Showing 39001 words to 42000 words out of 91747 words
mental health professionals ne wato wadanda suka kware akan fannin da ya shafi lafiyar kwakwalwa.
Zai iya kasancewa kuma ɓangarena ne da kuma Dakta Imran, shima ƙwararre ne ta wanan fanni, ita tana a matsayin majinyaciyarsa ne, dole mu jira idan ya zo sai muyi masa magana muga yiyuwar abun da za'ayi."
Risinawa yayi har ƙasa yana godema Dakta Anwar daga nan ya fice a office ɗinsa cikin sanyin jiki.
Zuciyarsa cike da ruɗani da gajiyawa 'Ko har zuwa yaushe ne zamu rabu da tulin matsalolin rayuwarmu ?' Tambayar da yayima kansa kenan yana kara kansa a jikin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Khadijatu, hawaye na sauƙa a kwarmin idanuwansa.
'Me yasa wanan abun da Khadijatu ya faru ba shi ba?' Inama zai dawo da hannun agogo baya da ya share komi da ya faru aranar ya dawo da shi kansa......'
🌷🌷🌷🌷🌷
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
0000000270000000
Sai da ya ɓata lokaci mai tsayi a jikin ƙofar, kana ya share hawayen fuskarsa ya tura ƙofar ya shige ɗakin.
Gadon da Khadijatu ta ke yaje ya tsaya yana shafa kwantaccen gashinta hawayen da bai san na miyeba suka ɗigo akan ƙwayar idanuwanta da suke rufe.
"Subhanallahi! Ishaƙ kuka kake fa! Me ne abun kuka a cikin wanan ciwon, bayan hanyoyin waraka sun fara samuwa?" Inna ta faɗa cikin faɗa dan bata son ganin yanda yake zubda hawaye agaban Indo da bakinta bai da sakata.
Kai ya girgiza "Har yanzu hanyar waraka bata ɓulleba Inna da saura! Wani sabon shafi na ƙaddarar Khadijatu ne ya sake buɗewa a yau.
Ashe duka tsawon shekarar nan da Khadijatu ke firgita da tsoron mutane ƙwaƙwalwarta ce ta taɓu? Inna Khadijatuna tana fama da ciwo a kwanyarta wanda kaɗan ya rabata da mahaukata. Likita ya faɗa min hakan ba hauka bane, amma ni banga ban-bancin dake tsakaninta da su ba."
Durƙusawa yayi akan gwuiwoyinsa yana ƙara sautin kukansa "Inna na gaza cikama Ammy alƙawalin dana ɗaukar mata na kula da Khadijatu? Na gaza zame mata Inuwar gajimare a cikin duniyarta! Na gaza bata inuwar da zata raɓe a ciki na samar mata da yayyafin sanyi a zuciyarta! Me yasa kuskure ɗaya tak na rayuwa kan caccaki ruhi har tsawon shuɗewar zamani? Anya Khadijatu zata yafe min kuskuren barinta da nayi?"
Kansa ya kifa a jikin gadon sautin kukansa na ƙara ci gaba da ƙaruwa.
Daga Inna har Indo kowa kuka yake a cikinsu, kalaman Ishaƙ ya datse musu ƙarfin gwuiwar zuciyoyinsu, ya caccaki ruhinsu da zallar karaya da kuma tausayawa mutnen da suke gabansu.
Da ƙyar Inna ta iya tashi daga kan sallayar da take ta ƙarasa kusa da Ishaƙ ɗin ta ɗaga shi daga tsugonnen da yake. Hannayensa ta riƙe ta janyoshi har kan tabarmar da ke shimfiɗe a ɗakin, itama ta zauna ta ɗora kansa akan cinyarta tana shafa kan nasa a hankali, yayin da yake ta faman jan zuciya.
"Rayuwar da ta zo ta wuce cikin ƙalubale da kuma tawaya ba zaɓinmu bane Ishaƙ! Idan Imaninka ya zama cikekke sai jarrabawarka tayi tsanani, ta yanda Allah zai gwada ma'aunin imaninka yaga zaka ci gaba da haƙurin nan ko kuwa zaka butulcewa ni'imar da yayi maka.
