Showing 72001 words to 75000 words out of 91747 words

Chapter 25 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

794

yasa 'yata ta mutu! Idan har na ci gaba da zama da kai wata rana zaluncinka kaina xai dawo nima a farmin kamar yanda aka farma ɗiyata.
Aabid bazan iya zama da kai ba a yanzu! Wallahi zuciyata ta riga data tsaneka, duk sanda na ganka sai na ganka a matsayin makashin da ka kashe min 'yatah."

Kai ya gyaɗa mata hawayensa na ƙaruwa, lokacin har su Dad da Mom sun fito jin hayaniyarsu, sai dai abun da suka ji Amrah na faɗa ya kashe musu jikinsu.
Hanya Aabid ya nuna masa da hannunta "Kije Amrah! Kije gida. Ba zan hanaki tafiya ba Amrah, sai dai ba zan iya sakinki ba."
"Aabid idan na tafi ba zan dawo ba, ka bani takardar sakina." Ta faɗa cikin hargowa.

Kai ya girgiza mata yana jin bugun zuciyarsa na tsananta saboda tashin hankalin da yake ciki, ba kinsa ne ya shiga rawa amma kuma ya kasa magana, hakan ya sashi ya juya yabar palon gaba ɗaya ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofar.
Jan jakarta Amrah tayi hawaye na xuba akan fuskarta, ji take kamar ta bar wani sashe na rayuwarta a wajen, wata zuciyar na gargaɗinta akan ta zauna, sai dai wani sashi na zuciyarta na hango rashin yiyuwar zamanta a gidan, dan tsaf takaicin Aabid zai haddasa mata bugawar zuciya.

Da sauri Mom ta bita tana kiranta amma bata tsaya ba, sai ƙara saurin tafiyarta da tayi tana girgiza kai tana kuka. Yayin da Dad yabi bayan Aabid sai dai yana murɗa ƙofar ɗakin yaji ta a rufe gam, bugawa ya shiga yi da ƙarfinsa amma kamar ba ya jin motsin kowa, a hankali ya kara kunnensa a jikin ƙofar ɗakin anan ya jiyo shesshekar kukan Aabid ɗin.

"Aabid ka buɗe min ƙofa." Dad ya faɗa da sigar lallashi amma kamar bai ji ba. Komawa yayi da sauri ɗakinsa ya lalimi wani mukullin ya buɗe ɗakin yana shiga yaga Aabid kwance akan kafet yana fidda numfashi sama-sama.
"Aabid me ya faru da kai?" Dad ya faɗa cikin tashin hankali.
"Hakki ne ke bibiyata Dad. Dan Allah ku je ku roƙa min yafiyar Khadijatu, ku bata haƙuri, na tabbata idan ba yafe min tayi ba rayuwata ba zata dawo dai-dai ba."

"Zamu je Aabid! Ka tashi ka yi wanka yau ɗinnan zamu je ba sai gobe ba da yardar Allah."
Yan jin haka ya tashi ya shige toilet cikin abun da bai gaza awa guda ba duk suka shirya har Mom suka tafi Air port, tuni dana an musu bukin ɗin jirgi suna zuwa suka shiga suka ɗauki hanyar Kaduna ....


🌷🌷🌷🌷
Ina dai ƙara baku hqr akan err da ake ta samu, saboda rashin wadataccen lkcn da nake da shi. Ngd da lkcnku.

GIRMAMAWA
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG.....


  5100000

Zame jikinta tayi daga rungumar da Ishaƙ ya mata, a hankali ta fara taka ƙafafuwanta zuwa gaban Aabid ta harɗe hannayenta biyu akan ƙirjinta "Kace me ne?"

"Kin haƙura zaki aure ni ?"
  Murmushi ta yi wanda kumatunanta suka lotsa "Inda ace duniya da mutanen cikinta za su ƙare, ya zama cewa a cikin wanan duniyar ni da kai ne kaɗai suka rage, ina baka tabbacin bazan aureka ba Aabid.
  Ban taɓa cin karo da wata halittar da nake ƙyamata da tsanarta ba fiye da taka halittar. Da ace babu hisabi akan hukuncin kisa to da nice zan zama ajalinka.
   Na yafe maka ne saboda yayana yace na yafe maka! Duhun da ya fice a cikin rayuwata ya tashi ya mamaye hasken da ke cikin duniyarka. Wanan itace nasarata, shi yasa banji buƙatuwar sake ganin mummunar fuskarka a gabana ba, shi yasa na yafema dan na huta daga kallonka.
  Dan Allah kada ka sake bayyana min fuskarka a gabana! Indai har da gaske yafiyata kake nema ba wai wani abu daga gareni ba. Bana sonka Aabid! Bana son ko da mai irin sunanka ne maa."

