Showing 69001 words to 72000 words out of 91747 words
kamar ba shine ya bashi abinci ba.
Labarinsa da na iyayensa ya bashi har zuwa dalilin yima Khadijatu fyaɗe da kuma abin da ya faru na rayuwarsa da 'yarsa, zuwa garin Toni da dukan da suka masa kafin su bashi adireshin Khadijatu.
Jinjina kai Abbie Imran yayi yana jin tausayin yarinyarsa da aka kassara mata rayuwa.
"Ba zance komiba a yanzu. Amma kuma ga Khadijatu nan kana iya tambayarta idan har ta yafe maka, nima zan yafe ma. Dalilin abun da ya samu 'yarka kaji abun da nima naji a tawa zuciyar.
Allah yana adalci akan bayinsa, yana kuma karɓar addu'ar wanda aka zalunta da sauri, shi yasa tun kafin aje lahira yake hisabi a duniya kafin kuma aje can gabansa.
A matsayina na uba nayi alhini amma kuma naji daɗi da kaji zafin da naji a zuciyata. Sai dai ban saniba ko wadda ka zalunta zata yafe maka ba. Kamar yanda ba zan iya cewa ta yafe maka ɗinba, dan mai ciwo shi yasan inda yake masa zafi."
Tashi Aabid yayi ya nufi gaban Khadijatu a karo na biyu "Dan Allah Khadijatu ki yafe min ba dan halina ba, ba dan na isa ba, sai dan girman ƙaddarar da ta ratso a kaina. A yanzu a shirye nake na aureki na gyara kuskuren da na aikata a gareki, zan goge duk wani baƙin fantin dana shafa a jikinki, na dawo miki da martabarki! Na tsaya a gabanki a lokacin da kike buƙatar kariyata! Na miki inuwa a lokacin da rana ta sauƙa akanki! Na zame miki lema a lokacin da ruwa zai sauƙa a jikinki! Dan Allah ki bani danar gyara kuskuren dana aikata akanki." Ya faɗa yana haɗe hannayensa waje ɗaya.
Murmushi ta yi ta miƙa masa hannunta ɗaya "Bani!"
"Me zan baki Khadijatu?"
"Martabar da ka ƙwace daga gareni! rufaffiyar ƙofar da ka ɓalle da ƙumajinka nake so ka maido min da ita! Alfaharina nake so ka dawo min da shi!"
Ido duk mutanen wajen suka zuba akanta suna kallonsu, yayin da shi kuma yake girgiza kansa.
"Ba zan iya dawo miki da wanan ba Khadijatu!"
Tashi tayi tsaye tana kallonsa murmushi na sauƙa akan fuskarta "Tunda har ba zaka iya dawo min da wanan ba, kaga kenan baka can-canta da na yafe maka ba. Nima ba zan iya yafe maka ba, kamar dai yanda ba zaka iya dawo min da abun da ka ƙwace daga gareni ba."
Tana gama faɗar haka ta wuce da sauri tabar falon duk kiran da yake mata bata saurara ta tsaya ba, ƙoƙarin binta ya shiga yi Ishaƙ ya dakatar da shi.
Durƙusawa yayi a tsakiyar falon yana kuka yana buga hannunsa a ƙasa......
🌷🌷🌷🌷
I LIKE THIS PAGE 💃💃
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG......
4700000
Cikin hanzari Likitoci suka ɗauki Aabid suka shigar da shi ɗakin agaji da taimakon gaggawa. Yayin da Amrah ta ke ƙoƙarin binsu tana kiran sunansa kamar zautacciya, ƙofar ɗakin suka ja suka rufe bayan sun dakatar da ita daga binsu da take.
Zubewa tayi a wajen ta fara kuka kamar ranta zai fita, ƙarasawa kusa da ita Mom tayi ta ɗagata "Ya isa haka Amrah! A yanzu addu'armu yake buƙata ba wai hawayenmu ba."
"Mom ta ya zan iya daina kuka? Mijina da 'yata suna cikin wata rayuwa ta halin mutu ko-kai rai ko-kai! Mom ko dai akwai wani abu ba dai-dai ba a cikin rayuwarmu shi yasa Allah ya aiko mana da wanan jarrabawar? Ƙaddara sanadinta da yawa amma kuma tamu kamar ƙirƙira ce Mom!" Amrah ta faɗa hawaye na biyo bayan maganarta.
