Showing 87001 words to 90000 words out of 91747 words
suka shiga gaisawa har zuwa lokacin bakin Amrah bai rufe ba daga murmushin da ta ke.
"Abokinmu ya hanya?" Ta aika da maganar a saitin Aabid da ya gagara ɗauke idanuwansa akanta.
"Alhamdlh! Fatan mun sameku lafiya." Ya faɗa yana wara haƙoransa waje kamar mai kyallan man goge haƙora.
Kai ta gyaɗa masa kawai tana mayar da kallonta ga Amrah da take ta mata hira "Ana cewa camera na ƙarawa mutum kyau,amma dana ganki sai na fahimci tana cutar mutane ne. Kinfi kyau a haka Matar yayana fiye da a hotonki da na gani."
Murmushi kawai ta yi tana yaba surutun Amrah "Nagode."Ta faɗa da sanyin muryarta.
Ruƙo hannun Amrah tayi "Taso muje kuci abinci, sai ku huta."
Shafa shafaffen cikinta Amrah ta yi "Kin san kuwa dan ɗoki ko abinci ban tsaya na ci ba, duk da cewa Hubbie yaso na tsaya na ci ɗin."
"Ayya dama ace ya miki ɗura ai." Khadijatu ta faɗa cikin sigar tsokana, hakan yasa su yin dariya a tare.
A tare suka ci abinci har Aabid da shi kam cakula shi ma ya shiga yi, ganin Khadijatu a yau ya ƙara hargitsa masa tunaninsa, kawai ƙoƙarin dannewa yake a lokacin da yake ga soyayyarta kwance a idanuwan Amrah.
Yana ji a ranta da ace Amrah tasan wacece Khadijatu to da kallon ƙiyayya zata masa, shi dai kam ya ji daɗi, ya haɗu da aboki nagari kasancewar Aabid a matsayin likitan Khadijatu kuma mijin da zata aura, amma duk da haka bai tonawa danginsa abun da ya faru da ita ba.
A cikin kwana ɗayan da Amrah sukayi a gidan su Khadijatu shaƙuwa ta shiga tsakaninsu sosai, haka ta fahimci su waye dangin Khadijatu, soyayyar da suke nuna mata kaɗai ta isa ta sanar da ita matsayin da take da shi a danginsu.
Haka kuma tun zuwanta ta ke ganin kulawar da Ishaƙ ke nunama Khadijatu, kamar mahaifiyarta, duk bayan awa guda sai ya ƙirata a waya ya tambayi ya take, tun abun na bata mamaki har ta gaza ɓoye mamakinta ta amshi wayar.
"Ina jin tsoron wanan shaƙuwar taku zata sa matarka da mijinta yin kishi da ku."
Dariya suka yi a tare shi da Khadijatu "Matar da zan aura tana tayani son Khadijatu, ƙila idan aka burma zuciyarta za'aga ta fini son Khadijatu fiye da ni da zan aureta.
Shi yasa naƙi yarda na faɗa soyayya da kowa sai wadda ta sanni ta san kuma ƙanwata, ta fahimci zuciyarta.Ni kamar INUWAR GAJIMARE ne a tare da Khadijatu, shi yasa nake mata rumfa wajen sauƙar da ruwa a jikinta ko kuma ranar da zata huda kanta.
Babu ni idan har babu Khadijatu Amrah, a tare da ita nake ganin hasken da ke huda zuciya, ban san komi na rayuwata ba kamar yanda nasan na rayuwarta.
Ina son ƙanwata fiye da rayuwata, shi yasa nake tunanin anya kuwa yayanki zai iya kula min da ƙanwata kamar yanda ni zan kula da ita?"
Tun da ya fara maganar take kallonsa tana jin zuciyarta na buɗewa da karɓan saƙonsa, yayin da rauni ya fara dirarma zuciyarta.
Amsar da zata bashi ta shiga lalime a kwanyarta.
"Ban ma alƙawarin kula da Khadijatu kamar yanda ka ke kula da ita ba. Amma na maka alƙawarin zan sota fiye da rayuwata, zan bata kulawa fiye da yanda zan bawa tawa rayuwar, zan zame mata haske a lokacin da duhu ya shigo cikin rayuwarta, zan zame mata inuwar bayanta da ke bibbiyar lamarinta.
Idan har ban zame mata INUWAR GAJIMARE ba to zan zame mata MADUBIN DUBAWARTA, a duk lokacin da ta ganni murmushi zai wanzu akan kyakkyawar fuskarta.
