Showing 6001 words to 9000 words out of 91747 words
rufe wancan kundin tambayar, abu guda ya ke muradi a yanzu "Waye ya keta ma Khadijatu mutuncinta? Me yasa ya aikata mata hakan?" Wanan tambayar ita take caccakar rayuwarsa.
"Dan Allah kada ka taɓa ni! Ni marainiya ce! Kada ka cutar min! Baka yi kama da mugu ba!" Maganar Khadijatu ta dawo da shi daga zurfin tunanin da ya shiga.
Kallonta ya yi idanuwanta a rufe amma tana magana tana jijjiga kai, gefe guda kuma jikinta ya ɗauki rawa.
"Kai Mugu ne Azzalumi! Ka cutar min da rayuwata! Ba zan taɓa yafe maka ba!" Ta faɗa jikinta yana ci gaba da rawa muryarta a sanyaye ba kamar lokacin da ta fara magana ba.
Ajiyar zuciya ta sauƙe da ƙarfi, bayan ta kai ƙarshen maganar, daga nan ta yi luƙus ta ci gaba da barcinta.
Fuskarsa ya rufe da duka hannayensa guda biyu, halin da Khadijatu ta ke ciki ya kasa barin zuciya da kwanyarsa su huta.
"WAYE WANAN MUTUMIN? A ina zan same shi?"
*********
LAGOS, NIGERIA.
Wani tamfatsetsen gida ne da yake ɗauke da manyan sojoji suna zagaye ko ina na gidan, suna kuma gadinsa, ko wanne fuskarsa ba rahama ya yin da suke ɗauke da bindigogi a hannunsu na shirin ta kwana.
Daga cikin harabar gidan kuma a cike yake da mutane, maza da mata, a taƙaice gidan ya amsa sunansa na gida, harabar gidan kanta zata iya ɗaukan gidaje bila adadin a cikinta.
Mutanen da suke cike da ita suna sanye da ƙananun kaya na shigar cort wanda ke alaƙanta su da ma'aikatan ne
Baka jin sautin ko me a wajen sai sassanyan kiɗan da ke tashi, yayin da aka cika gaban sauran mutanen da kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe.
Bayan wani lokaci kuma kiɗan wajen ya sauya ya koma wanda ya fi wanan sanyi da daɗi "Jama'a kowa ya tashi tsaye ga Ango da Amarya sun fito." M.C ya faɗa.
Nan take mutane suka tashi tsaye kamar yanda M.C ɗin ya buƙata.
A hankali suke tako da ƙafafuwansu zuwa harabar wajen taron, da aka ƙawatata da adon furanni da kuma ƙyal-ƙyali.
Ƙasan da suke takawa suma an kewaye su da nau'ikan furani daga kan farare zuwa jajare da kuma shuɗaye.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangiji!" Itace kalmar da ta suɓuce a bakunan 'Yan mata da matasan samarin da suke wajen, lokacin da sukayi tsinkaye da kyakkyawar fuskar mutane biyun da suka ratso wajen taron sanye da fararen shiga. Aka kuma ambace su a amtsayin AMARYA DA ANGO.
"Waɗan nan mutane biyun kamar dan su aka halicce kansu, ko a fusa kuka kallesu kun san haɗinsu ya haɗu, sun kuma dace da junansu. Dan Allah a tafama Mr. Aabidullah Isma'il da amaryarsa Amrah Khalil." M.C ya faɗa cikin bututun maganarsa.
Kamar jira suke nan take mutane suka fara tafa hannayensu. Wanda hakan ya fidda kyakkyawan murmushi daga bakin Aabidullah, anan masu hotuna suka fara ɗaukansu hoto duk inda suka cire ƙafafuwansu suna biye da su.
Zama suka yi akan kujewa ya yin da shi kuma ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, Yana daga cikin ɗabi'arsa yin wanan zaman, wanda kuma mutane suke ga hakan a matsayin Izzarsa da zamowarsa Saraki, wanda shi kuma hakan ya zame masa jiki tun yarintarsa.
Anan dai M.C ya gabatar da ƙwarya-ƙwaryar bikin da gayyatar manyan abokanai na ango da amarya su zo su taka kowa ya fito sai ya ajiye musu kyautar da suka kawo musu.
Shi dai Aabidullah banda murmushi ba abin da ke sauƙa akan fuskarsa, wanda dama ko yaushe murmushin shi ke nuna farin cikinsa, bayan haka ba zaka samu wani abu daga gare shi ba.