Rungumeta Mom tayi tana bubbuga bayanta, itama zuciyarta ta karaya da lamarin, ƙoƙarin nuna dauriyarta take dan ta ƙarfafa ma Amrah zuciyata, amma kuma abin ya gagara.
"Ba abun da ya gagari Allah Amrah. Ina da tabbacin zai kawo mana ɗauki akan wanan abun da ke faruwa da mu.
Dukkansu za su samu sauƙi da yardar Allah."
Shuru suka yi ba su ƙara magana ba, sai zama da suka yi jugum-jugum kowa da saƙar da yake ɗaurawa yana kuncewa.
Bayan wani lokaci Likitocin suka fito daga ɗakin, cikin sauri suka tareshi suna tambayarsa "Likita ya Ɗanmu yake?"
Kallon su Likitan yayi sanan "Ku biyo ni ofishina." Likitan ya faɗa yana tafiya gami da jijjiga kansa.
Basu ɓata lokaci ba suka bi bayan likitan da ya dage yake rubuce-rubuce a cikin fayil ɗin Aabid ɗin.
"Ku zauna." ya faɗa yana nuna musu kujerar da ke kallonsa.
Kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki suka zauna gabansu na faɗu "Likita me ya ke damun yaronmu?"
Shuru yayi yana kallon su can ya miƙa ma Dad fayil ɗin da ke gabansu "Dama yaronku yana fama da ciwon zuciya ne Alhaji?"
"Ciwon zuciya kuma likita?" Suka faɗa cikin haɗuwar baki suna dafa ƙirjinsu.
"Eh ya kamu da ciwon zuciya mai ƙarfin gaske, wanda dalilin haka
magudanar jininsa ta cushe wanda hakan yasa jini ya ɓalle a bakinsa da hancinsa.
Maganar gaskiya dai wani mummunan abu ya faru da rayuwarsa, ya kuma kamu da soyayyar wani abu daban, ya kamata ku nema masa wanan abun tun kafin ya kai ga zuciyarsa ta buga.
A yanzu munyi nasarar dai-daita bugun zuciyarsa, amma bana jin nan gaba idan har ya sake riskar kansa a haka zamu iya shawo kan abun."
"Inna lillahi wa inna Ilaihirraji'un! Na shiga uku ni Amrah!" Ta faɗa tana fashewa da kuka mai tsanani "Ya Allah idan wani laifi muka aikata maka ka yafe mana ba dan halinmu ba."
Kama hannunta Mom ta yi tana girgiza mata kai duk da itama hawaye ya ɓalle akan fuskarta "A'a Amrah kada kiyi saɓo. In sha Allah zai tashi."
"Likita ni ban taɓa ganin Aabid a cikin wanan yanayinba, asalima bai taɓa neman wani abu ya rasa ba tun tasowarsa.
Amma kuma duk da haka ace yanzu ya kamu da soyayyar wani abu! Na kasa jure jin wanan abun Likita." Dad ya faɗa cikin tashin hankali yana jin tasa zuciyar na tsananta bugawa.
"To Allah ne ya barwa kansa sani Alhaji. Mu dai abun da muka gani kenan muka sanar da ku, amma idan ya farka zaka iya tambayarsa anan ne zaka fahimci gaskiyar maganata."
"Zuwa yaushe zai farka?"
"Yanzu dai mun masa allurar barci dan ya samu ya huta. Amma nan da awa uku zata sake shi in sha Allah."
"Allah ya kaimu." Dad ya faɗa yana barin office ɗin shi da su Mom.
Sunyi jugum-jugum sun rasa matsaya guda, tashin hankalin da suke ciki ya kasa barinsu tuna mafitar abun da ya kunne a kansu.
A hankali ya ke tako da ƙafafuwansa yana kusantar inda suke, ƙamshin turarensu ne ya ankarar da su wanzuwarsa a wajen, hakan ya sa su saurin tashi suna kallonsa.
Kyakkyawan balaraben da fatar jikinsa ta gama gogewa ta ke sheƙi, gashin kansa ya nannaɗe saboda gyaran da yake samu, yana sanye cikin fararen kaya coat da t-shart sai farin takalmi da farin agogon da ke sheƙi akan hannunsa. Fuskarsa sanye cikin farin gilashin da ya ƙara fito da kyakkyawar fuskarsa da ta samu zagayewar saje a cikinta.
