Showing 3001 words to 6000 words out of 91747 words
babu Khadijatu? Astagfurillah! Ya Allah na tuba idan na aikata ma wani laifi bisa rashin sani!'
"Alhamdulillah, ta farka!" Maganar Nurse Ramla ta ratsa dodon kunnuwansa, wanda ya ke ji kamar ta watsa masa ruwan ƙanƙara a zuciyarsa ne.
Hakan ya sashi juyowa a hautsune dan ganin zahirin abin da kunnuwansa suka jiye masa "Tabbas ta farka." Ya faɗa lokacin da idanuwansu suka haɗe waje ɗaya.
Da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana zama "Khadijatu nah!" Ya faɗa yana ƙoƙarin ruƙo hannunta.
Sai dai hakan ya gaza faruwa saboda zaburar da tayi ta matse jikinta a can ƙuryar gadon, tana faman rarraba idanuwa akan mutanen da take gani.
Kallonta ya yi ya kalli Dr. Anwar wanda shima idanuwansa na kan Khadijatun. Mayar da kallonsa ya sake yi kanta, har lokacin tana maƙure a jikin gadon, sai zabura take tana sauƙe ajiyar zuciya.
"Khadijatu, ba ki gane ni ba ne? Ni ne fa Yayanki Ishaƙ!" Ya sake faɗa hawaye na zuba akan idanuwansa.
Kai ta girgiza masa cike da tsoron abun da idanuwanta ke gani a tare da shi, tabbas muryarsa yayi mata kama da ta yayanta, amma kuma fuskar mugun da ya cutar mata take gani, bama shi ɗaya ba, duka mutanen da ke ɗakin kallon mutum guda ta ke musu.
"Ka daina yin muryar Yayana, ka daina kirana da Ƙanwarka, Yayanah ba zai taɓa min mugunta ba.
Laifin me na maka da sai ni ce zaka cuta? Me yasa ? Me yasa ?" Kuka ta fashe da shi mai cin zuciya tana ƙara kiran "Me yasa sai ni? Wani zunubi na aikata haka a rayuwata?" Sosai take kuka ko ina a jikinta yana rawa saboda yanda take kuka mai sauti.
"Ina jin zafi sosai a zuciyata da jikina! Ban san tsawon wani lokaci zan ɗauka ina jin wanan ƙuncin ba, ban sani ba?"
Ido Dr. Anwar ya runtse yana jin zafin maganarta, yana kuma ji inama zai ga mutumin da ya ketawa wanan yarinyar haddinta da kuwa ko zai ƙare rayuwarsa a gidan maza sai ya azabtar da shi, azabar da babu wani mahaluƙi da aka taɓa yiwa irinta.
"Khadijatu ba murya na yi ba, ni ɗinne da gaske! Ɗago idonki ki kalleni?"
Kai ta girgiza tana ƙara haɗe kanta akan ƙafafuwanta, yayin da ta rufe kunnuwanta da dukkanin hannunta "Bana son jin wanan kalmar ƙaryar!"
Shuru yayi hawaye na bin kuncinsa, yana kallon Likitocin da suka kewaye shi "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." Ya faɗa a fili yana dafe kansa, yana ƙara jin sabon tashin hankali na kusantowa gare shi.
"Likita Khadijatu tsorona ta ke ji, ta gaza ga ne ni! Khadijatu ta haukace! Ya haukatar min da ƙanwata Likita!" Ya ƙarasa maganar da gunjin kuka, yana jin kansa kamar zai rabe biyu tsabar tsananin tashin hankalin da ya ke ciki.
"Khadijatu ta gaza gane ni, ni Ishaƙ! Ni ne yau Khadijatu ta ke cewa ba ni ba ne! Ni Ishaƙ Yayanta fa! Ya Allah na tuba." Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa.
Baka jin komi a ɗakin banda sautin kukan su biyun, ita tana kukan zafin da ke damunta da surutun mutumin, yayin da shi kuma ya cika mata kunne da kukansa na mamakin ƙin ganeshin da ba tayi ba.
Dafa shi Likitan ya yi, cikin tausayawa, yana ƙara kallon yanayin Khadijatun da har yanzu a tsorace ta ke da zamowarsu a wajen, ita kaɗai ma sai zabura ta ke.
"Ka nutsu Ishaƙ, ka kalli yanayin da ƙanwarka ta ke ciki. Ba kasa ganeka ta yi ba, har yanzu tana cikin tsoro ne da furgicin abun da ya sameta.