   Kai ya gyaɗa hawaye na zuba akan fuskarsa, yana jin zuciyarsa na tsananta bugawa. A iya rayuwarsa ta duniya bai taɓa jin abu mai ɗacin da ya tsaya masa a maƙoshinsa ba sai wanan.
  Ashe haka mutane suke ji idan suka rasa abun da suke so a rayuwarsu "Shikenan Khadijatu, zan fita a rayuwarki, zan ɓoye fuskata daga gareki kamar yanda kika buƙata.
Nagode da yafe min da kikayi! Nagode da kyakkyawan lokacinki da kika ɓata a tare dani."
  Yana gama faɗar haka ya juya ya fice a falon, hakan yasa iyayensa bin bayansa da sauri.
  Shima Abbie Yasir tashi yayi yabi bayansu a harabar gidan ya taddasu, sun kewaye Aabid da yake dafe da saitin zuciyarsa.

   "Dan Allah kuyi haƙuri akan abun da ya faru. Ni kaina banji daɗin abun da ta muku ba, da ina da iko akan hana faruwar al'amarin to da ban bari ta faɗa ba.
  Na so ƙwarai ace kune kuka bayyana  a gabana a farkon lokaci, to da babu abun da zai hanani na bawa Aabid auren Khadijatu. Sai dai kuma kun makara, waninku ya riga isar da neman aurenta a gabana."

  Tari ne ya tasowa Aabid jin abun da Abbie Imran ya faɗa, tari yake sosai yana ruƙe da saitin zuciyarsa, da yake ji kamar zata faso masa.
  Kafin wani lokaci jini ya fara zuba a hancinsa da bakinsa "Aabid!" Dad da Mom suka faɗa a tare cikin tsananin tashin hankali.

   Shi kansa Imran hankalinsa yayi kyakkyawan tashi, kamashi yayi suka sashi a mota suka nufi asibiti da shi.
   Likitoci suka tarar masa akai, yayin da hankalin Imran yayi mummunan tashi, gani yake kamar shine silar faruwar al'amarin nan.

   Duk da yana a matsayin likita amma bai iya taɓuka komiba, sosai yaron da iyayensa suka bashi tausayi "Ɗanmu ɗaya tak a duniya! Dan Allah ku ceci rayuwar yarona kada ku bari ya mutu. Idan ya mutu nima wallahi mutuwa zanyi." Mom ta faɗa tana kuka kamar ranta zai fita.

   Bayan a wanni biyu.

Dukansu sunyi jugum-jugum a gaban likitan da yake ta faman rubuce-rubuce, sai da ya gama sanan ya ɗago da idonsa ya kalli Imran "Naji mamaki sosai a tare da kai Imran! Duk da kana a matsayin babban likita amma ka yi sake yaronka ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani.
  A buncikenmu wanan ne karo na biyu da hakan ta faru da shi, idan har hakan ta sake faruwa gaskiya sai dai kuyi haƙuri.
  Ku  nema masa abun da yake so tun kafin lokaci ya ƙure muku."
  Haka ya gama maganarsa cikin faɗa yana ji kamar ya kwakkwaɗai su da mari ko ya huce takaicinsa a kansu.

  Shuru ne ya karaɗe ɗakin har zuwa wani lokacin daga bisani suka fice suka bar masa office ɗin nasa.
Kai tsaye gida Imran ya wuce yana zuwa ya kira Ishaƙ da Khadijatu, bai musu dogon bayani ba yace su biyo shi.
  Bin bayansa suka yi ba tare da sun tambaye shi ba, sai dai hankalin mutanen gidan ya tashi ƙwarai musamman yanayin da suka ganshi a ciki.
  Bayan futarsu kai tsaye motarsa suka shiga a hanya ya kira Nabil yana ɗagawa yace "Ka same ni a asibitina yanzu." Daga haka ya datse wayar.

  Shigarsu asibitin tayi dai-dai da zuwan Nabil ɗin.
  "Muje." Ya faɗa yana gaba suna binsa a baya, da hannu Nabil ya ke tambayar Ishaƙ me ya faru? Kafaɗa ya ɗaga masa alamun bai sani ba shima.

