Showing 24001 words to 27000 words out of 91747 words
da ɗan ƙarfi wanda ya sata sakin ƙara "Auwchh!" Ta faɗa tana murza kan hancin nata.
Murmushin gefen baki yayi yana goge mata hawayen kan fuskarta "Kin yarda ba mafarki kike ba yanzu?"
Kai ta gyaɗa masa tana murmushi da sunkuyar da kai "Idan kin huce ki shirya anjima zan zo na ɗaukeki mu koma.
Ki ƙara da musu sallama dan KANO zan koma da aiki."
Ɗago kai tayi tana kallonsa da son yin tambaya, kai ya girgiza mata yana sumbatar kumatunta "Kada kice komi, sai na zo."
Baki ta saki tana kallonsa har ya fice a ɗakin, tana ji kamar an dasa ta ne a wajen, wai da gaske wanan Imran ɗinta ne? Da gaske Imran Yasir Nasar ne wanan?
"Ya ALLah!" Ta faɗa tana faɗawa kan kujera da bubbugata tana jin wani farin ciki na cika zuciyarta.
🌷🌷🌷🌷🌷
Karku manta Book ɗin nan na kuɗi ne Idan ta Bank ne #200
Idan kuma katin waya ne 300
Zaku iya biya ta nan,
Acct: 0472282105
Ramlat Abdul Rahman Manga
GT BANK
A yi screen short ɗinsa a turo ta wanan no 08030990232
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
Oum-Nass
0017
Kano, Nigeria.
"Yaro wani asibiti zaku?"
"Malam Aminu Kano." Ishaƙ ya faɗa yana maida numfashi a hankali.
Gyaɗa kai Baban Indo yayi daga nan suka nufi hanyar asibitin Malam Aminu Kano, sai da suka sha wahala kasancewar cunkoson mutanen da suka yi yawa a asibitin, zuwa lokacin Khadijatu ta gaji, ta yi barci ya kai sau uku tana tashi, kanta har juyawa yake saboda tafiyar ta sha.
Har cikin harabar asibitin ya kaisu ya sauƙar da su, kuɗin hannunsa duka Ishaƙ ya miƙa masa wanda za su kai Dubu dubu biyar ɗin "Baba gashi kayi haƙuri iya abun da yayi mana saura kenan."
Amsar kuɗin yayi yana juyawa, sanan ya ruƙo hannunsu "Kuzo mu je shiga cikin asibitin." Binsa suka shiga yi, sai da ya musu cuku-cukun karɓan kati da fayil na asibitin, duk da tarin layin da ya samu amma ya roƙi alfarma a wajensu akan su barshi ya amsa, da yawan marasa lafiyan sun tausayama Khadijatu, ganin yanda ta takure waje ɗaya tana cusa kanta a ƙirjinta, daga nesan da take suna juyo zarnin da ke bugosu na jikinta.
Matan da ke wajan sun tausaya mata yayin da wasu suke son sanin abun da ya faru da ita.
Haka dai Baban Indo ya karɓi fayil ɗin ya kamo hannun Khadijatun da take tirjiya tana jin tsoron hannunta da ta ga a jikin nasa yana Ja. Kamarsa ta ga tana sauyawa a idanuwanta yana komawa zuwa ta baƙar damisar da ke farautar rayuwarta.
Hannunta ta fuzge tana ƙwalla ƙara wanda hakan ya ja hankalin mutane da yawa zuwa wajensu.
"Ka sake ni! Ka sakar min hannu!" Ta faɗa jikinsa na ƙara ɓari da rawa, tana ji zuciyarta kamar ta yi tsalle ta faɗo a kan ƙirjinsa.
"Ikon Allah!" Baban Indo ya faɗa cike da mamaki da al'ajabin abun da ta masa.
"Khadijatu me ya faru?" Ishaƙ ya faɗa yana rungumeta akan jikinsa, hannu ta ɗaga tana nuna masa Baban Indon wanda shima yake kallonta da mamaki.
"Ya daina riƙe min hannu! Bana so!" Ta faɗa cikin rawar murya.
"Daga taimako yarinya sai muguwar sakayya." Baban Indo ya faɗa yana kallon mutanen da suka fara matsowa suna kallonsu.
