Showing 12001 words to 15000 words out of 91747 words
sanin ma'anar tambayar tasa, duk abun da zai fito a bakinsa na ya tunanin zai kasance alkhairi ne.
"Gani Babba!"
"Kace Khadijatu an sallameta zaku koma asibitin Har kano?"
"Eh Babba!"
Kai ya gyaɗa yana ƙara kallonsa "To shi asibitin nan me ye amfaninsa kenan? Ko kuwa so kake kace min duk girman garin nan da jahar nan tamu ta maka kaɗan wajen lalata da ƙanwarka har sai ka koma wata jahar!"
Ƙirjinsa ya dafe da yaji yana barazanar ɓallewa, idanuwansa sun firfito waje jajir da su "Babba Lalata kuma? Ni ni Ishaƙ ne zan yi lalata da Khadijatunah? Khadijatu Ƙanwata fa? Ni ni...." Hawaye ne ya ci ƙarfinsa, yana jin maganar kamar a lokacin yake faɗa masa.
"Ban son munafurcin banza. Wa ye a garin nan bai san kai ne ka Lalata ƙanwarka ba? Wa ye kake tunanin zaka maida shasha da zaka zo ka faɗi labarin ƙarya akan abun da ya faru da ita? Dube ni da kyau! Ni ba yaro ba ne, na wuce ƙarfin ka zo ka karanta min labarin ƙanzon kurege. Ka je ka haiƙema yarinya ka zo kana mana wani zancen an mayarta asibitin Kano, duk girman Jahar nan tamu ba mu da asibitin da za'a sauya ma har sai ka ƙulla guzurin iskancinka ka tafi da shi Kano."
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil! Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fi musubati haza, wa kallafni khairan minha." Abun da Ishaƙ ya faɗa hawaye na zuba akan idonsa, bai tsaya ƙara jin wata kalma ɗaya ba ya bar fadar yana ji kamar numfashinsa zai bar jikinsa, zuciyarsa na tsalle tana barazanar fasowa daga ma'adanarta.....
Harara Mai gari ya bishi da ita yana ji kamar ya kwaɗe shi da mari ya bishi ya rufar masa "Aikin banza kai, ni ban taɓa sanin taimako yana zama mugunta ba sai yau. Lallai duniya ta gama lalacewa, wanda ta fidda balagurbin mutane masu tsartuwar dafi."
"Ai lamarin akwai ban mamaki, wa zai zaci kamilin yaro kamar Ishaƙ zai aikata wanan abun!" Wani daga cikin mutanen fadar mai gari ya faɗa.
"Kai jama'a muji tsoron Allah! Mu daina yanke hukunci babu bincike a cikinsa. Ku sheda ne akan irin halin da yaron nan ya shiga lokacin faruwar lamarin nan, amma duk wanan ba kome ba ne, kun masa hukunci akan sheda zurr."
Baki Mai gari ya buɗe yana kallon Limamin garin da ke magana, sai dai kafin ya yi magana na hannun damansa ya tara "Yanzu malam Liman so kake kace mai gari baya jin tsoron Allah ko kuwa mai? Ko mu da muka faɗi maganar ne kake son kafurta mu?"
"Tambayar mana shi Munkaila! Ƙila ya fudda mu a musulunci bamu sani ba." Mai gari ya faɗa bakinsa da kumfa yana jin zuciyarsa na tafasa.
"Subhanallah! Ni ba haka nake nufi ba, na dai faɗa muku abun da kuka manta ne, ko yaushe kuna zato alkhairi ga ɗan uwanku musulmi, domin ba yanda za'ayi wanan yaron ya lalata rayuwar ƙanwarsa da hannunsa. Musamman idan mukayi la'akari da tarin soyayyar da ke tsakanisu.
Duk garin nan wa ke da yaran da suke kula da tattalin rayuwarsu kamar su?"
"Ahaf ! Kaima kace babu mai halayya irin nasu, kenan dama soyayyar ba ta Allah ba ce?" Munkaila ya faɗa yana gwamutsa bakinsa.
Kai Malam Liman ya girgiza cikin takaicin halayyar mutumin "Duk inda akayi da jaki dai sai ya ci kara. Gaskiyar mutane da suke cewa ba'a mugun sarki sai mugun bafade. Allah ya shiryar da kai Munkalai."
Yana gama faɗar haka ya tashi yana ma mai gari fatan tashi lafiya, zuciyarsa cike da tausayi da kuma tsoron abun da zai biyo baya....
🌷🌷🌷🌷
Kuyi maleji.
