Showing 45001 words to 48000 words out of 91747 words
Mahaifinsu." Ummi ta faɗa tana share hawayen fuskarta.
Daɓas Ammu ta zauna daga tsayen da take "Ya Allah! Wani irin al'amari ne wanan mai sarƙaƙiya haka? Duka wanan shekarun kuna so kuce min ina tare da jinina amma ban sani ba?" Ammu ta faɗa tana dafe kanta da hannunta, hawaye na sauƙa akan fuskarta. Sai dai har yanzu wani sashi na zuciyarta yaƙi yarde mata akan gaskiya ne.
Dai-dai lokacin Dakta Anwar ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kamar yanda Ummi ta umarce shi "Ga kayan aikin UMMI jinin wa zan zuƙe?" Ya ƙarasa maganar cikin zolaya.
Harara ta aika masa tana masa nuni da Ishaƙ da Khadijatu, sai da ya ɗiba sanan ya kalleta "Imran da Ammu!" Ta faɗa masa yayin da kowa a falon ke kallonta.
Bayan ya ɗiba ta ce masa "Ina son ka musu gwadin zubin ƙwayar halittarsu ka tan-tance min ko sunyi dai-dai da na juna. Ka duba jinin Ammu da nasu Ishaƙ kaga ko ya zo ɗaya."
Kai Anwar ya gyaɗa sanan ya fita daga ɗakin. Babu wanda ya ƙara magana sai Ummi da ke Addu'a a zuciyarta akan Allah yasa abun ya zama gaske.
Bayan Awa ɗaya.
DAKTA Anwar ya dawo ya miƙawa Ummi sakamakon gwajin da yayi musu. Yana kallon Ishaƙ da Imran da suma suka zuba nasu idanuwan akan nasa.
"Ga Sakamakon ya nuna cewa ƙwayar halittarsu ɗaya ne dana Imran, wanda hakan ke nuna cewa su yaransa ne.
Ammu kuma jininta ya zo ɗaya da nasu kamar dai yanda kika buƙaci ji."
"Alhamdulillah! Allah nagode maka!" Ummi ta faɗa hawaye na silalowa akan idanuwanta.
Anan suka shiga rige-rigen rungume Ishaƙ ɗin kowa na shafa fuskarsa da kuma Khadijatun da ta ke barci.
Jikinsa ya zame daga nasu hawaye na sauƙa akan fuskarsa "Ya Isah haka! Dan Allah ku ƙyalemu ni da ƙanwata!" Ya faɗa cikin rawar muryar da ke fita da zafi-zafi.
Tsit ɗakin yayi suka fara kallon Ishaƙ da shima idanuwansa na kansu, hawayen fuskarsa ya share yana kallon yanda suka ƙame ba tare da sun iya yin magana ba.
"Dan Allah ya isa haka! Wasan kwaikwayon naku ya tsaya haka!" Ya faɗa yana mayar da numfashi da yake ji ƙirjinsa ya fara sama-sama.
"Wasan kwaikwayo kuma Ishaƙ? Mu ne muke wasan kwaikwayon?" Abbu Yasir ya faɗa cikin sanyin muryarsa.
Kai ya gyaɗa masa "Wasan kwaikwayo mai kyau kuwa kuke yi? Wasan kwaikwayon dai-daita ahalin da biyun da suke son zama abu guda. Dan kuna son dai-daita kanku ba sai kun shigo da mu cikin labarinku ba! Ni ban yarda cewa ina da sauran dangin da suka rage min a duniyata ba bayan ƙanwata sai kuma waɗan nan mutanen da suke kusa da ni." Ya ƙarasa maganar yana nuna Ammu da su Indo.
"Kada ku ruɗa ruɗaɗɗiyar zuciyar data shafe labarai da sa rai akan samun yayyafin da zata jingina a jikinsa."
"Ishaƙ wallahi wanan ba ƙirƙirar labari bane, zahiri ne da yake tafe da gaskiya a cikin labarin nan. Duk inda zaka, duk inda zaka je dole mune danginka na halaliyarka." Ummi ta faɗa cikin bashi tabbacin gwajin da akayi a kansu.
Idonsa ya lumshe ya fara tauna laɓɓansa, daga nan yayi murmushin gefen bakinsa "Sai yanzu? Duk waɗan nan shekarun kuna ina mukayi rayuwarmu? Me yasa baku zoba sai a yanzu da komi ya lalace mana? Ina dangin da zan kira halaliyata? Dangin da suka wofuntar da uwar da bata da ishasshen hankali, ko kuwa dangin da suka kori uwa da ɗiyoyinta tun kafin su mallaki hankalin kansu?