"Kayi haƙuri Baba, tana fama da furgicu ne, da yawan tsoro, dan Allah kada ka sauya kyakkyawar niyarka ta alkhairi."
Kai ya girgiza cikin tausayawa "Allah ya bata lafiy, kai ruƙo hannun nata ka zo mu tafi."
Hannayenta ya ruƙo suka biyo baya Baban Indo ɗin, anan suka tadda layi mai yawa a wajen babban Likitan.
Risinawa Baban Indo yayi ya gaida su, anan ya roƙi alfarma a wajensu a matsayinsu na matafiya.
Kai suka girgiza mafiya yawansu kuma suna rurrufe hancinsu "Mu ma ba zuwa mukayi fan mu kwana a nan ba. Kowa yana da nasa uzurin ya taho ya barshi." Wata kakkaurar mata mai baƙar fuska ta faɗa.
"Haka ne." Baban Indo ya faɗa yana komawa baya da tambayar wanda ke a matsayin mutum na ƙarshe.
Wasu kuma a ciki sun tausaya musu musamman ganin yanda suke a matse da yawa, ga Khadijatun da take ta rarraɓewa a jikin Ishaƙ "Baba Zo ku shiga a layina."
Wata matashiyar budurwa ta faɗa wanda da alama itace ta farkon shiga idan na ciki ya futo.
Juyawa sukayi suna kallonta cikin mamaki "To uwar kinibibi kin dai san idan kika basu layinki sai dai ki koma baya ki sake sabon jiran."
"Eh abun da zanyi kenan, ai layina ne!" Yarinyar ta faɗa tana tashi daga wajen.
Godiya sosai ya shiga mata sai dai kafin su zauna matar ta ƙara magana "Amma dai ba so kake kace itace zata zauna akan banci da wannan ruɓoɓɓun kayan da suke tashin zarni ba?"
"Sai ta tsaya idan an kira na gaba ta shiga." Ya basu amsa yana ji kamar ya bubbuge mutanen, haushi da takaicinsu duk ya cika zuciyarsu.
Anan dai mutane da yawa suka shiga yin magana suna ƙara aibata yarinyar da ta ba su nasu layin ƙarshe dai shuru sukayi suka ƙyalesu har aka kira layinsu suka shiga.
Mutumin da suka ga ya fuskancesu a matsayin Likitan shi ya daki zuciyarsu, hakan ya sasu kasa ƙarasa shiga cikin ofishin nasa.
🌷🌷🌷
KUyi maleji plss Yau ina da marar lafiya ne, zanje dubiya. Ngd sosai.IG
Oum-Nass
0018
Kallonsa suja ƙarayi suna son tantance kamanninsa da suke gani, baiyi kala da mutanen da suka saba gani ba, asalima kamanninsa bai yi musu kama da ɗan ƙasarsu ba.
"Baba wanan mutumin ne zai duba Khadijatu nah?"
"Mu ƙarasa mana Ishaƙ." Ya faɗa cikin bagarar da tunanin da Ishaƙ yake son yi.
Itama Khadijatun riƙeshi tayi gama kamar ba zata ƙarasa wajenba. Kallonsu Likitan yayi yana kallon jikinsa da yaga suna tsoron matsowa kusa da shi.
Kai ya girgiza saboda fahimtar abun da suke jin tsoro a jikinsa, bai wuce launin fatarsa ta fari kar da yake da shiba, yayin da suka zama mutanen ƙauye masu gajeran yawo.
"Ku zauna mana Baba!" Ya faɗa da hausarsa da bata gama fita sosai ba.
Maganar da yayi da kuma fuskarsa da ya saki itace ta sa ma su Ishaƙ kwanciyar hankali suka ƙaraso kusa da shi.
"Me ke tafe da ku?"
Khadijatu Baban Indo ya nuna masa da hannu "Yarinyata ce bata da lafiya, shine daga can garinmu aka turota nan."
Kallonta yayi cikin nazarin abun da ke damunta, sai dai bai samu damar ganin fuskartaba saboda har lokacin kanta na duƙunƙune da rigar ishaƙ, abun da kawai ya iya ganewa yanda jikinta yake jiƙe da kuma ɗigar da ruwan da take ta famanyi a waje da take tsayen.
"Me ke damunta aka turoku nan?" Takardar asibitin da Likita ya basu a malam madori ya miƙa masa.
