Showing 48001 words to 51000 words out of 91747 words
za'a ce wani abu zai hanashi lafiya ba.
Amma zamu bata maganin da zai kareta ya ƙara mata lafiya ita da abun da ke cikinta."
"Yauwa har na cin abincima ka rubuta ko a dace." Momy ta faɗa cikin fuskar alhini.
Shi dai likita murmushi yayi yana mamakin son da sukema yaron da bai zo duniyaba, kamar dai basu san ya yanayin mai ciki yake zama ba.
Maganin ya rubuta musu yana rakasu har wajen siyan maganin, sai da yaga har tafiyarsu sanan ya dawo office ɗinsa yana dariya.
🌷🌷🌷🌷🌷
Barkanmu da ranar juma'a.
Kuyi haquri da erro'rs saboda babu editing...[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
B000000330000000T
KANO, NIGERIA.
Bayan kwanaki biyu.
Rayuwa a cikin dangi abune mai mutuƙar daɗi da alfahari. Ko wani sashi na ahalinsu Ishaƙ tsere suke da rige-rigen nuna musu soyayyar da suke musu.
Kulawar da ake bama Khadijtu ta linka ta baya, daga ƴarshe da Abba Imran ya fahimcin abun da ke damunta, sai ya kira wani ƙwararren likita da ke ƙasar india, wanda dama asalinsa ɗan nan ne. Shi cikekken likita ne manazarci akan halayyar mutane da kuma abun da ya shafi ƙwaƙwalwarsu.
Kasancewar yasan ko waye Imran yasa ya amsa, sai dai tarin aiyukan da ke kansa yasa shi karɓan uzuru akan ya yi haƙuri zuwa kwana biyu ya kammala.
Ba matsala itace amsar da Imran ya bashi, amma ba wai dan zai iya tsayawa ya jira har zuwa kwana biyunba.
Tashin Ammu ya yi sukaje ya mata katin barin ƙasar, ita da Baba da Ishaƙ daga nan ya fara musu cuku-cukun barin ƙasar.
India suka tafi da shi da Abbu Yasir da Ummi kuma suka koma Kaduna da su Mairama da Indo dan Imran yace ba za su koma can ba, su huta anan kafin su dawo.
*****
CHANNAI, INDIA.
Tunda suka sauƙa a gari Ishaƙ yake ta jujjuya kansa, bama shi kaɗai ba harda su Ammu da basu taɓa tunanin za su bar ƙasarsu ta haihuba. Wanda sai da aka sha ɗan ƙaramin yaƙi kafin ta yarda ta shiga.
Manya-manyan gidaje da masana'antun da suka cika garin su kaɗai sun isa sawa kan mutum ya juye "Taɓɗijam! Waɗan nan basu shiryama kansu mutuwaba amma Imrana?" Ammu ta faɗa tana riƙe da haɓarta.
Murmushi Imran yayi yana ƙaara kallon yanayin garin "Ammu su ai basu yarda idan aka mutu ana dawowa ba, shi yasa suke shiryama kansu kyakkyawan rayuwa.
Wanan kuma da kikaga yana daga cikin tattalin arziƙinsu, da kuma bunƙasa ƙasar ta zama kafaɗa-da-kafaɗa da sauran ƙasashe na duniya, ta fanni kimiya da kuma fasaha."
Kai ta gyaɗa "Ikon Allah! Yanzu dai so kake kace min a duniya akwai wasu ƙasashen da suka ninka wanan da take so suzo ɗaya da ita?"
"Haka ne Ammu!" Ya faɗa yana kallon symbol ɗin asibitin da za su je.
Shuru sukayi basu ƙara maganaba har saida suka zo asibitin anan direban da ya kawosu ya sauƙesu bayan sun sallameshi ya tafi.
Anan likitoci suka zo suka musu maraba fuskarsu ɗauke da fara'a kasancewar fuskarsa sananniya ce a asibitin, domin akai-akai yake zuwa ana duba lafiyarsa wani lokacinma yakan rako Abbu Yasir shima aduba tasa lafiyar.
"Wai yanzu nan aljannar duniyarma asibiti ce Abdallah?" Ammu ta faɗa ganin ko ina asibitin an ƙwatashi da adon furani, babu warin nan na asibiti da yake tashi.
"Eh Ammu!" Ya faɗa yana danne dariyarsa.
