Showing 66001 words to 69000 words out of 91747 words

Chapter 23 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

810

ya kamata kayi shi ya riga da ya wuce ka. Ka tashi ka tafi wani lokacin ka dawo na tabbata wata rana Khadijatu zata yafe maka." Abbu Yasir ya faɗawa Aabid yana ɗaga shi daga durƙushen da ya ke.

   Kansa ya shiga girgizawa hawaye na ci gaba da zuba akan fuskarsa "Ƙurewar da lokaci yayi min yasa hawayen fuskata gaza ƙafewa! Idan har akwai fatsar da ta kasa kamo kifi a kogi bai wuce fatsar da na jefa ba! Madadin ta kamo min kifi sai ta ɗauko min duƙumemen dutsen da ya rinjaye ni ya dulmiyar dani a cikin kogin da ban da ƙwarewa wajen iyo a cikinsa.
  Ba iya yafiya kawai nake so Khadijatu ta min ba Kaka, so nake na ƙare rayuwata a tare da ita, na zame mata Inuwar gajimare a duniyarta! Na mayar da ita sarauniyar da ke mulkar mutane! Na ɗaukaka martabarta fiye da macen da ta kimanta kanta, zan ɗaga darajarta har sai taji tana yawo a tsakiyar gajimare! Zan giramama buƙatarta har sai ta ce ta wadatu a cikin ko wani abu! Zan durƙusar da  ƙafafuwana ta taka kafaɗuna ta yanda zan ɗagata na zaga duniya da ita."

   Hannayen Abbu Yasir ya kama ya ɗora akan ƙirjinsa saitin zuciyarsa nan ya dinga jin zuciyarsa na bugawa har yana jinta a hannunsa "Kaji yanda zuciyata take bugawa ko Kaka? Ina ji kamar zata faso tabar ƙirjina ne! Yanzu da naga Khadijatu sai naji bugunta ya ƙari, yayin da ta tafi tabar ni sai nake ji kamar na rasa wani sashi na rayuwata ne.
  Sam ba kuskure ne ya faru a rayuwarmu ba, ƙaddarar mu ce ta zo a mana a haka, ina ji a raina wani iko ne na Allah ya ƙaddara min tarayya da Khadijatu kaɗai ba wata ba.
  Zan sake dawowa na roƙi yafiyar Khadijatu! Zan dawo har sai ta haƙura ta yafe min."

Ya na gama faɗar haka ya fice ya bar falon, yana jin iska na kaɗa shi kamar zata fuzge shi ya faɗi.
Da ido suka bishi suna girmana maganarsa da kuma ƙwarin gwuiwar da yake da shi.
"Ina tunanin ya zauce wanan mutumin fa." Ammu ta faɗa cikin sanyin murya da jimamin abun da ya faru.

"Bai zauce ba Ammu. Toshin hankalin da yake ciki ne ya haddasa masa zafin kai, a yanzu bai ƙi ya samu abokin mutuwa ba." Imran ya faɗa yana zama akan kujera.
Suma zama sukayi gaba ɗayan su "Akwai matsala fa, naji yana ta nanata cewar yana son Khadijatu Abbie." Dr Anwar ya faɗa yana rafka tagumi.

"Ai ko maza sun ƙare a duniyar nan babu abun da Khadijatu za tayi da shi." Ishaƙ ya faɗa yana huci kamar baƙin kumurci.

"Um-Um Ishaƙ! Ba'a saurin yanke hukunci akan lamarin soyayya. Idan har ƙaddarar su a jone take da ta juna to duk duniya babu wanda ya isa ya hana tarayyarsu waje ɗaya." Imran yayi saurin tarar maganarsa, yana jin mikin da ke zuciyarsa na fitowa tun na shekaru.
Ƙila da badan ƙaddarar mahaifiyarsa ba da yanzu ba su fuskanci wanan tashin hankalin ba.
"Abarwa Allah komi!" Baban Indo ya faɗa yana jinjina lamarin a zuciyarsa.

Tashi Ummi ta yi tana kallon Fatima da ta rafka tagumi tun ɓulluwar al'amarin "Fatima je ki duba Khadijatu." Ummi ta faɗa mata cikin sanyin murya, dan maganar da Imran ya yi ta sanyaya mata zuciya ta fahimci kamar da ita yake maganar.

