Showing 75001 words to 78000 words out of 91747 words

Chapter 26 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

809

ita "Baki bamu amsar maganarmu ba 'yata."

  "Mun gama magana Baba."
"Dan Allah Khadijatu ki yafe masa badan halinsa ba." Mom ta faɗa cikin sanyin murya.
  Ja tayi ta tsaya daga tafiyar da take tana kallon Mom "A matsayinki na uwa nasan zaki fi saurin jin ƙunan da naji. Amma kuma a yanzu ba zaki gane abun da naji ba a wancan lokacin, saboda kina barci a ɗakin da ke ɗauke da ƙatuwar katifa, yayin da masuburbuɗar sanyi take kaɗaki.
  Ba ki duba yanayin da yaronki yake ciki ba ko ya dawo, balle ki tambaye shi ya yake mai ya aikata ba? Madadin haka sai kika bashi ragamar rayuwarsa ya tafiyar da ita yanda yake so.

  Ki tambaye shi lokacin da zai aikata min kuskuren da yake ta kira bai ji magiyar da na masa ba, ko kuma kunnuwansa ne suka rufe a lokacin? Ki tambayeshi a lokacin har sanar dashi nayi ni marainiya ce amma bai kula da hakanba ya aika mugun numfinsa. Hakan bai gamsheshiba har sai da ya ɓatar da hankalina daga jikina, sai da ya barni da ciwuka masu yawa a tare da ni."

  Kama hannun Ishaƙ ta yi ta ɗaga tana nuna masa "Kinga hannayen yayana, a lokacin shekarunsa sun kasa da aikin da ya ɗauka, duk da ya samu sauyi na wajen zama amma bai rabu da tabon ruƙon fatanyar da yayi ba. Ba iya raunin hannu kaɗai ke tare da shi ba, zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa duka ya bani, ya ƙarar da lokacinsa saboda ya kula da ni.
  Yana ina a lokacin? Me ya hana ya wai-waye mu yaga halin da ya tafi ya barni?
  Sai yanzu da yaji zafin da naji sanan ya zo ya ce nayi haƙuri! Kalma ɗaya kawai zai faɗa min a wuce wajen! Yi HAƘURI kawai fa! Sanan ku tsammaci maganar ta wuce ɗin?"

  Kai ta girgiza tana murmushi mai ciwo, hawayen da ke shirin zuba akan fuskarta ta shanye, tana shareshi da hannunta.

   "Yayi sauƙi da yawa Aabid! Yayi kusa da yawa kace min nayi haƙuri kawai a wuce wajen. 'Yar ƙaramar kwanyar da ke gareka ta yaudareka da kake tunanin zan yafe ma har na soka na yi zaman aure da kai."

   Jikinsu ne duk yayi sanyi, duk suka sunkuyar da kansu ƙasa, maganar Khadijatu da daki zuciyarsu sosai, duk abun da ta faɗa gsky ne basu ɗauka abun ya munana haka ba.

Tsugunnawa Aabid yayi aganta yana haɗe hannayensa biyu "Duk abun da kika faɗa gaskiya ne Khadijatu.
Ni azzalumi ne da ban cancanci yafiya daga gareki ba, saboda son zuciyar da na aikata a gareki. Amma bani da abun da zan iya a lokacin da ya wuce wannan. Ki yi haƙuri ki yafe mun badan halina ba, sai dan ƙaramar yarinyar da ta rasa ranta saboda hakkinki da ke kaina. Ina jin tsoron kada wata rana hakan ya sake faruwa ga wanina."

Kai ta girgiza masa "Ba zan iya ba."
"Haba mana Khadijatu! Wata zuciyace da ke haka bushasshiya? Ko Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke? ME YASA Ba zaki yafe masa ba? Wata baƙar zuciya gareki ne haka da ruƙo?" Abbie Imran ya faɗa cikin zafin zuciya kamar ya ɗauketa da mari, duk wani marar imani idan yaga yanda Aabid ya koma dole ya tausaya masa

Juyowa tayi a hautsine tana kallon Imran tana buga ƙirjinta da ƙarfi, idanuwanta duk sun kaɗa sunyi ja saboda tashin hankali "Babu zuciya ne a jikina Abbie! Zuciyar da ke tare da ni ta riga data bushe! Tsawon shekara goma sha biyar babu wani mutumin da ya ruƙo hannuna ya zaunar dani ya min kallon tausayawa bayan Yayanah! Ko da sau ɗaya babu wanda ya ɗauki Anini daga hannunsa yace gashi na baki! Koda sau ɗaya babu wanda ya ce Khadijatu ki gyara wanan bayan yayanah! Amma duk da wanan gararambar rayuwar bai sa ya zalunce ni ba. Bai sa ya tausaya minba lokacin da yaga bana numfashi ya kaini a duba lafiyata ba.