Da gudu Amrah ta ƙarasa kusa da shi bata jira wata-wata ba ta rungume shi sanan ta fashe da kuka mai tsanani "Na shiga Uku Yayanah! Rayuwata ta kusa tarwatsewa ta barni! Nuriee tana kwance rai a hannun Allah ga Aabid shima bai san wa ke kansa ba.
Ya Nabil idan ya mutu nima mutuwa zanyi wallahi ba zan iya rayuwa babu shi ba."
Bayanta ya shiga bubbugawa yana kallon su Dad da suka futa a cikin kamanninsu duk sun yi zuru-zuru kamar su ne basu da lafiyar.
"Ba abun da zai same su, duka za su warke da yardar Allah." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa da bata fita da amo mai ƙarfi, Da kuma hausarsa da bata goge ba har a lokacin.
Kamo hannunta yayi suka ƙarasa wajen su Dad da suka shagala da kallonsa, risinawa yayi ya gaisshe su, suka amsa a cikin rawar murya "Dad Nabil ne fa!"
"Ikon Allah Nabil kai ne haka ka koma balarabe sak? Masha Allah!" Dad ya faɗa yana ƙoƙarin faɗaɗa murmushin fuskarsa.
Shafa kansa Nabil yayi "Wallahi yanzu zuwana ƙasar, to jirgin da na hau na nan Legos ne, shine na biya ta gida na duba Amrah da Aabid dan mun daɗe bamu haɗu da su ba. To kuma sai mai gadi ya ce min kuna nan asibitin Nuriee ba lafiya."
Kai Dady ya girgiza masa "Wallahi fah abun sai hamdala kawai."
"Me ya samu Nuriee ɗin?"
Shuru su kayi babu wanda ya iya magana tsakanin Dad da Mom, haka ya sa ya kalli Amrah "Ƙanwata me ya ke damun Nurieeyah?"
Hawaye ne ya ƙara ɓallewa akan fuskarsa ta fara shessheƙar kuka tana girgiza kai "Fyaɗe aka mata Ya Nabil!"
Kamar sauƙar aradu haka ya ji maganar a tsakiyar kansa "Fyaɗe kuma? Ta ya? Nawa Nuriee take? Inna lillahi wa inna ilahirraji'un." Ya faɗa cikin rawar murya, idanuwansa sun rune sunyi jajir, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗo-raɗo.
"Balaraben da ke kula da ita a makarntar su ne ya mata Labib ƙasim basar. Likitoci sun ce ba lallai ta iya rayuwa ba Ya Nabil!"
"Ina Aabid ɗin? Me yasa ba ku fitar da ita waje ba tun lokacin? Gashi ba ku neme ni ko a waya kun sanar da ni ba."
Wani sabon kuka ne ya ɓalle mata "Aabid bashi da lafiya, tun faruwar abun ya fice sai yau ya dawo mana, ya kamu da ciwon zuciya Ya Nabil, na tabbata damuwar abun da ya samu da ita ya haddasa masa wanan ciwon."
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Nabil ya faɗa yana dafe da kansa.
'Me yake faruwa a wanan ƙasar ta mu? Me yasa matsalar fyaɗe ta yawaita a ƙasar nan tamu?' Tambayar da yayi a zuciyarsa, yana tuna adadun case's ɗin ya ke ta cin karo da su.
"Bari naga likita." Ya faɗa yana nufar ƙofar da yake zargin ta likitan ce.
Bai jimaba sai gashi sun dawo da likitan, kai tsaye ɗakin da Nuriee take suka nufa, tana kwance an sa mata bututun iska a hancinta. Fuskarta tayi fayau kamar yanda jikinta yayi, an sa ƙarfe an raba ƙafafuwanta an lulluɓe su da farin ƙyalle.
Miƙa masa fayil ɗin Likitan yayi "Wanan shine abun da bincikenmu ya nuna mana, wanda ya mata fyaɗen ya shigeta da ƙarfinsa, ya zazzago mata da ƙwayoyin halittarta wanda hakan yasa mahaifarta ta zazzago saboda rashin ƙarfin da ke tare da ita."