Abun da ya faru ga rayuwar Khadijatu ba kuskurenka ba ne Ƙaddararta ce ta zo a haka. Koda ace a wanan lokacin kana nan to bazaka iya sauya mata wanan ƙaddararba.
Haka kuma ciwon da ke kwanyarta ba yana nufin ya samu muhalli na har abada ba ne, ko wani ciwo da maganinsa, iyaka muyi addu'a mu sanya yaƙini akan Allah zai amsa mana addu'ar da muke yi.
Ina ji a raina Khadijatu zata samu lafiya, zata yi rayuwarta kamar sauran mutane. Ka kwantar da hankalinka ka tayata neman lafiyarta ta hanyar bata kulawa, ba wai ka narkar da zuciyarta ba wajen yin kuka a gabanta."
Kai ya iya gyaɗawa ba tare da yayi magana ba, saboda yawun dake bakinsa ya riga da ya ƙafe masa tun farko. Ciwon da ke kansa ma kaɗai ya ishesa garƙame bakinsa yayi shuru.
"Allah ya baki lafiya Khadijatu!" Indo ta faɗa cikin rawar murya ta wanda yasha kuka ya ƙoshi.
"Ameen." Duk suka amsa a tare.
*****
KADUNA, NIGERIA.
Tun da suka shiga tamfatsetsen gidan jikin Ammu ya fara rawa, shi kansa Baba jikinsa ya fara saki, kansa ya ɗaure da ganin duniyar da suke ciki.
Gari guda a matsayin gida ta ina Abdallah ya samu wanan dukiyar haka? Gaza haƙuri Ammu tayi ta tsaya ta coge daga harabar gidan "Nifa daga nan bani ƙara koda taku ɗaya ne Ado!" Ta faɗa cikin dakekkiyar muryar da take tunanin ta ɓoye tsoron dake cikin zuciyarta.
"Me yasa Inna?" Baba ya tambayeta duk d shima zuciyarsa cike take da tsoron.
"Yo kai makaho ne da zaka tambaye ni dalili? Ko kuwa baka da lissafi ne? Kana ganin wanan tamfatsetsen gidan gari guda kace mu ci gaba da cusa kanmu, kasan inda ya kawo mu ne?
Aradun Allah bani matsawa daga nan, kawai yaje ya fito min da ɗiyata shine kawai bayani ihe!" Ta ƙarasa maganar tana riƙe ƙugunta bakinta fal bala'i da kumfa.
"Dan Allah Inna ki yi haƙuri ki zo mu shiga. Wallahi babu wanda zai cutar da ke, asalima bamu da alaƙa da masu cutarwa." Imran ya faɗa cikin sanyin muryarsa.
"Affa farandai! Yaro banifa shiga wanan ƙasurgumin gidan, ka je ka cema Hajara ta fito mu gana tunda ita bata nemi niba, ni gani nazo ganinta da kaina."
Shuru yayi bai ƙara magana ba bai kuma motsa daga tsayuwar da yayi ba.
"Ba da kai nake ba Abdallah?"
"Dan Allah Ammu ki zo mu shiga daga ciki zaki samu duk abun da kike son sani akan Hajara."
"Nifa ba Inda zani."
"Ammu dan Allah muje muga abun da yake son nuna mana." Baba ya tareta da maganar jikinsa duk yayi sanyi ganin halin da Abdallah ya shiga a lokacin.
Bata ƙara magana ba ta bi bayansu a fusace ammafa zuciyarta na luguden faɗuwa ko wata laka ta jikinta babu kuzari, a haka suka shiga har ainihin babban falon da ke gidan.
Tunda suka shiga wani sanyi ya musu kyakkyawan maraba, sai mutanen da suke fuskantosu a gabansu, a zaune a cikin ɗima-ɗiman kujerun da suka zagaye falon.
Kallonsu Ammu tayi ta kalli Abdallah wanda bai da maraba da halittun da suke gabanta a yanzu.
Shima Baban mamaki ne ya cika shi 'Ta ya Abdallah da ya sani da bai da tsuntsu bai da tarko ya samu waɗan nan mutanen masu tsananin kama da su?' Ya aiyyana a cikin ransa.
"Ku zauna Ammu." Imran ya faɗa yana nuna musu kujerar sa ke fuskantar mutanen da ke gabansu.