Idan har baka ƙarfafa zuciyarka ka lallashi kanka ba, ta ina zamu gane bakin zaren wanan matsalar? Ta ina zamu fara shawo matsalar mu samu ta warke sosai? Ka na ga yanda ko ina a jikinta yake motsi, ga ɗinki da ke jikinta ba'a son kyakkyawan motsi da irin zaman da ta yi.
Ka yi haƙuri ka daina kuka, ka sake jarraba yi mata magana, kai kaɗai ne ƙwarin gwuiwar mu a yanzu." Dr. Anwar ya faɗa yana ƙoƙarin dai-daita tasa zuciyar, yana kuma fatan ganin ya ƙarfafa masa gwuiwarsa.
"Ban san ta ina zan sake yi mata magana ba Likita, ya riga da ya haukata min Ƙanwa." Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa.
"Ka sake gwadawa dai, ta iyu a yanzu ta gane ka, kaga ta ɗauki lokaci idanuwanta biyu."
Kallonsa ya sake yi, har a yanzu bata gyara zamanta ba, yawu mai kauri ya haɗiye sanan ya sake magana a hankali "KHADIJATUL ISHAƘ"
A hankali ta ɗago kanta tana kallonsa, idanuwanta cikin nasa, a hankali fuskar mugun mutumin ta fara ɓacewa tana komawa fuskar yayanta, sunan da yayi amfani da shi wajan kiranta da amon muryar da ya fita ta tabbatar Yayanta ne kaɗai ke mallakar wanan muryar.
A hankali ta buɗe bakinta "Yaya nah!" Sai kuma ta matsa daga takurar da tayi, shima yana isa kan gadon, rungume shi tayi tana ƙara sautin kukanta, shima hawayen yake yana shafa kwantaccan gashinta da ya gaji da hargitsewa, ga ƙura da karare duk sun maƙale a jikinsa.
"Ina jin tsoro Yaya! Ina jin fargaba na caccakar zuciyata Yaya! Laifin me nayi masa?"
Hawayen fuskarta ya shiga gogewa duk da shima nasa hawayen bai bar sauƙa ba "Ba kiyi laifin komi ba Khadijatu. Ba abun da zai sake samunki in sha Allah, ina tare da ke, yanzun ma laifina ne da na tafi na barki ke ɗaya."
Kai ta girgiza masa tana ƙara cakumarsa kamar wani zai ƙwace mata shi "A'a Yaya, ni ce nayi laifi da na taho ban jira ka zo ka ɗauke ni ba."
Gyaran Murya Likitan yayi wanda ya sa Khadijatu cakwui-kuye Ishaƙ tana cusa kanta akan ƙirjinsa, idanuwanta gam a rufe "Yaya kana jin maganarsa ko? Kana jin gyaran muryarsa ko?"
Kallon saitin likitan ya yi wanda yake riƙe da magani a hannusa, da alamu dalilin yi musu gyaran muryar kenan.
"Ba shi ba ne Khadijatu, wanan likita ne?" Ido ta ƙara runtsewa tana daɗa cakume shi.
"Bana son sa Yaya! Kace ya fita anan!"
Kallon Likitan yayi sai dai da mamakinsa murmushi yaga yana yi, ya miƙama Ramla maganin ya fice a ɗakin.
"Ya isa haka nan sha lele, maza tashi ki karɓi maganinki ki sha." Nurse Ramla ta faɗa cike da tausayin yarinyar.
Kafaɗa ta maƙale tana girgiza mata kai "Ishaƙ ya kamata a samo mata abincin da zata ci, ga maganinta nan zata sha."
Kai ya dafe cikin mamaki, saboda shi ya manta da akwai wani abu wai shi abinci, tun bayan karo da wanan tashin hankalin komi da ke kansa ya ɗauke. Ya sha ji ana cewa tashin hankali kan mantar da komi, ciki kuwa harda yunwa, amma bai ɗauki maaganar da gaske haka ba.
"Ya Allah! ko sallahr zuhur ban yi ba yau. Astagfirullah ya Allah." Ya faɗa yana ƙoƙarin tashin daga zaunen da ya ke, sai dai hakan ya gagara, saboda cakumarsa da Khadijatu ta yi.
"Sallah zanyi Khadijatul Ishaƙ."
Kafaɗa ta maƙale a hankali ta fara magana "Ni ma zan yi sallahr yaya! Yau ban yi sallah ba."
Kallon Nurse Ramla ya yi dan bai san ta ya zai tashi ba.
