Showing 81001 words to 84000 words out of 91747 words
samunsa ba.Kin haƙo lu'u-lu'u mafi daraja Ƙawatah!" Aabid ya faɗa yana murmushi da ƙoƙarin danne abun da ke taso masa a zuciya.
"Na sani Aboki! Nasan na samu miji ɗaya da ɗaya na nunawa sa'a, ba kowa Allah ke bawa irin wanan damarba sai wanda ya so. Ko a haka nagode Allah a bisa ni'imarsa gareni, abubuwa da yawa suna da sila da kuma sanadin faruwarsu. Ciki kuwa harda ƙaddarar da ke sabunya farin ciki ya koma baƙin ciki.
Kafin zuwanka gareni kullum rayuwarmu cike take da tambaya da gararin rashin samun madogara, amma a sanadin kuskuren da ka aikata mana sai ya zame mana amsar warwaruwar matsalarmu ciki harda haɗu da ahalinmu da kuma samun abokanan rayuwa na gari a tare damu.
Ta wanan fannin zan maka godiya sosai, duk da zalinci ka aikata mana amma kuma sai muka samu adalci daga Ubangijinmu."
"Tabbas Allah mai rahama ne ga bayinsa. Shi kuma ke tsarawa ko wani mutum rayuwarsa da zai yi. Nagode da yafiyarku gareni, nagode da bani kyautar ahalinki da kikayi." Ya faɗa hawaye na taruwa a idanuwansa.
Zungurarsa Nabil yayi yana murmushi "Na rasa yanda akayi soja ya samu raunin xuciya da kullum idanuwansa basa rabuwa da hawaye."
Murmushi Aabid yayi ya shafa fuskarsa "Daga lokacin da darrusan rayuwa suka zanu a mahangar hankali, sai zuciya ta tsinke da karayar akan dama takan kuskurema wanda ke ganin duniya a tafin hannunsa ta ke." Ya ƙarasa maganar yana kallon tafin hannunsa.
"Kasan ƙanwata na jiranka kuwa? Kullum sai ta tambaye ni ya kake? Muna waya da kai?"
Ido Aabid ya lumshe sanan ya kalli Nabil ɗin yana marairaice fuska "Dan Allah likita ku sallame ni naje naga matata!"
Baki Nabil ya rufe "Ai ba ni na riƙe ka ba, kawai kacema Abbie ya sallameka ka warke."
"Shawara mai kyau! Ƙawata ki karɓo mana sallama mana muje biko."
"Wanan shi yafi komi sauƙi." Ta ƙarasa maganar tana tashi akan ƙafarta.
Bata jima da futaba sai gata ta dawo da Abbie Imran da kati a hannunsa "Ance marar lafiyana ya warke, ya zan tabbatar da warkewar tasa?"
Miƙewa tsaye Aabid yayi ya shiga tsalle da zagaye ɗakin, hakan ba ƙaramin daria ya basu ba. "Tsaya haka nan ba sai ka wahalar da jikinka ba. Ga takardar sallamarka dama yau nake shirin sallamar taka."
Rungume Abbie yayi yana dariya da godiya. Bai tsaya ɓata lokaciba suka haɗa kayansu su Nabil sai tsiya suke masa amma bai kulasu ba.
Daga nan Ishaƙ ya ɗauke su a mota ya kaisu Airport shi da Khadijatu da Nabil sai Aisha da ta musu rakiya.
Suna tsaye har sai da suka ga tashinsu a jirgi kana suka koma gida, cike da kewarsu, dan sun fahimci mutane ne su masu sauƙin kai da kuma iya zama da mutane.
***
Lagos, Nigeria.
Lokacin da suka dawo gida, wanka Aabid yayi yace zai tafi ya gano Amrah idan ta amince ma ya dawo da ita.
Lallashinsa Dad yayi yace ya bari su ƙara hutawa kwana biyu daga bisani kuma sai suje tare har su.
Zuciyarsa bata so ba amma haka ya amince domin ko ba komi yana so ya je yaga halin da Amrah take, tun a asibiti yake ƙoƙarin kiranta amma bata ɗaga kiran nasa ba, ƙarshe ma sai ji yayi an kashe wayar gaba ɗaya.
A daddafe yayi kwana biyun da Dad ya buƙata ranar kuwa tun asuba ya hanasu sakat dole suka tashi suka ɗauki hanyar Jigawa, suka ma dutse tsinkaya.