   Bai tsayar da su a ko ina ba sai a ɗakin da Aabid ya ke kwance an sa masa majanyin iska a hancinsa da bakinsa.
   Ga jonin ruwa a hannunsa "Aabid! Me ya faru da shi?" Nabil ya faɗa cikin tashin hankali yana ƙarasawa wajensa.
"Kasanshi ne?" Imran ya tambaye shi.

Kai ya ɗaga cikin tashin hankali "Nasan shi Abbie. Abokina ne tare muka yi makaranta, haka mijin ƙanwata ne.
Me ya kawo shi garin nan yana legos? Shi da wa ya zo? Me ke damunsa?"

"Ciwon zuciyarsa ne ya tashi!"
"Ya Allah! Me yasa kake da sa abu ne aranka Aabid? Ban san yaushe ne ya koyi ruƙe abu a ransa haka ba Abbie." Ya faɗa hawaye na taruwa akan fuskarsa yana shafa kan Aabid da bai san me ake ciki ba.

"Naji daɗi da ka sanshi haka Nabil! Domin ina tunanin ba zan sha wahala wajen warware matsalar da ke damunsa ba.
A yanda ka nuna sanayya a kansa na tabbata kasan dalilin da ya sa ya shiga wanan matsalar."

Kai Nabil ya girgiza "Anyima Ɗiyarsa fyaɗe wanda hakan yasa ta mutu Abbie. Ya faɗa min shima ya taɓa yima wata fyaɗe ya nemi yafiyarta yana sonta zai aureta, wanan dalilin yasa ƙanwata barin gidansa ta dawo gida jiya.
Amma nasan Aabid ba mutumin banza bane, duk abin da ya faru da shi tabbas ƙaddara ce. Amma hakan ba halinsa ba ne."
"Kasan yarinyar da yayima fyaɗen?"

Kai Nabil ya girgiza yana ji a ransa inama ace ya san yarinyar to da ko ta halin ƙaƙa ne zai je ya nemawa abokinsa aurenta "Da ace nasanta da tuni abokina ya mallaketa Abbie. Zuciyata ba zata juri ganinsa yana shan wahalar nan ba."
"Kai ne ka santa kuwa Nabil. Yarinyar da Aabid ke shan wahala akanta ba kowa bace face Khadijatu.
Ni kaina zuciyata ta kasa jure ganin halin da ya shiga shi da iyayensa, wanan dalilin yasa na kawoku nan dan ku ganshi.
Nabil a yanzu da na fahimci Aabid abokinka ne sai naga babu amfanin na roƙeka akan ka bar masa Khadijatu ya aura, dan kaima da kanka zaka iya sadaukar masa da soyayyarta dan ya samu lafiya."

Kamar sauƙar aradu haka suka ji maganar Abbie Imran, musamman Nabil da ya ji kamar kunnensa ne ya masa gizo da mugun ji.

"Abbie me ka ce?" Khadijatu ta faɗa cikin rawar murya.

"Nabil ya haƙura da aurenki ya barma Aabid!"

Kunnuwanta ta dafe da hannayenta ta ƙwala wani mugun ƙara da yaja hankalin mutane ɗakin......



🌷🌷🌷🌷


Hhhh Abbie anyi mazantaka. Ko ya zata kasance kuma.

kuyi maleji yau muna fama da rashin nepa 🏇🏇🏇
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG..

  5000000

    KADUNA, NIGERIA.

Lokacin da suka zo ƙofar gidan sosai jikinsu Dad yayi sanyi, domin da fari sun zata yarinyar  'Yar talakawa ce, duba da cewa a hanya Aabid yace ya ganta ya mata fyaɗen.
 
   Hon suka yi mai gadi ya wangale musu ƙofar shiga gidan anan suka yi karo da manyan motoci a gidan, wanda ya basu tabbacin wani al'amari mai muhimmanci ne ke faruwa.
  Basu gama jimamin abun da ya faru ba suka ga mutanen da basu tan-tance kamarsu ba sun fito, Abbie Yasir da Abdul sai Baban Indo sun rakosu kowa fuskarsa ɗauke da fara'a suna ɗaga musu hannu har suka fice a giidan.

  A lokacin kuma idanuwansu ya sauƙa akan su Dad da Mom. Ƙarasawa  su Dad suka yi kusa da su fuskarsu a ɗan sake "Wa nake gani kamar Maitama?' Abbie Yasir ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi gami da mamakim ganin sa.