"Bari na taimaka ma." Nurse Ramla ta faɗa tana ƙoƙarin cire hannun Khadijatun a jikinsa da iya ƙarfinta.
Sai da suka kai ruwa rana sanan suka yi nasarar cire shi daga riƙon da ta masa, kuka ta saki da ƙarfi tana faman kiran "Yaya nah!" Bai juyo ba sai saurin da ya ƙara yi yana haɗawa da gudu-gudu dan ya samu ya hutar da kunnuwansa daga jin sautin kukanta.
🌷🌷🌷🌷🌷
#InuwarGajimare
#Dabanne
Oum-Nass
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
NAGARTA WRI. ASSOCIATION
OUM-NASS
Assalama alaikum
Barkanmu da sallah 'yan uwa, Allah yasa mai lada muka yi yasa muna cikin bayin da aka 'yanta a wanan watan.
HUƊU
Ba kalar lallashin da Nurse Ramla bata yi ma Khadijatu ba, amma bata bar kuka ba sai ma ƙara maƙale jikinta tayi a waje ɗaya, ta na matsawa daga kusa da Nurse Ramla.
"Ki yi haƙuri kada ku cutar min, ki kira min Yayanah!"
"Ba zan cuce ki ba Khadijatu, ni ma'aikaciyar lafiya ce, ko ƙuda ba zan iya cutarwa ba, balle mutum."
Kai ta girgiza tana tsuke jikinta waje guda "Mutane basu da tambarin da za'a gane ɗabi'arsu Anty! Ba a goshinsu ake ganin tambarin da zai nuna ɗabi'arsu ba. bani da kowa sai Yayanah! Ba ni da Mama da Baba! Amma hakan bai hana Mutum ya cuta mun ba! Me nene laifina dan ina marainiya? Me nene laifina dan ina neman ilimi?
Ki duba girman Allah kada kema ki cuce ni." Ta ƙarasa maganar numfashinta na sarƙewa kamar zai fita yabar jikinta, kukanta na ƙara tsananta.
'Ya Allah kada ka jarrabe ni da Abun da yafi ƙarfina da na zuciyata!' Nurse Ramla ta faɗa a zuciyarta, lokacin da take jin sautin maganar Khadijatu na huda ko wata ƙofa ta jikinta yana datsa zuciyarta.
Ba sai an faɗa mata komi ba, amma a ɗan ƙaramin Ilimin da tayi ta fahimci Khadijatu ta zauce, har yanzu a furgice take akan abun da ya faru da ita.
Dole ta tsorata, itama kuma zata iya tsintar kanta a hali irin nata, muddum akace ƙaddararta tayi kamancecceniya da ta wanan yarinyar.
A hankali ta zauna a bakin gadon tana dafa hannun Khadijatu da ta haɗe waje ɗaya "Ko kaɗan ba kiyi laifi ba Khadijatu! Ƙaddararki ce ta zo a haka. A cikin mutune har yanzu akwai nagari, kamar yanda mugu ya ke yawo a cikin su.
Kamar yanda kika faɗa ba'a gane mutum da kallo ɗaya, amma idan aka zauna da shi akan gane matsayin da ɗabi'arsa ta ke.
Ki bani wanan damar ta kula da ke! Ki ɗauke ni kamar Yayarki."
Kai Khadijatu ta sake girgizawa a karo na biyu "Bani da wanan haɓakon, bani da wanan ƙumajin, kamar yanda bani da wanan damar."
Shuru ne ya ratsa ɗakin na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta sake magana "Amma za ki bani damar kula da lafiyarki ko?"
Sai a lokacin ta ɗago kanta, ido suka haɗa sai kuma taji ba zata iya musanya mata ba, tana jin nauyin tanka matan da ta ke.
A idonta taga tausayawa kamar yanda take gani a idanuwan yayanta.
Kai ta gyaɗa mata ba tare da tayi magana ba.
Ƙofar ɗakin aka ƙwanƙwasa wanda ya kawar da shurun da ɗakin ya yi "Zan iya shigowa?" Dr Anwar ya faɗa kafin ya turo ƙofar.
Kallon Khadijatu Nurse Ramla ta yi, tana son jin mi zata faɗa, ga mamakinta sai taga tana lulluɓe jikinta da zanin gadon tana curewa a waje ɗaya, ko ina na jikinta ya ɗauki rawa.