Tun acan Dad ya kira ƙaninsa da ke can akan ya zo ya ɗauke su a filin jirgi. Jirginsu na sauƙa suka tadda shi har yazo ɗaukansu, kana ganinsu bashi da maraba da Dad sai shekarun da Dad zai nuna masa.
Rungumeshi Aabid yayi yana murmushi, bubbuga bayansa yayi "Ɗana jikinka yayi sanyi da yawa, mai ya faru da kai?" Ya tambaye shi lokacin da ke cikin ruƙonsa.
"Labarin nada tsayi Uncle Aliyu. Sai mun zauna."
"Ina fatan komi ya zama da sauƙi. Ina Amrah naganku iya ku kaɗai? Ba dai ita ɗaya kuka bari acan ba?"
Jan hannunsa Dad yayi "Kai dai har yanzu baka rabu da surutuba Aliyu. Ka bari mu zauna mu gaisa ai."
Kansa ya shafa yana murmushi "Yi haƙuri yaya! Anty barka da hanya." Ya faɗa yana ɗagama Mom hannu.
"Barka dai mai gidan roba." Ta faɗa tana mayar masa da martanin murmushinta.
Daga haka ya buɗe su mota suka shiga ya ja "Ka kaimu estate na Prince ANA."
"Ba gida zamu je ku huta ba Yaya?"
"Eh! Can zamu je bikon surukarka."
Ido Uncle Aliyu ya fiddo waje yana kai kallonsa ga Aabid da ke kusa da shi, sai dai shi ya lumshe nasa idon bai san halin da ake ciki ba "Me ya faru ta bar gidan Yaya?"
"Labarin nada tsayi Aliyu sai mun zauna tukun."
"To Allah ya warware shi."
Basu ɓata lokaci ba suka isa gidan gandu da za'a iya kiransa da unguwa guda, tun daga farkon gidan har zuwa wajensa cike yake da ma'aikatan tsaro wanda sun haɗa da sojoji da kuma 'yan sanda.
Aabid ne ya ɗauko musu katinsa sanan suka shiga buɗe masa suna sara masa har sai da suka wuce get na huɗu sanan suka iso ainihin inda zai sadasu da ɓangaran da ke a matsayin na su Amrah.
Waya Dad ya ɗauko ya shiga dannawa a kunnensa yana jin sanda aka ɗauki wayar ba tare da anyi magana ba, Murmushi yayi a zuciyarsa dan ya daɗe da sanin halin mutumin nasa "Allah ya taimaki Yarima, gamu a harabar gidan naka."
Kashe wayar yayi ba tare da yayi magana ba, bayan mintuna biyu sai ga wani ma'aikaci ya zo ya musu jagora har zuwa ainihin falon da zai sadasu da cikin gida.
Suna zama sai ga ma'aikatan da ke kula da shiga da ficen baƙin gidan, sun cika musu gabansu da kayan ciye-ciye da na shaye-shaye.
Sai da suka gama sanan suka zo suka kwashe kayan.
"Har yanzu dai ba abun da ya sauya daga ɗabi'un ANA suna nan a yanda suke." Mom ta faɗa tana goge bakinta.
"Aifa ba'a sauyawa tuwo suna madam."
Dai-dai lokacin suka jiyo ƙamshin turare na doso su, hakan ya basu tabbacin shine ya ke tahowa.
Yana sanye cikin dakyakkiyar shaddar gizna mai kalar siminta, sai baƙin agogon da ke saƙale a hannunsa da kuma baƙin takalmi mai saƙalalliyar maɗauka, kansa sanye da baƙar hula.
Duk da shekarunsa sun tura amma hakan bai hana kyansa futowa ba, fuskarsa zagaye da gashi da suka haɗa baƙi da ratsin fari wanda sai ka ƙura ido sanan zaka ganta.
Yana ƙarasowa suka miƙe tsaye, hannunsa ya miƙa musu fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Sai da suka gama gaisawa sanaan ya musu nuni da kujera alamun su zauna.
Zama sukayi kana shima ya zauna ya ɗora ƙafarsa ɗaya kaan ɗaya "Me ke tafe da ku?" Ya tambayesu kamar baya son magana.