#InuwarGajimare
#Dabanne
Wattpad @Oum_Nass[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE 💨
®NWA
©OUM-NASS
TARA
Tafiya yake yana riƙe da ƙirjinsa da yake jin zuciyarsa na gaf da ɓallowa daga ƙirjin nasa.
Hawayen da ke tsere akan idanuwansa sun gaza tsayawa _'Kana so kace min duk faɗin jaharnan da kewayenta sun maka kaɗan wajen lalata da ƙanwarka har sai ka bar garin?" Wanan maganar ke kai kawo a cikin kunnuwansa kamar a yanzu ne yake faɗa masa.
"Me yasa mutane ba su fiya adalci ba a rayuwarsu? Me ye laifinsa dan ya ƙaunaci Ƙanwarsa fiye da rayuwarsa? Ashe akwai kuskure idan ɗan uwa ya ƙaunaci ɗan uwansa?" Ishaƙ ya faɗa yana kuka shi kaɗai yake tafiya yana sambatu kamar wanda ya samu taɓuwar hankali.
Kuka ne ya ci ƙarfin idonsa wanda hakan ya sashi zama a tsakiyar rana ya haɗa kai da gwuiwa yana kuka. "Me yasa sai ni? Me yasa rayuwa tafi ƙuntatawa marar gata? Ashe maraicinmu ba kome bane? Ashe da can cikin rahama da gata muke?
Dawa zan samu mu raba wanan ƙuncin? Wa ke garemu a wanan duniyar da zai tsaya mana ya tayani kula da Khadijatu?"
"Ni zan tayaka kula da Khadijatu!"
Ba zata ya ji maganar hakan ya sashi saurin ɗago da kansa dan ganin wanda ke yin magana.
Babban Limamin garin ya gani a tsaye a kusa da shi, ya haɗa hannayensa akan ƙirjinsa, kai Ishaƙ ya shiga girgizawa hawaye na ci gaba da zuba akan idonsa "A'a Malam! Kai baka kama da mutane masu romon baka! Sam kamalarka bata can-canci ɗaukar nauyin mutane irinmu ba! Dan Allah kada ka sanya kyawawan hannunka ka ɗauki dattin da kowa ke gudunsa."
Takawa Malam Liman ya yi har ya ƙarasa kusa da Ishaƙ, a hankali ya tattara babbar rigarsa ya tsugunna kusa da shi, kana ya dafa kafaɗarsa "Kai ka yi addu'a aka amsa maka. Me yasa kuma zaka dawo da addu'ar baya? Shin baka yi farin ciki da gaggawar amsa addu'arka ba?
Allah yana saurin amsar addu'ar wanda aka zalunta, yana kuma aiko da wani ya zama silar amsuwar addu'ar, baa ka ji aranka ko nine wanan amsar? Lalai kana buƙatar abokin da zaka raba damuwarka da shi, ku tattauna akan rayuwarka, ya haska maka gabanka a lokacin da kake riƙe da sandar da bata rarrabe kwatami da tudu.
Babu wani datti a tare da ku da za'a ƙi ku, sai dai son zuciya na ɗan adam da gujema taimakon wanda ke ƙasa da shi. Ko wani mutum a duniya yana samun kansa cikin damuwa da matsala, amma wanda suka yi haƙuri suka kuma yi tawakkali sai rayuwarsa ta tsarkaka.
Hannayena cike suke da kwaɗayin cuɗanya da ku, zan tsaya muku da dukkanin ƙarfina! Zan kula da rayuwarka da ta ƙanwarka dai-dai ƙarfina! Sai dai ban saniba ko hakan zai iyu? Ban saniba ko zaka bani wanan damar? Amma ka sani, ni ba ni da wadatar hannu sai ta zuciya.
Zaka zauna a tare da ni?"
Kai ya gyaɗa masa, yana share hawayen fuskarsa da har lokacin ya qi tsayawa "Wa ye zai ƙi amsa wanan alkhairi? Karo na farko a rayuwata da naji a raina ina da sauran sa'ar zuwana duniya.
Kafin yanzu na fara tunanin rayuwata tana cikin mutanen da kanzo a sufuli su koma a cikinsa. Ashe idan da rayuwarka zaka ga abubuwan ban mamakin da suka fi mamaki zama abun tsoro.
Bani da bakin gode maka, amma ina addu'ar Allah ya faranta maka kamar yanda ka faranta mana."
Tashinsa ya yi tsaye yana yana riƙe da hannunsa "Ameen. Ina Khadijatu ta ke?"
