Showing 90001 words to 91747 words out of 91747 words

Chapter 31 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

807

A hankali ya fara buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyi, dururu yake ganin mutane na giftawa a idanuwansa.
Sake lumshe idon yayi ya buɗe, anan ya gansu tsaye a kansa, suna kuka suna kiran "Alhamdilillah."

A hankali ya buɗe bakinsa shima "Alhamdulillah!" Ya faɗa da sautin muryarsa da baya futa.
Kallon Dad yayi da Mom ya musu nuni da hannunsa, da sauri suka ƙarasa kusa da shi suna riƙe hannunsa "Kunga yanda zuciyata ta kumbura kuwa?' Ya faɗa yana musu nuni da idanuwansa.

Kai suka girgiza masa hawaye na zuba akan idanuwansu, da ƙyar ya sake buɗe bakinsa ya yi magana "Ina ji aka ɗaurama Khadijatu aure Dad! Hakan na nufin na rasata rasawa na har abada!"
"Allah bai karɓi Khadijatu daga gareka ba Aabid har sai da ya musanya maka da wadda ta fita alkhairi. Amrah ce ƙaddararka ba Khadijatu ba, shi yasa tun farko baku haɗu da ita ba." Dad ya faɗa cikin sigar kwantar masa da hankali.

Tari ya fara yi a hankali, suka iyo kansa, Nabil na cewa a barshi ya huta.

"A'a Nabil ka barni nayi magana da su, wata ƙila ba zan ƙara samun damar yin magana da su kamar haka ba."

Kuka suka fashe da shi mai sauti, musamman Amrah da ta haɗe kanta da gwuiwarta, ji take zuciyarta na bugawa kamar zata futo, bata shirya yin rayuwa babu Aabid ba, bata shirya yin takaba wa shi ba.

"A'a Aabid ka daina kiran mutuwa a yanxu! Ina ji a raina ba zaka mutu ka barni ba." Ta faɗa tana girgiza kanta.

Murmushi yayi ya lumshe idanuwansa da suka masa nauyi "Ina fatan haka Amrah! Ina fatan nayi tsawon rayuwa da ke ko dan na gyara baƙin fantin da ke gare ni."

Kallon Dad yayi a karo na biyu "Naji kamar kace Khadijatu ba ƙaddara ta bace Dad?"
Kai Dad ya gyaɗa masa hawaye na zuba akan fuskarsa, murmushi Aabid yayi "Amma me yasa baku taɓa ban-bance min tsakanin fari da baƙi ba. Kullum kana bani abun da nake so, me yasa yanxu ka kasa bani? Tun farko me yasa kuka raineni akan muradan zuciyata?" Ya ƙarasa maganar hawaye na sauƙa akan fuskarsa.
"Har yanzu gafalalliyar zuciyata na ruɗata akan Khadijatu tawa ce, ban yarda ta min nisa ba har sai da na ganni kwance a wanan gadon.
Nagode Nabil kai ne mutum na farko da ka koya min darasin rayuwa.! Na fahimci ba komi ake so ake samu a duniya ba."

Dukkansu kuka suke har da shi, da ya lumshe idanuwansa, Nabil ya sake masa allurar barci gudun kada ciwonsa ya tashi.

Sai da yayi sati biyu sanan aka sallameshi a asibiti Aabid ya sauya yayi sanyi da yawa. Ya kai takardar ajiye aikinsa na soja a cewarsa da babu aikin da ƙaddara bata kai shi garin su Khadijatu ba.
Ya karɓi ragamar kasuwancin mahaifinsa, yayin da ya mayar da ƙauna da kulawarsa ga Amrah.

******

Bayan shekara huɗu.

A hankali ta zuro ƙafarta cikin gidan tana sanye da fararen kaya a jikinta wanda ke alaƙantata a matsayin babbar likita, ta yi kyau iya kyau, kamala ta bayyana akan fuskata.
"Dakta Khadijatu akwai marasa biyu yanzu aka kawo su." Wata nurse ta faɗa cikin rawar murya.

Agogon hannunta ta kalla ta girgiza kai "Ki kira Dakta Bahijja ni yanzu gida zan koma, na tabbata Irfan sun dawo daga makaranta."