  "Ni ɗinne dai Dakta Imran." Ƙarasawa yayi ya taro shi suka haɗa hannu waje ɗaya.
  "Kace gaba ɗaya kai da iyalin kuke tafiya."
  "Aikuwa! Nanne gidanka kaddai?"

Murmushi Abbie Imran yayi yana yawata idanuwansa a harabar gidan "Ga dai ɗan akurkin da muke rayuwa da ahali gaba ɗaya."
  "Wanan ya wuce akurki ai Dakta. Allah ya sanya alkhairi a cikinsa."
"Ameen" Ya faɗa lokacin da suka shiga cikin falon.
  Bayan sun zauna ne aka sake sabuwar gaisuwa, fuskarsu ɗauke da fara'ar sake haɗuwa duk da ba wai shaƙuwa ce ta sosai ba, zama ne ya haɗasu a jirgi sama har kusan sau uku wanan dalilin yasa suka haddace sunayen junan nasu.

  Bayan an gabatar musu da abun sha da na motsa baki suka sake sabuwar gaisuwa anan Dad yayi gyaran murya "Wani al'amari ne mai girma ya kawo mu nan gidan Imran. Sai dai naji mamaki da na ganka a ciki ɗaya daga sahun mutanen gidan, amma zuciyata ta samu nutsuwa da nunkuwar kunya akan wanda na taho da ita a baya."

   "Wani al'amari ne wanan Alh. Maitama."
  Nuna masa Aabid yayi da hannunsa "Ko zaku iya gane wanan yaron?" Ƙura masa ido suka yi na ɗan lokaci, amma kuma suna cikin kokonto da shakku akansa.
  "Kai gaskiya ban gane shi ba. Amma kuma fuskarsa na kin kama da na wani da na sani a makwanni biyun da suka gabata."

  "Shine ba kama bace! Abubuwa da yawa sun faru bayan barinsa gidan nan kamar yanda ya bamu labarin ya taho neman yafiyarku.
  Hakkin da ya ɗauka ya aza akansa ya dawo yana caccakar ruhinsa da kuma farin cikin da ya masa saura a rayuwarsa, ciki kuwa harda rasuwar ɗiyarsa da kuma gujewar matarsa daga gareshi."

  "Kamar ya kenan?" Abdul ya faɗa yana kallon su a ɗage.

  Cikin nutsuwa Dad ya shiga basu labarin iftila'in rayuwar da ya faru da su tun daga farkon yima Nuriee fyaɗe da tafiyar Aabid da komawar da yayi da ciwon zuciya, har zuwa yau da suka taho da kuma dalilin zuwan nasu.
   "Inna lillahi wa inna ilahirraji'un!" Abun da mutanen falon suke faɗa kenan suna jijjiga kansu cikin jimami da kuma tausayawa halin da suka shiga.
  "Allah yaji ƙanta ya mata rahama, yasa mutuwa hutu gareta, yasa mai ceton iyayenta ce."
  "Ameen." Su Dad suka faɗa, yayin da Aabid ke goge hawayen da ke zuba akan fuskarsa.

   "Tabbas duk Abun da ya faru ga Aabid HAKKIn Khadijatu ne ya ke bibiyarsa. Hakkin da ya daƙusar da ko wani farin ciki da karsashin da yake da shi.
  Duk da cewa a rayuwa akwai ƙaddara akwai kuma sanadin ƙaddara. Shine silar ƙaddarar da ta afkawa ɗiyarsa, ko da iya wannan aka barshi ya samu ilimin rayuwa, ya kuma fahimci darasin da ke cikin zalunci da kuma hakkin wani da ke bebiyar mutum.
  A matsayina na uba ga Aabid ina ƙara baku haƙuri da ku yafe masa, dan Allah badan halin da ya aikata akanku ba, sai dan hukuncin adalcin da kuka samu daga mahaliccinsa."

   "Mu ai mun yafe masa tun ranar da abun ya faru da shi, abun da kuma ya rage shine tsakaninsa da yarinyar da ɗan uwanta.
  Sune suka fi mu jin zafin abun da ya faru da su, su ne suka sha wahala da fuskantar ƙalubale kala-kala a cikin rayuwarsu." Abbu Yasir ya faɗa tana ƙoƙaren dakatar da Imran daga son yin magana.

   "Dan Allah idan ba damuwa zamu iya ganinta a yanzu."

  Kallon Anwar Abu yasir yayi "Ka kira Khadijatu da Ishaƙ."