Zama tayi a cikin kujerar da ke shirin lotsawa da ita ciki, hakan ya sata zabura ta zauna akan kafet ɗin da ke malale a falon "Nanma ya wadatar. Ina Hajarana ta ke?" Ta faɗa ganin yana shirin yi mata magana.
Kansa ya juyar zuwa ga Umminsu da tun kiran da yayi mata a waya hawaye bai bar zuba akan idanuwanta ba, wanan shine dalilin da yasa ta kira duk yaranta suka zo gidan.
"Ummi tana son sanin inda ɗiyarta take! Ummi uwa da kanta tazo biɗar ɗiyarta! Ranaku dubu ne suke ɗauke da rashin adalci a cikinsu, ɗaya ce tak take zuwa ta wanke dattin da ya cika yayi male-male a cikinta.
Ba'a datse igiyar ƙaddara shi yasa sanadinta yake da mutuƙar yawa."
Kukan da ta riƙe ne ya ƙwace a bakinta, wanda hakan ya tada hankalin duka yaranta da suke palon.
"Imran me yasa kai abu baya wucewa a wajenka ne? Wananfa duk ya faru ne saboda ɗan ƙaramin kuskuren da akayi a baya, amma yanzu ka zo ka tada mata hankali, fisabilillahi me yasa kai baka basu amsarsu ba har sai ka kawo su nan?"
"Anty Aisha idan ya wuce ni a wajenta to su kuma iyayenta da basu san asalin labarinba fa? Me ne ɗan ƙaramin kuskuren da kike faɗa a cikin dukkanin abun da son zuciya ya wanzar da shi? Ta ina zan iya bada labarin butulcin da ya maye gurin alkhairi da kyautatawar da suka min? Dattin hannuna bai kai wajen nan ba, dole ita da ta ƙirƙiri labarin ta kawo ƙarshensa."
"Wai me ke faruwa anan ne Abdallah? Me yasa suke kiranka da suna daban da wanda muka sanka da shi? Su waye waɗan nan mutanen masu kama da kai? Ina ƙanwata ta ke?" Baba ya faɗa cikin ƙosawa da jin raɗaɗɗiyar maganarsu marar kan gado.
Zubar da gwuiwarsa Imran yayi ƙasa, yana sunkuyar da kansa ƙasa a gaban Baba "A duk rayuwata ban taɓa jin abun da ya kai ƙarya kunyatarwa ba! Ban taɓa ɗauka za'a sake samun labarin cin amana irin wanda aka samu a tare da ni ba!
Na yi kuskuren musauya yarda da kuka min da butulci! Nayi kuka akan son dawo da kuskuren da nayi baya amma hakan ya gagara a gareni.
Har yanzu ina girbe kuskuren da nayi a rayuwata! Hakkin da na ɗauka naku kaɗai ya isheni."
"Dan Allah anan wani ya faɗa min abun da ke faruwa. Raunatacciyar zuciyata mai ɗauke da shekaru ta gaza gane inda maganarsa ta ƙunsa. Dan Allah ku fidda ni a cikin wanan duhuwar." Ammu ta faɗa tana baza idanuwanta akan mutanen falon.
Ido Anty Aisha ta rufe sanan ta buɗe hawaye na biyo bayansu "Wanan dake gabanku sunansa Imran ba Abdallah da kuka sani ba. Mu yayunsa ne ga kuma mahaifiyarsa, Abbanmu kuma baya ƙasar ya tafi india wajen duba lafiyarsa.
Shi ba maraya ba ne kamar yanda kuka sani, haka shi ba talaka bane gama gari kamar kowaba.
Asalima shine IMRAN YASIR NASAR Minister lafiya na ƙasar Nigeria, mamallakin kamfanonin kayan alatu da na masarufin da suke arewacin ƙasar nan. Duk wani abu da ke ɗauke da tambarin Imran yasir nasar nasa ne."
Daga Ammu har Baba miƙewa sukayi tsaye suna dafe da ƙirjisu da yake tsananin bugawa "IMRAN YASIR NASAR?" Suka faɗa a tare kasancewar sanannen sunane da ko yaushe ake magana akansa, har zuwa janyewar da yayi a bakin aikinsa.