Kai Nurse ɗin ta sunkuyar ƙasa "Matsalar fyaɗe ne aka yima yarinya 'yar shekara huɗu! Sai kuma mahaifiyarta da aka yiwa fyaɗen gabanta da bayanta. Ga mijinta can sai kuka yake yana roƙonmu."

Kafin ta kai ƙarshen maganar Khadijatu ta juya da sauri, bata tsaya ɓata lokaci ba ta shige ɗakin, idanuwanta ya sauƙa akan fuskar kyakkyawar yarinyar da ko numfashi bata yi, yayin da mahaifiyarta ke kwance itama a sume, jikinta duk shatin duka da jini.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Khadijatu ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta.

Ji take zuciyarta tana tsalle kamar zata faso a ƙirjinta, tasan ba zata iya wanan aikinba, zuciyarta ta riga da ta yi rauni.
Wayanta ne ya shiga ƙara hakan yasa ta ɗaga ganin Habibiey a jiki yasa ta ɗaga tana danne sautin kukanta "Habibiey ka zo dan Allah yanzu." Ta faɗa tana kashe wayar.

Cikin tashi suka taho asibitin dama wani bazata suka shirya yi mata, na muranar ƙarin shekarar haihuwarta.
Dukka mutanen gidan sun zo tun daga kan Ishaƙ da Aisha matarsa da ɗiyarsa mai suna Khadijatu.
Sai Aabid da Amrah da suka haifi tagwaye duka mata. suma sun zo su, Khadijatu ce dai ta haifi nata yaran maza 'yan uku.
IRFAN, ISLAM, IZZADEEN. Dukkansu yanzu suna cikin shekara ta uku ne. Amma wayonsu yayi yawa.

A ruɗe suka taho asibitin domin suna jin muryarta da ta sha kuka ta ƙoshi.
Suna zuwa ta tare shi ta faɗa jikinsa tana kuka "Sai yaushe ne mata za su samu 'Yancinsu Habibiey? Matsalolin mata ba za su ƙareba kullum sabbin shafi ake buɗe musu. Maza na nuna ƙumajinsu akan mataye, Me yasa a cikin ko wani mummunan abu na mace idan an duba sai aga namiji ne silarsa?"
Na gaji da karanta matsalar maza Habibiey, rashin imanin ya isa haka." Ta faɗa tana sambatu hankalinta ya gama ficewa a kanta.

"Wai me ya faru Habibaty?"
"An yima yarinya 'yar shekara hudu fyaɗe. An kuma aikata hakan ga mahaifiyarta gaba da bayanta."
"Me?" Suka faɗa a tare kafin su haɗa da salati.

Dukkansu shiga suka yi suka ga fuskokinsu, take gaban Aabid da Amrah ya faɗi ganin fuskar yarinyar kamar lokacin da hakan ya faru ga Nooriey ɗinsu.
Hawaye ne ya shiga silalowa akan fuskarsu, take Nabil ya fidda su ya kira sauran ma'aikatan asibitin ya ce su musu aiki Khadijatunsa ba zata iya ba.

Ya ruƙo hannunta da xummar barin asibitin sai dai ba su kai ga haka ba, suka ga wani Mutum ya zube a gaban Nabil ya riƙe ƙafafuwansa yana kuka.

"Ka yafe min dan Allah! Na tabbata hakkinka ne ke bibiyar matata da 'yatah! Abun da na aikatawa Nooriey yau ya dawo kaina. A gaban idona aka yiwa 'yatah da matata fyaɗe." Ya ƙarasa maganarr yana ruƙe ƙafafuwansa.

Tunda ya ji maganarsa ya fahimci waye shi, hannu yasa ya ɗago shi lokacin da yaga fuskarsa sai da gabansa ya faɗi, domin shati ne na wuƙa aka tsattsga fuskar tasa manya.

"Labib Ƙasim Basar?" Ya faɗa da tsananin mamaki.
Kai ya shiga gyaɗawa "Kaga yanda rayuwa ta zame mun baƙi da duhu ko? Kaga yanda Allah ya amsar muku hakkinku akaina ko?"
"Me ya faru da kai?" Aabid ya faɗa har yanxu yana mamak.