Da kuka zo kuke magana a kanmu me zaku mana a yanzu? Me ya rage wanda zaku bamu na sauran jin daɗij rayuwa?"
Hannayensa ya ɗaga ya shiga nuna musu "Kunga yanda hannuna ya koma! Nayi aiki tuƙuru, nayi aiki babu dare babu rana saboda rayuwar ƙanwata. A yayin da rana ke gasani tana huda ɓulolin jikina, ku kuna kwaance a gini mafi kyawu, mafi nagarta da kuma raɓar iska. Ko da sau ɗaya baku taɓa tunanin zuwa kubi sawun uwar da ta ɓace tare da yaranta ba. Ba kuyi tunanin ya danginta suke ba.
Sai a yanzu zaku fara taɓamu da muka mallakin dukkanin wani zafi da ƙunci na rayuwa! Sai a yanzu da aka gama tagayyara mana rayuwa! Ba kuji kunyar bayyana fuskokinku a gabanmu ba! Ba kuji bai dace ku kiramu da jininku ba?" Ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka, yayin da ya zauna ya rungumo Khadijatu a jikinsa.
Jikinsu ne yayi sanyi hawayensu na ƙara tsere da hanzarin sauƙa, kawunansu da suke ɗage duk suka maida su ƙasa.
"Da tun farko baku koremu ba da ƙila rayuwar ƙanwata tayi kyau! Da ace baku yi jinkirin biyo bayanmu ba da bamu rasa kimar da aka ƙwace da ƙarfi ba! Yau ƙanwata na kwance cikin tsoro da motsawar kwanya ne duk saboda kun fitar da mu daga gidan da aka samar da mu ba! Da ƙila ƙanwata bata rasa komi nata ba.
Yanzu kam bama buƙatar kwalliyar cikar labarinmu, domin mun daɗe da rasa wanan ƙawar, bama buƙatar ɗaga kai mu kalli ahalin da ya shafe labarinmu a cikin lokacin da muke buƙatar zama da su.
Mu kaɗai zamu zamarwa kanmu inuwa muyi yayyafin ruwa ga bushasshun zuciyoyinmu ba sai an bimu da igiyar ruwa ba."
🌷🌷🌷
IG DABANNE
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG
B000003200000T
"ISHAƘ kasan abun da kake faɗa kuwa? Ka san suwaye a gabanka kake wanan maganar?" Dakta Anwar ya faɗa yana mamakin maganarsa.
Ido Ishaƙ ya buɗe waje yana kallon Dakta Anwar "Ai kaikam ka riga da ka san komi! Kada kace komi akan abun da na faɗa a yanzu! Na tabbata da kaine a matsayi irin nawa zakayi fiye da abun da nayi."
Ɗakin ne yayi shuru aka rasa wanda zai iya bama Ishaƙ baki, duk a cikinsu babu mai ƙwarin gwuiwar yin magana.
Tashi Imran yayi yana goge hawayen da ke kan fuskarsa "Tabbas kayi gaskiya, kuskure ne mu kiraka a matsayin ɗanmu, bayan shekarun da ka shafe kana fafutuka da rayuwa! Sai dai abu guda da kayi kuskuren faɗa shine meƙe ƙafafuwan da mukayi sanyin na'ura na ratsa mu. A cikin shekarun nan koda na yini ɗaya ne bamu taɓa kuskuren mantawa da ku ba! Ko wata rana tambaya ɗaya garemu itace ya kuke a yanzu da kuna raye? Domin bamu da tabbacin kuna raye har lokacin kasancewar gawar direban da ya ɗaukoku ta dawo mana da kuma lambar motar da kuka tafi a cikinta. Mun bi ko wata asibiti dan samun shedar gawarku amma bamu samu hakanba, kunya ta hanamu zuwa gidan su Ammu dan mu tabbatar gudun kada mu tadda babu ku su tuhumemu akan ɓacewarku.
Sai gashi kwatsam nayi karo da ku anan, tun lokacin dana ganka da ƙanwarka nasan ko ina kuka fito ku yarana ne, amma bani da hujjar da zan faɗi hakan kai tsaye. Ba zamu maka dole akan ka amshemu a matsayin iyayeba, domin mun rasa wanan lokacin, Sai iyaka muyi ƙoƙarin cike muku gurbin da kuka rasa. Zamu baku kulawa da ƙawata rayuwarku da dukkanin ƙarfinmu, kamar dai yanda iyaye kan shinfiɗa rayuwarsu dan cikar mafarkan 'ya'yansu.