"Na barta a gida da niyar na samo mana abincin da za mu ci, kaga kuma na sha'afa ban siyo mana ba." Ya faɗa yana ƙoƙarin ƙwace hannunsa daga riƙon da Malam Liman ya yi masa.
Ƙara damƙe hannun Malam Liman yayi yana kallonsa fuskarsa ƙunshe da murmushi "Yanzu ai baka buƙatar neman inda ake siyar da abinci, zan ci gaba da ciyar da ku a gidana.
Mu je ka amsar mata abincin, daga nan sai a gyara mata ɗakin da zaka zauna, dan barinta a gida ita kaɗai a yanzu akwai hatsari."
Kai Ishaƙ ya gyaɗa yana kallon Malam Liman zuciyarsa na cike da mamakin mutumin "Ashe zuciyarsa na da kyau har haka? Shi dai a saninsa da shi tun tasowarsa maganarsu bata wuce a ƙirga ba, lallai gaskiyar mutane da suke cewa ba'a sheda ɗan balbela a kallo guda.
******
Gidansa ya shiga da shi kai tsaye bakinsa ɗauke da sallama, hakan yasa duka hankalin matan gidan juyowa kansa.
Mata ne guda biyu a gidan da kuma yaransu wanda a ƙalla za su kai Bakwai, Huɗu mata uku maza, wanda matan ne manya, sauran mazan kuma yara ne.
Tabbarma Babbar yarinyarsa ta shimfuɗa masa wanda shekarunta ba za su haura goma sha biyu ba a duniya.
"Bismillah zauna Ishaƙ." Malam Liman ya faɗa yana bayan ya dai-daita zamansa akan tabarmar.
Sai a lokacin matan suka lura da baƙuncin mutumin, kamar an zaburesu suka wara idanuwansu waje suna kallon sa.
Tun kafin ya zauna, Ɗaya matarsa ta yi saurin tararsa "Dakata Yaro kada ka zauna min akan Tabarma!"
Cak ya tsayar da ƙafarsa da ke ƙoƙarin taka tabarmar, shi kansa Malam Liman da mamaki akan fuskarsa yake kallon matar tasa.
"Kamar ya kar ya zauna a tabarmarki Habi?"
Idonta ta ƙanƙantar wanda ke nuna tsan-tsar masifarta da kuma tsanar Ishaƙ ɗin "Saboda tabarmata ba ta ƙazaman mutane ba ce. Waɗanda suka cuɗanya suka futo ta haramtacciyar hanya, kana suka watsa magunyar dauɗarsu wajen tabbatarwa da duniya cewa su ɗin haramtattune, wanda basu samu kyakkyawan raino da kula ba."
Ido Malam Liman ya fiddo waje, cikin kunya da takaicin matarsa, yana ƙara kai kallonsa ga Ishaƙ da ke tsaye ƙafarsa a ɗage kansa a ƙasa, wanda hakan ya hana shi gane ainihin abun da ke damunsa.
"Habi kin san me kike faɗa? Kin san hukuncin ƙazafi kuwa a musulunci? Wai me yasa ku mata ba ku da tunani mai kyau ne? Me yasa duk abun da aka faɗa muku kuke saurin yarda da shi ne? Da kike faɗar haka wani tabbaci gareki na cewar abun da koke faɗa gaskiya ne? "
"Ni kuwa nasan me nake faɗa malam! Ina faɗar gaskiyar da babu sirkin ƙarya a cikinta ne. Ina kuma faɗar zahirin da idanuwa da yawa suka gani a tare da wanan tsageran yaron.
Ni idanuwana basu makance da son yin gwaninta ba, ba zan janyo annoba da hannuna na zaunarta a kusa da ni ba.
Ina da yara mata, ba zan zama silar kawo abun da zai wargaza musu rayuwa da tunaninsu ba, kamar yanda ya zama silar jefa rayuwar ƙanwarsa ciki.
Indai har bai iya ganin Khadijatu ya ƙyaletaba to wata yarinya kuma kake tsammanin zai ƙyale malam.?"
Dafe kansa Malam Liman ya yi hawaye na sauƙa akan idanuwansa na tozarcin da matarsa ta yi masa "Inna lillahi wa inna ilahirraji'u! A gabana Habi kike aibata mutumin da na kawo gidana tun kan ki amshi baƙuncinsa? Ashe dama ni ban isa da gidanaba ban sani?
Hasbunallahu wa ni imal wakil!"