Ido Nabil ya runtse yana zare farin gilashin da ke idanuwansa, sai da ya goge hawayen da ya zubo akan idonsa sanan ya mayar da gilashin ya fara karanta fayil ɗin yana ganin abun da ya ƙunsa.
"Ku mana transfer zan fitar da ita India."
"Amma Dakta koda ka fitar da ita asara za'ayi, dan bincikenmu ya nuna mana ba lallai ta iya rayuwa ba a nan gaba.."
"Wanan ba kai zaka yanke hukunci ba Dakta, mu za muyi abun da zamu iya ne, sauran mu barma Allah ikonsa."
"Anan ma ƙoƙarin da muke kenan Dakta! Me zai hana tunda muna da kayan aikin kai ka mata aikin da kake ganin zai iya gyara ɓarakar da ke tattare da ita."
Kallonsa Nabil yayi yaga shima kallonsa ya ke, kafin yayi magana wayarsa ta shiga ƙara wanda hakan ya sashi ɗaukan wayar 'My Khadijaty. Sunan da ke ta yawo akan wayar yana jin kiran na shiga da bugawar zuciyarsa dan.....
🌷🌷🌷🌷🌷
I'm sorry Aabid..
Ya kuke ganin kasancewar NABIL abokin Aabid kuma Yaya a wajan Amrah! Har na hango sadaukarwar da zai ma abokinsa 😄😃🏇[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG.....
490000
Rayuwa na bada sauyi da zaɓi ga ko wani ɗan Adam, sai dai kasawa da gaggawa ta mutum takan sa ya ƙosa akan zaɓin alkhairin da ke gareshi.
Wani ɗan siririyin layin da ya raba tsakanin farin ciki da baƙin ciki, ya haɓɓaka ya keta duk wata alfarma da mutane biyun nan suke da shi. A yayin da igiyar aminci ta datse daga ruƙon da suka ma junansu, zargi, dana sani, da kuma ɓallewar teku daga mahangarsu ya taimaka musu wajen rarrabuwar kawunansu.
Bayan sa'a guda.
Wanan wata sa'a ce da ta naɗe farin ciki da kuma rayuwarsu, hawayen da ke ɗiga akan idanuwansu ya gaza ɗauke ƙuncin da suke ciki. Tun bayan farkawarsu daga suman da suka yi idanuwansu ke hasko musu fuskar kyakkyawar ɗiyarsu, tunaninsu na wullasu wata duniya daban da ta zo ta gifta musu a tare da ita.
Amma kuma kamar suna son ƙaryata abun da idonsu yake, suna so suce mafarki ne da ya ɗaukesu cikin wahalallen barcin da ba'a shirya yinsa ba.
Sai dai dan-dazon mutanen da suka yi karo da su a ƙofar gidan shi ya ƙara daddatsa ko wani sassa na jikinsu. Da gaske ne Nuriee ta tafi ta barsu a wanan duniyar! Da gaske ta tafi tafiya ta har abada da ba zata ƙara dawowa a cikin rayuwarsu ba.
Tun zuwansu mutane suke musu kallon tausayawa da alhini akan fuskarsu, motar da ta ɗauko su bata iddasa tsayawa ba suka ɓalle mabuɗanta suka fito.
Duk a cikinsu babu mai yiwa wani magana, asalima sun zama kamar baƙin halitta ga junansu, a haka suka isa babban palon gidan, suna shiga suka yi karo da wasu dan-dazon matan a zazzaune cikin hijabai da carbi a hannayensu.
Tashi Mom ta yi ta ƙarasa kusa da su ta ruƙo hannayensu, kamar wanda take sarrafa tunaninsu haka suka bita har zuwa palon Dad, suna shiga suka ci karo da gawar Nuriee lulluɓa cikin likkafani, a kwance a cikin makara.
"Tun tuni aka shiryata, sai dai ba'a kaita makwancinta ba ana jiran ku dawo ku mata addu'a da kuma kallon ƙarshe." Mom ta faɗa tana ƙoƙarin matse kukan da ke zuba akan fuskarta.