Bayan an gama ne ya tashi yayima mutane godiya abokanansa da yayyensa da duk wanda ya samu damar halattar aurensa, wanda wanan itace rana data waye musu a gidan a matsayin ma'aurata ta kuma zama ranar bikinsu ta ƙarshe, bayan kwanaki bakwai ɗin da aka ɗauka ana ta shagali a cikinta.
Anan ya ja hannun amaryarsa da ya ke ji duk duniya babu wanda ya kai shi sa'a a wanan duniyar, babu kuma wanda ta fi matarsa ta ko wata fuska.
Itama kuma a nata gefen haka ne, ji take kamar tana yawo ne a tsakiyar GAJIMARE da ko wani taku da take da shi tana ji kamar su shimfiɗa rayuwarsu har abada a haka.
Daga ƙarse ciɗak ya ɗauketa dan ya sauƙaƙa mata tafiyar da take, da kuma nisan da ke tsakanin sashinsu da na wajen perty.
*****
Ƙauyen TONI.
Bayan mako guda
"Khadijatu zarni nake ji a ɗakin nan tun kwanaki biyun da suka wuce. Kuma gashi ba wahala kayanki sun jiƙe, hatta katifar nan ma ta jiƙe.
Anty Ramla ke bakya jin zarnin da ɗakin nan ya ke." Dr Anwar ya faɗa cike da ƙyanƙyamin ɗakin, yana toshe hancinsa saboda zarnin da yayi mata shigar bazata.
Jikinta ta haɗe waje guda saboda tsoron hargowar da Dr Anwar ke mata a wanan lokacin. Hakan ya sa jikin Nurse Ramla yin sanyi ta matsa kusa da Khadijatun, sanin matsalar da take ciki.
"Me ya faru kuma Khadijatu? Mu da muke shirin sallamarki gida ganin yanda yayanki yake wahala da ke, amma kina ƙara ɓallo masa aiki kina fitsari a zaune da girmanki! Me yasa haka Khadijatu?" Ta faɗa cikin sigar lallashi da son kawar da abun da ta yi niyar yi mata da farko.
"Tun Jiya nima nake jin sauyin ɗakin Dr Anwar, amma ban kawo hakan a matsayin matsala ba. Na ɗauka yanayin gyaran wajen ne aka samu tsaiko a kansa, sai yanzu kuma naga jiki Khadijatun a jiƙe wanda yake nuna cewar ita ce ta yi fitsarin.
Ido ya fiddo waje cikin mamaki "Fitsari a zaune Khadijatu!" Ya faɗa da buɗaɗɗiyar muryarsa me cike da mamaki.
Shessheƙar kuka ta shiga yi, tana girgiza kanta, cikin rawar murya ta fara magana "Ni ban san ina fitsarinba Anty! Bana jin zuwansa sai dai naji jikina ya jiƙe, ba da gayya na ke yin hakan ba, kuyi haƙuri kunji Anty!"
Ido ta fiddo waje cikin mamaki da tsoro "Kika ce bakya jin fitsari a mararki? Kamar yanda bakya jin zubowarsa!"
Kai ta gyaɗa cikin raunin muryar da ta gaji da kuka "Eh Anty! Kuyi haƙuri."
"Yaushe kika fara rashin jin fitsarin?" Dr Anwar ya faɗa gumi na tsattsafowa daga idanuwansa.
"Tun lokacin da aka kawo ni nan, ban ƙara jin futsarin ba."
Dafe kansa ya yi da ya ji yana barazanar fashewa saboda tashin hankalin da ya shiga a ɗan lokacin nan.
Bama shi kaɗai ba ita kanta Nurse ramla hankalinta ya tashi sosai da al'amarin nan.
"Kawo keke mu kaita gwaji." Ya faɗa cikin sanyin murya.
Futa tayi da sauri kafin wani lokacin ta dawo da keken da ake ɗora marasa lafiya ana tura su "Sauƙo ki hau muje."
A hankali ta sauƙa ta hau kan keken cikin hanzari ta fara turata suka fice a ɗakin, wani ɗaki na musamman ta shigar da ita, bayan ta kira wasu Nurse's guda biyu.
Da hannu ta nuna mata wani gado "Kwanta anan."
Kwanciyar tayi suka rufu a kanta.
**
Bayan wani ɗan lokaci:
"Inna lillahi wa inna ilahirraji'un! Bladder ki ta taɓu dole ba zaki iya jin fitsari ba, kamar yadda ba zaki ji sauƙarsa ba.
Ku mayar da ita ɗakinta Labiba."
"Likita wani abun ne ya same ni kuma? Ku faɗa min menene bladder da ta taɓu a jikina?" Khadijatu ta faɗa cikin son yin turjiya da ƙin barin ɗakin.