Duk tsawon lokacin da muka ɗauka tare da ku baka taɓa lura da bushewar da zuciyata tayi ba sai yanzu Abbie? Kai a ranka baka ga wani abu na tafiya a rayuwata da ya kamata ace an sauya shi ba sai yau Abbie? Me yasa zuciyarka bata zargi lammura na ba sai a yanzu? Ko da sau ɗaya baka zaunar da ni ka tambaye ni me ke faruwa da rayuwata ba? Me nake so? me ne bana so? Duk baka ga gyara akan hakan ba sai yanzu Abbie? Me yasa? Ko dan bani da Mama a duniya ne?"

Numfashinta ne ya fara sama, tana jin yawun bakinta na bushewa akan harshenta, saitin zuciyarta ta ruƙe da ƙarfi, hakan yasa Ishaƙ saurin rungumeta hawaye na sauƙa akan idanuwansa, ya fara shafa bayanta yana hura mata iskar bakinsa a saitin kunnenta "Ya isah haka Khadijatu! Babu mai tilastaki, ina tare da ke a duk abun da ya miki na rayuwarki."

"Bana son ganinsa Yayanah!" Ta faɗa tana ƙan-ƙame jikinta ana Ishaƙ, hawaye na biyo bayan idanuwanta.

"Na sani Khadijatu na. Zuciyarki mai kyau ce, koda baki son abu nasan saboda ni xaki so shi. Bai can-canci yafiyarmu ba, amma kuma muma muna aikata kuskure a rayuwarmu. Kodan mu samu rahama daga Ubangijinmu da ladan da masu haƙuri suke samu zamu duba lamarinsa mu yafe masa.
Darrusa da ya samu na zahiri yafi namu darrusan da muka samu na wahala. Ko ba komi mu ai mun tsira da rayuwarmu Khadijatu, yayin da shi kuma ya kashe tasa rayuwar.
Ba zamu barshi da kisan mummuƙen da ya riga yayiwa kansa ba Khadijatu? Inaga ko a nan ma ai mun samu ribar haƙurinmu, mun kuma tsinci nasarar da ta daɗe tana jiranmu.
Mutumin da ya aikata zalinci agaremu ya dawo yana roƙonmu yafiyarmu, wanan kaɗai ma Nasara ce Khadijatul Ishaƙ."

Ajiyar zuciya ta sauƙe da ƙarfi tana jin kalaman yayanta na huda sassan jikinta, da gaskiyar da take tafiya.

"Na yafe masa Yayanah! Wallahi na yafe masa duniyata da lahirata." Ta faɗa hawaye na sauƙa akan fuskarta, tana jin kamar ta sauƙe wani gungumemen dutse akanta.

Yayin da Aabid ya sauƙe tasa ajiyar xuciyar yana durƙusar da kansa ƙasa wajen yin sujjada shukuriy.
Ji yayi ƙofofin jikinsa sun buɗe, yayin da wata iska mai daɗi take ratsa jikinsa, yana jin zuciyarsa na harbawa da aminci a tare da ita madadin tsoro.
"Alhamdulillah!" Shine kalmar da mutanen palon suka faɗa a tare, idan aka ɗauke Imran da kansa ya shiga chajin maganar da ta faɗa masa.

"Nagode Khadijatu! Nagode sosai! Kin yafe min hakan na nufin zaki aure ni kenan?"

Ido ta fiddo waje tana kallonsa, kamar dai yanda mutanen palon suka buɗe baki suna kallonsa.


🌷🌷🌷🌷

Wow long page, 3pages   a lkc guda. lolx kuyi hqr yau na shiga rububi da yawa ban baku pages uku kamar yanda zahra tace ba, haka ban baku breakfast ba kamar yanda na so, amma ga abokin brc nan.

Ngd da uzurinku gareni.
Girmamawa.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG.....