Tashi rayi cikin nata sanyin jikin ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakin Khadijatu, duk da cewa ba wai sun shaƙu da yaran bane, musamman da suke ganinta a matsayin silar wargajewar farin cikinsu, da kuma rasa mahaifiyarsu da sukayi.
Tana iya bakin ƙoƙarinta wajen dai-daita lammuransu, da ita amma abun ya gagara, gashi ita da kanta ba zata adar daɗin aure ba balle tace ta tsinci wani abu a cikinsa a shekaru da suka shuɗe na rayuwar aurenta da Imran.
Amma kuma a yanzu zata iya cewa ta samu sauƙi, domin dai-dai gwargwado tana samun kulawa daga Imran. Abun da ta gaza samu a tare da shi shine haihuwa! Har yau bata taɓa yin koda ɓatan wata ba ne, balle tasa ran zata samu ɗanta na kanta.

Tura ƙofar ɗakin tayi a hankali kamar marar gaskiya, bakinta na ɗauke da sallama.
Muryar Khadijatu taji ta amsa mata sallamar ta fes babu alamun damuwa, sai sanyin muryarta da bata fita da amo.
Ƙarasa shiga tayi ɗakin ta tadda Khadijatu zaune akan sallaya da hijab a jikinta, sai ƙur'ani a hannunta, wanan ya nuna mata sallah tayi ta zauna tana tilawarsa.
Idan har akwai abun da ke burgeta a cikin rayuwar yaran nan bai wuce yawan addininsu ba da kuma ibadarsu.
Zama tayi kusa da ita tana jin sautin ƙira'arta na ratsa zuciyarta da gangar jikinta, muryarta na da zaƙi amma yanzu da take karatu sai taji zaƙin muryarta ya linka na maganarta.
Shuru tayi tana lumshe ido bata dakatar da ita ba har sa da ta kai aya ta dakatar dan kanta, sanan ta ɗago da nata kan tana kallon Khadijatun da itama kallonta take.
"Kin gama kenan?"

Kai Khadijatu ta gyaɗa "Akwai matsala ne Aunty?"
Kai Fatima ta girgiza mata "A'a na zo ne kawai na duba ki."
"Nagode!" Khadijatu ta faɗa tana jingina a jikin bakin gadonta, tana lumshe idanuwanta.

"Khadijatu! Ki yi haƙuri kada kisa damuwar wanan a zuciyarki. Duk abun da zai faru da ke a yanzu ba zai kai wanda ya faru da ke a baya ba. A matsayinmu na iyayenki muna tare da ke akan duk wani muradinki, zamu tayaki cimma mafarkanki, ba zamu tilasta miki akan abin da kike ganin dai-dai ne a rayuwarki ba."

Murmushi Khadijatu ta yi tana kallon Fatima "Wani Abun ya faru ne Aunty?"
Mamaki ne ya kama Fatima, amma kuma sanin wace Khadijatun da tayi a yanzu ya sa ta shanye mamakin nata "Akan maganar mutumin da ya zo neman yafiya wajen ki nake dannarki. Bana so ki sa hakan a ranki ya zo ta daameki."

Murmushi tayi mai sauti har haƙoranta na bayyana "Wanan bai cikin jadawalin batun da za'a mai-maita shi Aunty. Ki kawo wata sabuwar maganar da ta fita muhimmanci a wajena."

"Kina so ki ce min wanan bata da muhimmanci a wajenki Khadijatu?"
Kai ta gyaɗa mata har a lokacin murmushi bai ɗauke akan fuskarta ba "Haka ne Aunty! Abun da ya riga da ya wuce ba zai dawo ba Aunty, to me zai sa na ɗauki rayuwata na miƙa a wajen hararoshi bayan ba zan iya dawo da jiya yau na goge shi ba.
A yanzu nafi tunanin rayuwar da ke kusantowa gareni wadda ban da sanin da me zata zo min. Shin wanan bai fi wancan ƙalubale ba?"

"Ya fishi Khadijatu! Amma kuma kamar ƙoƙari kike wajen binne damuwarki a kan fuskarki, tunda har fuskarki da idanuwanki sun kasa ɓoye ƙiyayyarsa a idanuwanki."