Hakan kuma ba zai faruba har sai da amincewarku! Kana da zaɓi na gyara rayuwarka da kuma yi mata tanadi, wata ƙila harda kasancewarka a ankare da kuma zumma wajen neman hanyar da zaka cika mafarkan ƙanwarka. Ta iyu ka na neman hanyar da zaka ɗaukar mata fansa wajen bata dukkanin kulawa da farin cikin rayuwa! Amma kuma idan kace kai ɗaya zaka ɗauki wanan nauyin wata rana zaka iya yin nisa da ita da zata buƙaci abokin ɗauke hira.
Ka tsaya ka saurari zuciyarka, ka kuma bi muradin cikinta."
Yana gama faɗar haka ya fuce a cikin ɗakin, zuciyarsa na tafasa da ƙuncin abun da ya faru. 'Yaran da ya rayu cikin kaɗaicinsu, ya ɓata rayuwarsa wajen mayar da kansa bagidaje kurman da bai tsallake iyakarsa, duk saboda rashinsu da tunanin wani hali suke ciki? Amma sai gashi kwatsam yau ya gansu, yana murna da haba-haban ganinsu, ƙuncin da ke zuciyarsa na shekaru ya gushe, amma sai gashi daga ƙarshe ɗannasa bai amshe shiba! Asalima tuhumarsa yake da zama silar wargajewar rayuwarsu.
Ta wata hanya zai wanke kansa?' Hawayen da bai ji taruwarsu ba su ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinsa, sharewa yayi ya ƙarasa cikin office ɗin da ke a matsayin nasa, ƙirjinsa ya riƙe saboda zafin da yake ji, numfashinsa sai sama-sama yake wanda hakan ke nuna zuciyarsa ta riga da ta hau sama.
"Anwar yi sauri kabi bayan Yayanka kada ciwonsa ya tashi!" Abbu Yasir ya faɗa.
Kafin ya rufe bakinsa ya fita a cikin ɗakin.
Gyara tsayuwarsa yayi yana kallon su Ammu da jikinsu ya riga yayi sanyi, shi kansa nasa jikin ya daɗe da sanyaya, amma baya so ya nuna karayarsa a gaban yaransa "Duka wanan matsalar ta faru ne saboda hakkin Hajara da ke ɗauke a kawunanmu. Idan mukace ku yafe mana kamar mun so kanmu da yawa ne. Tabbas dukanmu nan mun san cewa akwai ƙaddara, akwai kuma silar Ƙaddara. To mune muka zama wanan silar da ƙaddarorin yaran nan suka sauya ciki kuwa harda rugujewar rayuwarsu.
Wanan kaɗai isharace a garemu. Nusaiba kinga irin abun da son zuciya ke haifarwa ko? Kinga yanda cutar da wani ba abusa hakkinsa yake ba ko? Shi sharri ɗan aike ne duk inda ya je zai dawo kan mai shi, shi yasa hausawa suka ce idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi kaɗan, dan wataƙila kai ne zaka zurma a cikinsa.
Yau gashi muguntar da kika haiƙa ta afkawa jininki, da hannunki kika tarwatsa farin cikin ɗanki da na iyalansa, kika kuma shafa baƙin fantin da ba zai gogu a zuciyarsu ba har abada.
A gabanki jikanki yake musanta maganarmu yana kiranta da sunan wasan kwaikwayo, ya ƙaryata gabatarwar da muka masa, saboda lokacin da yake buƙatarmu bamu so kasancewa da shi ba."
Shafa kafaɗar Ishaƙ yayi yana jin soyayyarsa na ratsa jini da tsokarsa, bubbuga kafaɗarsa yayi "Duk duniya babu wanda zai soka kamar mahaifinka, hatta mahaifiyarku da tana raye zata baku labarin soyayyar da yake muku.
Yasha wahala lokacin da ya dawo ya iske babu ku. Ya mana hauka iya hauka musamman da gawar direbansa ta dawo babu ku, wanan ya haddasa masa ciwon zuciya a ƙirjinsa, sai da ya shekara biyu ana kula da lafiyarsa a ƙasar india. Da ƙyar muka iya kawar da ƙuncin da yake yi, ganin damuwarmu ta yi yawa ya koma yaƙe.