A hankali suke cira ƙafafuwan su, har suka ƙarasa gaban gawar Nuriee, tsugunnawa suka yi a tare, suna shafa fuskarta "Da gaske dai kin tafi kin barmu Nuriee! Ashe dama rayuwarki ba mai tsayi ba ce? Kin zo ne ki nuna mana fuskarki kana ki tafi ki barmu! Indai har akwai wani hakki nawa da kika ɗauka to na yafe miki Nurieeyyah! Na yafe ki duniya da lahira! Allah ya miki rahama yasa mutuwarki hutu ce a gareki. Ya miki sakayya akan zaluncin da aka aikata miki." Amrah ta faɗa cikin tsananin kuka tana shafa fuskar amrah da suka buɗe.
Daga haka ta tashi ta bar palon ta koma ɓangaranta.
Shima Nabil addu'ar rahama ya nema mata, amma kuma ya kasa magana saboda abun da yake ji ta dunƙule masa a maƙogwaransa.
Da shi aka je aka kaita makwancinta yana gani ya rufe ɗiyarsa da yake sonta fiye da rayuwarsa a makwancinta.
Shine tsanin komi, ƙila badan abun da ya aikata ba da har yanzu Nuriee na raye.
Yana ji yana gani ya baro Nuriee ɗinsa kwance cikin gidanta na gasky, shikenan rayuwar, shikenan duniyar ba komi a cikinta face tashin hankali.
Rayuwarsu ta ƙara hautsinewa dukkansu sun fita a kamanninsu, musamman idan mutane suka musu gaisuwa suna yaban halayyar Nuriee kasancewarta yarinya mai shiga rai, ga shi ko kaɗan bata fushi fuskarta ɗauke da fara'a.
A shekarunta shida na duniya duk wanda ke zaune a gidan yasan alkhairinta, hatta masu aikin gidan sunyi kuka, kasancewar shiga ransu da tayi, itace dalilin ƙarin albashinsu a lokacin da taga ana raba musu kuɗi, sai ta tuna nauyin da ke kansu, hakan yasa tace Dad ya ƙara musu ya musu kaɗan, ko ita tana amfani da fiye da hakan a sati guda.
Shafa kanta yayi yana murmushi bai tsaya ja ba ya ƙara musu albashinsu daga dubu talatin ya koma dubu hamsin.
Wanan alkhairin da ta musu shi yasa su kokawa akan mutuwarta.
***
Bayan Sati ɗaya.
Mutanen da suka zo gaisuwa sun koma gidajensu da garurruwansu, gidan ya dawo daga su sai su, ma'aikatan gidan suna gudanar da aikinsu cikin taka tsan-tsan, basa so suyi koda ƙwaƙƙwaran motsi ne.
Ishaƙ yayi bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya dawo musu da walwalarsa amma kuma abun ya gagara, kamar dai yana ingiza su ne akan su ƙara shiga damuwarsu.
Hakan yasa ya bi iyayensa da suka zo gaisuwa suka tafi jaharsu, sun bar Amrah da kewa mai yawa.
A hankali ta futo daga ɗakinta hannayenta janye da ƙatuwar jaka ta matafiya, fuskarta tayi fayau ta rame kamar da ta shekara tana rashin lafiya.
Komi na rayuwa ya sirema mata, tana ganin ƙawar da ke cikin duniyar ta fice mata akai.
Kai tsaye babban falon da Aabid yake zaune ta nufa, yana zaune da waya a hannunsa yana kallon allon wayar hawaye na zuba akan fuskarsA.
Hoton Nurrie ne yasa a gaba wani tana dariya wani kuma shi da ita, yawanci ma nasa da ita sunfi yawa a cikinsa.
Ja tayi ta tsaya a gabansa ta bubbuga jakarta dan ta dawo da shi hayyacinsa, cikin sa'a ya ɗago da kansa, mamaki yayi ganint sanye da hijab ga kuma wata uwar jaka a hannunta, sai dai baiyi magana ba asalima kallonta yake kamar yanda take kallonsa.
"Aabid ni zan tafi gidan mu, ina so ka bani takardar sakina!"
"SAKI kuma?" Ya faɗa da mamakinsa.
"Saki nake so ka min Aabid! Domin abun da ya haɗa mu ya rabamu, Nurrie ce dalilin da zan ci gaba da zama da kai, amma kuma tunda yanzu babu ita, kaga kenan gara na barka ka wataya a gidan, ka auro Khadijatu da kake so.
NI bazan iya ci gaba da zama da azallumu irinka ba, kai ne dalilin da