"A'a malam ba rashin isa da gidane ba ka yi ba. Gaskiya ne Yaya ta faɗa. Mu muna da yara mata a gida, idan ka bawa wani namiji baligi damar shigo mana gida kai tsaye me kake tsammanin zai biyo baya? Balle kuma shi da kowa ya sheda halayyarsa.
Gaskiya ni banga aibun maganar Yaya anan ba."
Hannu ya ɗaga musu yana ɗago kansa da kallonsu Idanuwansa sun yi jajir saboda ɓacin rai da takaidin matansa.
Juyawa Ishaƙ ya yi da zummar barin gidan, yana ji kamar zai iya tsintsuwa ya ganshi a waje, yayin da wani sashi na zuciyarsa ke ji inama ace ƙasa ta buɗe ya afka ciki ya rufe.
"Ishaƙ kayi haƙuri ka zo ka zauna."
Juyowa ya yi a hankali ya saki murmushi wanda ba zaka gane ko na miye ba "Kayi abun da zaka iya Malam. Ka kuma gwada min soyayya da ƙauna, ko a haka ka barni na gode sosai, zan kuma ci gaba da tuna hakan har ƙarshen rayuwata.
Akwai hanyoyi da yawa da Allah kan amsa addu'ar bayinsa, tabbas ka so zama sila, amma ba kai ne ba. Wata ƙila wani ne daban yana can yana dakonmu.
Mutanen duniya dukkansu raunatattu ne, kuma gajiyayyu ne, masu ɗauke da abubuwa guda biyu, sai dai basu iya rarrabe wanne ne yafi amfani a garesu."
Yana gama faɗar haka ya juya yabar gidan.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
#IG
#DABANNE
Wattpad @Oum_Nass
[10/14/2020, 3:48 PM] +234 703 602 1861: INUWAR GAJIMARE
®NWA
©OUM-NASS
Wattpad @OUM_NASS
GOMA
Jiki ba ƙwari ya fita a gidan yana ji a ransa wanan ne lokaci na ƙarshe da zai ƙara bari hawayensa ya zuba akan matsalar Khadijatu.
Dole yana buƙatar ƙwarin zuciya da zai fuskanci mutanen da suke kewaye da shi. a baya ya ɗauka komi zai zo masa da sauƙi, amma sai gashi labarin ya sauya, ya sabunta tunani da duniyarsa.
A hankali yaci gaba da tafiya akan ƙafafuwan da yake ji kamar basu da ƙarfin ɗaukarsa, yana ji komi da ke tattare da shi na sassan jikinsa na raunana.
To wani ƙarfi gareshi ma da zai iya takawa da ƙumajinsa? Duk majalisin da ya wuce sai an nuna shi ana zanɗensa da kuma yi masa ahuwo. Wasu a ciki da basa jurewa sai sun tanka masa a gabansa.
Da ƙyar ya iya kawo kansa gida asalima nisa ya ga gidan nasu ya ƙara yi musu.
"Kada ka matso kusa da ni! Wayyo Yayanah gashi nan yana biyo ni! Yayana kana ina zai sake cutar min? Zai sake yi min wata muguntar!" Ihun khadijatu da sunbatunta ya daki kunnuwansa a lokacin da ya zura ƙafafuwansa cikin gidan.
Da gudu ya shiga ɗakin ya taddata tana ta faman haɗa gumi sai buga kanta take a jikin bangon ɗakin.
Da ƙarfi ya figeta daga jikin bangon kanta duk ya fashe jini yana zuba saboda bugashin da ta yi "Khadijatu!" Ya kira sunanta da raunin murya yana ɗora hannayensa akan fuskarta.
Idonta ta buɗe a hankali wanda jini ke ɗiga a kansa, jikinta kuwa sai ɓari yake kamar wanda zazzaɓi ya yima mugun kamu.
"Yayanah!" Ta faɗa a hankali hawaye na sauƙa akan fuskarta wanda ya gauraya da jinin da ke goshinta.
"Kace masa ya daina bibiyar rayuwata! Duk lokacin da na rufe idanuwana ina ganinsa. Dan Allah kace ya yi haƙuri kada ya ƙara cuta min! Har yanzu ina jin zafi a ƙasana da ƙirjina! Ina jin kaina kamar an ɗora masa ƙaton dutse Yayanah!
Anty ta hanani addu'a akan mutuwa amma inaji kamar mutuwa hutu ce a gareni! ME ne laifina idan na roƙi Allah wanan hutun?"
Rungumeta ya yi gam a jikinsa yana ƙara ƙanƙameta a jikinsa, hawayen da yake yaƙin daina zubarsu sun ɓalle daga killace sun da yayi.