Tashi tayi ta buɗe masa ƙofar ɗakin bai shigo ba ya tsaya daga waje, ya miƙa mata falas ɗin shayi da kuma wata baƙar leda "Ki bata abinci ta ci, daga nan sai ta sha maganinta. Kafin Yayanta ya dawo."
Karɓa ta yi tana mamakin halayyar Dr Anwar na taimako.
"Ina jin tsoro Dr Anwar! Ina jin tsoro akan yawan furgicin da take da tsoron mu, ban so zargina ya tabbata a kanta."
Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi, yana furzar da iska a bakinsa "Ki bata abinci ta ci, in sha Allah zuwa gobe zamu sake dubata, kafin nan ina kyautata tsammanin ta samu nutsuwar zuciya, tsoron da ke tare da ita ya ragu."
Jiki a sanyaye ta gyaɗa kai "Shikenan Allah ya kaimu gobe."
Daga haka ta koma ɗakin, ledar ta buɗe abun mamaki harda doguwar riga kala biyu a ciki da sabbin wanduna, ga kuma sabon brush da makilin a ciki.
Sai kayan haɗin shayi "Lallai Dr Anwar yayi nisa." Nurse Ramla ta faɗa a fili.
Sai da tayi da gaske sanan ta iya tada Khadijatu, da kanta ta wanke mata baki sanan ta haɗa mata shayi mai kauri, shima sai da suka kai ruwa rana ta samu ta sha, daga nan ta bata maganinta wanan kam bata sha wuya ba, ba musu ta karɓa, amma tana sha tana hawaye.
Anan ta gyara mata zamanta ta huta, ganin ta ɓungire da gyangyaɗi yasa ta gyara mata kwanciyarta tabar ɗakin.
Tana futowa suka yi kiciɓus da Ishaƙ ya dawo da leda a hannunsa sai sauri yake "Kin ganni sai yanzu na dawo likita."
Murmushi ta masa tana kallonsa cike da tausayawa "Ai ka yi sauri ma. Amma kana fita Dr Anwar ya kawo mata abinci, tama ci har ta sha magani yanzu barci ya ɗauketa."
"Ikon Allah ashe har yanzu akwai mutanen kirki a wanan duniyar?" Ya faɗa cikin mamakin abun da ta faɗa.
Yana risinawa har ƙasa "Ban san da wata kalma zan gode muku ba wadda zata cika ma'aunan aikin alkhairinku a gareni." Hawaye ne ya zubo a idonsa wanda ya sa shi dakatawa daga yin maganar ta sa.
Kansa ta shafa cikin tausayawa "A iya rayuwata ban taɓa ganin namiji mai saurin kuka irinka ba Ishaƙ! Badan badan ba sai na ce hawayenka sunyi kusa da idanuwanka." Ta faɗa cikin sigar tsokana da son bagarar da zancen nasa.
Hakan ya yi tasiri kuwa, dan sai da yayi dariya yana share hawayen kan fuskarsa "Akan Khadijatu ba abun da bazan iya ba Likita. Ita ce mutum ɗaya tilo data rage min, ban san kowa a dangina ba sai ita ɗin." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa wanda kana ji kasan hawaye ne ke barazanar sauƙa akan idonsa.
"Ban san me yasa nake jinku a raina ba kai da 'yar uwarka, Amma na tabbata akwai wani abu da ya alaƙanta hakan da abun da ya faru da ku.
Yanzu ba lokacin magana ba ne, amma idan hankali ya kwanta zan so jin tarihinku."
Murmushi yayi sanan ya gyara tsayuwarsa yana kallonta "Mu ai bamu da tarihi wanda ya wuce na mu biyun nan, na dai san mamana ta zo damu da niyar nunawa danginta mu, anan mukayi hatsarin mota ita da direban da ya kawo mu suka rasu, duk da ita ta yi janya mai tsayi har tsawon watanni shida, a lokacin bata tuna kowa sai Khadijatu.
Har ta mutu sunan Khadijatu take nanata min, bani da wayon da zan tuna daga inda muka fito a lokacin, hakan yasa na fara fafutukar sabuwar rayuwa da Khadijatu a wanan ƙauyen na TONI."
Ya ƙarasa maganar yana shafa fuskarsa "Na yarda da wanan kalmar ta bahaushe da yake cewa, rabon bawa da arziƙinsa duk inda yake sai ya taka, kamar yanda ƙaddara ke kiran mutum zuwa inda aka rubuta masa sai ya taka.