Shuru sukayi aka rasa mai jarumtar magana a cikinsu saboda yanda ya cika musu ido da kwarjininsa, ƙarin daɗawa kuma ɗaurarriyar fuskarsa da take ɗauke da rashin walwala.
🌷🌷🌷🌷
Good morning
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG...
5600000
Kallonsu yayi yaga yanayinsu duk ba daɗi, sai kuma ya ɗan sassauta fuskarsa "Ku nake sauraro Yallaɓai!" Ya faɗa yana aika murmushi ga Dad.
Kansa Dad ya shafa yana jin nauyin abun da zai futo a bakinsu "Mun zo dubaku ne da kuma bada haƙuri akan abun da ya faru, wanda har Amrah ta taho ba tare da izinin mijinta ba."
Kallonsu yayi da mamaki yana buɗe bakinsa "Kuna so kuce min Amrah yaji ta yi mijinta bai san da zuwanta ba?"
Kai suka gyaɗa a tare kamar ƙadangaru, take zuciyarsa ta hautsine ta fara tafasa, wayar da ke hannunsa ya shiga dannawa kana ya karata akan kunnensa "Ku zo babban falo yanzu ke da Amrah." Ya faɗa cikin muryarsa mai amo.
Ba'a ɗauki lokaci ba sai gasu sun sauƙo ita da mahaifiyarta, dukansu suna sanye da hijabi a jikinsu.
Da sallama a bakinsu suka shigo palon su Dad suka amsa, zama Mahaifiyar Amrah tayi a kusa da mijinta yayin da Amrah ke zaune a ƙasa kanta a sunkuye tun bayan haɗuwar idanuwanta da mutanen da suke falon.
Zuciyarta na bugawa kamar zata yi tsallen kura ta faɗo a kan ƙirjinya.
"Sannunku da zuwa Hajiya Zahra. Ashe kune a gidan namu amma ban da labarin zuwan naku?" Mahaifiyar Amrah ta faɗa fuskarta cike da fara'a.
"Wallahi fa mune Hajiya Jiddah! Duk da ba mu daɗe da zuwaba mu ɗinma."
"Masha Allah! Ya kuke ya gajiyar hanya? Irin wanan doguwar tafiyar ya kamata kuna sanar da mu zuwanku kafin ku ƙaraso, dan a tanada muku sauƙa ta musamman. Ai yanzu an zama ɗaya."
"Alhamdulillah! Wallahi a hakanma mun gode Hjy Jiddah. Muma zuwan namu ba na lafiya ba ne mun biyo sawun ɗiyarmu ne, shi yasa ba mu sanar da ku zuwan namu ba."
"Toh ikon Allah! Ai mu cewa tayi wata guda ta zo mana hutu, saboda Aabid ba ya gari.
Dama ba da gaske ba ne Amrah?"
Jikinta ne ya jiƙe da gumi sharkaf yayin da ko ina a jikinta ya shiga rawa, cikin abun da bai gaza mintuna biyu ba hawaye ya fara ambaliya akan kyakkyawar fuskarta.
"Ba ke ake tambaya ba?" Prince ANA ya faɗa mata cikin tsawa.
Kai ta girgiza hawaye na sauƙa akan fuskarta "Ni bana son sa ne Abbu! Ba zan iya sake zaman aure da shi ba!" Ta faɗa muryarta na rawa kamar ana ƙwato maganar a bakinta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil! Me nake ji haka ni Jiddah?" Umminta ta faɗa cikin salati da mamakin maganar tata.
Yayin da Ana ya kwantar da kansa a jikin kujera kamar ba zai yi magana ba "Tashi ki haɗa kayanki kibi mijinki." Ya faɗa idanuwansa a lumshe kamar ba zai buɗe su ba.
"Abbu bana sonsa wallahi! Idan na koma mutuwa xanyi nima kamar yanda Nuriee ta mutu. Bazan iya zama da azzalumi kamarsa ba Abbu!" Ta faɗa tana jan hanci kamar zata cireshi daga maliƙarsa.
Idonsa ya buɗe ya kalleta sanan ya kalli Aabid da ya sunkuyar da kansa hawaye na zuba akan fuskarsa.
"Me ya faru Aabidullah?"
Kansa ya girgiza ba tare da ya ɗago da shi sama ba.
"Ni nasan na aikata kuskuren da bazan iya kankare shi a rayuwata ba. Amma Allah ya sani ba da son raina na aikata shi ba.
