Showing 36001 words to 39000 words out of 91747 words

Chapter 13 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

808

a duniya tsoronsa take ji. Nima da fari ƙin yarda ta yi dani sai da na kirata da sunan Khadijatul Ishaƙ.
Mamanmu ke kiranta da haka a duk lokacin da take cikin damuwa ko kuma ta tsorata." Ya ƙarasa maganar yana share hawayen kan fuskarsa.
Jikin Dakta Imran ne ya shiga rawa ya manta inda yake da wajen da yake, sai wurga kallonsa yake akan yara biyun da suke gabansa.
"Ina Mamanku take?" Tambayar ta ƙwace akan bakinsa, muryarsa har rawa take yana son sanin ƙarashen labarin.

Murmushin gefen baki Ishaƙ yayi yana bubbuga bayan Khadijatu da tayi barci akan kafaɗunsa.
"Gata can a bayanka." Ya faɗa masa yana nuni da hannunsa.
Cikin sauri ya juya dan ganin wanda ya kira da maman nasa, sai dai abun da ya gani a gabansa shi ya ƙara dagula masa da sauran lissafin da ya rage masa.
"ABDALLAH!" Ammu da Baba suka faɗa a tare.
"Abdallah ashe dama kana raye duk tsawon wanan lokacin? Ina Hajara take ABDALLAH?" Ammu ta ƙarasa maganar bakinta har rawa yake.

Kai ya shiga girgizawa hawayen da bai shirya fitowarsu ba suka fara sauƙa akan fuskarsa.
"Me yasa tsawon wanan shekarun kuna raye baku taɓa faɗa mana ba Imran? Laifin me muka aikata muku a rayuwa?" Baba ya faɗa hawaye na zuba akan idanuwansa.
Su kansu mutanen wajen tsayawa sukayi suna kallonsa.
"Baba wananfa sunansa Imran ne ba Abdallah da kake kiransa da shi ba." Dr. Saleem ya faɗa cikin sanyin murya, domin shi kansa ya tsorata da ganin halin da Dakta Imran yake ciki, jikinsa sai rawa yake ga bakinsa na motsi amma ya kasa faɗar koda kalma ɗaya ba ne.

"Kaine baƙo anan wajen Likita, amma ni koda duniya zata taru suna ce min wanan Imran ne ba zan taɓa yarda ba.
Ina ka kai min 'yata tsawon shekaru goma sha biyar baka waiwaye mu ba?"

Durƙusawa Imran yayi a kan gwuiwoyinsa yana jin ɗacin da ke maƙoshinsa ya gaza faɗawa.
Wayarsa ce tayi ƙara wanda hakan yasa shi saurin dubata sunan wanda ya gani a jiki yasa shi saurin ɗagawa ya buɗe sautinta a fili yanda kowa zai ji.
"Ummi na haɗu da Iyayen Hajara suna tambayata ina ɗiyarsu ta ke? Ummi gasu a gabana suna tambayata abun da ya hanamu nemansu tsawon lokaci! Wata amsa zan basu Ummi?"

Daga inda suke suna jiyo sautin salatin Ummi "Imran da gaske kake?"

"Zamu zo da su ki basu amsar tambayarsu."
"Imran!" Ta ƙwala kiransa amma ya kashe wayar.
Danna madanan wayar yayi ya kara a kunnensa "Anwar ka zo asibiti ka kular min da marar lafiyata."

Yana gama maganar ya kashe wayar ya kai kallonsa ga Dakta saleem "Ƙanina zai zo ya kula da ita, zai duba abhn da ke damunta."

Kai Dakta saleem ya gyaɗa, sanan ya maida kallonsa ga su Ammu "Ku zo muje Kaduna ku samu amsar tambayarku."
Biyo bayansa sukayi su duka biyun banda Mairama da Ishaƙ da suke binsu da kallo cikin kullewar kai, ita dai Mairama tasan sunan Hajara da daɗewa amma kuma ya akayi yanzu ake batu akanta da mijinta bayan ance sunyi hatsari sun mutu?
Juyowa yayi ya ƙara kallon Ishaƙ da Khadijatu fuskarsa na zubar hawaye bai ƙara magana ba ya juya yabar ɗakin su Ammu na biye da shi.