Baƙo kan zama ɗan gari a garin da babu nasa, musamman da duniya takan zama mashimfuɗin karɓa da kuma bayarwa. Idan kuma ɗabi'arka ta ban-banta zaka samu masu kamancecceniya na son kwaikwayonka."
Kawar da kanta tayi daga kallonsa, tana share hawayen idanuwanta "Ka samu kaima kaci abincin da ka kawo. Khadijatu ta ci abinci da yawa, zata so kaima ka ci."
Ledar da ke hannunsa ya ɗaga yana kallo "Tun bayan rashin lafiyar mamanmu ban ƙara cin abinci ni kaɗai ba, sai tare da Khadijatu.
Zan jirata, idan ta farka mu ci tare."
Bai bari ta sake magana ba ya wuce ya shige ɗakin da Khadijatu take.
"Ya Allah ka sakama waɗan nan yaran! Ka bi musu hakkinsu!" Nurse Ramla ta faɗa tana goge hawayen kan idonta.
******
Washe gari.
"Ya Allah!" Dr Anwar ya faɗa yana sharce gumi a goshinsa.
"Nifa ban ga komi ba Anty Ramla. Ban san ko hakan na nuna min ko me lafiya ne ba kamar yanda muke tunani ba ne."
Ajiyar Zuciya Nurse Ramla ya sauƙe "Alhamdulillah! Har naji daɗi a raina."
Shuru ya yi yana ƙara juya takardar da ke hannunsa, yana ganin kome da ke cikinta na nuna masa lafiya lau ne, amma wani sashi na zuciyarsa ya ƙi aminta da hakan, musamman da ya yi la'akari da rashin ingancin kayan aikin da suke da shi, da kuma matakin karatunsa da bai zurfafa ba.
'Asibitin ƙauye! Mai cike da ban al'ajabi, kamar yanda mutanen ƙauyen su ke da ban mamaki, zai iya cewa Khadijatu itace mutum ta farko da ya fara karɓa tun bayan zuwan su wanan asibitin.
Ba wai dan ba'a jinya a garinba, a'a sai dan ƙarancin wayewa da mutanen garin basu yi ba, da kuma rashin bawa asibitin muhimmanci da suke yi.
Ya fara da matsala mai wahala, ya kuma kasa ganin zuwan warwarewarta a tare da shi, abu ɗaya ya ke da tabbaci akansa, shine samun lafiyar ɗinkin da aka mata, bayan haka kuma bai san me zai ci gaba da bijiro masa ba.'
"Ya Allah ka sauƙaƙama baiwarka wanan matsalar!" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa da karaya da al'amarin da yake ganin haske da ratsin duhu a cikinsa.
"Ameen Dr Anwar.
🌷🌷🌷🌷🌷
#InuwarGajimare
#Dabanne
Oum-Nass
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
OUM-NASS 🏇
BIYAR
A hankali ya ja kujera ya zauna a gaban gadon da take kwance, idanuwanta a lumshe, tana sauƙe ajiyar zuciya, kamar ta yi tseren gudu.
Fuskarta ta yi fayau, idanuwanta sun ƙara girma,tsinin hancinta ya ƙara fitowa, shekarunta sun gaza ɗauke tashin hankalin da take ciki.
Da ƙyar ya cira hannunsa ya fara shafa kanta, wanda ta hargitse ya tattare saboda rashin nutsuwar da ke tare da mamallakinsa.
"Indai har za'a tambaye ni wasu ranaku ne suka fi zama masu wahala a gareni ? To kai tsaye zan bada amsa akan waɗan nan ranakun, wanan lokacin shine lokacin da na taɓa jin furgici da tsoro.
Dan Allah Khadijatu kada ki tafi ki barni! Kada ki bari zuciyarki ta karaya."
Ishaƙ ya faɗa yana shafa kanta hawaye na zuba akan fuskarsa.
Kwanaki biyu da faruwar wanan al'amarin amma ji yake kamar yanzu ne abun ya faru, ba zai iya tuna lokacin da ya zauna ya ci abinci ba, badan kada ya yi ƙarya ba ruwama mantawa ya ke da shansa sai idan zai yi alwala.
Ko me da ya tsara a rayuwa da duniyarsa ya dawo kamar rusasshen mafarki, kyawawan lokutan da yake hasko musu shi da Khadijatu wani ya zo ya ɓata masa sa ran da ya ke.
A da tambaya ɗaya yake ma kansa "Ina AHALINSu su ke? Me yasa ba su neme su ba?"
Amma kuma a yanzu tambayoyin sun ninka wancan, ya