  5200000

Ruƙeta Ishaƙ yayi yana girgizata da ƙarfinsa "Ki yi shuru Khadijatu. Muddum ina raye a duniya babu wanda zai tilastaki auren wanda bakya so." Ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai idanuwansa sun kaɗa daga kalarsu sun koma jajaye.

    Kallon Aabid da yake kwance yayi ya kana ya kalli Imran da shima kallonsa yake "A matsayinka na likita kana da damar yin komi dan ganin marar lafiyanka ya samu lafiya, ciki kuwa harda kasuwancin siya da siyarwa.
  Sai dai ni matsayi uku gareni, Yaya kuma Uwa da uba a gareta, wanda ya kasance duniyarta tun kafin ta san wanda ya zama silar kawota wanan duniyar.
  Bayan wasu shekaru mun haɗu da kai yayin da ka bayyana fuskarka a matsayin mahaifinmu. Mun karɓeka mun kuma yafe abun da ya faru a rayuwarmu ciki harda rashin mahaifiyarmu da kuma wargajewar farin cikinmu.
  Ko wani lokaci yaƙe muke muna haba-haba akan danne mikin da ke garemu, sai dai wani ƙuncin ba'a ita ɓoyeshi, da kanmu muke haƙa mu binne ba tare da wani ya sani ba.
  A yanzu kuma da ƙanwata ta samu wani jigon da ya tsaya mata, ya kula da ita, ya ƙarar da lokacinsa da soyayyarsa wajen dawo mata da farin cikin da ta rasa har na tsawon shekara shida, bai taɓa gajiya akan hidimarta ba, baiga aibun kuskuren da ya faru da ita ba, asalima kirari yake akan duk abun da ya faru da ita ƙaddara ce. Yayin da ya ambaci ƙaddararsa a cikin tasa shine yanzu kake tunanin maye gunsa da hamagon nan?
Na rantse da Allah da ya halicce ni! Muddum ina raye babu wanda zai aura ma Khadijatu wanan mutumin, koda ace zai mutu ne. Domin mu ma munyi mutuwa dubu a lokacin da ya keta alfarmarta."

   Ruƙo hannun Khadijatu yayi "Zo mu tafi ƙanwata."
  Tafiya suka yi har sun buɗe ɗakin Ishaƙ ya ja ya tsaya "Idan har ka matsa da yawa zamu bar maka gidanka. Mu dama ba baƙi bane a duniya, balle yanzu da muka san cewa ko ina masallaci ne a cikinta."
Suna gama faɗar haka suka fice a ɗakin suka bar Imran baki buɗe, jikinsa duk yayi sanyi da maganar da Ishaƙ ya faɗa masa.

   "Ni mene laifina anan Nabil dan na yi ƙoƙarin ceton rai?" Abbie Imran ya faɗa cikin sanyin muryarsa.

  Kai ya girgiza masa "Baka yi laifiba Abbie a matsayinka na likita kai ceton rai ka sani. Sai dai kuma ba yanda ya kamata kayi ba ka yi.
  Khadijatu 'yarka ce da baka bata farin ciki mai yawaba a rayuwarta, asalima a duniya bayan yayanta bata san wata kalmar uba ba. Yayin da kazo kuma sai ka gaza jansu a jikinka ta yanda zaka fahimci matsalarsu abin da suke so da wanda basa so.
  Ishaƙ ya san zafin Khadijatu, duk lokacin da ta ji ciwo shine yake jin zafin ciwon. Da ace Ishaƙ bai ce ta yafema Aabid ba na tabbata da har yanzu bai isheta kallo ba.
Ta yafe masa saboda yayanta, hakan ba yana nufin zata so shi ba Abbie! Hakan ba yana nufin zata zauna da shi ƙarƙashin inuwa ɗaya ba ne.
  Da ace ba Aabid bane yayima Khadijatu fyaɗe ba wani ne da ban, wallahi da zan iya bar masa ita ya aura.
  Sai dai kuma da kaina na ɗauki alwashin duk lokacin da naga wanda ya keta alfarmar Khadijatu sai iya inda ƙarfina ya ƙare. Sai kuma akayi sa'a ya so abun da nake so, shi abokina ne tun yarinta, zan hukuntashi da zalincin da ya aikata, kamar yanda Allah ya jarrabe shi da soyayyarta. Ko da wanan aka barshi ya isheshi ishara.
  A matsayinka na likitansa ka bashi shawarar ya rayu kodan iyayensa amma ba zai samu abun da yake so ba a karo na farko a rayuwarsa." Yana gama faɗar haka shima ya fuce yabar ɗakin.
  Zama Imran yayi yana jujjuya kalaman su akansa, yana jin wata kunya na lulluɓe shi. Ance so so ne amma son kai yafi, shi ya akayi ya gaza son yaransa madadin haka ya so wani bare.
   Ganin yana ƙara ɓata lokaci da yawa ya sashi tashi ya fuce a ɗakin kai tsaye gida ya nufa, zuciyarsa na bugawa tana tsalle kamar zata tsaga ƙirjinsa ta futo.
   Yana shiga palon yaga duk mutanen gidan a tsaye sunyi shuru basa magana, kallon gabansu yayi yaga ƙananun jaka guda biyu a tsakiyar palon,  Ishaƙ da Khadijatu na riƙe da ɗaya a cikinsu.
  "Alhamdulillah gara da ka zo Imran! Ga su nan kana ganinsu janye da jaka wai za su bar gidan su koma inda suka fito. Babu juyin duniyar da bamu yi ba amma sun ƙi saurararmu ƙila kai da kake ubansu za su yarda su zauna idan ka musu magana." Abbu Yasir ya faɗa cikin jin haushin ƙin kulashin da suka yi.