***

Kuyi maleji da wanan dan Allah yau muna bikin yayana ne, amma in sha Allah zaku samu more ɗinsa da safe in sha Allah.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

    0000025000000

LAGOS, NIGERIA.

   Jifa yayi da takardun a gabanta, sanan ya zauna akan kujerar da ke kusa da ita, ya dafe kansa da hannunsa.
   "Har yanzu sakamakon gwajinmu abu ɗaya yake badawa Amrah cewar lafiyarmu ƙalau. Na gaji da ganin wanan sakamakon, zuciyata ta ɗokantu da son ganin gudan jinina yana yawo a duniya Amrah!
  Ko wani lokaci na kusance ki ji nake kamar na dasa ƙwaina a cikin mahaifarki, amma da wuta yayi ƙarshe sai labarin ya sha bam-bam wajen dawo min da abun da na dasa."
  Ya ƙaarasa maganar yana kallonta da runanun idanuwansa, kamar dai yana zarginta akan rashin haihuwarta ne.

    Hannayensa ta riƙe cikin nasa, tana shafawa, fuskarta ɗauke da tarin damuwa. Idan har akwai wani ƙalubale da take fuskanta a cikin rayuwar aurenta to bai wuce na rashin haihuwar da bata yi ba akan lokaci.
   Gaba ɗaya Aabidullah ya takurama rayuwarta, ko wata rana yini suke yana sasiƙarta kamar abincin cinsa, duk yanda ta so ya barta ta huta ya hanata hakan, abu ɗaya yake cewa shine ta yi ciki ta huta da shi, muddum ba ciki ta ɗaukar masa ba to ba zai barta tayi hutu koda na awa ɗaya ba ne muddum yana gidan.
   Lokaci mai yawa har mamakin son haihuwarsa ta ke yi, amma kuma ba wai abun mamaki ba ne idan tayi la'akari da iyayensa shi kaɗai suka haifa, ƙanwarsa da take bi masa kuma  ta rasu tun kafin ta girma. Iyayensa sun ɗauki soyayyar duniya sun ɗora a kansa.
 
  A tarihin Aabidullah Isma'il Mai tama, bai taɓa neman abu ya rasa ba, saboda mahaifinsa jinin sarauta ne, haka kuma fitaccen ɗan kasuwa ne, da yake da manyan jiragen ruwa da suke shigo masa da kaya, yana da ikon faɗa aji a duka yankin kudancin Nigeria, duk da jinin sarauta na gudana a jikinsa amma hakan bai hanashi neman aikin soja ba, wanda hakan bai masa wahala ba, kasancewarsa jajirtacce kuma ingarama da yake da kuzari sosai a jikinsa.
Sai dai abu guda da yake da shi wanda mutane suke shakkarsa baƙin miskilancinsa da kuma jiji da kai irin nasa, ƙarin daɗawa fuskarsa ba zakq taɓa ganin fara'a da walwala a cikinta ba, sai a wajen iyayensa shi ɗinma iyakarsa yayi murmushi amma ba dariya ba.
Abokinsa guda ɗaya ne Nabil wanda suka tashi tun ƙuruciya a matakin farko na makarantar gaba da firamare ɗinsu, alaƙarsu ta girmama har zuwa iyayensa yayin da Amrah ta kasance ƙanwarsa ce da yake nuna mata tsan-tsar soyayya, da basa jituwa da Amrah amma yau da gobe da kyautata masan da take yasa ya kamu da tsananin soyayyarta. Musamman da ta kasance kyakkyawa ajin farko komi nata ƙarshe ne wajen haɗuwa.
Aabidullah yana son abu mai kyau, yana son ace komi nasa mai aji ne, yana da alfahari a komi nasa.
Yana son yara da yawa, wani lokacin har mamakin kansa yake yanda ya damu da son haihuwa haka, wanda duka shekara ɗaya kenan da aurensu da Amrah ɗin.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana shafa kan hannunsa har zuwa fuskarsa "Ko mi lokaci ne Aabid. Na tabbata Allah bai manta damu ba, ni kaina ina son ganin gudan jininka saƙale a cikin marata." Ta faɗa tana shafa kan mararta.

