Showing 27001 words to 30000 words out of 95282 words

Chapter 10 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6642

plate dina, tace


" Ki cinye tas ko zaa samu ki Dan murmure, ramar nan tayi yawa"


Haka mukaci Amma ko rabi kasa ci nayi saboda cikina yanzun ya Saba a bashi abinci kadan, ni na fara dawowa parlor na zauna Ina kallon wani movie, sallamar Yaya Sarki da Yaya Shehu tasa na maida dubana kansu, suka shigo Basu zauna parlon ba Suka nufi dining sukai joining dinsu, seda suka Gama sannan Suka sakko duka Suka fara Hira, ni bama hi nake ba hankalina Yana kan tab din Mummy dake hannuna Ina surfing internet. Shehu ya dubi Mummy ya matsa gefen ta yace


" Mummy wacece wannan?"


Ta dubeni sannan ta dubi sarki dake kallon ta with so much curiosity tace


" Ki tambayi baban ku"


Sarki ya matsa gefen Abban Rooks ya maimaita Masa tambayar da Shehu yayi, a take ya aje wayar shi yace


" Kun tuna Anty dinku ta Lagos, sister Ummin ku?"


Shehu yace


" Of course! Anty Halima ba! Allah ya jikanta, Taya zamu manta ta. Ina yawan tambayar Ummiey Ina babyn data bari, se tace wai tana Nigeria!"


Abbah ya gyada Kai yace


" She's the Baby! Afiyya is your cousin"


Duka Suka kalloni, intense din kallon yasa na dago se Naga sun sakar min Murmushi, na danyi yake kadan Zan maida kaina kan tab din Mummy ta dakatar dani, ita tayi min bayanin su, nayi murmushi bance komai ba saboda banida abinda zance din. Shehu ya dauki waya ya fita, Sarki Kuma shi ne bashida magana sosae Dan haka duka mukai shiru, Abbah da Mummy sun koma daki, Ina Rooks na tayi Masa hira muakji sallamar Harith da Nadia suna bin bayan Shehu, Ashe zuwa yayi ya kirasu. Naji dadi sosae it was like a mini reunion. Wajen azahar zasu tafi Yaya Sarki yace min nazo muje na gaida Ummin su, har na Mike Zan bisu se nace da Rooks Bari na gayawa Mummy, Ina fada Mata ta hade Rai tace


" A'a kiyi zamanki, fita zamuyi"


Cikin rashin jin dadi na fito I wanted meeting her, ko mutum daya da Zan nuna nace Dan uwan mamata ne, Amma nasan Mummy nada nata dalilin. Ina kallo Suka tafi Rooks ta bisu zata he gaida kakarsu a fada. Yaya Shehu dake tsaye gefena yace min


" Zan zo da yamma, Zaki bani labari kinji?"


Na gyada kaina, Nadia ta Dan rungume ni Suka tafi abinsu.








Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 First bank of Nigeria Aisha Hassan kwalam, send evidence of payment to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 22




" Mom Rooks, Anty Mariya karku manta kokarin karbar Afiyya daga hannun Yaya Sa'idu ma ya gagare mu, balle mu kawo zancen auren ta. Ya kamata kowannne Abu muyi solving din shi one at a time. Amma bamu Gama fita daga wani ba kada mu saka kanmu a cikin wani."


Uncle Babawo ya fada cikin nutsuwa, dukka suka Yi shiru Dan sure he has made a point, Amma Kuma dukda haka suna bukatar abinda zai kubutar damu.


" Yanzun haka yarinyar zata cigaba da Zama a hannun shi kenan"


Ummiey ta dubi Shehu da yayi kalar tausayi tace


" Oya tashi ka fita, manya na magana kana saka musu Baki, bansan Ina kabar manners dinka ba"


Ya mike sumsum ya nufi karamin parlon da muke ciki, kana kallona kasan I was not ok! Gefena ya zauna Yana kirkiro murmushi yace


" Haeee! Tunanin me kike Yi?"


Na girgiza Kai bayna nayi firgigit nace


" Nothing!"


Ya Dan tsira min idanu sannan yace


" Afeey wani ya taba ce Miki Yana son ki?"


Na kalleshi da sauri Ina zaro idanuna waje, na kalli gefena yasan Rooks nake nema, ya danyi murmushi yace


" Tana daki ni dake ne kawai, nasan you're too young for love words Amma Ina ganin su kadai zasui saving din ki da wannan rayuwar da kike ciki.."


Bai Gama ba nace


" Anan Zan cigaba da Zama ko? Kawu Bai yarda ba ko?"


Ya girgiza Kai yace


" No...!"