"Aunty ba'a hora horarre ai sai dai a maida asirka. Mayar da fushi ya koma murmushi ba ƙaramin yaƙi ba ne, nasan ko da sau ɗaya ne fuskarki bata taɓa ɓoye damuwar da zuciyarki take ciki ba.
Amma kuma ni na yi hakan."

Murmushi Fatima tayi tana shafa kan Khadijatu "Kamar kumbo kamar korenta! Ke kamar farin zinaren da ke rayuwa a cikin fararen tagulla kike! Ba dasa ƙwan jimina ba fidda kansa wajen ƙinƙisa.
Allah ya albarkaci rayuwarki." Tana gama faɗar haka ta tashi tabar ɗakin nata, tana jin idanuwan Khadijatu na yawo a jikinta.

*****

Legos, Nigeria.

Tashin hankalin da Dad suke ciki ya musu yawa, musamman da yayi ta kiran Aabid bai same shi ba. Ga har zuwa yau da akayi kwana biyu da kwantar da Nuriee bata farka ba. Duk da cewa zuciyarta na bugawa amma har a lokacin bata farka daga dogon suman da tayi ba.
Ga tarin kuɗaɗen da yake kashewa akan neman Labib Ƙasim Basar amma ko mai kamarsa ba'a samu ba.
Idan da za'a gwada shi to tabbasa za'a ga jininsa ya hau, hawa mai yawa, amma ganin tashin hankalin da iyalansa suke ciki yasa yake daurewa yake shan ƙoƙarin yaƙar tashin hankalin da yake ciki.

Yauma kamar kullum suna zaune jugum-jugum sun saka Nurie a gaba suna kallonta, Amrah kam kamar mai zaman takaba haka ta koma, duk ta fige ta fita a kamarta, tun faruwa abun hannunta bai rabuwa da carbi da hijabi kamar mai zaman takaba.

Burum suka ji an bugo ƙofar ɗakin wanda ya sa su saurin juyowa, kamar wanda aka wullo suka ga Aabid ya shigo musu ɗakin wurjan-jan ya fita a hayyacinsa, kamanninsa duk sun sauya.

"Aabid!" Suka faɗa a tare suna taroshi gaba ɗayansu.

Rungume Dad yayi sanan ya fashe da kuke "Tace ba zata yafe min ba Dad! Taƙi tsayawa ta yafe min Dad! NI ne silar komi Dad! Ni ne tikitin wargaza ko wani farin ciki namu! NA CUCI KU! NA CUCI KAINA!" Daga haka numfashinsa ya fara sarƙewa ya fara tari da ƙarfi, zuwa wani lokaci kuma jini ya fara ɓallewa a bakinsa ya fara futa guda-guda.
"Na shiga uku! Aabid me nake gani?" Dad ya faɗa cikin tashin hankali, da gudu amrah ta fita tana ƙwala kiran Likita....


🌷🌷🌷🌷🌷

😢😢ABUN TAUSAYI
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG


450000



Kallonta yake kamar wani soko ya kasa yin magana sai nuna kansa yake bakinsa yana rawa "Waye ni kika ce?" Ya faɗa cikin rawar muryar da mamaki ya ƙara cikata.

Kai ta gyaɗa masa har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi "A ina ka sanni ka ke neman yafiyata?"
Yanzu kam ya wuce ƙarfin mamaki, tsoro ne ya kamashi jin idanuwan mutanen falon na yawo a jikinsa.

"Ina tunanin na samu matsalar adireshin da aka bani. Ba wajenki ya kamata na zo ba!"
"Amma kuma ni ce wanda ka tambaya ai." Ta yi saurin bashi amsa tana kafe shi da manyan idanuwanta wanda kalarsu ta fara sauyawa daga farare zuwa ja.

"Idan har ke ce na tabbata kin san ko ni waye! Me yasa kuma kike ƙara son neman sanin waye ni? Dan Allah Khadijatu ki yafe min, kada ki hukunta ni akan rashin sanin ko ni waye a wajenki."

