Showing 30001 words to 33000 words out of 91747 words

Chapter 11 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

799

ya manta lokacin da aka faɗa masa ita.

Dafashi yaji anyi wanda haka ya sashi juyowa daga tsayen da yake, Baban Indo ya ga abayansa yana dafe da kafaɗarsa "Zo muci abinci Ishaƙ." Baban Indo ya faɗa masa yana masa nuni da tabarmar da ke gabansu.
Bai yi musu ba ya bi shi suka zauna tuwon laushin hatsi ne da miyar busasshiyar kuɓewa da ta sha ƙananun kifi, ga man shanu sai tashi yake a cikinta.
Yawun bakinsa yaji ya tsinke wanda ya sashi saurin haɗiya ba shiri, yayin da cikinsa ke bada kalar sautin ƙara ƙululu alamun ya daɗe bai yi tozali da kyakkyawar cima ba.
Ruwan wanke hannu Mairama ta miƙo musu suka wanke hannayensu duka sanan suka fara cin abincin a tare.
Daɗin abinci da laushinsa yasa Ishaƙ lumshe idanuwansa 'Idan da ranka ba zaka taɓa yanke tsammani daga rahamar ubangiji ba."
Har suka ƙare cin abinci magana bata shiga tsakaninsu ba. Sai da suka ƙare sanan suka tashi suka ɗauro alwala.
"Mairama zan je na zazzaga da shi gonakin namu."
"To a dawo lafiya."

Khadijatu ce ta miƙe zata bisu, Mairama ta yi saurin riƙe ta, nan ta fara turjiya tana kiran "Yayana Nima zan bika."

Kai ya shiga girgizawa yana murmushi "Ki zauna da Inna zan je yanzu na dawo kinji Khadijatul Ishaƙ?"
Kafaɗarta ta maƙale alamar ba zata yarda ba.
Ruƙota Mairama ta yi cikin rarrashi "Yanzu zai dawo Khadijatuna, ki barsu su tafi."
Baki ta buɗe da niyar yin kuka amma kuma sai taji an bige bakin nata. Saurin dafe baki tayi da kallon wanda ya bige mata bakin. Indo ta gani ta riƙe ƙugunta sai faman zabga mata harara ta ke "Tuleliya da ke kikema mutane kuka zaki wani bishi? To ba inda zaki ki zo muje mu zauna muyi wasa, zan nuna miki kayan wasana dewa da Baba yake kawo min."
Bata jira maganarta ba ta kama hannunta ta shiga janta da ƙarfinta, dan dole Khadijatu take binta abaya tana waiwayen Ishaƙ har suka shige ɗaki.
Ajiyar zuciya Ishaƙ ya sauƙe yana bin bayan Baban Indo da yake ta ƙunshe dariyarsa "Indo manya."
"Kuyi sauri ku tafi kada ta fito ta ganka a sake sabuwar rigima."Mairama ta faɗa tana kallon ɗakin da su Khadijatu suka shige.