    Tashi yayi ya haura sama bai jimaba sai gashi sun sauƙowa daga matakalen benin, tana sanye da doguwar riga fara an mata ado da ja da farin duwatsu masu sheƙi.
  Ta yane kanta da ɗankwalin doguwar rigar, tunda ta fito su Dad suke binta da kallo a zuciyarsu kuwa sai kiran "Barakallahu suke, saboda tsantsar kyanta da nutsuwarta.
  Gefen Aabid kuma ji yake ko wani takun da tayi tana yinsa ne da bugawar zuciyarsa, idanuwansa kamar za su faɗo saboda kallonta, ya shagala ƙwarai.

  A jikinta take jin ana kallonta, hakan yasa ta tamke fuskarta, ta ƙara tsuke ɗan ƙaramin bakinta, hakan sai ya ƙara fito da kyanta.

   A hankali ta motsa bakinta tayi sallama, suka amsa a tare sanan ta zauna a ƙasan kafet ɗin, ita da Ishaƙ.
"Abbu gamu." Ta faɗa cikin sanyin muryarta.
  "Ga baƙi nan zun zo ganinki." Abbu Yasir ya faɗa yana mata nuni da hannunsa da inda suke.

  Ɗago da kanta tayi ta kallesu ta gaida su cikin girmamawa, amsawa sukayi fuska a sake "Sai dai ban sanku ba. Ko zan iya sanin abun da ya kawo ku?" Ta tambayesu tana ɗora idanuwanta akan Dad da take ganin kamar ta san shi.
  "Sosai kuwa 'yatah. Mun zo neman alfarma a wajanki ne, akan abun da yaronmu ya aikata miki shekarun da suka wuce.
  Dan Allah badan halinsa ba ki yafe masa, ko zai samu Allah ya yafe masa shima."
  "Wani ɗan naku kuke magana Baba? Laifin me kuma ya aikata min?"

   Aabid ya nuna mata da hannunsa "Wanan shine ɗanmu, wanda ya keta miki alfarma da mutuncinki tun kafin kisan wacece ke! Yanzu kuma ya gane kuskuren da ya aikata. Dan Allah ki yafe masa, idan da halima muna so mu dawo miki da abun da kika rasa ta hanyar aurenki, saboda shi kaɗai ne yafi dacewa da ya aureki. Shi ne kaɗai mijin da zaki aura ku zauna cikin rufin asiri ba tare da gori ya shiga tsakaninku ba.

   A yanzu ya kamu da soyayyarki me yawa, wanda silar haka ya kamu da ciwon zuciya. Dan Allah ki amince mana da buƙatarmu!" Ya ƙarasa maganar yana haɗe hannayensa waje ɗaya.

   Murmushi Khadijatu tayi mai sauti, wanda har sun ji hankalinsu ya kwanta akan zata amince da buƙatarsu "Sai dai kamar naji kunce yafiya kuka zo nema wajena ba Bara ba!"

   Ido duk mutanen palon suka fiddo waje cikin mamakin jin kalmar baran da Khadijatu ta faɗa.
  "Haka ne 'yata, yafiya muka zo nema wajenki." Mom ta bata amsa cikin sanyin jiki.

  "To idan haka ne me ya haɗa yafiya da Bara?"
  "A ina akayi bara anan?" Dad ya faɗa cikin jin zafin kalmar da ta jefe su da ita.

  "Magiyar da kake min akan na auri ɗanka, sai ta min kama da mabaracin almajirin da ke yawo da kwano a tsakiyar sahara."

   "Khadijatu wani irin shashanci ne wanan? A gabana kike cima manyan mutane fuska dan ki nuna cewa bamu baki tarbiyya mai kyau ba ko kuma ƙasa zaki watsa mana a ido?" Abbie Imran ya faɗa yana ƙoƙarin tashi ya maketa da hannunsu.

  "Ka kwantar da hankalinka Abba ba shashanci nake musu ba ko Baba?" Ta ƙarasa maganar tana tambayar Dad, da yake jin zuciyarsa na ƙuna, yana ji inama ƙasa ta tsage ya shiga cikinta, bai taɓa kin kalmar da aka jefeshi da ita mafi muni ba kamar wanan.

  "Haka ne ba shashanci kika faɗa ba 'yatah."
  "Yauwa kaji ai Abbie."
"Tashi ki tafi ki bamu waje?" Imran ya hargowa har palon na amsa amo.
  Miƙewa tayi tana murmushi Dad yayi saurin dakatar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login