Tabbas ni azzalumi ne da bai cancanci a zauna da ni ba. Abbu ina son Amrah sosai, wallahi ba da son raina na aikata ba asalima bani cikin nutsuwata sanda na ma yarinyar fya..."
"Aabid!!" Amrah ta faɗa da ƙarfi cikin tsawa wanda sai da ya tsorata yayi shuru. su kansu mutanen ɗakin saida suka juyo suna kallonta.
"Wa ya tambayeka akan wanan matsalar da zaka faɗa? Shin kai baka iya ɓoye sirrinka ne a rayuwa? duk inda kaje sai kayi magana akansa."
Kai ya girgiza hawaye na daɗa ƙaruwa a idonka "To ai tambayata yayi Amrah! Gara shima na faɗa musu gaskiya wata ƙila su mana shari'ar da zata xama adalci akanmu."
"To ba'a so! Ka ƙyale gaskiyarka."
Dariya ce ta kama Jiddah ta toshe bakinta tana kallon Ana da shima yake murmushin gefen baki "Malam Aabid matarka bata so ka bayyana sirrinka sai ka yi shuru kawai.
Ke kuma tunda haka ne ki tashi ki haɗa kayanki ki bisu ku bar min gidana ku je can ku ƙarata."
Tashi tayi ta makawa Aabid ɗin harara "Ai gara mu tafi da dai wanan abun kunyar da zaka janyo mana." Ta faɗa tana gunguni wanda hakan yasa su dariya idan aka ɗauke ANA da shi dama ba dariya ce ta dame shi ba.
"Dan Allah ku yi haƙuri, wallahi banda masaniya akan yaji ta iyo da tun ranar na korata ta koma." Ana ya faɗa cikin sanyin muryarsa.
"Ba komi wallahi mun gode sosai da karamcinku."
Daga nana suka cin gaba da hirarsu cikin farin ciki da mutunta juna, ana haka sai ga Amrah ta fito janye da jaka tana cika tana batsewa bata yima kowa magana ba ta shige su, da sauri Aabid ya tashi ya amshi jakarta duk da fuzgewar da take amma bai haqura ba haka ya ci gaba da janta har ta sakar masa.
Har ta je zata ja ƙofar ta fita sai ta juyo "Kuma ba zaku min sallama ba haka zan tafi."Ta faɗa cikin shagwaɓa kamar zata yi kuka.
Baki Ana ya taɓe "Mun ga kamar zaki tada gari ina zamu miki magana ki haɗa da mu."
Idonta ne yayi raurau kamar zata yi kuka, hannunta ya wara mata yana murmushi, da gudu ta dawo palon ta rungume shi sai kuka, bayanta ya ke bubbugawa yana murmushi "Yi shuru 'Yar baba muma zamu kawo miki ziyara kamar yanda kika kawo mana, ba mu kaɗai ba harda su Antynki ma."
"Da gaske Abbu?"
"Da gasken gaske, amma sai kin daina yin yaji a gidanki."
"Ai ban taɓa yiba Abbu! Yanzuma hutu na kawo muku fa."
"To shikenan zaki ganmu in sha Allah ƙanwata."
"Nagode Abbu. Ina sonka Babana."
"Nima ina sonki 'yatah."
"Ni kuma da ba'a so sai a kashe ni ai." Jidda ta faɗa tana yamutsa fuskarta.
Sakin Abbu Amrah tayi sanan ta rungume Jiddah "Uwa mafi uba koda uban sarki ne Ummi! Amma ni nawa uban farin wata ne da ke cika duniyata da haske.
Ina sonki Ummi. Ki daɗe kiyi ƙarko kamar bishiyar dabino."
Ta faɗa tana sakinta sanan ta zo kusa da Abbu ta yi masa raɗa "Har yanzu Ummi na kishinka Abbu.
"Dama romon baka kika min yanzu Amrah?" Jiddah ta faɗa tana wara idonsa.
Dariya Amrah ta fuce da sauri tana ɗaga musu hannu. Yayin da suka bita da dariya suma.
Su Dad na tashi suna musu sallama.
Bayansu su Jiddah suka biyo sai da suka ga tafiyarsu sanan suka koma gida cike da kewar Amrahn su.
Daga nan gidan Uncle Aliyu suka wuce sosai matarsa ta karɓe su hannu bibiyu, ita da yarnt suna da kirki sosai.