Ganin Khadijatu a cikin wanan halin ya isa ya ƙara raunata raunatacciyar zuciyarsa. Lallai ko da wanan aka barsu ya ishesu tashin hankali a rayuwarsu, ko iya wanan mutanen garin suka barsu da shi ya isa su rataye kansu ba sai sun haɗa musu da wani ƙazafin ba.
"Duk wanda kika ga yana rayuwa a duniya akwai dalilin rayuwarsa a ciki Khadijatu! Idan da ace babu amfanarwa a barinki a raye na tabbata da tuni Allah ya ɗauki rayuwarki tun kafin yanzu.
Bakya ji a ranki cewa mu kyawawan musali ne ga rayuwar wasunmu, musamman idan kikayi la'akari da hatsarin da ya zama silar rashin mahaifiyarmu.
Ni na tabbata Allah yana sane da mu, zai kuma karemu! Zai gyara mana rayuwarmu ta gaba.
Ki daina kiran mutuwa da sunan hutu, domin tana zama hutu ne ga wanda yayi aiki tuƙuru ya bautama Allah da dukkanin zuciyarsa! Shin me kika tanadarma kanki na wanan ladan idan kin mutu yau?"
Kai ta girgiza tana ƙara ƙanƙame shi, jikinta na ɗaukan rawa, ba ta sake magana ba, sai dai akai-akai takan zabura.
Shuru shima yayi yana jin sauƙar numfashinta da ke tafiya da ƙarfi, shi yasan idan har za'a auna jininsu shi da khadijatu to babu makawa sai an gano ya zarta misali, kamar yanda ya ke jin bugawar zuciyarsu ta ban-banta da yanda ta ke bugawa a baya.
******
LAGOS, NIGERIA.
Karo na uku kenan yana shiga ɗakin ya tararta tana barci, gashi baya so ya tadata gudun kada ya katsar mata da daddaɗan barcin da ta ke, wanda yake da tabbacin barcin wahala ne ta samu ta ke yi. Kasancewar daren jiya bai barta ta yi barcin kirki ba.
Agogo rolex ɗin da ke hannunsa ya kalla, ƙarfe 8:30am shi da ya kamata ace yabar gida tun 7:30am.
Wayarsa ce ta yi ƙara da sauri ya kashe ƙaran gudun kada ya tashi masoyiyarsa. Kara wayar ya yi a kunne, yana jin sautin muryar da ke futa da faɗa-faɗa.
Idonsa ya lumshe a hankali yana jin ɓacin ran da bai shirya amsarsa ba a yau, a hankali ya yi magana kamar yana koyan yanda ake maganar ne "Hutuna bai ƙare ba, ba zan iya barin iyalina na zo aiki ba." Yana gama faɗar haka ya datse wayar.
Yanayin maganarsa bai yi kama da mai ɓacin rai ba, amma yanda yake sauƙe numfashi, shi zai tabbatar ma da cewar ya hassala da wanda ya kirashi a wayan.
Tashi ya ke ƙoƙarin yi ganin wayansa na sake ƙara, shi me yasa ma ya shiga wanan jarababben aikin? Da yasan zai shiga tsakaninsa da masoyiyarsa da ba zai taɓa gigin shiga ba.
Duka yau kwana huɗu da yin aurensa, amma kuma ana so ace masa ya koma bakin aiki, wani irin aiki ne wanan da bai ɗaukan uzuri? Ko dai dama duk wani soja rayuwarsa na ƙarewa ne akan iyakar ƙasa da gadin mutanen da ke kwance a raɓa.
Hannun da ya ji an ɗora akan nasa ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya, musamman sanyin da ya ji akan hannayen nasa, idonsa ya ɗaga da suka riga suka sauya kala daga ainihin golding kala nasu zuwa jajaye.
Ƙayataccen murmushi ta shimfiɗa masa akan fuskarta "Wa ya taɓa min Sojanah!"
A hankali ta yi maganar cikin sigar shagwaɓa wanda ya sashi saurin kwantawa akan ƙafafuwanta, kamar ƙaramin yaro.
"Me yasa sai a wanan lokacin za su katse min jin daɗina su kirani? Anya ban yi kasada ba da na zaɓi zama soja akan ko wani aiki?"
Fuskarsa ta shafa cikin sigar murmushi da ƙwarara gwuiwa "Saboda kai namiji ne! Namijin gaske wanda kowa ke alfaharin kasancewa tare da shi. Nasha jin labarin mazaje amma ban taɓa