Karɓa yayi ya fara karantawa cikin sanyin jiki ya kalli Khadijatu da take jikin Ishaƙ har lokacin.
"Yoyon futsari ke damunta?" Ya sake tambayarsu dan ya tabbatar da abun da takardar ta ƙunsa.
"Eh Likita!" Baban Indo ya amsa masa.
Kai ya gyaɗa yana sake kallonsu "Zamu baku gado na zaman jinyarta, za kuma akaita sashe na musamman da za'a bata kulawar da ake bama masu laruri irinta ta. Akwai maganunnuwa da kayan aiki na yau da kullum kasancewar larurarta tana buƙatar linkuwar tsafta da kuma kula akai-akai."
Murmushi Ishaƙ yayi yana shafa kan Khadijatu yana jin farin ciki na shiga zuciyarsa kamar ance masa ta gama samun lafiya ne ta warke.
"Mun gode Likita Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Zan rubuta muku adadin abun da muke amfani da su da matakin larurarta, sai kuje ku biya kuɗaɗensu."
"Kamar nawa ne kuɗin da za'a biya Likita?" Baban Indo ya tambaya a zuciyarsa kuma yana addu'ar Allah yasa kuɗaɗen ba su da yawa.
"Eh to! Da yake dai ba ɓangarena ba ne, sai dai na muku hasashen yawansu. Wanda a ƙiyasina ba zasu wuce Naira dubu ɗari uku ba (#300,000)."
Ido Ishaƙ ya buɗe waje yana dafe ƙirjinsa "Dubu ɗari uku kace likita?"
"Eh a hakanma ƙiyasi na yi, ta iyu ya fi haka ko kuma ƙasa da hakan ya dai danganta da hawan ababen amfanin ko kuma sauƙarsu."
"Ya Allah! Ina zan samu wanan kuɗin? Ni da ko dubu goma ban da ita ta kaina." Ishaƙ ya faɗa idanuwansa na kawo hawaye, yana ƙara rungume Khadijatu, duk wata murna da yake yi a yanzu ta koma ciki.
'Anya kuwa suna da sauran wani farin ciki da za suyi ƙiyasinsa a gaba a wanan duniyar? Gaskiya babu!' Ishaƙ ya faɗa yana share hawayen da ke sauƙa akan fuskarsa.
Tausayinsa ne ya kama Baban Indo ya kalli Likitan "Likita ba zamu iya samun sauƙi akan wanan kuɗin da ka faɗa ba?"
Kai Likitan ya girgiza "Gaskiya babu wani sauƙi akan hakan, a hakama gobnati ta ɗauki nauyin wasu abubuwan na larurar tata, inda ace gaba ɗaya akace ku biya to da abun ya munana, da lissafin ya hauhawa."
Shuru ɗakin yayi babu wanda ya ƙara magana a cikinsu, sai can Ishaƙ ya buɗe bakinsa cikin sanyin murya "Likita yanzu dole sai mun bada kuɗin sanan za'a fara duba Khadijatu?"
Kai ya gyaɗa cikin bashi tabbacin tambayarsa "Haka tsarin namu ya ke."
Hannun Khadijatu ya riƙo sanan ya kalli Baban Indo "Zo mu tafi Baba."
"Ina za muje Yaro? Ka tsaya ko da wani hanyar da za'a iya bi a samu alfarma a bata koda magani ne da zai rage zubarsa."
"Baba a ina ne zamu nemi wanan alfarmar? Mutumin da ke gabanka mai jan kunne ko kuma duka mutanen asibitin da ma'aikatansu? Ta ina zan iya ƙara neman alfarma a wajen mutum bayan izayar da duk wani mai dama ke lanƙaya mana.
Duka rayuwarmu tafe take cikin tambaya da lalime amma a haka babu abun da ya sa mutum tausaya mana, sai da ya bamu damar kore wancan lalimen muka koma dudduƙe. Zuciyata ta riga data bushe da tsoron da yarda akan neman alfarma daga ko wani ɗan Adam."
Daga wanan ranar zanyi fafutuka da dukkanin ƙarfina, zan nemi halak da gumina! Zan yi kutse a cikin ɗan abun da ya rage min. Idan har muna da sauran rayuwa, da rabo na tabbata Allah ba zai wofintar da mu ba, zai dubi lamarinmu ya isar mana akan muradanmu da kuma mafarkinmu."