"Ikon Allah! Ishaƙ kaga wani duniyar da mutum bai kawowa kansa akwai irinta ba ko?"
"Eh musamman wanda yake jiran ƙasa ta kirashi ba! Amma idan kana gajiyar ƙuruciyarka ai zaka sa rai akan ganin fiye da haka."
Harara ta buga masa tana tafa hannu da salati "A taƙaice dai so kake kace ni ce ban kawowa kaina irin wanan rayuwarba ko?"
Dariyarsa ya ƙunshe "Kema ai kin faɗa." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.
Duka ta kawo masa yayi saurin guduwa daga kusa da ita ya koma kusa da Imran.
Kunnensa Imran ya ja da ƙarfi wanda ya sashi yin ƙara yana dafe kunnuwansa.
"Ka fita a idanuwana Isiyaku! Ka matsama uwata da yawa."
Dafe kunnensa yayi yana yarfe hannu, sanan ya matsa daga kusansa ya koma gefen Baba "Ban san tsautsayin da yasa kuka rakico mana wanan tsohuwar a tafiya ba. Da ace suna jin yarenmu ai da mun kwashi kunya a hannunmu." Ya faɗa yana yamutsa fusa.
"Ungo amshi wanan ɗan ƙaniya!" Ammu ta wurgo masa daƙuwa da hannunta, saboda ta rasa ta ina xata fara ta huce akan abun da ya mata.
Gwalonta yayi yana dariya wanda Baba na tayashi yin dariyar. Dai-dai futowar wani balaraben Likita sanye da fararen kaya. Matashin saurayi ne wanda shekarunsa ba za su wuce ashirin da uku ba.
Fuskarsa zagaye da gashi wanda ya ƙawatata ya kata kyau ƙwarai da gaske.
"Wow masha Allah!" Ishaƙ ya faɗa yana kallon saurayin da ke kusantosu hannayensa sarƙafe cikin aljihun wandonsa.
"Abbie kaga wani Balarabe anan! Koma dai shima ɗan india ne sune naji ana cewa ƙarshen kyau!" Ishaƙ ya faɗa yana ƙawata fara'ar fuskarsa.
"Abbie ka masa magana kada ya wuce mu, kaga kansa a ƙasa da alamu bai lura da mu ba." Ishaƙ ya sake faɗa.
"Kai da Allah ka rabu da mutane! Naa an faɗa maka ƙauyen Toni ne da zamu tsayar da mutum muna ta masa magana bamu da alaƙa da shi." Ammu ta faɗa cikin faɗa da son ta huce haushin da Ishaƙ ya guma mata.
Ai kuwa nan take fuskarsa ta sauya numfashinsa ya fara sama-sama kamar zai fito waje, idanuwansa har sun kaɗa, saboda jin sunan TONI da yayi. A wanan yanayin da yake na farin ciki me yasa Ammu zata tuno masa da baƙin garin da yake ƙoƙarin rufe shafinsa.
"Abokina rabu da wanan tsohuwar da alamu tana cikin rikicin tsufa ne." Ya tsinkayi wata tattausar murya da ke fita a nutse ta masa magana.
Kansa ya kai ga inda yaji muryar, ido ya fiddo waje ganin balaraben matashin da yake so ayima magana.
Kallon Imran yayi bakinsa na rawa yana nuna mutumin. Dariya Imran yayi shi da balaraben "Dakta Nabil Ahmad Nasir ANA." Imran ya faɗa yana faɗaɗa murmushin kan fuskarsa.
Dafe kai Ishaƙ yayi yana kallon balaraben da ke gabansa wanda yaji tambarin sunansa cikin na su na hausawan da ya saba ji. Musamman inkiyar sunan da ta zama ruwan dare a cikin ƙasarsa.
"A ina na taɓa jin sunan ANA Abbie? Kaddai kace min balaraben dake gabana bahaushe ne kamarni anan?"
"EH hAKA MAGANAR TAKE!" Abbie Imran ya faɗa yana kallon Abbu Yasir da tunda suka zo wajen yake kallon yaron.
"Ka barmu a tsaye Ɗan bamaina! Ga shi mun sha hanya da yawa bamu huta ba, ya kamata mu tattauna akan abun da ya kawo ku. Dan idan muka biya shirmen Ishaƙ to zamu kwana anan."
Risinawa NABIL yayi yana shafa kansa "Afwan Abbu Yasir! Gashi ƙafafuwanka sunyi laushi basa jure tsayuwa dama.
