Showing 51001 words to 54000 words out of 91747 words

Chapter 18 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

803

zan ke kula da ke fiye da yayannaki.
Sanan kuma mutanen sunce ba za su haƙura ba har sai kin karɓeni a matsayin yayanki."

Ɗagowa tayi da sauri nan suka haɗa ido shi da ita, saurin kawar da idonta tayi ta fara kallon tarin mutanen da suke tsaye a ɗakin, mafiya yawansu mazane masu kala ɗaya, gabanta ne ya shiga faɗuwa musamman da taga sun fara juye kamarsu zuwa ta mugun mutumin.

Da sauri ta dawo da kallonta kan Nabil tana maida numfashi "Na amince dan Allah kace su tafi, daga yanzu kai ne a matsayin yayana. Amma kace su fita su barni kada su cuta min."

Ɗagowa yayi ya musu alama da hannu nan suka fice a ɗakin. Sai lokacin ta sauƙe ajiyar zuciya.
Flask ɗin dake wajen ya buɗe ya haɗa mata shayi mai kauri kana ya zauna kusa da ita "Haaa bakinki na baki!" Ya faɗa yana buɗe nasa bakin.

Kallonsa tayi taga yanda ya buɗe baki kamar ƙaramin yaro hakan ya sata yin murmushi da girgiza kai "Yayana zai zo ya bani!"

"Shikenan ba na kira mutanen su dawo kin karya alqawalin da kika ɗaukar musu."
Riƙe rigarsa tayi idanuwanta sunyi rau-rau ba tare da tayi magana ba ta buɗe bakinta.
Komawa yayi ya zauna ya shiga bata shayin a hankali, duk da ranta a ɓace yake amma sai ƙoƙarin dannewa take gudun kada ya fita ya kira mugwayen mutanen.
'Waima Ina Yayana da Indo suka tafi ne? Sun barni da wanan mai jemammiyar fatar da hanci kamar ya zagi biro.' Ta faɗa a zuciyarta.

"Kina magana da ni ne? Ki yi maganarki ba sai kin zageni a zuciyarki ba!" Nabil ya faɗa yana kallonta.
'Na shiga uku! Ko dai maye ne suka kawoni wajensa?' Ta dake faɗa a zuciyarta zuciyarta kamar tayi tsalle ta faso ƙirjinta.

"Ki daina wahalar da zuciyarki, ni ba maye ba ne! Amma idan kika matsa min da gardama zan iya cinye zuciyarki." Ya faɗa yana kawar da murmushin da ke kan fuskarsa.

"Ni bance maka maye ba! Na dai ce kafi kama da Aljannu. Farinka yayi yawa, idanuwanka kamar na miyau-miyau." Ta ƙarasa maganar tana lanƙwasar da kanta ƙasa.
Dariyace ta ƙwacema Nabil yarinyar nan me take so ta ce masa ne.
"Dama kina magana ashe?" Kai ta girgiza masa, ba ta ƙara magana ba kuma.
Ajiyar zuciya ya sauƙe ko banza yanzu ya san ta yanda zai ɓullowa aikinsa, yana tunanin komi zai zo masa da sauƙi, idan har yayi la'akari da maganar da ta shiga tsakaninsu a yanzu.

"Nurse!" Ya kira ta hanyar danna wata na'ura a ɗakin, nan take sai ga Nurse's guda biyu sunzo, nuni ya musu da Khadijatu da hannunsa "Ku gyara mata jikinta."
Kallonsa ta shiga yi alamun tana jin tsoronsu, da kai ya mata alamun "Zan jiraki." ya faɗa yana gyara zamansa akan kujerar da yake zaune.
Kamata sukayi suka kewaya da ita toilet ɗin sai da yaga sun shige sanan ya tashi ya duba jakarta ya ɗauko mata doguwar riga mai kalar sararin samaniya da aka yima ado da dutsuna launin baƙi da da ja.
Ajiye musu yayi akan gadon bayan ya gyara shi, saboda har sun cire mata robar futsarin da ke jikinta, dalilin gyaran da suka mata, suna son ganin ko aikin da suka mata ya karɓeta.
Ita kanta robar takan sa mutum ya sangarce ya kasa riƙe fitsari a mararsa na mintuna biyu.