Ficewa suka yi agidan gaba ɗaya. Suna tafiya Baban indo na bashi labarin rayuwarsa "Kaganni nan lokacin da nake kamar kai na fuskanci ƙalubale mai yawa a rayuwata, kasancewata babban namiji a gidanmu, ina da ƙanne mata guda biyu da suke bi min. Bayan mu kaɗai iyayenmu basu sake haifar wasu yaranba, nasha wahala sosai wajen kula da su, musamman da ya kasance mahaifinmu bashi da wadatacciyar lafiya ga kuma rashin ƙafafuwa da yake fama da su a wancan lokacin.
Cikin haka muka taso na fuskanci matsala da yawa, da kuma ƙalubalen rayuwa a haka na nemi gonar haya na fara noma da ita, babu rani babu damina, ga kuma buga-bugar da nake ta neman aiki, yau ina nan tashar dako gobe ina can koyon kanikanci, a haka nake ciyar da ƙannena da iyayenmu.
Lokacin da girma ya kamasu na fuskanci ƙalubale sosai musamman da aurensu ya gabato haka na shiga faɗi tashi wajen haɗa musu abun da zai wankesu daga gori, har na aurar da su.
Cikin sa'a ƙanwata Hajara mijinta ya samu ci gaba saboda karatun bokon da ya samu yayi a wancan lokacin, a haka suka tashi daga wanan garin suka koma Birnin Kano tun daga lokacin ban sake samun labarinta ba, daga baya labari ya samemu akan sun yi hatsarin mota sun mutu.
Yanzu ƙanwata ɗaya ce, a duniya Ramlatu tana can Haɗajia da zama ita da mijinta da yaranta da take ɗaukan ɗawainiyar rayuwarsu saboda rashin ƙarfin da mijinta yake da shi.
A taƙaice dai ragamar gidan duka tana hannunta.
Babanmu da daɗe da rasuwa sai Mamanmu da take kusa da ni, yanzu ma da alama ta je unguwa shi yasa bamu haɗu da ita ba.
Kaga duk waɗan nan matsalolin su suka taru suka min rotso akai har na gaza samun damar yin aure akan lokaci, da ƙyar Ammu ta samarmin ɗiyar ƙanwarta na aura itace Mairama da kake ganinta a gabanka ita ɗiyar ɗanwar Ammu ce. Da kanta ta nema min aurenta.
Ban taɓa samun matsala da itaba duk abun da nake so tana sonsa, komi na kawo da hannu bibbiyu take karɓa.
Saida muka shafe shekara goma sanan Allah ya azurta mu da samun haihuwar Indo, tun bayan ita ban sake haihuwaba, shi yasa muka maiƙa ko wata kulawarmu a kanta." Numfashi yaja ya tsaya yana kallon gonakin da suke gabansu.
"Waɗan nan duka gonaki nane, da na mallakesu bayan na sha wuyar noma, a yanzu ƙarfina ya ragu bana samun damar yin noma mai yawa sai dai na bada hayarsu, na kuma noma aika ɗaya.
Amma yanzu saboda matsalar Khadijatu zan kama maka muyi noma tare har mu haɗa kuɗin nomanta. Na tabbata in sha Allah nan da shekara guda zamu tattara kuɗaɗen idan har munyi dace yayi kyau."

Risinawa Ishaƙ yayi har ƙasa yana jin hawaye na sauƙa akan kuncinsa "Wallahi har kunyar yi maka godiya nake ji Baba. Inaga kamar idan na gode maka ya gaza cika ma'aunin kyakkyawar sadaukarwar da ka mana.
A baya na ɗauka mutane duka masu son kansu ne, amma dalilin haɗuwata da kai na fahimci akwai nagari a cikin mugwaye. Ina fatan Allah ya bani tsawon rai da rayuwar da zan saka maka fiye da abun da ka min."

Tashinsa yayi tsaye yana murmushi "Ɗa na kowa ne Ishaƙ ban yi maka haka dan ka saka min wata rana ba.
Ko sanda nayi maka maganar auren Indo nayi hakan ne dan na jarrabaka, naga ko zaka iya yin kasada da ƙarya, amma sai na sameka a cikekken mutum mai ƙoƙarin neman halak ɗinsa, ina fatan ka cika ma'aunan rayuwarka a hakan."
Kiran sallahr da akayi yasa suka dawo cikin gari domin duhun magrib ya fara riskarsu, a haka suka shiga masallaci suka yi sallah, sai da suka tsaya akayi sallahr Issha'i sanan suka tafi gida.

Tun daga ƙofa yake jin dariyar Khadijatun hakan ya sashi saurin shiga gidan, tarar da ita yayi kusa da Indo tana ta mata surutu tana riƙe da kunnenta da kuma zaro idanuwanta waje. Gefe guda kuma tarkacen kayan wasa ne su gwangwamaye da su ƙyallen kaya, sai abun da ba'a rasa ba duk sunyi baja-baja da wajen sun janyo futular gabansu.
Shi kansa farin ciki yaji ya mamaye zuciyarsa har ya ƙarasa kusa da su basu sani ba, sai sautin dariyarsu da take tashi.
Hannayensa ya tafa da ƙarfi nan take suka tsorata anan shima ya fara musu dariya, ganinsa yasa Khadijatu maƙaleshi tana murna da nuna masa Indo ɗin.
Shafa kansu yayi duka ba tare da yayi magana ba, yana ga wata kyakkyawar rayuwa na kusantowa garesu, haske ya fara ratsa baƙin duhun da ya mamaye rayuwarsu.