  A hankali Imran ya fara tako ƙafarsa yana kallon fuskarsu da suka haɗeta gam kamar ba su taɓa fara'a ba, tsayawa yayi yana kallonsu yana ga tsananin kamannin da suke da shi, yana ga soyayyar junansu da kuma shaƙuwar da suka yi da junansu.
  Murmushi yayi mai sauti yayin da hawaye ke biyo bayan murmushin nasa, wata soyayyar 'ya'yan nasa ke ƙara huda zuciyarsa.
  "Tafiya za kuyi ku barni! Ni ban muku dole ai akan ta aure shi ba, zaɓi na bata dan ta ceci rayuwarsa. Amma idan tace bata so ai bazan tilasta mata dole akansa ba.
  Ku 'ya'yana ne na cikina, ba zan zaɓi wani na fifita soyayyarsa fiye da taku ba. Duk abun da kuke so shine zaɓi na, idan har kuka ce zaku tafi dan kuna so dole zan haƙura na yaƙi zuciyata, ba zan ci gaba da zama uba mai son kansa da daƙusar da muradin yaransa ba.
  Kuje idan har za kuyi farin ciki! Ku tafi idan hakan muradin zuciyarku ne!"
  Jakakkunan hannayensu suka zubar ƙasa suka rungume shi "Abbie!" Suka faɗa a tare suna kuka, shima ƙanƙamesu yayi yana jin tausayi da ƙaunarsu a zuciyarsa.
  Sai yanzu ya fahimci kuskuren da ya so aikata musu a karo na biyu a rayuwarsu, sunyi fafutuka da rayuwa a karo na farko, bai kamata yanzu ya barsu su sake fuskantar wani ƙalubalen ba.
   Sun daɗe suna rungume da juna a yayin da mutanen da ke palon suke matse hawayen tausaya musu.
  Tsakanin ɗa da uba sai Allah ba mai shiga wanan maganar, da ace sun shigeta da tuni sun sha kunya.

   Bayan wani lokaci suna zaune anan Imran ya basu labarin abun da ya faru, Abbu Yasir da Ummi suka rufe shi da faɗa akan dan me zai yanke wanan shawarar ba tare da ya yi shawara da su ba. Ya auna babban arziƙi da ya dawo ya samu yaransa suna nan, da tuni sunyi tafiyarsu sun barshi.

     Shi kansa ya fahimci baima yaransa adalci ba, amma kuma a matsayinsa na likita mai ceton rayi ba xai iya bari mugu abu ya samu wani mutum ba alhalin yana da damar da xai taimaka masa.
  "Abbie muje asibitin ina so nayi magana da shi." Khadijatu ta faɗa wanda hakan ya ja hankalin mutanen gidan nasu kanta.
  "Tashi muje." Imran ya faɗa yana tashi akan ƙafafuwansa.