Komi nasa ya barshi ciki kuwa harda aikinsa da kasuwancinsa, yana yini bai yima kowa magana ba. Ni kaina na manta yaushe rabon mu zauna da shi muyi magana, kullum yana zaune shi kaɗai abunsa, hatta matarsa ma mantawa yake da ita.
Ba zance ka yafe masa kai tsaye ba, amma koda sau ɗaya ne ka tsaya kaji uzurinsa."
Kai Ishaƙ ya sunkuyar hawaye na sauƙa akan fuskarsa, yana lissafa irin magan-ganun da mutumin ke a matsayin kakansa ke faɗa masa.
'Dama duk wanan tsawon lokacin suna da iyayen da suke sonsu haka? Ashe rayuwa zata basu dama da kyakkyawan zaɓi irin wanan? To shikam me ya rage da zai tsaya mahaifinsa ya kwanta dama? Duk abun da ya faru a rayuwarsu dama an riga da an rubuta zai same su.'
Ɗaga ƙafafuwansa yayi zuwa gaban Ammu, yana kallonta wanda itama kallonsa take babu ko ƙiftawa, jinin 'yarta da ke gudana a jikinsa take gani yana yawo. Duk tsawon lokacin nan yaran Autarta na raye bata sani ba sai yau, sun zauna da su har tsawon shekara guda amma duk bata taɓa hasashen su a matsayin yaran da ke da alaƙa da jininta.
Gwuiwoyinsa ya zube a ƙasa yana yana ruƙo hannun Ammu wanda take jinsa har ranta, idanuwa ta lumshe saboda jin wani abu ya tsargar mata a zuciyarta.
"Kalmar Uwa abu ne mai mutuƙar tasiri a cikin rayuwar yaransu. Uwa ke shimfiɗa rayuwarta a tsaye ta zaunar da yaranta! Uwa ke kare zubar ruwa daga jikin yaranta ya sauƙa a jikinta.
Ko wata uwa burinta taga ta cika rayuwar yaranta da basu farin cikin abun da suke so har ƙarshen rayuwarta. A matsayinki na uwa kin samu duka wanan burukan naki ya cika, fatan da kike na rayuwar yaranki ta dai-daita sun kammalu. Ko wacce kin sadata da rumfar da zata raɓa a cikinsa, kin sauƙe haƙƙin da ke kanki a matsayinki na Uwa.
Amma ni tawa Uwar da burin haɗuwa da ke ta mutu. Ta so ace kece mutum ta ƙarshe data gani, amma lokacin da ta tuna kanta da sanin wacece ita lokaci ya ƙure mata.
Bata samu ganinku ba amma ta samu damar roƙa mata yafiya a wajenki idan har nayi tsawon rai. Ta kuma ce ta yafema Ummi da Abdallah da duk wanda zama ya haɗasu, idan nayi tsawon kwana mun haɗu na nema mata yafiyarsu."
Hawayen da yaci ƙarfinsa ya tsaya yana sharewa, yana jan numfashi da ƙyar "Shekaruna sun gaza a lokacin, amma ta ƙwarara min girman matsayina na yaya ga ƙanwarsa. Hannayen Khadijatu ta ɗora akan nawa tana kiran "Na kula mata da rayuwar Khadijatu fiye da rayuwata. Na bama Khadijatu dukkanin wani farin ciki, na ƙawata duniyarta da hasken Ilimin addini. Koda sau ɗaya bata ce na kula da tawa rayuwarba, amma ta min addu'ar neman albarka da roƙon yafiyata akan nauyin da zata tafi ta bar min. Kalmarta ta ƙarshe taƙi ɓacewa a kaina kalmar da take ta nanata min "Kayi haƙuri! Ka zama mai yafiya!" Duk lokacin da na tuna waɗan nan sai nayi kuka Ammu.
A gabana Idanuwan Mami suka rufe daga ganinmu, ta tafi tabarmu a garin da ba namu ba, tabarni da rashin sanin madafar da zan dafa.
Khadijatu tayi kuka a lokacin har muryarta ta dashe, ban san ya xan kula da rayuwarta ba saboda a lokacin komi sai Mami ta min.
A haka rayuwarmu ta ci gaba cikin fafutuka da neman abun da zamu kai a bakinmu. Ko yaushe tambayata "Su waye mu? Ina danginmu suke?" Bani da mai bani amsar wanan tambayar."