Nayi saurin katse shi Ina Murmushin takaici nace


" You don't have to lie, nasan Bai yarda ba, dama bana expecting ya yarda, wannan itace rayuwar da Allah ya tsara min"


Yayi shiru yana sauraro na, idanun shi sun tashi da asalin milky color dinsu Dan dama idanun shi ba fararare bane irin nawa, sunyi ja Amma ba jajawur ba, I can see tsagoran tausayina a ciki, he looks helpless yace


" I'm sorry!"


Na Mike tsaye saboda Ina jin gurin yayi min zafi I'm suffocating, na kalleshi nace


" Why? Bakai min komai ba, karka manta ance duk abinda yazowa bawa ya karba, nasan watarana I'll be happy, nasan watarana komai zai Kare, kilan sede labari. I've to live tunda haka Allah ya kaddara min."


" AFIYYA I love you!"


Zan iya rantsewa cewa hatta dogon hannun dake jikin agogo wato second hand ya daina juyawa, tamkar lokaci ya tsaya Haka na gani, komai ya tsaya cak se bugun zuciyata kawai da ya karu, idanun shi cikin nawa, wasu molecules ke fita a nashi suna Shiga cikin nawa, a wañnan shekarun I couldn't comprehend abinda nakeji, se de da muka cigaba yiwa juna kallon kurilla se naji tamkar jiri zai daukeni, cikin sauri nayi shutting idanuna tareda Jan dogon numfashi na koma sofar Dana tashi na zauna jagwab! Nafi mintina biyar kafin a hankali na bude idanuna sede ni daya ce a zaune a parlon, shi din baya nan. Cikin sauri na Mike na bude kofar da zata hada ka da main parlor Amma Babu kowa cikin parlon, na lumshe idanuna na koma parlon na zauna, Rooks ta shigo tana cemin naje Mummy tana Kirana, na Mike tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki na sameta a bedroom dinta. Na zauna gefenta kamar yadda ta nuna min, ta Jima tana min tambayoyi akan makaranta da Kuma yanayin zaman da nake gidan Kawu Sa'idu, Amma mirsisi na ki fada Mata, a ganina Babu wani amfani da zaiyi, tunda dai komawa gidan ya zame min dole se nayi, tace


" Kiyi hakuri da duk yadda rayuwa take zuwa Miki, Allah shi yasan me yake nufi da faruwar hakan, saboda wasu dalilai min Bari ki zauna anan ki karasa makaranta, Kinga na Miki alkawari da kin Gama secondary Zan tafi dake. Kinji?"


Nayi Dan murmushi da zai karfafa Mata gwiwa nace


" Allah ya kaimu Mummy nagode!"


Ina Gama fadar hakan na sauka na fita daga dakin nayi bayan gidan na tsaya, na tsugunna na Kara tashi wani irin abu nake ji cikin zuciyata, Banda tafasa Babu abinda takeyi, na lumshe idanuna da na tabbatar sun kada sunyi ja, jinsu nake har zafi suke min saboda bacin Rai, na Kara tsugunna wa nasa kaina tsakanin cinyoyi na na fara kuka a hankali, na Jima inayi seda naji zuciyata ta Dan rage radadin da take min sannan na wanke fuska na koma daki, Rooks na samu idanunta sunyi jawur tana hada Kaya, na zauna nace


" Me ya samu fuskar ki?"


Tana jin abinda nace se ta fara kuka, na tsaya Ina kallonta Ina ayyana me yasa zatayi kuka da uwarta, da ubanta, cikin gata da kwanciyar hankali kukan me zatayi ita kuwa?


" Wai anan Zaki zauna, Wai ba zamu tafi dake ba"


Naja tsaki nace


" Shi ne kike kuka? Allah ya kyauta"