  "Khadijatu!" Ishaƙ ya kirata yana kallonta.
  "Ba abun da zai faru Yayanah! Ina tare da Abbie." Murmushi ya mata ya gyaɗa kansa daga haka suka fuce suka bar palon.
Shima kallon Aisha yayi da take kallonsa, a ranta tana girmama ƙauna da soyayyar da yake ma ƙanwarsa, a zuciyarta ji take inama tana da yayan da zai sota kamar dai yanda Yayan Khadijatu ke sonta.

   Ƙarasa wajenta yayi ya hure mata ido da bakinta, hakan ya sa ta lumshe idanuwanta "Wanan kallonfa ƙanwata?"
  Baki ta taɓe ta kawar da kanta gefe "Ba kai nake kallo ba ai."

Murmushi yayi ya kalli mutanen da suke palon wanda hankalinsu baya wajensu suna tattaunawarsu daban ne.
   "Na faɗi abun da kike cewa?"
Kallonsa tayi ba tare da tayi magana ba sai kai da ta gyaɗa masa "Faɗi."

   Zama yayi kusa da ita yana danna wayarsa da ke hannunsa, ba tare da ya mata magana ba, hakan ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba.
  Ƙoƙarin tashi tayi tabar wajen saboda rashin ganin amfanin zaman nata a wajen "INA SON KI!"
  Ba zata taji maganar tasa hakan ya sata juyowa dan ta gaskata abun da kunnuwanta yake ji mata, idanuwanta ne suka shiga cikin nasa, wanda ya sa zuciyarta bugawa da ƙarfi "Ina son ki!" Ya sake faɗa mata daga haka ya miƙe yabar wajen ya barta da masa rakiyar ido da kuma zamowarta wani saƙaƙo daban a wajen.
   'Wani irin so Ishaƙ ke mata! Me yasa yace yana sonta ya barta kuma a wajen? Ko dai tsokanarta yake kamar yanda ya saba? Amma kuma ai baya mata irin wanan wasan. '
"Ya Allah! Kada ace ya san ina sonsa ne fa?" Ta faɗa tana rufe hannayenta da bakinta tana ƙara kallon mutanen da suke falon wanda basu san me take ciki ba, sai Ammu da ta kafe ta da ido.
  Kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka ta tashi tabar palon dai-dai lokacin da saƙo ke shigowa wayarta. Hannu tasa ta buɗe saƙon wanda kalmomi biyu ne a cikinsa _"Cikar buri cimma nasara!"_
  "Me kenan?" Ta tambayi kanta ganin baƙuwar lambar da bata san da wanzuwarta akan wayarta ba _"Ke ta musamman ce a duniyata! Kamar yanda kika zama tsanin kawo haske cikin rayuwarmu! Bazan soki fiye da rayuwata ba amma zan baki kulawa fiye da tawa rayuwar! Ina son ki!"_
  Wani saƙon ya sake shigowa wayarta a karo na biyu, sai a lokacin ta gane lambar Ishaƙ ce.
  Murmushi tayi ba tare da ta rubuta masa amsa ba, ta kashe wayar gaba ɗaya, saboda tana so ta bawa kwanyarta damar nazarta me ke faruwa da ita?

  *****
  Tun zuwansu Asibitin suka ci karo da su Mom a cikin ɗakin, wanda a lokacin Aabid ya farka, amma banda sunan Khadijatu ba abun da yake kira.
  Shigowarsu yasa su sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, domin ganinsu da sukayi sai suka ga kamar ya samu abin da yake so ne, kamar burin ɗansu ya cika.

  A hankali Aabid ya fara ƙoƙarin tashi zaune "Kin zo Khadijatunah? Ni nasan zuciyarki mai kyau ce, ba zaki barni na mutu ba."
  Zama yayi da taimakawar su Dad har lokacin idanuwansa akan Khadijatu "Naji daɗin ganinki Khadijatu, hakan na nufin ina da sauran rayuwa anan gaba."

  Murmushi tayi ta zauna a bakin gado kusa da shi tana kallon yanda ya rame ya fita a kamanninsa, ya zama kamar wani zararre. Lallai ba abun da ya gagari Allah musamman idan ta tuna haɗuwarsu na farko, mutum ingarama mai ji da ƙarfi da ikonsa, duk da magana bata shiga tsakaninsu ba amma ta tabbata yana da ji da kai a lokacin.
   "Ya jikinka?" Ta tambaya tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta.

   "Na samu lafiya tun da na ganki a gabana a yanzu."

Murmushi ta yi har kumatunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login