Ba daɗin baki nake maka ba, tabbaci nake baka akan zan shimfiɗa tawa rayuwar wajen kula da tata rayuwar."
Juyowa suka yi a tare suka ga Nabil ne tsaye a kansu, ya zura hannayensa akan aljihun wandonsa, fuskarsa ta yi fayau da ita sai ƙyalli ta ke.
Baki Amrah ta buɗe kafin daga bisani ta bugawa tsalle ta rungume shi "Na sani yayanah! Wallahi ina da tabbacin zaka aikata abun da ka faɗa ko ma fiye da shi." Ta faɗa muryarta na cika ɗakin.
"Idan har ka min haka zan rayu ina maka addu'a da sanya ma albarka har tsawon zamanin da zanyi a duniyata." Ishaƙ ya faɗa yana yalwata fuskarsa da murmushi.
Kai Nabil ya risina ƙasa "Ka fara tun yanzu babban Yayah!" ya faɗa muryarsa da girmamawa.
Dariya sukayi a tare daga nan ya suka ci gaba da tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, kasancewar Khadijatu bata da ƙawaye ita ɗaya take rayuwa sai Aisha, take Amrah tace itama ta koma ɓangaren Amarya, dan haka ta zo kenan sai bayan biki.
Duk kalar hararar da Aabid ya ke mata yi tayi kamar bata san yana yi ba "Haba are ni muje biki, abu saura wata ɗaya kice ba zaki koma ba, ai kya zo mu tafi idan ya rage saura mako ɗaya mu dawo." Aabid ya faɗa yana ƙoƙarin danne zuciyarsa.
Kai ta langare "Haba mana Hubbie kana ganin bata da ƙawaye, ni zan tayata rabon I.V"
Ido ya waro waje kafin yayi magana ta rufe masa baki da hannunta "Dan Allah fa. Kaima sai ka zauna kuyi naku rabon ai kana cikin manyan abokanan ango." Bakinsa ya rufe musamman da yaga Khadijatu na kallonsa, itama tana langare masa kai da kuma gyaɗa mata nata kan, alamun dai roƙo.
"Ai shikenan." Ya faɗa kawai yana kallon Nabil da ke gimtse dariyarsa.
"Adawofa da magana baya, dan bikin ba ɗaya xa'ayi ba. Bari na samu Ammu." Ishaƙ ya faɗa yana bar musu falon da sauri yana haɗawa da gudu.
Kallon Aisha suka yi a tare sai kuma suka kwashe da dariya gaba ɗayansu.
****
Lokacin da Ishaƙ ya je wajen Ammu zama yayi kusa da ita, ya ɗauki hannunta ya haɗa a cikin nasa "Ammu masoyiyah."
Harara ta aika masa tana lumshe idanuwanta "Yau kuma da kalar daɗin bakin da ka zo min da shi kenan?"
"Haba wane ni da miki daɗin baki Ammu masoyiyah."
"Faɗi abun da ke tafe da kai, bana son ƙumbiya-ƙumbiya."
Shafa sumar kansa yayi yana kallon Ammuh ɗin da ta kafe shi da idanuwanta.
"Ammuh dama akan maganar auren Khadijatu ne, inaga me zai hana a haɗa harda namu da Aisha, hakan zai fi sauƙi ai."
Ido ta wara waje kafin ta haɗa da salati "Yaushe kuka zama masoya kai da Aishan da za'a haɗa da aurenku ana maganar wata ɗaya ya rage."
"Wallahi da gaske, ki tambayi Aisha ɗin, ko Baba ai ya san da maganar tun muna ƙauye."
Hannunta ta finceka a cikin nasa "Abun kuma ya koma shashanci, duk tsawon lokacin nan Ado bai min maganar haɗin naku ba sai yanxu kai zaka faɗa min."
Dai-dai lokacin kuma Baban Indo ya shigo ɗakin shi da Imran wanda sun zo akan batun auren Khadijatun ne "Yauwa Alhamdulillah gara da kuka zo, ku tayani jin soki burutsun da yaron nan yake min!"
"Me kuma ya faru ke da mai gidan naki Ammu?" Baban Indo ya faɗa yana zama akan kujerarsa.
Shima Imran zama yayi yaana kallonsu murmushi ɗauke akan fuskarsa "Yo meye bai faru ba. Yanzu kai dama ADO zaka haɗa irin wanan kitimirmira ɗin amma ka kasa shawara da ni?"