🌷🌷🌷🌷
Girmamawa
Oum-nass
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
00000028000000
Jikin Ammu ne ya shiga karkarwa tana kallon Imran da ke gabanta a tsugunne kansa a ƙasa hawaye na bin kuncinsa "Me yasa ka mana ƙarya? Me yasa ka ɓoye mana matsayinka tun a wancan lokacin? Idan kai ne Imran me yasa ka zauna a garinmu ka siye zuciyoyinmu da yardar da muka baka? Ina Hajara? Hatsarin da akace kunyi shima duk ƙirƙira ne kenan?"
Zama tayi daɓas akan kafeta ɗin da ke palon "Ta ina Hajara zata tuna damu bayan ta riski kanta dumu-dumu a cikin wanan daular?"
"Hajara bata taɓa mantawa dakuba dai-dai da rana ɗaya tak a duniya. Kullum maganarta akan Ammu ɗinta! Kullum tuhumata take akan rufe mata asalina da nayi.
Ni kuma nayi hakan ba dan na ci amanarku ko ha'intarku ba ne, nayi haka ne dan na samarwa kaina macen da zata soni dan Allah, matar da zata ji tausayina a cikin halin talauci ita da iyayenta wanda basu da kwaɗayin abun duniya.
Na auri mata aƙalla guda huɗu amma ko wacce a cikinsu dukiyata da rayuwata take farauta, watama kwangilar rayuwata aka ɗaura da ita ta shigo a matsayin matata.
Wanan dalilin yasa na ajiye komi nawa na yi nisa da wanan yankin, na yada zango a garinku, har Allah ya haɗani da Hajara.
Duk a cikin rayuwata ban taɓa haɗuwa da macen da nake so ba kamar Hajara, wanan dalilin yasa na sha wahala wajen shawo kanta, da ƙin saurarata tayi har sai da nace mata ni maraya ne, wanan dalilin ne yasa ta fara kulani, daga haka kuma ta gabatar da ni a wajenka.
Da hannunka ka nema min sana'ar yi a garin, ka samar min yaron mota ba tare da ka san waye ni ba, ka ɗauki ƙanwarka ka danƙamin ita a hannuna, ka nema mana gidan hayar da zamu zauna da kuɗinka.
Dai-dai da rana ɗaya ban taɓa manta halaccin da ka minba kai da 'yan uwanka, lokuta masu yawa sai nayi kamar naje na faɗa maka abun asalin ko ni waye, amma kuma na gagara, inajin kunya da nauyin ƙaryar da na maka.
A cikin haka ne aka kirani a waya aka sanar dani ma'aikatar lafiya ta ƙasa tana son ganina a garin Abuja, Zaman da zai iya kai ni ƙasar waje dan ƙara horo akan wani abu da ya shafi ɓangaran lafiya. Wanan shine dalilin da yasa nace maka na samu aiki zamu komo kano da zama, nayi mamaki lokacin da ka amince min muka taho ba tare da ka tsaya dogon nazari akaina ba.
Har tasha ka rako ni, daga nan muka ɗauki hanyar kano, bamu fi gumel ba na ce a tsaya a lokacin motocin da za su ɗauke ni sun zo, muka hau mota muka tafi.
Muna gaf da shiga Abuja mota ta ƙwacema direban da ke janmu, birkin motar kuma ya tsinke nan take mukayi hatsarin mota. Ikon Allah ne ya fidda mu lafiya a wancan lokacin aka kaimu babban asibiti, rashin sa'ar da akayi hajara ta bugu a cikin ƙwaƙwalwarta ta manta duk abun da ya shafi rayuwarta na baya."
Kuka ya ɓalle a idanuwansa ya tsaya yana jan numfashi da ƙyar, suma su Ammu kuka suke jin Hajara ta dawo matacciya.
"Komi na rayuwarta ta manta shi. Kasancewar ni ban bugu sosai ba nine na dinga shan fama da ita da koya mata komi na rayuwa har ta gane mene matsayina a wajenta.