Yana gama faɗar haka ya ja hannun Khadijatu yana ɗaukan fayil ɗinsu daga wajen Likitan, da ya kasa magana sai binsa yake da kallo baki buɗe.
"Idan har gwabnati ta gaza wajen ɗaukewa talaka sauƙin kuɗin larurasa to ba amfanin a kira hakan da sunan sauƙi."
Futa sukayi dukkaninsu, shi kansa Baban Indo biyo bayansa yayi ba tare da ya samu damar yin magana ba.
A yanzu ya ji tsanar kansa da bai dage ya nemi kuɗi da guminsa ba, sai yanzu yake ganin amfanin kuɗi ba wai ka samu ka ci abinci ba ne, harda tanadi saboda larura. Kafin yau ya meƙe ƙafa idan suka ci suka ƙoshi bai tunanin adana wani sabon kuɗin, ashe akwai ranar da suka fi ci ma amfani, gashi a yau yama manta da batu akan ciki da sha.
"Yaro yanzu ina zaka je? Ta ina zaka fara neman aiki da samun kuɗin da zaka biya na jinyar Khadijatu?"
Hannu ya wara yana watsashi a fili "Ban sani ba nima Baba! Amma nasan duniya da faɗi take, kamar yanda mutanen cikinta suke da yawa. Ina da yaƙini a raina zan samu wani sana'ar da zan ware na yi aiki da ƙarfina har na tara kuɗin jinyar Khadijatu!"
"Kenan zaka sake neman wata alfarmar a wajen wasu mutanen daban?"
Kallonsa yayi cikin rashin fahimtar maganar a yayi "Kamar me kenan Baba?"
"Abun da ka ƙi na neman alfarma a wajen wasu mutane shine kake ƙoƙarin yi a yanzu! Idan har idanuwanka basu buɗeba to zai zamana kana wahala ne wasu na jin daɗi."
Kansa ya dafe da ɗaya hannun nasa, yana kallon Khadijatu da ƙafarta ke rawa alamun ta gaji da tsayuwar "Ya Allah!" Ya faɗa yana sosa kansa da hannunsa.
Dafa shi Baban Indo yayi cikin sanyin murya ya ci gaba da magana "Idan har zaka iya zan baka gonata kayi noma tuƙuru da ƙarfinka, zan kuma ɗauki nauyin ara maka wasu 'yan kuɗin da zaka yi aikin da su wajen siyan taki. Zaka dawo garinmu da zama, a cikin wanan ɗan lokacin zaka kular min da kiwon dabbobina ba zan baka koda ƙwandala bane a matsayin kuɗin kiwonka.
Zan baku ɓangare guda mai ɗaki biyu kai da ƙanwarka ku zauna, zan ciyar da kai da ƙanwarka, zan kuma ɗauki nauyin duk wasu buƙatar ku idan har ta taso.
Sai dai zan maka wanan ne a bisa sharaɗi guda ɗaya tak!"
Ido Ishaƙ ya buɗe yana kallon Baban Indon da yake jin maganarsa na ratsa zuciyarsa "Wani sharaɗi ne BABA?"
"Sharaɗi akan zaka Auri 'yata INDO! Zaka zauna da ita a matsayin matar da kake so, zaka kular min da ita fiye da yanda nake kula da ita. Zaka bata soyayya da kulawa kwatankwacin yanda kake nunama ƙanwarka."
Kallon Baban Indo yayi yana kallon Jikinsa da kuma ƙarantar shekarusa, shi duka nawama ya ke? Ta ina zai iya haɗa soyayyar wata da Khadijatunsa? Wanan yasasshen zance ne da kunnuwa kaɗai za su iya jinsa amma ba dan su gaskata shi ba.
Kai ya girgiza cikin sanyin murya yana kallon Baban Indo "Ba zan iya ba! Ba zan iya son wata da bata kulawar Khadijatu ba! Ba zan samu lokacin tunanin wata da sauƙe nauyinta akaina ba idan ba Khadijatu ba! Nifa ina rayuwana da ƙarfafa zuciyata saboda Khadijatu.