Na shiga neman kuɗi ta ko wata hanya, saboda na goge fantin da 'yan gidanmu sukewa ahalinmu na zamowarmu masu ƙashin tsiya, hakan yasa na baro ƙasarmu nazo nan naa nemi aiki, na fara da kula da yara, ganin har a lokacin kuɗi bai zuwar min yasa na faɗa bin bokaye ta hanyar shawarar wata mata.
Anan bokan ya bani laƙanin yiwa yarinya 'yar shekara biyar ko ƙasa da haka fyaɗe.
Lokacin da nakema Nooriey wanka naji a raina itace maganin wahalata anan na aikata rashin imani nabar ta a wajen na gudu da nauki matata muka koma wata unguwa mai yawan mutanen da vasu da wayewa. na sauya suna da aiki.
Kamar wasa kuɗi ya fara xuwar min a hankali komi na taɓa yake ruɓanya ya zama kuɗi, wanan dalilin yasa muka tashi daga legos muka dawo nan Dutse anan na ci gaba da kasuwanci na.
Kwatsam daren jiya ɓarayi suka min dirar mikiya, basu samu kuɗi agidana ba saboda bana ajiye kuɗi, sai a banki, wanan dalilin yasa suka yima 'yata fyaɗe suka kuma lalata min mata ta. Ni kuma suka min shatin wuƙa a fuskata waii idan naga ni zan daina ƙin ajiye kuɗi a gida." Ya ƙarasa maganar yana kuka.

Shima Aabid kuka yake shi da Amrah, kafin suyi magana suka ji wani sauti tass, kafin su ankare an ƙara masa, a tare suke ganin Khadijatu tana ta wankawa mutumin mari dama da hagun ɗinsa, hankalin mutane ya koma kanta da ƙyar Nabil ya ɓam-ɓareta daga jikinta.

"Kaji ba Habibiey? Kuna ji ba,matsalar mata ba zata ƙare ba muddum akwai azzalumain da ke siyar da imaninsu saboda kuɗi.
Kaico! Kaicon wanan duniyar da ta cika da hargitsi da son zuciya da neman duniya fiye da lahira.
Ya Allah ka yafe mana, ka kare mana zukatanmu da imani." Ta faɗa tana kuka.
Rungume Khadijatu Nabil yayi yana shafa bayanta.
Aabid kam sai kallon Labib yake yana jin abun kamar a mafarki.
'Ashe shi nasa mai sauƙi ne? Shi yasa Allah ya tsayar fitinar iya Norrie kawai.
Astagfurillah ya Allah.' Ya faɗa a zuciyarsa.

"Na yafe maka nikam Labib! Ko wanan tashin hankalin da kake ciki ya isheka. Sai dai ka makara, domin Noorie bata raye balle ka roƙi yafiyarta."
Yana gama faɗa ya fice yabar wajen hawaye na sauƙa akan fuskarsa "Lallai shi Allah yana sonsa da rahama, shi yasa ya tsayar da matsalarsa a ƙaramin waje. Tabbas zina bashi ce, duk inda aka je dole ta dawo kan mai ita ta karɓi bashinta.
Matsalolin fyaɗe na yawaita ka rasa dalilin faruwarsu, amma da za'a bi diddigin lamarin sai ka tadda wani tsani aka hau na matattakalar rayuwa ya rubje da mai hawansa ya faɗo da shi.
Ya Allah kada ka jarrabe mu akan laifun wasunmu, ka yafe mana kura-kuranmu.


🌷🌷🌷🌷🌷


ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo ƙarshen labarin INUWAR GAJIMARE ina fatan Allah ya yafe min kuskuren da nayi a cikinsa, wanda nayi dai-dai kuma ya raba mana ladan tare da ku.
Ina fatan kun samu darrusa a cikin labarin, kun kuma fahimci saƙon da nake son isarwa a cikinsa.
Idan kunci gyaran karo da kuskuren da nayi a cikinsa dan Allah ku sanar da ni kai tsaye, zan amsa da hannu bibbiyu.

INUWAR GAJIMARE na nufin sadaukarwar da ISHAƘ yayima KHADIJATU.
Duka labarin nan na KHADIJATUL ISHAƘ ne amma jigonsa matsalolin fyaɗe a duniyarmu.

Sai kun jini a sabon book ɗina AL-HABBU DAYYI'AN

GIRMAMAWA.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login