Kawar da kanta Ramla ta yi daga baya ta fuce a ɗakin baki ɗaya, kai tsage office ɗin Dr. Anwar ta shiga, saboda barinsu da ya yi akan su duba abin da ya sameta.
Yana 'yan rubuce-rubuce wanda ya sashi ɗagowa cikin tsorata.
Ganin Nurse Ramla ya sashi dakatar da rubutun da ya ke, duk da dama hankalinsa na gareta, yana jin tsoron ɓulluwar abun da zai sake samun yarinyar.
Da ƙyar ya buɗe baki ya yi magana "Lafiya Aunty Me ya faru da ita?"
Hawayen da take riƙewa shi ne ya sauƙa akan fuskarta "Anya zan iya ci gaba da aikin asibitin nan kuwa Anwar? Zuciyata tana gaf da tsinkewa akan matsalolin da bani da iko ko ƙumajin kawo ƙarshensu! Bani da dogon hannun da zan tare na hana faruwarsu?"
"ME kuma ya sake faruwa Aunty?"
"Ko me ya faru Anwar! Idan nace kome ina nufin kome da ya shafi rayuwar Khadijatu ya ƙara lalacewa! Wani sabon kundi ne ya buɗe daga cikin shafukan ƙaddararta. Bladder Khadijatu ta taɓu wanda hakan ya haifar mata da larurar YOYON FUTSARI!"
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Dr Anwar ya faɗa yana wullar da biron da ke riƙe a hannunsa zuwa ƙasa.
Zama itama Nurse Ramla ta yi akan kujerar da ke fuskantar sa "A wanan ɗan ƙaramin ƙauyen, da ke zagaye da gajiyayyun mutane, wanda basu da yakanah balle kyautatawa na kusa da su.
Yaran da suke fafutuka wajen nemawa kansu abincin da za su kai bakinsu, suke faɗi tashi akan muhallin kwanciyarsu, yaran dai da basu da uwa da uban da za su tsaya musu. Ta ina za su fara tunkarar wanan matsalar? Ta wata hanya za su kula da kansu? Ta wata hanya za su fara neman maganin ciwonsu?
Wanan tunanin da wanan fargabar su suke caccakar zuciyata. Har nake ji inama ni wata ce da zan iya kula da Khadijatu! Inama ace hannayena sun kewayo sun kuma yi tsayin da za su tsayama wani.
Amma babu wanan damar! Bani da wanan ikon, bani da hanyar da zan taimakawa Khadijatu ANWAR!"
Tunda ta fara maganar ya ke jin gashin jikinsa na miƙewa, yana jin sanyi na huda ko wata ƙofar gashi ta jikinsa tana iske ƙashinsa, yana jin kansa ya yi masa gingirim, a yayin da yake hango rashin sa'arsa na fara aiki a asibiti mafi ƙanƙanta da lungu, yana hango kamar bai kula da kyau ba ne, ba nan ne ya dace ace matsalar Khadijatu ta ɓullo ba.
Lallai Ƙaddara da girma ta ke, kamar yanda sanadinta ya ke da yawa.
"Ya Allah!"
Ya faɗa yana dafe kansa da yake jin kamar zai ɓalle daga maɗaukarsa, kwanaki biyu rak suka rage masa yabar wanan asibitin saboda tafiya ƙarin karatun da zai je ya yi a ƙasar India. A cikin wanan kwanaki ta ya zai samu lokacin dai-daita matsalar Khadijatu.
Shima ba shi da wanan damar! Kamar yanda Anty Ramla ta rasa ta ta damar.
🌷🌷🌷🌷
#IG
#DABANNEINUWAR GAJIMARE 💨
® NWA
© INUWAR GAJIMARE 💨
SHIDA
Shuru ne ya ziyarci office ɗin na ɗan lokaci, tsakanin Nurse Ramla da Dr. Anwar babu mai motsin kirki.
Gyaran murya Dr. Anwar ya yi wanda ya kawar da shurun da ya ziyarci office ɗin nasa.
"Muje wajenta na ganta." Ya faɗa yana tashi akan ƙafafuwansa.
Jiki ba ƙwari Nurse Ramla ta tashi itama suka jera a tare babu mai yima ɗan uwansa magana.
Tura ƙofar ɗakin yayi a hankali wanda hakan ya ja hankalin Khadijatu da Ishaƙ da ke ta faman tambayarta abun da ya sameta.