Sai da ya gyara musu ɗakin fesheshi da abun ƙamsasa ɗaki kamar ba asibiti ba sanan ya ja musu ƙofar ya fice da niyar kafin ya dawo an gama shiryata.

******

KADUNA, Nigeria.

Tun bayan zamansu a gidan hankalin Indo ya tashi, musamman da takega yanda mutanen gidan suke tafiyar da rayuwarsu cikin nutsuwa babu hayaniya. Ɗan kayan wasan nan ma babu daga karatu sai masu danna waya.
Abun duniya ya taru yayi mata ca a rai, musamman kewar Khadijatu data addabi ruhinta. Babu wanda zai zo yace mata "Indo muyi wasa! Indo abinci zanci! Bani ruwa Indo!" Ido ta lumshe tana girmama lamatin Khadijatu a cikin ranta.

Dukan da aka mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Inna ta gani a gabanta "Anya lafiyarki kuwa Indo? Tun yaushe na shigo amma nayi magana baki ji koda motsina ba.

Ajiyar zuciya ta sauƙe sanan ta yamutsa fuskarta "Inna yaushe Khadijatu zata dawo? Gidan babu daɗi da babu Khadijatu. Inna mu koma gidanmu nan babu mutane ba ƙawaye kullum muna zaune ɗam kamar kwalliyar ɗaki."

Shafa kafaɗarta tayi "Ayya mana INDO! In sha Allah zata dawo da ta samu lafiya. Harda yayanku da Ammu. Amma kafin nan ki bar batun komawa gida domin mun zo kenan, zamu zauna anan tare da Khadijatu da Ishaƙ, kema ki zama 'yar birni. Ko ba kya so?"

Idonta ta rufe cikin jin kunyar maganar da Inna ta faɗa, wanan mafarkinta ne na tsawon shekaru, a rayuwarta tana son shiga babban gari musamman da taji labaransu a gidajen radio da bakin ƙawayenta su Biyutalliya suna ƙawata mata dogayen benin da ke cikinsa.

Sai dai rashin Khadijatu yasa ta manta wanan burin nata, a yanzu burinta ɗaya shine zamanta tare da Khadijatu.
"Inna ina so amma nafi son zama da Khadijatu!"
"Itama zaku zauna in sha Allah. Har sai kunce kun gaji da zama waje ɗaya."

Kai ta girgiza "A'a Inna ni bazan gaji da zama da Khadijatu ba. Ina sonta sosai Inna, kuma itama nasan ba zata ce bata sona ba."
"Tabbas jini ba ƙarya ba Indo, har abada Khadijatu ba zata ƙiki ba."


🌷🌷🌷🌷

WAI yau nayi da yawa ko? 😀 Afwan kuyi malejinsa, in sha Allah da na dai-daita sai kun gaji ganin more pages
Girmamawa
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

    B00000036000000L

  Bayan dawowar su Abbu Yasir aka yima Indo cuku-cukun komawarta makaranta, mai kyau da tsada aka sata.
  Kana Baban Indo da kansa yaje Haɗejia ya sanar da ƙanwarsa Ramlatu sun koma Kaduna da zama, duk abun da faru ya kwashe labari ya bata. Tasha kuka ƙwarai da gaske na nisan da suka mata, amma kuma aure ba wasa ba, ta so ƙwarai ace taga yaran ƙanwarta amma kuma ba komi Allah yana nan idan suna da nisan kwana za su haɗu ne.
  Lokacin da zai tafi ya bata Dubu Hamsin wanda Abbie Imran ya bashi ya bata. Sosai ta sha godiya har tana hawaye, ya bata shawarwarin kula da yaranta.
Har ƙofar gida ta rakoshi suka sai da taga tafiyarsa sanan ta dawo gida tana jujjuya kuɗin da ya bata 'Lallai idan da ranka baka fidda tsammani. Wai Ammu ɗinsu itace ta tsallaka tabar ƙasar, su da basu da kowa basu san kowa ba amma sai gashi rayuwa ta tsallaka da su rayuwa a ɗaya daga cikin biranen da ake ji da su.
  Allah al-hakimu!" Ta faɗa cikin sanyin murya tana share hawayen fuskarta.