Bismillanku." Ya faɗa yana wara hannunsa da nuna musu hanya.
Ranƙwashi Abbu Yasir ya masa wanda ya sashi dafe kansa yana shafa wajen......
🌷🌷🌷🌷🌷
Kuyi maleji plx In sha Allah zan baku karin kumallo gobe.
Nagode.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
B000034000000L
"Barkanku da hanya!" Nabil ya faɗa bayan an gabatar musu da abun da za su ci.
"Yauwa Likita. Sai kuma ka ganmu kwatsam duk da kace mana kana zuwa nan da kwana biyu. Kayi haƙuri ba zamu iya jure jiran waɗan nan kwanakin da ka faɗa ba ne, saboda halin da yarinyar ta ke ciki." Imran ya faɗa cikin sanyin murya wanda yake nuna al'amarin ya tsaye masa a zuciya.
"Ayya Abbie! Da ka faɗa min ai da na katse aiyukana na nan naje can ɗin. Ban san al'amarin na gaggauwa bane, musamman dana ga kaima ƙwararre ne ta wanan fannin."
"Gaskiya ne, amma ni kaina nafi son zuwa nan ɗin saboda anan zata fi samun kulawa babu hayaniya kamar can ɗin.
Zamowata likita ba yana nufin zan iya kula da kowa bane, amma kai ina da tabbacin zaka kula min da ɗiyata."
"In sha Allah! Amma dai kun san dokokin asibitin namu, bama buƙatar masu zaman jinyarta, domin muna da Nurse's ɗin da za su kula da komi nata. Daɗin daɗawa ni kaina zan bata kulawa ta musamman."
"Ina da tabbaci akan zaka iya ne Nabil. Na bar maka komi a hannunka."
"Abbie kana nufin mu zamu tafi mu bar Khadijatu ne a hannun wasu? Khadijatu zan bari wasu su kular min da ita?" Ishaƙ ya faɗa yana jujjuya maganar.
"Eh Imran! Amma hakan ba yana nufin zamu tafi ba zamu dawo bane. Lokaci zuwa lokaci zamu ke zuwa muna ganin halin da take ciki, su ne zasu bata kyakkyawar kulawa da kuma buɗa mata abubuwan da ya kamata ya korar mata da tsoron da ke cikin kanta.
Amma idan muka zauna duka ba zamu bawa kwanyarta damar da zata huta ba, asalima mun yi mata yawa da ƙara rikita mata zuciya."
Kai ya shiga girgiza "A'a Abbie ba zan iya tafiya nabar Khadijatu ba! Duk duniya babu wanda zai kular min da Khadijatu kamar yanda zan bata kulawa."
"Ni zan tayaka kula da ita abokina!Ba zan bari koda ƙuda ya hau kantaba balle ya dameta. Ka yarda da ni!" Nabil ya faɗa yana kallon Idanuwan Ishaƙ da shima ya ke kallonsa, ji yayi ba zai iya jura kallon ƙwayar idanuwan Nabil ɗinba hakan ya sashi sauƙe nasa idon.
'Wanan wani irin mutun ne mai idanuwa wasu kala da su?' Ishaƙ ya faɗa a cikin zuciyarsa yayin da ya gyaɗa kansa ƙasa "Na yarda zan baka amanar Khadijatuna kamar yanda kace zaka kula min da ita. Ina fatan kada naga sauƙar ƙuda akan fatar jikinta kamar yanda ka min alƙawalin zaka kula min da ita."
Murmushi Nabil yayi yana miƙa masa hannu alamun suyi musabaha "In sha Allah zan yi dukkanin ƙoƙarina wajen kula maka da ƙanwarka."
Sanan ya juyar da kallonsa ga Abbu Yasir "Abbu Tsoho baka ce komi ba fa!"
Baki ya taɓe sanan ya aikama Ishaƙ da harara "Me zance ina ga sabon fi'ili, ɗan yaro yana mana maganar da mu ba muyita ba. Kai kace shi kaɗai ne mai ƙanwa a duniya."
"Aifa da alamu su kaɗai ne suka zo a matsayin yaya da ƙanwa, sauran mutane kuma inaga a rarrabe suke." Ammu ta cafe maganar itama cikin jin haushin kinibibin da Ishaƙ ke musu.
"Da alamu waɗan nan kishi suke da kai Abokina!" Nabil ya faɗa cikin sigar tsokana.