Ina fadar hakan na wuce toilet saboda wata kwalla ke son zubo min daga idanuna. Wani Abu da Suka manta Babu Wanda yayi tunanin ya gudu Dani, na kanyi tunanin me yasa Suka dinga bin Kan Kawu Sa'idu Basu daukeni min tafi ba. Duk lokacin da wannan tunanin yazo min se zuciyata tace saboda haka Allah ya tsara. Kwana biyu da suka zo gaba daya bana cikin dadin Rai, gani nan gani nan dai, ana uku mukaje Mummy ta duba kayana, ta samu duk an kwashe haka ta loda min wasu, komai seda ta siya min sabo hatta panties, ta bani kudi me yawa tace na boye, tana tsaye na boye sannan ta siya min sabuwar katifa da tafi tawa girma. Washegari ta dawo dani Akan a Daren zasu tafi Kano zasu bi jirgi zuwa Abuja zuwa NY, a wañnan Daren nayi kuka kamar Zan cire idanuna, bana tunanin bacci kodan bacci barawo ne nasan ya dauke ni na farka. Da safe Dana tashi na kalli tsakar gidan hawaye ya kara gangaro min, na dauke su day hannuna nayi alwala nayi sallah sannan na fito ko komawa banyi ba na fara aikin Dana saba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. A wañnan kwanakin shakuwa me karfi ta Kara Shiga tsakanina da Yaya, se na manta da abinda Yaya Shehu yace min Wanda tunda akai abin kullum kwakwalwa ta na tariyo min abin, idanuna na hasko min idanun shi, duk lokacin Dana tuna hakan se nayi gasping kadan, wani irin nishadi nake tsintar kaina a ciki. Haka kunnuwa na Basu gazawa wajen echoing wannan L word din daya furta. Amma influence din Yaya seda yasa gaba daya abin ya daina tasiri cikin Raina da zuciyata, saboda shi se na daina jin wahalar zaman gidan su, saboda shi nayi ta tolerating abubuwan da Zan iya maganin su. Ummiey da suka dawo Kaya ta kawo min sosae sannan tazo ta ganni ta bini da nasihu, ana gobe zasu tafi Istanbul na dawo daga islamiyyar da Mummy ta sani a marakawa, Yaya Shehu zaune yayi kyau cikin carton brown shadda, dinkin kanshi abin kallo ne, idanun shi masu kaifi na kaina dukda Yana sanye da farin glasses Wanda nafi tunanin medical glasses ne, Dan kusan ko da yaushe Yana fuskar shi, kanshi yasa hula wadda ta kafu kasancewar Yana Tara gashi, a hankali se naji yanayin nan ya fara dawowa, na dinga daga kafata a hankali har na Isa inda yake nace


" Yaya! Ina wuni"


Ya bini kallo, inaga Yana mamakin yadda na koma ne tamkar an zuke ni yace


" Me yake damun ki? Kingan ki kuwa?"


Nayi Dan murmushi nace


" Nothing a Little stress"


Ya harareni yace


" Ban yarda ba, see Zan iya Kai karar kawun ki nan wajen human right fa"


Se ya bani dariya dukda he's serious nace


" Human right? Time ne"


Se ya gyada Kai kawai ya fara tambayata yadda nake na Dan Jima a tsaye sannan ya Miko min Leda yace


" I'll miss you so much, tunda like zuwa Nigeria Bata taba min dadin da tayi min irin wannan ba. I've found and uncut gem here"


Na bishi da kallo Ina jin yadda words dinsa ke sinking a hankali ya dage min gira yace


" Take care of yourself, ki tuna Ina sonki da lokaci yayi Zan aureki Inshaaa Allah"


Na tura Baki nace


" Wanne irin aure Kuma? Kai Yaya"


Yayi dariya tareda sunkuyar da Kai yace


" I'm serious ba lallai karamin kanki ya gane ba, just know someone somewhere loves you alot!!"


Wannan kalaman nashi were deeply buried in my heart, Yaya seda ya saka na binne su saboda yadda ya dinga showering Dina da tashi kalar soyayyar. Dukda Bai furta ba Amma ni Kam zuciyata dumu dumu ta kamu da son shi, lokaci lokaci takan tuna Yaya Shehu Amma na yarda Zama wake daya is very toxic, wannan dalilin yasa Yaya Shehu baiyi tasiri cikin zuciyata ba! Duk wannan bidirin iyayen shi Basu sani ba sun tafi bin bokaye yadda zasu karba dukiyar hannun Uncle Babawo Amma Abu ya faskara, ko address din guraren ba su sani ba, se takurar da ake min ta Kara yawaita, Amma idan na fito Naga dansu se naji Babu komai watarana zai wuce. A hakan na Gama ss2 inada shekara Sha hudu, ni kaina na kasa lissafa yadda akai a 14y har nake ss2. Bikin Siyama ya tashi Amma bansan yadda akai ba kamar an binne maganar se ta mutu, tayi kuka kamar zata mutu, nasha jinta cikin dare tana fadin ita guduwa zatayi, ban taba tambayar ta abinda yake faruwa ba.










Junaidu




10years leap!










Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment through 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 21


Ita kadai take ta kallon gurin da Kawu Sa'idu ya tashi tana Kuma tantamar ko tana cikin hayyacinta da har ta kasa magana dashi, ita dai Mummy Abu daya ta sani tunda Suka hada idanu da Kawu Sa'idu taji tamkar an Mata format ne cikin kanta, taji gaba daya tsoron shi ya kamata Wanda tunda take Bata taba ji ba, kasancewar yayi rashin ji Yana yaro Kuma shi kadai ne bashi da madogara a gidan yasa Suka Raina shi, Dan ita se ta ga dama take ce Masa Yaya, lokuta da dama idan kowa ya kasa fada Masa laifin sa to ita ke tunkarar shi ta fada Masa, dalilin da yasa basa shiri ko kadan gasu Kuma sako da sako.