   ****
INDIA.

  BAYAN WATA BIYU.
A cikin watanin nan shaƙuwa ta shiga tsakanin Khadijatu da Dakta Nabil saboda kulawar da yake bata, a yanzu ko wata hidima tata shi ke mata, duk da cewa akwai Nurse's ɗin da suke kula da hakan.
Haka kuma ta rage yawan zubar fitsarin da take, dan da kanta take zuwa ta yi da ta ji, wanan wata babbar nasara ce ga Dakta Nabil da sauran ahalinta.
Ishaƙ yayi kuka yayi sallah saboda nuna godiyarsa ga Allah, haka ma iyayenta sunyi farin ciki sosai kusan duk bayan sati biyu suke zuwa su dubata, wanan yasa shaƙuwa sosai tsakaninta da su, har ta fara warewa daga jin tsoronsu da take, tana zama ayi hira da ita, duk da bata sakewa take da su ba, amma tana bada lokacinta wajen kula da su.

Matsalarsu ɗaya Ammu da ke takura musu da yawa faɗa, da kuma sukuntunta.
Haka a ɓangaren Karatu Ishaƙ ya dage sosai yana yi, burinsa ɗaya a yanzu ya zama babban lauyan da zai tsayama mata marasa galihu, waɗanda ake keta musu haddinsu.

****

  Yauma kamar kullum sun fito shi da ita suna zaga asibitin, sai faman janta da hira yake tana murmushi, wajen da ke da taron mutane kuma idan sun zo sai ta ƙan-ƙame jikinta, tana ɓuya a bayansa.
  Har suka fito a harabar asibitin, mutanen da taga suna zirga-zirga ne ya sata faɗuwar gaba, har ta kama rigar Dakta Nabil bata sani ba.
  Juyowa da ita yayi gabansa yana kallon cikin idonta da itama ta kafeshi da nata idon, kai ya girgiza mata "Khadijatu waɗannan fa mutane ne kamar ke anan! Babu abun da za su miki na cutarwa."
  Kai ta girgiza sanan ta maƙale kafaɗanta "Ban san ya zan faɗa makaba Dakta Nabil ka gane! Ina jin ƙirjina na bugawa da ƙarfi duk lokacin da naga mutane, musamman idan a cikinsu akwai jinsin Maza."

  "Ba abun da za su miki Khadijatu! Abun da ya faru da ke ba zai sake faruwa da keba In sha Allah! A cikin mazan da kike gani anan wasu basu damu da yanayin da kike ba, asalima su za su iya baki kariya daga kawo miki farmakin mugwaye.
Ki kalleni da kyau nima ina cikin wanan jinsin da kike jin tsoronsu, amma a cikin zuciyata babu cutarwa! Misali akan Yayanki Ishaƙ shima namiji ne, mai ɗauke da kyakkyawar zuciya.
  Da akwai da yawa a cikin 'yan uwa da dangin da suka kasance maza ne, amma ba suna nufin za su cuta miki ba Khadijatu."
  Hawayen fuskarta ta goge tana ƙara kallon fuskarsa, ba zata iya fahimtar yanayin da idanuwansa suke ba, amma a tata zuciyar yarda ce mai yawa, da amincewa a gareshi, kasancewarsa mutum na biyu da ya kula da rayuwarta fiye da tasa.
   Ya kuma haɗa kanta da ahalinsa wajen bata labarin 'yan uwansa da ƙannenta.
  "Na yarda da kai Dakta, mutanen da suke kewaye da kai ne na kasa yarde musu."
  "Ki ɗauki mutanen a matsayin ke ce, sai zuciyarki ta basu kulawa da dukkanin yarda."
  Murmushi ta yi tana kawar da fuskarta daga kallonsa  "Idan nace maka kana da idanuwan mage sai kace zaka cinye ni! Amma ni har tsoro nake idanuwana su shiga cikin naka."

"Uhm yanzu kam na fasa cinye ki ai! Abu ɗaya kawai zaki yi shine ki horar da matsoraciyar zuciyarki zuwa jaruma! Ƙilan daga nan na fara tunani akan....!"
"Akan me? Ƙarasa mana." Ta faɗa tana wara idanuwanta waje.
Dariya yayi dai-dai lokacin da wayarsa ta shiga ƙara "Rabin raina!" Ya faɗa yana kara wayar a kunnensa.
"Ina shirin kirankifa kika kirani! Yi haƙuri masoyiyata! Nima nayi kewarki sosai, amma in sha Allah da na kammala abun da nake zan dawo."
Shuru yayi yana murmushi shi kaɗai, har zuwa lokacin da aka kashe wayar. Yana bin wayar da kallo kamar yana kallon wanda suka ƙare maganar.