Da sallama a bakinsu suka shigo ɗakin wanda Ishaƙ ne ya amsa musu, yana jin tsoro da fargabar ganinsu a tare.
"Yauwa Likita gara da kuka zo, ban san me ne ya sake samun Khadijatu ba, tun da na shigo na ganta haka tana kuka."
Kallonta suka yi a tare anan suka ganta ta haɗe kai da gwuiwa tana faman sauƙe ajiyar zuciya akai-akai, wanda ke nuna cewar ta yi kuka ta gaji har muryarta bai fita da kyau.
Zama Dr Anwar yayi a kujerar da ke kusa da gadon har a lokacin idanuwansa na kallon Khadijatu a hankali kukanta ke ratsa kunnuwansa yana jin shigarsa a jikin ko wata ƙofa ta jikinsa.
Idanuwansa ya rufe kana ya buɗesu a hankali "KHADIJATU!" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa.
Hakan ya sata ɗagowa a hankali, idanuwanta sun kumbura sosai launinsu ya koma jajir, wanda ke nuna ta sha kuka ta ƙoshi, musamman da take faman sauƙe ajiyar zuciya akai-akai.
"Kiyi haƙuri Khadijatu! Allah yana jarrabar bayinsa ta ko wata hanya, yana kuma gwada imaninsu dan ya jarrabe su ne.
Wanda suka yi haƙuri kuma sune masu samun babban rabo a nan duniya da kuma lahira."
"Me ya faru kuma Likita? Waɗan nan maganganun me ya kawo su?" Ishaƙ ya faɗa yana baza idanuwansa akan Dr. Anwar da Khadijatu da har lokacin ta ke jan zuciya bata iya magana.
File ɗin hannun Nurse Ramla ya karɓa ya shiga buɗe su "Ina ƙara baku haƙuri Ishaƙ. Zamu sallame ku a wannan asibitin zuwa wani asibitin a Kano!"
Ido Ishaƙ ya fiddo waje cikin mamaki da jin sunan garin da bai taɓa tunanin zuwa ba a wanan rayuwar, garin da sai ya shiga cikin gari ya ke jin labarinsa.
"Kano fa kace Likita? Me zai kaimu asibiti a babban gari irin kano? Bayan ga asibiti nan kuna kula da Khadijatu."
"Matsalar Khadijatu bamu da maganinta anan Ishaƙ! Larurar da ke tare da Khadijatu a yanzu bamu da kayan aikin da zamu kula da ita a wanan ɗan ƙaramin asibitin."
"Hasbunallahu wani imal wakil! Wata sabuwar larura ce ta sake samun Khadijatunah bayan ta Fyaɗen da aka mata?" Ishaƙ ya faɗa cikin sanyin murya idanuwansa tuni sun sauya kala daga ainihin kalarsu ta farare zuwa ja, wanda ke nuna tsantsar tsoro da tashin hankalin da ke tare da shi.
A hankali itama Khadijatu ta tsayar da kukanta, zuciyarta na ƙara ci gaba da bugawa kamar zata faso daga ƙirjinta.
"Ba wani babban larura bace ta ke damunta. Kawai dai acan zata fi samun kulawa ne, duba da ƙarancin kayan aikin da muke da su anan." Tashi tsaye yayi yana kallon Khadijatu da har a lokacin idanuwanta ke kansa, abun da ya ke gani a idanuwanta yasa shi saurin kawar da kansa gefe yana kallon Ishaƙ.
"Zo muje office ɗina."
Jiki a sanyaye ya bi bayansa yana ji kamar akwai wani abu da ke faruwa da ƙanwarsa. Ko a labarin da ke kai kawo a garin bai taɓa cin karo da matsalar da ta kai aka fidda wani mutum har asibitin Kano ba. Abu ɗaya ya sani idan abun ya kakare a tura mutum Asibitin ƙaramar hukumarsu ta MALAM MADORI, sai gashi su abun ya girmi nan kamar yanda ya girmi a kaisu Haɗejia, har sai sun dangana da babban birnin KANO.
"Ya Allah ta ina zan fara da wanan sabon al'amarin?" Ishaƙ ya faɗa a ƙasan laɓɓansa, yana hasko tarin ƙalubalen da ke gabansu.
Lokacin da suka shiga office ɗin Dr. Anwar kujera ya nuna masa alamun ya zauna.
Zama ya yi yana kallonsa ba tare da yayi magana ba, saboda ji yake kamar ko wata kalma da ke bakinsa ta gudu ta barshi, kamar yanda yawun da ke bakinsa ya riga da ya ƙafe.
"Ka san me yasa nace ka biyo ni nan office ɗina?"