A cikin haka ne ƙarin karatuna ya kaini ƙasar india muka tafi tare da ita, munyi shekara biyu acan har ta haihu acan, muka samu ɗa namiji, da kanta ta zaɓi suna ta raɗa masa ISHAƘ. Daga nan muka dawo gida Nigeria mu kai tsaye nan gidan muka zo dan na gabatar musu da matata da kuma ɗana, dan suma har a lokacin basu san nayi aureba duk da muna yin waya da su akai-akai har lokacin da ina India.
Tarbar da muka samu bata mana daɗiba mu dukanmu, domin Ummi har korata tayi tana cewa ta yafema duniya ni saboda yanda nayi gaban kaina, ban tashi zuwa mata gidaba sai da mata da ɗanta. Ƙarshe bata yarda cewa aure mukayi ba tafi yarda karuwanci ta haɗamu."
"Inna lillahi wa inna ilahirraji'un!" Mutanen falon suka ɗauki salati a tare. Yayin da kunya ta gama lulluɓe Ummi tana ji kamar ƙasa ta tsage ta shiga cikinta.
"Ba irin magiyar da ban mata ba akan ta tsaya ta saurare ni amma fur taqi yin hakan.
Gidan Anty Aisha naje na kirata saboda ita tasan komi na rayuwata bana ɓoye mata komi da ya shafeni, da kanta tazo ta yima Ummi bayani amma a lokacin bata yardaba, ƙarshe sai guzurin kyawawan maruka ta bama Anty Aisha ta kirata da sunan munafuka maƙaryaciya da ta siye ƙarya da mugun bakinta.
Ranar nayi kuka sosai, domin Hajara sai tambayata take me ya faru ne, dan har a lokacin bata iya magana sosai, ciwon da yaci ƙarfinta ya gaza bata damar yin kuzari da walwala kamar farko.
A haka muka shafe shekara da Ummi ta ƙi amsar Hajara a matsayin surukarta, tana kiranta da marar asali, wani lokacin sai dai na ɗauketa na kaita gidan Anty Aisha idan zani wajen aiki.
Daga ƙarshe Ummi ta hanani kaita ko ina, ta zaunar da ita ƙarƙashin mulkinta tana yanka mata azaya dai-dai ikonta. Ba zan iya faɗa muku abun da ya wuce haka ba, saboda ban taɓa ganin haƙuri irin na Hajara ba, duk abun da Ummi ta mata bata taɓa faɗa minba, asalima sai dai tace min ba komi.
Na sha ritsata a ɗaki ita da Ishaƙ tana kuka yana kallona amma idan na tambayeta sai tace ba komi.
Sai da Ishaƙ ya shekara biyar bata ƙara haihuwa ba, ganin hakan yasa Ummi taje ta nema min auren Fatima ɗiyar ƙanwarta ni ban saniba, sai gani nayi ana shirye-shiryen aure, ban kawo akan nawa ba ne, nima naci gaba da sabgata.
A lokacin ni hankalina ya karkata akan nemawa Hajara magani dan na kaita wajenku, ina jin tsoron sanar daku halin da ake ciki. A kuma tsakankanin nan tana da shigar ciki na wata biyar su kansu su Ummi basu sani ba.
Ranar ɗaurin aure naji ance aurena aka ɗaura da Fatima, bayan ko kamanninta ba zan iya tan-tancewa ba a lokacin.
Ranar nasha ƙunci sosai, ƙarshe da tafiya ta kamani na ɗauki Hajara muka tafi ƙasar maroco dan taron ƙara sani na na manyan 'yan kasuwa masu ma aikata, acan muka tsaya har bayan ta haihu ta haifi ɗiyarta mace bayan shekara ɗaya muka dawo.
Dawowar da ta zame mana ƙaddarar rabuwa da juna, domin tun lokacin Ummi ta kafa min doka akan ko kallon Hajara nayi bata yafe ba, auren da ta ɗaura min kuma babu mai warwareshi ko mugun kallo nayima Fatima bata yafe ba.
Rayuwar Hajara da ta yaranta ta zame mata sabon kurkuku a garesu, lokaci mai yawa takan haɗa kan yaranta tana kuka suna tayata wani lokacin ina ji tana haɗa sunan Ishaƙ dana ƙanwarsa waje ɗaya, musamman idan tana musu wasa. Su uku suke rayuwarsu a gidan basa jin daɗin kowa domin yanda Ummi ta kafa ta tsare, ta