"Da gaske ka kusa tafiya ka barni?"
Muryar Khadijatu ta dawo da shi daga kallon wayar da yake.
Kai ya gyaɗa mata yana lumshe idanuwansa "Wa zai kula da ni?" Ta sake faɗa cikin sanyin muryarta.

"Ni ne zan ci gaba da kula da ke har zuwa lokacin da zaki warke."
Kai ta girgiza ba tare da ta ƙara magana ba, ta koma juya baya ta nufi ɗakinta.
Shekarunta sun gaza ta gane yanda taji a ranta, amma kuma tana jin wani abu ya tsaye mata a maƙogwarnta, ɗaci ya gauraye mata bakinta.
Hakan ya sata haɗe kanta da gwuiwa tana kuka.
"Khadijatu!" Ya kirata ciki sanyin muryarsa.
Kai ta ɗago taga shi ɗinne sai ta sake mayar da kanta ƙasa.
"Me yasa ki kuka?" Ya tambayeta.
"Ina son naga Yayana ka kira min shi!"
"Nima ai yayanki ne Khadijatu!"
"Yayana ba zai yi tunanin tafiya ya barni ba! Duk duniya banda yayan da ya wuce Ishaƙ!" Ta faɗa muryarta na rawa.

Murmushi yayi yana kallonta, sai yanzu ya fahimci inda maganarta ta dosa.
Yana jin farin cikin da bai san na miyeba, wata ƙila saboda Khadijatu ta nuna damuwarta akan shi.
"Cewa za kiyi bakya so na tafiya yarinya!Ba wai ki tsaya kina kuka ba.
Shikenan nima na fasa zuwa gidan."

Ɗago da kanta tayi "Da gaske ka fasa tafiya?"
"Eh! Na fasa tafiya har sai tare da ke."
Murmushi tayi tana rufe hannayenta da fuskarta saboda yanda yayi maganar.


******
LAGOS, NIGERIA

BAYAN WATANNI TAKWAS

Cikin tashin hankali suka nufi asibiti da ita, yanayin gudun da Aabid yake yi ya isa yasa cikinta ƙara hautsinewa.
"Wayyo Allah bayana! Cikina Momy ki riƙe min bayana zai ɓalle!" Amrah take faɗa gumi duk ya jiƙata sharkaf, duk da sanyin na'urar sanyaya motar da ke motar.

Malejin motar Aabid ya ƙara takawa yana jin zuciyarsa na ƙara tsinkewa da lamarin, ashe haka mata suke shan wahala wajen haihuwa? Yanda yaga tana rintse ido ga gumi na zuba a jikinta ya kasa jurewa.
Lokacin da suka isa asibitin tuni likitoci suka iyo ca akanta suka ɗauketa akan gado suka turata zuwa ɗakin haihuwa.

Dakatar da Aabid sukayi, saboda kada ya bisu, amma ya kasa jurewa so yake ya musu jan ido ya nuna musu shi soja ne, da ƙyar Momy ta riƙe shi.
"Haba Momy ta yaya zan barta ita ɗaya ba tare da na shiga ba Momy? Kinaga fa yanda take shan wahala Momy!"
"Kowa da haka ya girma Aabid, idan ka shiga ba zaka ɗauke mata ciwon da take ji ba."
"Amma ai zan kula da ita Momy! Zan mata addu'a ta samu sauƙi wajen fito min da ɗiyata."
"Anan ma zaka iya ai."

Kai ya girgiza bai tsaya sauraran Momy ba ya tura ƙofar ɗakin, nan ya shiga ba tare da ya tsaya biya kallon tuhumar da suke masa. "Ni mijinta ne, zan iya kula da ita kuyi aikinku."
Hannu Nurse's ɗin ta ɗaga musu alamun su barshi ya shiga wajenta, mayafi suka sa suka kare tsakanin cikinta da ƙafafuwanta.
Yayin da Aabid ya zauna kusa da kanta "Aabid dama haka haihuwa take ka dameni sai na haihu? Ka cuceni tunda kasan kai ba kaine mai naƙudar fidda yaronba!" Amrah ta faɗa gumi na zuba akan fuskarta.
Fuskarta ya shafa da hannunta "Ki yi haƙuri ni kaina da nasan da wahala da bazan bari ki haihun ba."