Riƙe hannunta yayi yana kallon fuskarta "Amrah nifa na fara wani tunani daban akan haka!"
"Wani irin tunani kake Rabin raina."
Cusa kansa yayi akan wuyanta yana busa mata iskar bakinsa wanda ya sata jan zuciya "Idan har wanan watan baki ɗauki cike ba zamu fita India a miki dashen ƙwayar halitta ta. Dan na fara zargin raguwar mahaifa gareki da take tunkuɗo min da duk abun da na sa mata."

Baki ta buɗe da shirin yin magana, sai dai kafin ta samu damar maganar ya haɗe bakinsu guri ɗaya, yana cire mata duk kayan da ke jikinta yana wurgi da su.
Ido ta rintse cikin jin daɗi da zafin abun da yake mata, wallahi ita kam ta fara gajiya, amma bata da damar hanashi neman halak ɗinta. Bayanta banda ciwo ba abun da yake mata, anya kuwa zata ci gaba da jure wanan azabar?
Numfashinta ne ya ɗauke sanadin jin yanda jikinta ke buɗewa yana amsawa, idanuwanta ta buɗe fes akan Aabidullah da yake ta sasiƙarta yau babu lallami balle ya bi da ita cikin nutsuwa, ya zame mata kamar mayunwacin zakin da ya farmaki abinci.

"Kayi haƙuri Aabid da zafi!" Ta faɗa cikin runtse ido, bakinsa ya tauna yana kai hannunsa ƙasan ƙugunta ya ɗagota sama daga kwanciyar da tayi, yana cusa abinsa can cikin mararta.
Wani razanan nan ƙara ta saki jin azabar da ta tsarge mata har ƙwaƙwalwar kanta.
"Muddum baki amshi cikiba bazan taɓa ƙyaleki ba." Ya faɗa fuskarsa babu walwala ko kaɗan.
"Dan Allah kayi haƙuri! Ba ni zan bama kaina cikinba Aabid."
"Na sani! Shi yasa ni nake miki abun fa zaki same shi ai."
Hawayen ne ya zubo akan idonta, bata taɓa yardaba idan akace mata soja mugu ba ne, domin yanda Aabid ke kula da ita kamar uwa da ɗiyarta.
Ko da wasa baxata yarda ba idan akace mata zai iya mata wanan kalar muguntarba.
Ashe shi kansa aurenma wahala ne? Ko a cikin wanan abun za'a iya cutama ɗiya mace?" Ƙanƙametan da taji yayi da ƙarfi ne ya dawo da ita, tana ji yana sauƙe numfashi da ƙarfi yayin da axabarta yake ƙaruwa, nauyin da take ji a jikinta shi ya isa har cikin zuciyarta, tana ji kamar zata faso ta faɗo ƙasa.
Can kuma ya saketa ya hankaɗata gefe ya kwanta rigingine yana maida numfashi.
"Ina ji a raina yau na dasa ƙwaina a mararki! Lallai kada ki kuskure ki barshi ya bi muguji."
Harara ta aika masa duk da ba kallonta yake ba, tana ji kamar ta tashi ta rufeshi da duka ko ta ji sauƙin zafin da ke zuciyarta.
"Bari na zo na ƙara sai kiji daɗin hararata."

"A'a ba harararka nake ba! Dan Allah kayi haƙuri."
Tashi yayi ya sukuceta zuwa toilet ya sata a ruwa anan ɗinma saida ya mai-maita mata wata kalar azabar tana kuka tana roƙonsa akan ya ƙyaleta amma sai da ta jikkata sanan ya barta "Gobema ki ƙara hararata." Ya faɗa mata yana ficewa a toilet ɗin.

Kuka ta saki mai ƙarfi sai da tayi mai isarta sanan ta gasa jikinta, banda yunwa da gajiya ba abun da ke ɗawainiya da ita.



********

Kano Nigeria[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

   00000026000000

  "Inna waye wanan? Maganar wa su Ammu suke da Baba?"  Indo ta tambayi Mairama da tayi shuru tun bayan fitar su Ammu da Dakta Imran.
  "Inna ina jin tsoron kada ya cutar da su fa! Daga ganin mutum kawai sai su bishi har Kaduna."
  Ishaƙ ya amshi maganar fuskarsa cike da tsoron abun da zai iya zuwa ya dawo.
  Murmushi Mairama tayi tana shafa kan Indo da ke kusa da ita "Labarin yana da tsayi Indo, ni kaina ban san waye shi ba. Amma sunan Hajara da suka sa a maganar ya sa ni a cikin ruɗani, ƙanwar Babanku ne da ta rasu tun daɗewa."
  Ido suka fiddo waje "Ta rasu kuma Inna? To amma ya akayi suke tambayarsa ita?"