****
Bayan kwana kwana biyu.

A cikin wanan kwanaki Ishaƙ ya fara sabawa da aiki wahalar gonar da su ke shida Baban Indo da ya jingine motarsa bai fita tasha sai sau biyu a sati ya ware.
Aiki suka fara da gaske kasancewar noman shinkafa yana da wahala sai an jure, amma kasancewar Baban Indo horarre ne a wanan fagen sai aikin ya zo musu da sauƙi. Noma suke na gaske babu hutu a cikinsa, tun safe idan suka tafi sai yamma suke dawowa.

A ɓangaran Khadijatu kuma ta saki jikinta da Indo saboda labarin da take bata da kuma janta da surutun da take, daɗin daɗawa indo ce wankinta da kuma tursasa mata yin wanka kullum.
Wani lokacin idan ta farka a tsorace to a jikin Indo take kwana saboda ɗakinsu ɗaya da ita. Shi kansa Ishaƙ yana ganin tarin ƙoƙarin yarinyar akan kula da Khadijatu da take kamar Babba. Ɓangaran Ammu mahaifiyar Baban Indo ma ba'a barta a baya ba wajen kyautata musu.
Ranar farko data fara ganinsu da jin labarin rayuwarsu tayi kuka kamar numfashinta zai cire, ƙarshe dai itama tace daga ranar sun zama jikokint halak malak muddum ba iyayensu ne suka bayyana ba.
Duka garin a yanzu sun san waye Ishaƙ da yawa suna masa kallon Babban ɗan Ado ne, saboda babu wanda ya sanarma asalin labarinsu.


*****
Bayan shekara ɗaya!

LAGOS, NIGERIA.

Takardar hannunsa ya shiga jujjuyawa idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir, jijiyoyin kansa duk sun tashi raɗa-raɗa.
"Likita ko yaushe sakamako ɗaya kake bamu. Kullum cewa kake lafiyata ƙalau nida matata amma har yanxu ban gamsu da wanan amsar ba. Me yasa idan ƙalau muke har yanzu matata bata samu ciki ba? Duk wahalar da nake sha kullum tana tafiya a banza ne likita?"

Kai Likitan ya girgiza yana mamakin ƙawa zuci irin na Kanal Aabidullah, kusan tunda ya sanshi duk wata sai yazo asibiti aduba masa matarsa ko ta samu ciki, amma har yanzu da aka shekara guda babu wani sauyi da sakamakon ke badawa sai na babu.
"Abun da muka gani kenan muke faɗa maka Kanal, lokaci ne baiyi ba kamar yanda muke sanar da kai, ka ƙara haƙuri."

Takardar ya cilla waje "Har zuwa yaushe ne zan ci gaba da wannan haƙurin Dr. Saleem? Ina son yara da yawa! Ina son ganin gidana cike da sautin kukan yara!"
"Kayi haƙuri ni ba abun da zan iya maka akan haka."

Harara ya buga masa "Zan san abun da zanyi a yanzu." Yana gama faɗar haka yaja hannun Amrah suka fice a office ɗinsa.




🌷🌷🌷🌷🌷🌷IG

   00000220000

Malam Madori.
 
  A cikin shekara ɗaya nan Ishaƙ ya aikatu ya kuma gane muhimmancin da lafiyarsa take da ita, ya godema Allah a bisa ni'imar lafiyar da ya bashi.
  Kamar yanda yake godema mutanen da suka zame musu kariya a rayuwarsu, suka ɗauki matsalar ƙanwarsa suka raba a tare da shi. Tun bayan zuwansu gidan su Indo ya nauyin zuciyarsa yayi sauƙi, musamman da basu taɓa nuna musu tsan-tsani da kyara akan larurar Khadijatun ba. Asalima sai tattali da kulawar da suke nuna mata ce ta ninku.
    Sai dai abu ɗaya ne har yanzu bata bar yinsa ba, tsoron mutane da kuma yawan zabura idan suna zaune. Haka ko barci take kullum sai ta farka a furgice tana ihu da kuka. Hakan yasa ko yaushe tana maƙale a jikin Indo, yanzu tabar maƙalema Ishaƙ sai Indo, idan zata je makaranta kuwa sai anyi da gaske take haƙura ta barta ta tafi.
  Haka tana dawowa kuma zata koma kusa da ita su zauna, a taƙaice dai Indo ce komi nata a wanan lokacin, kamar yanda itama Indo ta sadaukar da lokacinta da kominta wajen kula da ita, sai a mata faɗa bata ji haushi ba amma da anyi ma Khadijatu anan ranta zai ɓaci ta shiga yin guna-guni.