Ido ya waro waje "Me na haɗa kuma Ammuh?"
"Auren Indo da Isiyaku, yace tun kuna ƙauye kace ka bashi Indo. Shine yanzu yazo min da batun a haɗa auren nasu da na 'yar uwar tasa."
Kallonsa Baban Indo yayi, yayin da Ishaƙ ya sunkuyar da kansa, ƙasa yana ji inama ƙasa ta buɗe ya nutse a cikinta "Amma kuma ai tun a lokacin yace min baya sonta ba zai iya aurenta ba. Hakan yasa ni har na mata miji dan tuni na karɓi sadakinsa rana ɗaya da na Khadijatu."
Sauƙowa yayi daga kusa da Ammuh ya koma wajen Baba yana riƙe ƙafafuwansa, idanuwansa har sun sauya kala sun koma ja "A'a Baba kada ka min haka! Ban taɓa ce maka bana son Indo ba tun a lokacin da ka buƙaci na aureta, a lokacin dai nasan na faɗa maka ba zan iya sonta da kula da ita ba kamar yanda zan Kula da Khadijatu, ba zan sota kamar yanda zan so Khadijatu ba.
Haka na faɗa ma tun a lokacin, amma tun lokacin dana ganta naga tana son Khadijatu naji duk duniya ba matar da ta dace da ni kamar ita, na ƙi sanar da kai ne saboda a lokacin na raina girmanta, haka kuma ina ƙoƙarin nemawa Khadijatu lafiyarta ne.
Dan Allah Baba kada ka datse igiyar nasararmu ka sanya tazara a tsakaninmu. Duk wanda zaka aurama Aisha ba xai kai ya ni ba, domin nine ɗan uwanta da nafi saninta fiye da wanda zai sota, jini kuma ya tsaga a tsakaninmu, duk daɗin ƙwanƙwi bai kai maƙogwaro ba dan Allah Baba ka maida musu sadakinsu."
Dariya duka suka sa a tare har Ammuh da take ƙarawa da "Jini kuma yafi ruwa kauri ko Ishaƙ?"
"Eh! Ammu ki faɗa masa ya mayar musu da kuɗinsa."
"Koda ace kuɗin sadakin ka ne?" Abbie Imran ya faɗa yana harɗe hannunsa a ƙirjinsa.
Kallon Abbie yayi cikin rashin fahimta "Kamar ya kenan?"
"Yana nufin kuɗin sadakinka ne ya nema maka auren Aisha a wajena, maganar da ta kawo mu nan kenan, amma tunda kace a mayar da kuɗin gasu sai na baku."
Kai Ishaƙ ya girgiza hawaye na zuba yana dariya, rungume Baban Indo yayi "Nagode sosai Baba."
"Au baka kunyar surukin naka ka rungume shi ? Yau naga abun da ya isheni na Luba." Ammu ta faɗa wanda hakan yasa Ishaƙ sakin Baban Indo ya fice ɗakin da gudu.
Anan suka bishi da rakiyar ido suna dariya.
****
Bayan wata ɗaya.
Duk abun da aka sa masa rana to zuwansa ba wahala, musamman a wanan rayuwar da shekaru suke gudu sa'a take hauhawa tana gudu.
Dubbanin mutane daga garurruwa daban-daban, ƙasashe mabanbanta na kusa da na nesa sun zo sun sheda ɗaurin auren Khadijatu Imran Yasir da Nabil Ahmad ANA sai ISHAƘ Imran yasir da Aisha Ado.
Bakunansu ba za su iya fayyace tarin godiyarsu ga ɗaukacin mutanen da suka samu halattar aurensu ba, sai dai mutuntaka da jinjina a garesu na amsa gayyatarsu akan lokaci.
Babu wata sabuwar bidi'a ko gutsuri tsomar da akayita a bikin, wanda tunda ga kan iyayensu har su kansu basu da tsarin gudanar da tafiyar zamani a cikin tafiyar aurensu, basu gayyaci sheɗani a matsayin ɗan rakiyarsu ba, sai karatun da aka sauƙe da kuma walimar da akayi na auren nasu.
Wanan wani tsari ne da bada ƙafa ga mutanen da suka ci buri akan gwangwajewa a auren 'yan boko irin na ahali biyun, musamman Imran da ya yi shura a azamani da tafiyar boko da mutane ke kallonsa dumu-dumu a cikinta.