Kallon Ishaƙ tayi da shima yake kallonta, yana jin zuciyarsa kamar an cinna mata wuta saboda haushin mutumin da bai san alaƙarsa da ƙanwarsa ba.
Hannu ta ɗaga masa alamun ya zo, hakan yasa ya zo wajenta, tashi ta yi a hankali ta bama Ishaƙ ɗin wajen da take "Yayana ka tambaye shi waye shi? Dan kaima kana son saninsa, musamman da ya kasance duk abun da ya shafe ni kana fina saninsa kafin na san da shi."
Tana gama faɗar haka ta wuce zata bar palon "Idan nace ni ne mutumin da na miki Fyaɗe shekara shida za ki tuna ni?"
Cak ta tsaya daga tafiyar da take, kamar yanda mutanen falon suka tashi tsaye daga zaunen da suke. Suna kallonsa suna kallon Khadijatun da ta juyo a lokacin tana harɗe da hannunta a ƙirjinta, har lokacin fuskarta da murmushi a cikinta.
"Har yanzun ban tuna da kai ba. Kai kuma gashi baka yi kama da mugu ba balle na yarda kai ne ka min fyaɗe shekara shidan da ta wuce."

Goshinsa ya buge da hannunsa yana jin wani sabon tozarci na ƙara lulluɓe shi, rainin hankalin da yake gani a tare da Khadijatu ya zarta tunaninsa, murmushi take a bakinta yayin da idanuwanta suke aika masa da kallon tsana mai yawa.
Kallonta ya sake yi yaga itama shi take kallo da duk mutanen da suke cikin palon "Wallahi da gaske ni ne mutumin da na miki fyaɗe! Dan Allah ki tsaya ki yafe min, dan Allah Kha...." Shaƙar da yaji an yiwa wuyansa ne ya sa shi yin shuru yana ƙoƙarin ƙwatan wuyansa daga ruƙon da aka masa, amma kuma hannunsa ya gaza ƙwacewa.
Kallon wanda ya shaƙe shin yayi yana mamakin ƙarfin da ke tare da mamallakin hannun, sai dai da mamakinsa Ishaƙ ya gani, idanuwansa sun kaɗa sunyi ja, jijiyoyin kansa sun fito raɗo-raɗo, ko ina a jikinsa rawa ya ke. Bai gama mamaki ba, yaji ya ɗaga shi ya bugashi a ƙasa, kafin ya gama tsinkewa da mamakin ƙarfinsa ya fara jin duka ta ko ina a gefen fuskarsa hagu da kuma dama.
Kafin wani lokaci jini ya wanke masa fuskarsa, ganin dai da gaske Ishaƙ zai yi kisan kai yasa su Abbie Imran da Anwar ƙoƙarin ɗagashi amma fur suka kasa "Dan Allah Baban Indo ka zo ka taimaka mana kada yayi kisan kai, ya ɗauki zunubin da ba nasa ba." Abbie Imran ya faɗa, saboda kasa ɓanɓare Ishaƙ da sukayi a jikin Aabid ɗin.
Basu taɓa tunanin yana da ƙarfi haka ba.
"Ku sake ni Abbie. Ku ƙyaleni na kashe shi! Irin waɗan nan mutanen basu da wani rana da amfanin da za su yima mutum a duniya." Ishaƙ ya faɗa hawaye na zuba akan fuskarsa saboda ɓacin ran da ya ke ji a zuciyarsa.
Da ƙyar su uku suka cireshi daga kan Aabid da baya numfashi sosai. Ajiyar zuciya ya sauƙe lokacin da ya ji an ɓan-ɓare shi daga jikinsa, yana jin kamar dai a kwanakinsa ajalinsa ke kusantowa gareshi.

"Dama kun barshi ya kashe ni. Duk da na san ko da ace ya kashe ni ba zai huce baƙin cikin da na sa shi ba a cikin shekaru shidan da yayi."
Kai ya girgiza yana ƙara kallon fuskokin mutanen da suke falon, wanda ko ba'a faɗa masa ba yasan tsanarsa ce male-male akan fuskokinsu.
"Na aikata zalunci akanku, na cuci rayuwar yarinyar da bata gama sanin wacece itaba. Sai gashi daga ƙarshe zalincin ya dawo kaina, daga ƙarshe dai na girbi abun da na shuka, na tsunke mugunyar ɓarnar da na aikata. A yanzu kaico nake da rayuwata da duniyata, da ta cika da duhu da sarƙaƙiya.
Wanan shine lokaci na farko da nake ji inama mutuwa tace ta ɗauke ni tun kafin nasan kaina." Kuka ne ya ɓalle masa hakan ya sa yayi shuru yana yi har sai da ya yi mai isarsa sanan ya yi shuru.