   "Amsar da nima nake son sani kenan Ishaƙ." Inna ta basu amsa cikin ƙosawa da tambayar da suke mata. Dan tashin hankalin da take ciki yafi gaban wanan tilin tambayar da suke mata.

  Shuru ne ya cika ɗakin bayan amsar da Inna ta basu, kowa na ƙullawa da saƙawa a ƙasan zuciyarsa na abun da zai iya faruwa a tafiyar su Baba da farin mutumin da nasu tan-tance matsayarsaba a garesu.

  Ƙofar da aka turo ta ɗakin da sallamar da ta biyo baya ita ta kawar da shurun da suka yi a lokacin. Cikin haɗuwar baki suka amsa sallamar banda Ishaƙ da bakinsa ya masa nauyi, ya gaza ƙarasa amsa sallamar.
   Mutumin da ya gani a gabansa ko a mafarkinsa baya jin zai manta da wanan fuskar. Domin itace fuska ta farko da ta taimaki rayuwar ƙanwarsa, ta nuna tausayawa da ƙauna a garesu tsawon lokaci.
   Duk da sauyin da yayi na hasken fata da murjewar jiki amma hakan bai hanashi gane kamilallan mutumin ba.
   "Likita!" Ishaƙ ya faɗa bakinsa har rawa yake.
  Shima ƙarasawa yayi kusa da shi yana kallonsa fuskarsa ɗauke da mamakin ƙara ganinsu a wanan lokacin.
  Kallon halittar da ke kwance akan cinyarsa yayi ta duƙunƙune shi tana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai.
  Idanuwansa ya rintse da ƙarfin gaske yana ƙara kallon yanda suka fita a kamaninsu da kuma irin baƙin da suka ƙara yi, duk da ya lura girma ya ɗan ƙara kama Ishaƙ ɗin, amma bai wani yi jikiba, asalima ya gaza akan sanin da ya musu a baya.
  "Ishaƙ ku ne?" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa da take fita da ƙarfi.
  Kai Ishaƙ ya gyaɗa masa bakinsa ya kasa motsawa yayi magana.
  
   "Kana so kace min har yanzu Khadijatu bata samu lafiya ba?"
  Murmushin gefen baki Ishaƙ yayi "Eh Likita?"

  Kansa ya dafe da ƙarfin gaske, yana jin ɗaci a ƙasan maƙoshinsa "Duka tsawon shekarar nan da aka ɗauka tana fama da wannan larurar, ya akayi haka Ishaƙ?"
  Hannayensa ya wara kana ya murza babban yatsansa da manuniya "Saboda bamu da masu ikon faɗa aji Likita. Bamu da wanan gumbar susar da ke sanya himma da hanzari a tare da mu."
   Kansa ya girgiza yana shafa sumar kansa da hannunsa. Yana kallon Khadijatun da har lokacin take maƙale da Ishaƙ ɗin.
  "To yanzun me ya faru da ita, naga tana maƙale da kai kamar za'a ƙwace maka ita?"

   "Shima dai tun wanan matsalar farkon da take fama da ita ne, na yawan tsorata da zabura, da kuma tsoron mutane da  hayaniyarsu."
  Ido Dr. Anwar ya fiddo waje "Kana so kace min shima ɗin bata rabu da shi ba?"
Kai ya gyaɗa masa kawai ba tare da yayi magana ba.
  Zama yayi a kujerar dake fuskantarta, yana gyaran murya, hakan ya sata ƙara cakumar rigar Ishaƙ, jikinta yana ƙara karkarwa.
Tashi yayi ya fita bai jimaba ya dawo da wasu nurse's suka fita da ita akan keken tura marasa lafiya, duk da tana miƙewa da yin ihu.

****
Bayan sa'a guda.

Shuru Dakta Anwar yayi yana kallon Ishaƙ da ke zaune a cikin office ɗinsa, ba tare da yayi magana ba amma yanayin zaman da yayi ya nuna cewar a mutuƙar takure ya ke.
Gyaran murya Dakta Anwar yayi wanda yasa gaban Ishaƙ mummunan faɗuwa.