Bayan gama ko wani abu aka kai Khadijatu gidanta da ke Jahar dutse esitate ɗin su Nabil, gidan da ta samu sauƙa da mutumtawa a cikinsa, suka mayar da ita wani sashi na cikinsu.
Yayin da Ishaƙ suka samu wararen sashi a nasu gidan, sunyi kuka shi da Khadijatu kamar ba za su sake haɗuwa ba, sai dai ya mata alƙawalin zai ke ziyartarta duk makonni biyu a gidanta.
A yayin da Aabid ya ɓoye kansa yake kuka, domin ya san ya rasa Khadijatu rasawa na har Abada. Tun lokacin da mashedin ɗaurin aurensu ya sanar da an ɗaura, ya ji wani maƙoƙon abu ya tsaye masa a wuyansa da kuma ƙirjinsa.
"Inna lillahi wa inna ilahirraji'un" Ya ke ta nanatawa dan ya samu sauƙin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa.
****
Dare ya rabe tsakanin haske zuwa duhu, sai dai wanan daren ya zama farin dare ga ma'auratan da suka cure suka zama abu guda ɗaya.
Kamar yanda Nabil ya ɗauki alƙawalin kula da Khadijatu fiye da rayuwarsa haka ya sadaukar ga gaɓɓan jikinsa ga nata.
Badan shi ya ma Khadijatu aiki ba da babu abun da zai hana ya kirata da sunan budurwa, tana cikin jerin matan da suke da wahalar samu a duniya, waɗanda halittarsu take komawa ta haɗe.
Shi kansa ya sha wahala kafin ya samu hanyar kamar yanda itama tasha wahala, dukkansu sunyi kuka, ita tana kukan wahala shi kuma yana na tausaya mata da soyayyarta da take nunkuwa a zuciyarsa.
Allah ya dubu zuciyarsa, a matsayinsa na kamilin mutumin da ke kare kansa ya bashi kamilalliyar mace, wadda ta tsare kanta da martabarta, yayin da zalincin da aka aikata mata ya zame mata alkhairi a tare da ita.
Lokacin da ya dawo nutsuwarsa ya fahimci ya yi mata aika-aika da yawa, wanda har numfashinta na barazanar ɗaukewa.
Ruɗewa yayi sosai, hakan ya sashi ɗaukanta ya shigar da ita banɗaki, lokacin da ya sata a cikin ruwan zafi saida ta ja zuciya, kana numfashinta ya dawo daga nan ta lumshe idanuwanta hawaye na zuba akan kumatunta.
"Sannu Khadijatu nah! Ba abun fa zai sameki!" Ya faɗa cikin ruɗewa yayin da yake tuhumar kansa a matsayin silar janyo mata wahala. Me yasa bai ƙara haƙuri ya bata damar sabawa da shi ba? Ya manta da wahalar da ta sha a baya? Gani yake ya so kansa da yawa.
A haka yayi mata wanka ya naɗota a cikin tawul ya ɗauko wata riga mai sauƙin nauyi ya sa mata.
Bayan nan ya ɗauki ɗan akwatin taimakon gagauwarsa ya mata allurar rage zugi, da kuma magani.
Wani wawan barci ne ya ɗauketa na take ya sauƙe ajiyar zuciya, sanan ya samu ya shiga wanka shima.
Bayan ya fito ya daɗe ya sake gabatar da sallahr godiya ga Allah a bisa ni'imar da ya masa. Ya daɗe yana musu addu'a tun daga kan iyayensu har zuwa su ɗin.
****
Bayan wata ɗaya.
Kwanakin da suka zo suka wuce sun kasance kwanaki masu tsada masu tsayawa a zuciyar masoya biyun, kulawa da tattalin junansu ya zame musu wata alƙibla a cikin rayuwarsu.
Kamar dai yanda ya faɗama Ishaƙ ya zame ma Khadijatu Madubin dubawarta, wanda duk lokacin da ta ganshi sai murmushi ya suɓuce akan fuskarta.
Duk wanda ya ganta yasan hankalinta a kwance yake, haka ko wata rana sai sunyi waya da Ishaƙ yana tambayarta "me tayi? Me take yi? Ba abun da ya ke damunta dai?" Amsa take bashi da ba komi.