Hannunsa ya kare da bakinsa ya yafito Imran ɗin "Haushi suke ji su basu da yayan da zai kula da su haka!"
Dariya suka yi duka daga nan suka tashi "To Likita mu zamu tafi masauƙinmu, sai zuwa gobe in sha Allah." Abbu Imran ya faɗa ganin lokaci ya ja, gashi suna tare da gajiya.
"Shikenan! Allah ya amince mana. Kafin ku tafi ya kamata ku duba ɗakin da aka kai Khadijatun."
"Hakan yana da kyau Dakta." Baban Indo ya faɗa.
Daga nan suka fita a office ɗin suka nufin ɗakin da aka kai Khadijatu. Daga cikin glass ɗin da ke kewaye da ita suka hangota kwance akan gado an sa mata na'ura a kanta da saitin zuciyarta, hannayenta ma duk sune a jiki.
"Muna kan gaɓar bata taimako na gaggawa, saboda ciwon ya riga da yaci jikinta sosai."
Kai suka gyaɗa a tare kamar wasu ƙadangaru "Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta."
Suka faɗa a tare sun daɗe anan suna kallonta daga bisani kuma suka fito suka tafi masauƙinsu, Ishaƙ sai share hawayen da ke kan fuskarsa yake, yana hango Khadijatu maƙale da na'ura a jikinta.
A rayuwa bai taɓa hasashen bawa zai iya samun kansa a cikin wanan yanayinba, a 'yar ƙaramar kwanyarsa marar tunanima bai kawo ƙaddara zata cimma matsayinsu ta ƙara daƙusar musu da tasu rayuwarba.
Sai dai hakan wata sabuwar rayuwace a garesu, ta karɓa da kuma dawo musu da abun da suka rasa, idan ka rasa wani abu sai Allah ya dawo maka da wani abun daban.
Ba dan wanan larurar da ta faru da Khadijatuba da ƙila haka za su ci gaba da rayuwarsu ba tare da sun haɗu da ko mutum ɗaya na daga danginsu ba.
Sai gashi komi da ya faru yana da sanadi da kuma ƙaddararsa.
Daren ranar dai bai iya rintsawa ba, dan ko yaushe ya rufe idanuwansa Khadijatunsa yake gani, juyi yake akan makeken gadon da yake ji kamar yana cikin ƙaya ne.
Duniyar tayi shuru babu sautin komi sai na na'urar sanyaya ɗakin da ke sanyaya masa jikinsa, amma a nasa jiki sai yake ji kamar ana watsa masa ruwan zafi ne.
Ganin barci ba zai samuba ya sashi tashi ya ɗauro alwala ya fara jero nafula yana toƙarma Khadijatu sauƙi daga wajen Allah.
A hankali yaji nauyin da ke ƙirjinsa yana raguwa, zafin da ke ratsa jikinsa ya fara ficewa."
******
Washe gari.
Sunyi sammakon ganin Khadijatu sai dai yau an samu sauƙi an cire mata na'urar da ke maƙale a hannunsa, sai iya ta kanta da kuma ta ƙirjinta.
"Idan babu damuwa ku koma gida Abbu saboda zamanku anan zai kawo tsaiko akan aiyukanmu, kuma kuma an tsayar muku da aiyukanku."
"Haka ne kuma. In sha Allah zuwa gobe zamu koma gida." Abbu Yasir ya faɗa.
"Banda ni gaskiya." Ishaƙ ya faɗa cikin dakiyar muryarsa.
"Dole kuwa mu koma da kai! Idan ka zauna anan uwar mi zaka tsina mata, tunda ga Likitoci nan zasu kula da lafiyarta." Ammu ta faɗa cikin hassala kamar zata buge shi.
Nan ƙirjinsa ya fara hawa da sauƙa jijiyoyin kansa suka fara tashi "Baba kama Ammu magana ba ruwanta da ni." Bayansa Baba ya shiga bubbugawa, yana ma Ammu alama da ido akan tayi shuru. Shi ya rasa wata irin zuciya ce da Ishaƙ da an masa magana da fatar baki sai ƙirjinsa ya fara hawa da sauƙa, jijiyoyin kansa ya fito raɗo-raɗo.
"Shikenan zamu barka kai da Ammu, amma sai dai mu je gidan da muke sauƙa, kana ba wai zaman banza zakayi ba makaranta zan saka da nemo maka malamin da zai maka darrusa ta yanda zaka goge." Abbie Imran ya faɗa yana kallon Ishaƙ.