"Ina baku haƙuri Ishaƙ domin bincike da dukkan alamun da muka duba sun tabbatar da cewa knawarka ta sami wata 'yar karamar matsala a kwakwalwarta."

A zabure Ishaƙ ya miƙe tsaye cikin firgici da salallami yana dafe fa ƙirjinsa da yake jin kamar zai faso daga ƙirjinsa "Tabin hankali kake nufi likita ko me!? Dan Allah kada kace min ƙanwata ta haukace Likita, kada kace min Khadijatuna ta samu taɓin hankalin da bata da maraba da mahaukata!" Ya ƙarasa maganar hawaye na sauƙa akan kuncinsa.

Kai Dakta Anwar ya girgiza masa "Kar ka tashi hankalinka sosai Ishaƙ, idan ance larura a kwakwalwa ba wai yana nufin shi kenan babbar matsala bace ko tabin hankali ya sami mutum a'a ba haka bane, mutaanen mu ne suke dauka a haka, amma akwai matsaloli da larurori da suka danganci kwakwalwa wanda da yawanmu suna fama dashi ba tare da masaniyarsu ba, sbd karancin wayewar kai a ilimi na wannn fannin ne mutane da yawa ba su sani ba,  tunaninsu matsalar kwakwalwa larura ce kawai ta masu tabin hankali.

Kar ka damu kanka larurar kanwarka ba wani babba bane sosai, Post traumatic stress disorder(PTSD) shine abin da na faahimci yana damunta.

PTSD larura ce da take shafar wanda wani mummunan lamari ya faru dasu a rayuwarsu, kamar misalin ace wani wanda kake matukar so ya mutu a gabanka dalilin hadarin Mota, ko ya fado daga sama wuri mai nisa naan take ya mutu, ko kuma irin wanda aka yiwa fyade ta karfin tsiya. Kamar yadda ya sami kanwarka. Irin wann hadarin idan ya faru yakan zama barazana ga ainihin tunaani daa lafiyar kwakwalwar wanda abin ya faru akansa, za su rinka yawan tunano abin, yawan tunanin kan sanya su yawan firgici, tsorata, mugayaen mafarkai rashin yarda da mutane, cin abinci ma kansa yana gagararsu a wasu lokutan.

Sukan koma ware kansu da kebewa daga shiga cikin jama a, suna yawan zama cikin damuwa da tunani wanda ke haifar musu da bacin rai, gami da kyamar kansu idan abin yayi kamari barci ma yakan gagaresu."

Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, 'Tabbas kusan duk wadan nan alamomin sun fara bayyana a tare da kanwarsa.' Ishaq ya raya a zuciyarsa.

Dakta Anwar ya ci gaba da cewa "Kawai babban abin da kanwarka  tafi bukata fiye da komai a rayuwarta yanzu shine tsantsar kulawa, tana bukatar kulawa ta sosai ta hanyar kirkiran abubuwa da za su rinka sanya ta farin ciki, da kokarin mantar da ita abin da ya faru a baya, a takaice dai kulawar da take bukata muna kiranshi da *Psychotherapy* (talk therapy) da kuma *cognitive behavioural therapy* wato hanyar da za a bi wajen kokarin ganin an canza mata yadda take tunani akan al amarin da ya faru, da kuma kokarin dawo da d'abiunta zuwa daidai. Yawan tsoro da firgicin da take ya zama ta daina su.

Amma fa lallai wannn aikin ba na lokaci guda bane, abu ne da yakan dauki lkc kafin a samu ta dawo daidai kamar yadda take gudanar da rayauwarta da."

"Amma Likita babu wani maganin da za'a bata ta warke dole sai ta wanan hanyar kaɗai?"

"Akwai maganin da ake ba dawa amma ita zai iya yuwa a shekarunta magungunan su zama sunyi mata karfi, don ko ga manya ma ba magani ake fara ba su ba, sai dai akan hadasu da therapist ne wanda zai rinka ba su kulawa da support din da ya dace mu anan Nigeria ne ba mu da ci gaba ta wann bangaren."

"Ta ina zamu samu wanan likita, waye zai taimaki ƙanwata ya bata wanan kulawar da kake ta magana?"

Kai Dakta Anwar ya shafa wanda hakan ɗabi'arsa ce "Eh to! masu ba da irin wann therapy din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login