Sai dai kamar yanda ya mata alawali yazo a sati biyu da aurensa yanda yaga hankalinta a kwance da kulawar da Nabil yake bata yasa ya samu gamsuwa. A lokacin kuma ya gabatar masa da karatun shekara ɗaya da Khadijatun xata sake yi, a ƙasar india dan zama cikekkiyar Likita.
Yayi murna sosai, wanda har saida ƙwalla ta taru a idanuwansa, wanan shine burin Khadijatu da ya so cika mata shi.
Sai kuma gashi Nabil ya wanzar da shi "Nagode Nabil." Ya faɗa muryarsa da rawa.
"Haba mana Babban yaya! Wanan burin da nake da shi ne, kamar yanda nake likita zan so ace matata ma likita ce, musamman a fannin mata da suka yi ƙaranci a yanzu."
Kai ya gyaɗa "Kai na musamman ne dole na gode maka."
Daga nan suka rungume junansu. Yayin da Khadijatu take kallonsu tana share hawayen fuskarta.
'Anya a duniya za'a samu yaya kamar nata? Domin shi ba iya yayanta ba ne, Rayuwarsa gaba ɗaya ya bata, ya zama uwa da uba a gareta duk da tana da uba a raye.' Idanuwanta ta lumshe tana share hawayen da ke zuba akan fuskarta.
"Ina sonka sosai Yayanah!" Ta faɗa akan laɓɓanta da sautin da ya tsaya a kunnuwanta.
***
Rayuwar Ishaƙ da Aisha wata rayuwa ce mai abun burgewa, kowa a cikinsu tattalin junansu, yake, kamar dai yanda yace mata zai kula da ita, hakan ce, ko wani motsin da zata yi yana tare da ita, duk lokacin da yake gida tare suke komi, tun daga kan girki, wanke-wanke zuwa shara.
Ya siye zuciyar Aisha da kyautatawarsa, ko wata rana ƙaunarsa na linkuwa a zuciyarta, sai dai ta san ƙaunarta na shiga zuciyarsa ne a duk lokacin da labarinta ya shiga cikin zancen Khadijatu.
Anan zai meƙa mata dukkanin kulawarta, da kuma lokacinta. Aisha tasan a duniya babu abun da Ishaƙ ke so fiye da Khadijatu, hakan yasa ta gyara soyayyarta wajen magantuwa akan duk abun da ya shafi Khadijatun.
Tuni aikinsa na ɓangaren lauya mai zaman kansa, ya fito, Imran ya buɗe masa babban office ɗin da ke ɗauke da sunan aikinsa a matsayinsa na lauyan mata da kuma talakawan da suke da ƙaramin ƙarfi.
Mafi yawan cases ɗin da yafi ɗaga masa hankali shine na fyaɗe, duk lokacin da ya ci karo da irinsa, hankalinsa yana tashi ya dugunzuma, da aljihunsa da lokacinsa yake kashewa har sai yaga ya samarwa da yarinya hakkinta.
****
Legos Nigeria.
Tun bayan Ɗaurin auren Khadijatu da Nabil jikin Aabid ya rikice, duk da cewa yana iya bakin ƙoƙarinsa wajan danne zuciyarsa, amma kunnuwansa ya gaza daina jiyo masa sautin sanarwar auren Khadijatu.
Ji yake kamar zuciyarsa zata yi tsalle ta faso a ƙirjinsa, hankalin Mom da Dad ya tashi ƙwarai, hakan yasa suka kwasheshi zuwa asibiti, wanda sai da suka kai ruwa rana kafin likitocin su dubashi, zuciyarsa ta kumbura da yawa.
Ta kai mataki na kusan ƙarshe tsakanin rayuwa da mutuwa. Amrah tayi kuka kamar ranta zai fice, ta tsinewa Khadijatun da bata da laifi yafi a ƙirga.
Saida ya yi wata ɗaya kwance bai san wake kansa ba, kana ya dawo hayyacinsa, a lokacin Imran da Nabil sun ɗauki alhakin kula da lafiyarsa a hannun sauran likitocin, wanda Dad ya so a fitar da shi waje amma suka ƙi yarda, domin koda an fitar da shi, likitocin ba abun da za su masa, sai abun da Allah ya so akansa.
Addu'a kam sun duƙufa wajen yinta, Dad yayi laushi duk wani aikin da yake na kasuwanci ya jingineshi.
Haka sojojin da ke ƙasan Aabid da manyansa sun zo dubashi, da yawansu sun tausaya masa akan abun da ya sameshi, wasu kuma na tambayar dalilin ciwon nasa.