   Haka kuma kuɗaɗen da aka buƙata na lafiyar Khadijatu sun kammala, dan da kuɗin ya gaza cikama Ammu ce ta bada sarƙar zinarenta da take ta ɓoyenta tace a siyar.
  "Haba Ammu ya zaki bada sarƙar da kika ɗauki shekaru kina tsaronta fiye da lafiyarki." Ishaƙ ya faɗa idanuwansa kamar za su fidda ruwa, dan bai manta labarin da ta basu ba na cewar ta siyeta ne a lokacin da mutanen gari suke mata gorin, ta bautar da Ado shi ke ɗawainiya da ita, a wancan lokacin ta saida ko wata kadara da ta mallaka ta shiga neman sana'ar da zata tallafa masa, duk da Ado yayi ƙoƙarin dakatar da ita, amma a lokacin amsa ɗaya ta bashi "Ka sauƙe nauyin da na ɗora akanka a matsayinka na babban ɗana, ka yi fafutuka da dukkanin ƙarfin ikonka ka auren da ƙannenka ba tare da na tsaya na taimaka maka ba. Amma a yanzu dole nima na miƙe tsaye na tallafi rayuwarka na sauƙe maka sauran nauyin da na ɗaura maka, ina da lafiyata bani da igiyar wanda zata hanani shiga na nemi halak da gumina." Tun daga lokacin ta fara shiga gidaje masu kuɗi ta fara aikatau ana biyanta daga baya kuma ta bari ta haɗa jarinta take siyo kayan gwanjo tana saidawa a unguwar, wanan shine babban arziqin da ya amsheta ya zame mata tsanin rufuwar asirinta, take cin gajiyar arziqinta, bayan komi ya ɗore ta siyi kayan ƙawa na mata, harda sarƙar da ta ke nunata da alfahari idan sun haɗu da ƙawayenta a gidan bikin. Amma kuma sai gashi yanzu itace zata bada sarƙar da take jin kanta a gajimare a duk lokacin  da ta sakata.
 
   "Ammu ki barta sai muyi aikin rani in sha Allah zamu sake samun nasara mu samu kuɗin da zamu mata maganin."

   Ranƙwashinsa ta yi akansa tun kafin  ya iddasa kaiwa ƙarshen maganar, tana haɗa masa da duƙuwa "Ungo amshi wanan ɗan banza mai kai kamar naɗaɗɗiyar buta! Kana tafe lamo-lamo da kai wandonka na zamewa a ƙugunka zaka wani ce zaka ƙara wani aikin noman rani.
  To buɗe kunnenka da kyau kaji wanan shekarar ba wanda zai ƙara mana aikin noman rani, kun zo duk kun fice a kamannin mutane daga kai bar Ubannaku.
  Sanan da kake batu akan na sha wahala na siyi sarƙa ince dai ba kai ka min wahalar ba ka siya min da naka kuɗin ko?"
  Kai ya sunkuyar ƙasa dan yasan halin masifar Ammu wani lokacin kamar ta gari idan ta fara magana a nitse amma da haukanta ya hau kanta nan zata hargitsa musu ƙwaƙwaluwa.
  Baki ya taɓe shima ƙasa yana shafa wajen da ta ranƙwashe shi "Daga naji tausayinki shine zaki zo kina min masifa." Sarƙar ya warce ya fice yana gun-guni.
  "Oho dai dole ka karɓa ɗin, itama ba kyauta na bata ba ai da ta samu lafiya za muyi lissafi ta biyani."

  Ranar da za su tafi asibitin gaba ɗayansu suka tafi da Baba da Mairama da kuma Ammu sai Indo da take cikin ruƙon Khadijatu, ta ƙanƙameta sosai kamar za'a ƙwace mata ita. Musamman da ta ga yara sun kewayesu sai kiran Indo suke.
   Baban Indo yaso ace sun zauna a gida har su je su ji ya abun zai kasance, amma Ammu ta buga ƙafa tace ƙafarsa ƙafarta dole ta je taga yanda za su kaya da abu.
Dan dole ya yarda suka tafi dukansu, suka sa mukullu suka datse gidan.