Kai ya girgiza masa ba tare da ya yi magana ba. Shima kuma bai damu da son jin maganar tasa ba, duba da yanda yake kallon tsantsar tashin hankali a tare da shi.
File ɗin gabansa ya buɗe a hankali ya ɗago ya kalli Ishaƙ "A binciken da mukayi a yanzu mun gano ƙanwarka na fama da larurar YOYON FITSARI."
"Larurar Yoyon fitsari kuma? Kamar ya kenan Likita?" Ishaƙ ya faɗa yana ciro ko wata kalma a hankali da kuma hasashen adadin tashin hankalin da kalmar ke da ita.
Shi bai taɓa jin wani abu mai kama da wanan ba, ta ya mutum zai kamu da wata larurar yoyon fitsari?
"Ita larurar futsari tana faruwa ne ga yawanci yaran da aka yima fyaɗe ta ƙarfi ko kuma yarinyar da bata isa haihuwa ba, ta haihu da kanta, wanda hakan ke taɓa musu bladder ɗinsu ta kai ga basa iya ruƙon fitsari, a taƙaice dai basa jin ma fitsarin kansa balle zubarsa, sai dai suga wajen da suke ya jiƙe da fitsari."
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Likita kana so ka ce min itama Khadijatuna ta kamu da irin wanan ciwon? Kana so ka ce min Khadijatuna ta dawo miskiniya wadda baza ta iya ji ko yin fitsari da kanta ba?"
"A'a ba ta dawo miskiniya ba Ishaƙ! Kawai ta kamu da larurar ne, kuma zata warke da yardar Allah.Akwai mutane da yawa da suke kamuwa da irin wanan larurar kuma su warke a ɗan ƙanƙanin lokaci, kamar yanda nake da sa rai akan Khadijatunka zata samu lafiya itama da yardar Allah."
Wata takarda ta miƙa masa "Wanan itace takardar da ke nuna transfer aka muku daga wanan asibitin zuwa kano, in sha Allah ko me zai zo ya wuce kamar ba'ayi ba."
"Ya Allah ka dubi maraicinmu ka kawo mana sauƙin wanan matsalar! Idan kuma wani laifi muka aikata a gareka kake jarrabtarmu akan laifinmu ka yafe mana badan halinmu ba, sai dan rahamarka da kuma tausayawarka akan bayinka." Ishaƙ ya faɗa hawaye na zuba akan fuskarsa.
Wanan maganar da yayi ta ƙara karya zuciyar Dr. Anwar yana ƙara jin tausayinsu na cika zuciyarsa, bai san ya zai yi ya taimaka musu ba a yanzu.
Aljihunsa ya lalima babu komi a ciki sai kuɗin da bai wuce dubu uku ba, duk ya kashe kuɗinsa wajen siyayya wasu kuma ya sanjar da su daga Naira zuwa Rufi na ƙasar india.
Dubu ukun ya miƙa masa yana jin ba daɗi a zuciyarsa, yanaga gazawarsa da kuma ƙarancin bayar da ita a matsayin gudunmawar da xai iya basu.
"Ga wanan ko kuyi haƙuri kusha ruwa a hanya idan kun tashi tafiya."
Hannu biyu Ishaƙ ya sanya ya karɓa "Nagode Likita, Allah ya saka maka da alkhairi, ya biya maka buƙatunka na duniya da lahira, ya ji ƙan mahaifanka.
Tabbas bazan taɓa mantawa da irin wanan halaccin naka ba. Ina fatan Allah ya sake ƙaddara saduwarmu da alkhairi."
Daga haka ya miƙe jiki a sanyaye yabar office ɗin, yana ɗaga ƙafafuwansa a hankali ko wata laka ta jikinsa ta saki, ji yake kamar ba da ƙafafuwansa ne ya ke takawa ba, ko wani taku yana yinsa da fargaba da tsoron abun da za su iya tararwa anan gaba.
Jiki ba ƙwari ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, har lokacin Nurse Ramla tana ɗakin.
Bai mata magana ba ya fara tattara 'yan tsurarun kayansu.
"Tashi mu tafi Khadijatu." Ya faɗa bayan ya kammala haɗa kayan nasu.
A hankali ta sauƙo da ƙafafuwanta ƙasa ta sauƙo, ganin ba takalminta ya cire nasa "Sa takalmana mu tafi." Daga gadon ta sauƙo doguwar rigar da ke jikinta ta jiƙe jagaf har tana ɗiga ƙasa bayan sauƙarta a kan gadon.
Ƙullin kayansu ya kunce ya zaro wani