Ciwon ne ya ciyota ta zabura "Ƙarya ne ka sani Aabid! Ka sani! Na daɗe da sanin ka daina sona! Wayyo Umma nah, ka kira min yayaana da Umma nah!
Aabid ruƙe min kaina! Kaina zai ɓalle! Wayyo ruƙe min hannuna zai cire a jikina!"
Duk ya bi ya rikice bai san ina zai riƙe mata ba, asalin ciwon da take ji ba wai na kan bane, ciwo ne tunda ga mararta zuwa bayanta, sai dai tana ji kamar kanta zai ɓalle daga maɗaukarsa.
Ciwon ne ya lafa ta maida numfashinta ta lumshe Idonta "Kasan ya nake ji kuwa Aabid? Ba zaka gane yanda nake ji ba! JI nake kamar rayuwata ce ta zo ƙarshe! Dan Allah idan na mutu ka yafe min, ka kula min da abun da zan haifa! Kacema Ummana ta yafe min, ashe haka tasha wahala wajen samar dani! Wallahi ina sonta sosai, duk duniya ba wanda nake so kamar Ummana."
Hawaye ne ya zuba akan fuskar Aabid bai taɓa tunanin mata suna shan wahala haka a wajen haihuba, musamman yanda yake ganin yara suna yawo kara zube a gari.

Sabon ciwon ne da ya ciwota yasa ta kama hannunsa, kallon ɗan hannun nata yayi yana jin ruƙon har cikin ƙashin hannunsa.
Ido ya wara yana ga yanda take nishi kamar wani rago, sai kuma maganar likitocin da suke cewa "Yauwa ƙara nishi ga shi nan ya taho!"

Hannunsa ta ƙara damƙewa da ƙarfi sai da yaji ruƙon har tsakiyar kansa, daga nan yaji ta sauƙe ajiyar zuciyar, sai kuma kukan jaririya ya cika ɗakin.
"Alhamdulillah!" Ya faɗa yana shafa hannun Amrah da ke cikin ruƙonsa.
Jaririn aka miƙa musu "Muna tayaku murna kun samu ƙaruwa ɗiya mace!"

Hannunsa har rawa yake ya amshi yarinyar "Wow Masha Allah! Amrah kinga kyakkyawar ɗiyarmu!! Ya faɗa yana nuna mata ita.
Ido ta lumshe tana kallon yarinyar da bata da maraba da mahaifinta "Nurieeyyah!" Ta faɗa tana shafa kanta da hannayenta.

"Sunan da kika saka mata kenan!" Kai ta gyaɗa masa.

MAFARIN LABARI!

🌷🌷🌷
Karku manta sai yanzun zamu fara labarin! Inuwar gajimare yanzun ya fara ɗaukan hanya.
Ina fatan shafukan da suka gabata a gareku sun ƙayatar da ku, kun kuma amfana da wasu abu daga cikinsu?
Ina giramama kowa da ke cikin tafiyar IG.
[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG


B000003700000L


Kafin wani lokaci labarin haihuwar Amrah ya cika dangi, tun kafin a sallamosu mutane suke tururuwar zuwa ganinsu.
Alh.Mai tama da kansa ya taso ya zo asibitin, bakinsa har kunnensa yaƙi rufuwa saboda farin cikin da ke tattare da shi. Wanan wata rana ce mai cike da tarihi a cikin jerin ranakunsu na rayuwa.
Momy kam sai juya baby take cike da alfaharin kasancewarta jika a gareta, haka kuma wani tsatso daga jinin jikinta "Dady Aabid kalli yarinyar nan sai tsotsar baki take! Da dukkan alamu mayunwaciya ce." Ta faɗa cikin sigar tsokana irin ta kaka.

Hannunsa ya ke ya shafa fuskarta yana murmushi "Matata ba zata zama mayunwaciya ba, dole za'a samar mata abun da take so."
"Tun yanzu ka fara nuna son kai?"
Dariyar manya yayi wadda ke nuna tsantsar farin cikinsa "Ke baki lura da yanda ta sato kamata ba! Me ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login