Kwana biyu suka musu sanan suka dawo gida legos har a wanan lokacin magana bata shiga tsakanin Amrah da Aabid ba, duk da ƙoƙarin da yake wajen son ganin ya shawo kanta.
"Amrah na gaji da horon da kike min! Na gaji da shuru ɗin da kike min, ni wallahi gara ma kiyi ta zagina da ace kina min wanan shurun."
Ɗago kanta tayi daga kallon littafin da ke hannunta, ta kalli Aabid ɗin sanan ta mayar da kanta akan littafinta.
Zuciyarsa ce ta motsa sosai har yaji kamar yayi ta dukan Amrah ko ya samu ya huce raɗaɗin da yake ji, sai dai a yanzu jinta yake kamar rayuwarsa ko da wasa hannunsa ba zai iya taɓa lafiyar jikinta ba.
"Me yasa kika ƙi bari na sanar da su Abbu laifin da na aikata miki idan har ba ki yafe min ba? Me yasa Amrah kike hukunta ni da shurunki? Me ne laifina dan Allah ya jarrabe ni da aikata kuskure a rayuwata?"
Ajiya littafin ta yi ta tashi tsaye tana kallon Aabid sama da ƙasa, a hankali ta rufe idonta kana ta buɗe su a kansa "Da ace na bari ka faɗama Abbu abun da ka aikata da ya kasheka Aabid! Da ace na bari bakinka yayi kuskuren faɗar kalmar da zai shekara dubu yana zargin kansa bisa aura min kai da yayi.
Mahaifina yana sona fiye da rayuwarsa, yana girmama abun da ke gareni koda ace bai da kyau Aabid. Ka san komi da ke gareni ba sai na baka labari akan wacece ni ba.
Tunani nake akan wata kalmace zan yi amfani da ita wajen yi maka magana Aabid, bayan da saninka ka aikata kuskure amma ka kasa waiwayarsa har sai da ya faru da kai. Duk da haka ka gaza wanke dattin da ke tare da kai.
Ko baka faɗa min ba na samu labarin Khadijatu ta yafe maka Aabid! Amma kuma ya kamata ka nemi yafiyar Allah ka je a share maka dattin da ke jikinka ta hanyar kai kanka kotun musulunci dan a maka hukunci dai-dai da laifinka.
Anan zan gamsu kayi tuba na gaske!Anan zan yarda cewa Allah ba zai sake jarrabata da wani abu makamanci wanda ya faru da Nurrie ba. Zan ci gaba da mu'amula da kai kamar ba abun da ya faru da kai."
Baka da laifi saboda ko wani mutun baya kuskurewa jarrabawar Ubangijinsa, sai dai idan abu ya haɗu da hakki Allah ba ya yafe shi Aabid.
Ina sonka ba shi zai baka damar yin kuskure na ci gaba da zama da kai gaba kaɗi ba."
Tana gama faɗar haka ta fuce ta barshi a ɗakin, shiru yayi ya dafe kansa da hannayensa yana jin sauƙar hawaye na zuba akan fuskarsa.
Shi dai kam bai san yaushe zai daina hawaye a rayuwarsa ba? Amrah ta faɗa masa gaskiya, duk da Khadijatu ta yafe masa yana buƙatar kwanciyar hankali a zuciyarsa.
🌷🌷🌷🌷
ANYA AMRAH BATA WUCE GONA DA IRI BA? INA RUWANTA DA SHIGA HURUMIN DA BA NATA BA?
KU santa MAMANA a addu'arku bata da lafiya tana fama da ciwon ciki, wanan dalilin yasa aka samu tsaiko a rubutuna.[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG.......
570000
Washe gari sassafe ya fice a gidan bai yima kowa sallama ba, kai tsaye babbar kotun shari'ar musulunci ya wuce ya samu alƙalin da ke zaune a wajen.
Bayan sun gaisa ya sanar da shi ƙara ya kawo.
"Ƙaran wa ka kawo yaro?"
"Ƙaran kaina na kawo yallaɓai. Na aikatawa yarinya fyaɗe shine nake so a min hukunci dai-dai da abun da shari'a ta tanadar da shi."
Gilashin idonsa alƙalin ya zare ya kalli ma'ajinsa da ke kusa da shi da shima ya buɗe bakinsa "Yaro kasan abun da kake faɗa kuwa?"