaransu cikin farin ciki, kamar haka ne mu a wajenku?"
Baban Indo ya faɗa yan shafa kan Ishaƙ da share masa hawayen da ke fuskarsa.
Yayin da Mairama take bubbuga bayan Khadijatu.
"Ku yi haƙuri!" Khadijatu ta faɗa cikin sanyin muryarta mai rauni.
"Sallama alaikum!" Wata zazzaƙar murya ta ratsa su wanda ya sasu juyowa a tare.
"Ye muma yau munyi baƙi a gidanmu, na tafi na faɗa ma Ladidiya!"
"Indo! Indo!!!" Mairama ta shiga ƙwala mata kira amma ina tuni ta kai da ƙafafuwanta, wanda su da suke nan ba su ganta bama balle su tantance kamarta......
🌷🌷🌷🌷
OUM-NASSIG
000021000
Dariya Baban Indo yayi yana girgiza kai "Indo duniyar Allah."
Shine abun da ya faɗa fuskarsa ɗauke da fara'a wanda ke nuna tsantsar soyayyar da yake yi mata.
Baata ɗauki tsawon lokaciba sai gata ta dawo da cincirindon yara, wanda duka sa'aninta ne.
"Hajiya kun ga baƙinmu nan, kuma dukansu yayuna ne anan za su zauna."
Matsawa tayi kusa da Ishaƙ ta riƙo hannunsa "Kunga nima nayi Yaya! Daga yanzu ba za ku ƙara min gorin yaya ba."
Tunda ta shigo gidan ya ke binta da kallo yana mamakin ƙanƙantar shekarunta, domin a girme Khadijatu ma ta fita girma, to me yasa yace zai aura masa ita da ƙarancin shekarunta?
Shokin ɗin da yaji a hannunsa ne ya sashi saurin dawowa daga tunanin da yake, bin hannun yayi da kallo yagan shi cikin ruƙon yarinyar da aka kira da Indo.
Bai san me take cewa ba sai motsin da yaji bakinta na yi, kalma ɗaya yaji ta shiga kunnuwansa itace kalmar 'Yayanah ne!"
Mamakinsa ɗaya shine yaushe ta shigo gidan har ta samu ƙwarin gwuiwar kiransa da sunan yayanta.
Sakin hannunsa ta yi ta kamo na Khadijatu anan hankalinsa ya tashi, domin sanin halin da Khadijatu take ciki, sai dai ga mamakinsa bai ji tayi magana ko ihuba kamar yanda ta saba yi, sai kallon Indon ta ke da kallo.
"Kunga Yayuna masu kyau ne, duk da ba su yi wanka da kwalliya ba. Dukanku baku da yayu masu kyau."
"Ciyau lallaima Indo nan! To kuma sai meye idan yayunki sunfi namu kyau? Ke da sai yau kika gansu ma."
Kallon yarinyar tayi da harara "Eh ko yau suka zo dai sun fi yayinku kyau sosai."
Anan musu ya kaure tsakaninsu ƙarshe dai sai da Ishaƙ ya shiga maganar yana dariya, ganin yanda kowa ya riƙe ƙugu cikin shirin ta kwana.
"Ya isa haka kada kuyi faɗa! Ku da kuke faɗa idan kuka yi faɗa kuma ai a tsokaneku.
"Kumafa haka ne yayan indo!" Suka faɗa a haɗe suna riƙe haɓa.
"Yauwa karku na faɗa kunji ƙawayena?"
Kai suka ɗaga a tare daga nan suka fice a gidan dukansu har Indo ɗin.
Tsayawa yayi yana kallonsu fuskarsa ɗauke da murmushi, shi har ya manta yaushe rabon da yayi murmushi ma? Magana mai sanyi ma