"Da ace ban lalatama Khadijatu rayuwarta ba da wani bai farmaki rayuwar 'Yata ba! Da tun farko na yaƙi zuciyata da abun da nake ji da ban jefa yarinta a cikin komawar mugwaye ba.
Sharrin da na aika ya dawo gareni ya duƙunƙune rayuwata, ina ji a raina dama tun farko ban zama wanzazze a wanan duniyarba. Akwai abu da yawa da yake zama ƙaddara amma kuma ni sai na zama tsanin rubutu akan ƙaddara 'yata.
Dan Allah ku yafe min ko ahalina za su tsira daga muguwar ɓarnar da zata kunno musu a gaba. Yau an lalata rayuwar ita 'yar shekara shida ban san me zai faru ba kuma a gaba idan har baku yafe min ba." Aabid ya faɗa cikin sarƙewar muryar, numfashinsa ya fara fita sama-sama.
"Anwar kawo akwatin gaggawa." Abbie Imran ya faɗa cikin sauri, ganin yanda jini ya ci gaba da zuba ajikinsa, ga kuma numfashinsa na fita akai-akai.

Ganin halin da yake ciki yasa jikin mutanen falon yin sanyi, masu rauni a cikinsu kuma suka fara kuka, musamman jin an yima yarinya 'yar shekara shida fyaɗe.
"Wata rayuwa muke ciki a wannan duniyar? Ya Allah ina mutane za su kai hakki a kansu?" Ummi ta faɗa tana sharar hawaye akan fuskarta.
"Lallai idan kana raye a duniya baka ga komi ba." Ammu ta faɗa tana shafa fuskarta da tafukan hannunta.
Shi kansa Ishaƙ jikinsa ne yayi sanyi jin abun da ya faru da yarinyar mutumin, "Yarinya 'yar shekara shida a duniya aka yima fyaɗe! To ya rayuwarta ta ke a yanzu?" Tambayar da yayi kenan cikin sanyin murya yana kallon fuskar Khadijatu da har a lokacin bai tan-tance yanayinta ba. Shi mamaki ma yake da murmushi yaƙi ɓacewa akan fuskarta a lokacin.
Ƙarasawa yayi kusa da ita ya dafa ta saboda tsoron da yake ji na ganin ko gezau ba tayi ba "Khadijatuna!" Ya faɗa yana dafa kafaɗarta.
Ɗago da kanta tayi tana kallonsa "Yayanah!" Ta faɗa tana murmushh da ya kasa sani na miye.
Rungumeta yayi a jikinsa yana bubbuga kafaɗarta, amma kuma ko gezau batayi ba, asalima bata ƙanƙameshi ba kamar yanda ta saba yi masa.
Sakinta yayi yana kallon fuskarta da ta fara sauyawa "Zo muje ki zauna!" Ya faɗa yana ruƙo hannunta zuwa wata kujera ya zaunar da ita. Bata motsaba har ya zauna shima ya kwantar da kanta akan cinyarsa yana shafa kanta.

Ko ba'a faɗa masa ba yasan Khadijatu bata cikin nutsuwarta a yanzu, duk abun da yake faruwa hankalinta baya tare da ita, zai iya kasancewa mamakin da ke kanta ne bai bari tayi tunani akan wanda ke gabanta ba, ko kuma tsoron da take ta yaƙar zuciyarta ne a cikinsa yasa zuciyarta gama bushewa ne.

Bayan wani lokaci Aabid ya dawo hankalinsa, abinci Abbie Imran ya tasa shi agaba ya ke bashi kamar ɗansa, amma kuma ya kasa ƙwaƙƙwaran cinsa baifi cokali uku yaci ba yace ya ishe shi "Ka ƙara dan yunwa na barazanar naɗe maka uwar hanjinka." Abbie Imran ya faɗa cikin murmushi
Karɓa yayi yaci kaɗan ya kawar da kansa "Na ƙoshi Abba. Dan Allah kace ma Khadijatu ta yafe min." Ya faɗa hawaye na biyo bayan maganar tasa.

Ruwa ya miƙa masa yasha sanan ya kalle shi "Bani labarinka. Waye kai? Me yasa ka lalata min rayuwar 'yata?" Abbie Imran ya faɗa yana tsuke fuskarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login