Kayi haƙuri idan na ci maka fuska, amma idan har na raba zuciyata biyu wajen kula da mutane biyu ta ina zan maida hankali wajen neman kuɗin maganin Khadijatu? Iya abun da ka min nagode, amma ban shirya ɗaukan wata kasadarba a yanzu."
Yana gama faɗar haka ya juya yana riƙe da hannun Khadijatu, bai san kuma ina rayuwa zata sake jefa su ba, bai san ina zai je ya fara lalimen kuɗaɗen da zai zama tsanin warakar Khadijatu ba.
"Ishaƙ!" Tsayawa yayi ya juya yana kallon Baban Indo da yake matsowa kusa da shi.
Kuɗin da ya bashi dubu biyar ya miƙa masa "A matsayina na uba ba zan iya bari wani ya sha wahala a rayuwa ba.
Zan baka gona kayi noma iya son ranka har sai kace baka so. Zan baka aron kuɗin da zaka yi noman a madadin kyautarsa da zan baka idan ka auri Indo. Ba zan iya barinku ku tafi ku kaɗai ba a gari mai girma irin wanan, a garin da babu wanda ya damu da rayuwar wani. Ɗa na kowa ne, na tabbata Allah zai dubi nawa yaran nima."
Da mamaki yake kallon Baban Indo! Wani irin uba ne wanan? Wata zuciya gareshi wanan mutumin? A gabansa nace ba zan so ɗiyarsa ba, amma duk da haka ya dawo min da kyautatawa a madadin ƙuncin da na cusama ruhinsa.
Ya Allah!"
Risinawa yayi ƙasa zai masa godiya, ya tada shi.
"Kada ka damu daga yanzu kuna a matsayin yarana ne kuma. Allah bai bani haihuwa mai yawa ba, da ya tashi bani kuma sai ya bani ita a girman kai. yanzu kuma da na sameku sai naji Allah ya ƙara bani wata kyautar ne. Ta ina zan butulce masa na ƙyaleku ku tafi?"
Kamo Hannun Khadijatu ya yi suka shiga mota daga nan suka bar garin KANO suka ɗauki hanyar MALAM MADORI.
🌷🌷🌷🌷🌷
Afwan kuyi haƙuri yau ban baku akan lokaci ba, abubuwa sun sha kaina, gashi kuma na yini da ciwon kai. Kuyi malej in sha Allah zaku samu gobe da safe.
Ku yi haƙuri da erros dan bana samun damar yin editing.
Girmamawa.[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
Oum-Nass
0019
Kaduna, Nigeria.
"Abba ni na haƙura zan koma gidan Imran."
A hankali ya ɗago kansa ya kalleta cikin son gaskata abun da kunnuwansa suka jiye masa.
"Kika ce zaki koma gidan Imrana Fatima?"
Kai ta gyaɗa masa cikin bashi tabbacin maganarsa "Eh Abba zan koma. Na haƙura da duk abun da ya faru a tsakaninmu a baya."
Bakinta taji an gwaɓe mata wanda ya sata saurin ruƙe bakin tana kiran "Auwchh!" Saboda zafin da taji tana dubawa taga jini ya biyo hannunta.
"Amma bansan ke shasha bace sai yau Fatima! Ban san cewar baki da tunani da lissafi ba sai yau! Duk wulaƙanci da tozarcin da Imrana ya miki shine kike kallon tsabar ƙwayar idanuwan mahaifinki kice zaki koma gidansa, ba tare da kin tsaya kin yi shawara da ni ba.
Har a ɗan lokacin da ya zo ya ɓata ya ƙara siye miki zuciyarki da turɓunenniyar fuskarsa. Wallahi ke dai Fatima baki da zuciya! Ko kaɗan baki san ciwon kanki da 'yancinki ba."
Kuka ne ya ƙwacema Fatima tana girgiza kai saboda jin kalaman Mahaifiyarta a gareta "Mama kiyi haƙuru dan Allah, kada ki ga laifina akan maganar komawa gidan Imran. Mama idan har nace zan rabu da Imran bani da tabbacin mijin da zan aura a gaba yana da wararren halin mai kyau.
Gara na zauna da wanda na saba, ina sa rai akan zai gyara halayyarsa, na yi haƙurin shekaru goma a baya ki barni na ƙarasa aikin ladana Mama. Dan Allah kada ki yanke min