Shuru yayi yana kallon Ammu da kuka yaci ƙarfin idanuwanta "Duk da sanin da Mami tayi zata barmu a cikin wata rayuwa bata kasa yafewa wanda suka zama silar zamanta cikin rayuwarba. Buri ɗaya take da shi a lokacin "ki yafe mata na ƙin sake waiwayarki da tayi! Ki mata addu'ar samun rahama a wajen ubanginta."
Ammu ni kaina dana ga su Ummi sai naji na yafe musu, da naji dalilin da yasa muka bar mahaifarmu sai na hango ƙadarar data afkama Khadijatu wanda aka riga aka rubuta a littafin. Duk da ta kasance sila ta faruwa komi na rayuwarmu amma naji na yafe musu kamar yanda Mami ta yafe musu, na amshesu a matsayin dangina.
Ke 'ya ɗaya kika rasa, amma Allah ya barki da sauran yaranki, yayin da ni na rasa uwar da ban samu madadinta ba, ban samu wadda tace na zo na zauna ta amsheni a matsayin ɗanta ba, har sai da muka haɗu da Baba."
Rungume Ishaƙ tayi tana kuka shima yana kuka duka mutanen da suke ɗakin kowa kuka yake. Ummi kam zuwa lokacin ji take inama itace ta mutu da mugun halin nata, duk itace ta jaza musu wanan bala'in.
"Na yafe musu Ishaƙ! Na yafe musu duniya da lahira! Allah yaji ƙan Hajara ya yafe mata. Lallai Allah yana sona da rahama da ya amshi rayuwar Hajara sai ya bani wasu madadinta. Allah ya haskaka makwancinki Hajara." Ammu ta faɗa cikin muryar data gama dashewa wadda tasha kuka ta ƙoshi.
"Mungode sosai Ammu, mun gode Ishaƙ Allah yaji ƙan Hajara!" Ummi ta faɗa cikin sanyin murya.
"Ameen duka 'yan ɗakin suka amsa."
Daga waje kuma Dakta Imran ne ya jingina daga jikin ƙofar, tun bayan zuwan da Anwar yayi ya masa allura, ba yanda bai yiba akan ya samu ya huta amma yaƙi, saboda zuciyarsa ta gaza jure barin yaransa a wajen.
Zuwansa ya tsinkayi maganar da Ishaƙ yake wanda ya sashi tsayawa yana saurara. Zuciyarsa na karaya da dulmiya akan soyayyar Hajara da ta riga ta masa nisa, nisa na har abada. Shi yasa Hajara nada kyakkyawar zuciya amma bai ɗauka zata yafema Umminsa a lokacin da take gaf da barin duniya ba.
"Allah yaji ƙanki da rahama Hajara." Ya faɗa yana barin ɗakin, saboda baya son ya katse musu maganarsu, yana so su samu damar tattaunawa da kyau a tsakaninsu.
*******
LAGOS,NIGERIA.
Tun bayan komawarsu gidansu Aabid take samun kulawa ta musamman, zata iya cewa wanan cikin ya zama wani abu na alfarma a gareta. Kwacankwam suka ɗauki kulawa da soyayya suka ɗora akanta.
Hatta cokali ba'a bari ta ɗauka, saboda likita yace kada ta motsa jikinta da kyau.
Aabid har hutu ya ɗauka na wata ɗaya wanda shi ya so yafi hakama, kasancewar dokar aikin su yasa aka bashi wata ɗaya da ƙyar, a hakanma saboda yana da alfarma da dama ne a hannunsa.
Rayuwarsu Amrah ta haska sosai, domin ko ƙwaƙƙwaran tari tayi sai hankalinsu ya tashi. Abinci kuwa sai sunyi da gaske take samu taci, domin ko kaɗan cikin bai sata sha'awar komi ba, bata jin ɗan-ɗano a bakinta.
Wani lokacin kuma idan Aabid ya mata jan ido ne take ci kaɗan, idan ya matsa mata ta ƙara tas take dawo masa da shi.
Hankalinsu ya tashe sosai gudun kada ta haifo musu yaro babu lafiya shi da iyayensa suka sake kwasarta suka kaita ganin likita.
Da ƙyar likitan ya musu bayani akan "Wani cikin yana sa haka, idan ya yi ƙwari zata ci abinci da yawa."
Cikin damuwa Aabid yace "Likita kuma yarona ba zai zo a rame ba?"
Murmushi likitan yayi yana girgixa kai "In sha Allah hakan ba zai shafi rayuwar yaron da lafiyarsa ba, saboda har yanxu baiyi ƙwarin da