Kai ya girgiza "A' a Abbie ni kaina ba zai ɗauki karatu ba gaskiya. Tunda na taso ban taɓa shiga aji na zauna ba, ta ya kuma yanzu goɗai-goɗai da ni zan zauna a koya min karatu?"
Dariya Dakta Nabil yayi yana nuna Ishaƙ da hannunsa "A wanan shekarun naka kake cewa kayi girma da karatu? Yo ko Abbu Yasir aka sashi a aji ai zai amshi kwalinsa da kyau! Kada ka bada maza ka zauna kayi karatunka ta yanda zaka ƙwatarma ƙanwarka 'yancinta."
Fuskarsa ya shafa har zuwa kansa, sanan ya tauna laɓɓan bakinsa "Shikenan Abbie Zanyi!"
"Ɗan ƙotar uwa yaji ance nafi shi kai shine zai ce zai yi." Abbu Yasir ya faɗa yana dariya.
Suma dariyar sukayi, daga nan suka yima Dakta Nabil sallama suka tafi.
Sai da suka yima su Ishaƙ komi aka gyara musu gidan kasancewar akwai 'yan aikin da suke kula da shi, daga kan share-share zuwa girki da gadin gidan. Duk dama gidan ba wani girma gareshi ba amma tsarinsa kaɗai abun burgewa ne.
Daga nan suka nufi makaranta da yake Abbie ƙwararre ne wanda yake da kyakkyawar mu'amula da makarantar suka karɓeshi hannu bibbiyu, aji uku aka sashi a matakin skandrt kasancewar shekarunsa sun yi sama, amma da kyakkyawan sharaɗi akan dole ya zama gogge ta ko wani fanni da samar masa malamin da zai ke bashi darrusan baya.
Wanan shine abu mafi sauƙi haka Abbie ya nema masa ƙwararrun malamai har uku wanda za suna zuwa suna koyar da shi safe yamma zuwa dare duk da malami daren na Addinine zai koyar da shi abun da ya shafi addininsa wanda bai sani ba.
Komi ya kammala a ciki kwanaki biyu dan sai da suka tsaya suka ga yanayin karatun nasa sanan suka dawo gida Nigeria aka barshi daga shi sai Ammu suna cakawa.
🌷🌷🌷
AFWAN nace zan baku karin kumallo, kuyi haƙuri komi sai Allah ya yarda. ga dai wanan ya samu, fatan zaku yafe bashin da na kasa biya. Mura ta mun kamu mai kyau kaina ya riƙe amma Alhmdlh na samu dama na muku rubutun duk da ba yawa...
GIRMAMAWA[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
B0000035000000L
Jiniyar asibitince ta fara ƙara tana kawo haske tana ɗaukewa, wanda hakan yasa hankalin likitocin tashi, suka fara kaiwa-da-kawowa saboda ganin abun da ya faru.
Da sauri Dakta Nabil ya shiga ɗakin Khadijtu, nan yaga ta faffasa duk na'urar dake ɗakin, wanan shi ya tabbatar masa da cewar matsalar dga ɗakinta ta taso.
Kafin yayi wani yunƙuri ɗakin ya cika da ma'aikatan asibitin "Me ke faruwa anan Dakta Nabil?" Shine tambayar da suka masa da yaren ingilishi.
Ƙarasawa yayi kusa da ita yaga ta takure jikinta waje ɗaya, ko ina a jikinta sai rawa yake "Me kikayi haka Khadijatu?" Ya mata magana da sanyin muryarsa.
Kai ta girgiza masa tana ƙara cusa kanta a cikin gwuiwarsa "Bana so!"
"Ana nema miki lafiyarki ne fa! Yanzu gashi duk kin hargitsa mana asibiti, hankalin mutane da yawa ya tashi duk saboda ke!"
Hannayenta ta haɗe waje ɗaya har lokacin kanta na jikin gwuiwarta "Dan Allah kuyi haƙuri kada ku cuta min! Ina Yayana yake?"
Karo na farko da yaji muryarta tun bayan kawota asibitin, muryarta batayi masa kama da ta hausawa ba, domin yanda wasu harrufan basa fita.
Duk da yake bafullatanin asali amma hakan bai hana shi jin daɗin muryarta ba "Daga yanzu ai nine yayanki! Saboda ni