   ****

ASIBITIN MALAM AMINU KANO.

    Lokacin da layi yazo ta kansu dakatar da su Baban Indo yayi, yace dole su bari shi ya shiga da ita dan kada a cika masa ofishinsa.
   Sai da ya haɗa da jan ido sanan ta ƙyale Indo ta biyo shi, amma tana ta wai-wayenta "Karki tafi ki barni INDO!" Ta faɗa cikin sanyin muryarta.
 
  Murmushi Indo ta mata tana gyaɗa mata kai "Ba zan tafi ba har sai kin dawo."
   Kai Ishaƙ ya girgiza yana gyara tsayuwarsa da sarƙe hannayensa a cikin ƙirjinsa, girman ƙaddara yake hangowa da kuma iko na Allah da yake sanya soyayya da shaƙuwa a zukatan bayinsa. Idan da za'a bashi labarin cewa al'amari irin wanan zai faru da shi to tsaf zai ƙaryata labarin.
  Khadijatun da take cikin halin larura da furgici da ƙauracewa magana itace ta miƙa yardarta ga Indo wadda bata fi ƙanwar bayanta ba, amma kuma a yanzu Indo ɗince ke a matsayin yayarta, wadda ta ɗauki nauyin larurarta, bata taɓa harararta ko kyararta akan larurarta ba, madadin haka soyayya take nuna mata, da cin abinci tare da ita da kuma yin soyayya tare da ita.
    Shi yasa akace ɗan Adam gajeran tunani gareshi, da kuma gundulallen tsammani.
  
  ***
  Juya fayil ɗin likitan yake yana ƙara kallon mutane biyun da suke gabansa "Shekara guda kenan rabonku da asibitin nan!"
 
   Kai Baban Indo ya gyaɗa "Eh likita mun zo da kuɗin aikin da za'a mata."

    "Masha Allah!" Likitan ya faɗa yana rubuce-rubuce ajikin fayil ɗinta.
  Daga nan ya miƙe tsaye "Ku zo muje na nuna muku wajen da zaku biya kuɗin aikin."

   Futa sukayi a ofishin nasa anan suka haɗu da su Ishaƙ hannu Likitan ya miƙa masa "Yayan Khadijatu ko?" Ya tambayeshi yana murmushi akan fuskarsa.
  Kunya ce ta kama Ishaƙ musamman da ya tuna baƙar maganar da ya faɗa masa ta mai jajayen kunnuwa, risinawa yayi ƙasa ya gaida shi ba tare da ya miƙa masa hannun ba.
   "Ko suma hannayen nawa sun yi ja da yawa ne?" Likitan ya faɗa yana duba hannunsa cikin sigar barkwanci.
   Kai Ishaƙ ya girgiza yana nuna masa nasa hannun da kanta ta cika shi "Idan nasa hannuna cikin naka ji za kayi kamar ƙaya na sukanka. Shekara guda nayi ina saran ƙasa da ciyawa da su."
   Kai Likitan ya girgiza yana murmushu ba tare da yayi masa magana ba "Ku zu muje kada mu ɓata lokaci da yawa."
  Daga nan suka bi bayansa yana tsaye a wajen suka ɗauki duk kuɗin aikinsu, harda sauran sanjin dubu hamsin akai. 
   Ɗaki na musamman ya kaisu ya miƙa musu wani kaya mai launin shuɗi "Ta sanya wanan kayan, nan da minti goma nurse zasu zo su ɗauketa zuwa ɗakin da za'a mata aikin."

   "To Likita mun gode." Suka faɗa a tare.
  Yana futa ya shiga danna wayarsa bayan wani lokaci ya karata a kunnensa "Dr. Imran akwai aikin gaggawa yanzu, dan Allah ka zo."
  "To!" Shine amsar da ya bashi ya kashe wayar.

   Ajiyar zuciya ya sauƙe dan yasan halin Dr. Imran tun bayan zuwansa, miskilini na buga a jarida bai damu da shiga harka mutane ba, iyakarsa ya zo yayi aikin da ya kawo shi ya fice.
  Yanzu shekara guda kenan da zuwansa wanan Asibitin, zai iya cewa ya kirashi yafi sau a ƙirga amma idan ba ƙarya yayiba shi ko darajar adana lambarsa ma bai samu yayi ba, ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login