" Mom Rooks seda na fada Miki Yaya Sa'idu..."


" Me ka fada min Tijjani? How do you want me to believe ni dinnan na kasa karbar Afiyya a hannun shi? Dan Allah Bari mana! Me Sa'idu yayi da na kasa fuskantar shi nayi maganaI'm a failure kenan"


Uncle Babawo ya mike ya riko hannun Mummy cikin lallashi shi kanshi he's confuse sosae da sosae, shima when it comes to him baya tsoro dama Tijjani ne me tsoro, shi kuma Abbuna Yana da dauke kai, mutum ne me kawaici shiyasa tafiyar su tayi nisa shida Kawu Sa'idu.


" Mom Rooks ki daina daga murya, tabbas something is fishy kizo muje mu hada Kai muyi tunanin possible solution"


Mummy na dawowa ta wuce mu a zaune a parlor Muna game din whot, ko sannun da muke Mata Bata amsa mu ba, se naji jikina yayi matukar sanyi naji na daina gane su star, carpet, pick 2, general pick and stuffs. Na aje na hannuna tareda ja da baya na jingina kaina da jikin sofa, Rooks ta dubeni tace


" Menene?"


Na girgiza Mata Kai, ta bude baki da niyyar yimin magana taji Mummy na kwala Mata Kira, Haka ta mike ta tafi Babu jimawa ta dawo fuskarta kawai na kalla Naga Bata cikin jin Dadi,whot din ta tattare ta aje gefe tace min


" Mu tafi daki"


Na mike nayi gaba tabi bayana, wani iri nake ji na dinga jin kamar nabi Mummy daki na tambaye ta me ya faru? Ya sukai itada Kawu Sa'idu Amma se naki kawai na hakura, idan nabi a hankali zanji me akace, tunda a kaina ne na tabbatar.






" Kina ganin kukan da kikeyi shi zai samo Miki mafita kenan?"


" Darling ya zanyi? Na kasa tunanin yadda zanyi fa, ko magana kwakwara na kasa Yi a gaban shi"


Abban Rooks ya ruko hannun ta cikin sigar lallashi yace


" Allah ya kaddara zaman ta Bai Kare anan ba se kiyi hakuri kawai, Allah ya San me yake nufi"






Bangaren Ummiey sunata Shirin tafiya maiduguri Dan suyi sati daya sannan se su dawo Ringim su Kara sati sannan su wuce Istanbul. Gaba daya Ummiey ta hautsuna gidan Kai ka rantse da koami na gidan zata tafi maiduguri din, Daddy na zaune shi da Shehu suna kallo ta fito rike da wayatta a hannu,




" Wato Kai kowa Yana aiki Kai shi ne kazo ka tasa TV a gaba kenan?"


Shehu ya kalli Daddy, Daddy ya kalle shi, ya Masa alamar ya tashi, Babu musu ya Mike yace


" Ummiey yanzun me ya rage?"


" Ko sannu ba zaka dinga leko ni kana min ba? "


Ya sauke ajiyar zuciya yace


" Kiyi hakuri Ummiey sannu da aiki, is there any thing I can help with?"


Ta girgiza Kai tace


" Yi zamanka kafin Baban ku yace bullying dinka nake"


Daddy yayi dariya yace


" Ummiey indai tafiya ta tashi ba Zaki zauna ki huta ba"


Nadia ta karaso ta zauna kana kallonta zakaga so much stress a tattare da ita, ta kalli Daddy zatayi magana Ummiey tace


" Kin hada boxes din guri guda, bana son mantuwa fa"


Shehu dake tsaye ya saki dariya, Nadia ta tura Baki tace


" Na hada komai fa Ummiey"


Shehu ya zauna Yana kallon iyayenshi yace


" Ummiey can I share my opinion here?"


Ta gyara zaman ta tace


" Why not? Me ya faru?"


Yace


" Ummiey tunda zamu tafi gobe, me zai hana mu tafi da Afeey Kinga it's an opportunity tayi reconciling da Yan can."


Tayi shiru tana kamar tunani yayinda Daddy dasu Nadia Suma suke kallonta suna sauraron amsar ta, ta Dan kalli Daddy sannan ta maida kallon ta Kan Shehu tace


" Tunanin hakan Bai ma zo min ba, Nads jeki kawo min wayata a bedroom na Kira Maryam"


Daddy ya girgiza Kai yace


" Not Maryam, Afiyya hannun Sa'idu take so shi ya kamata kije ki tambaya"


Ta gyada Kai ta dubi Harith da shigowar shi kenan tace ya fita da mota zasu je gidan Kawu, Daddy ya dubi Shehu yace


" Kaji Ummin ku fa tafiyar da zata iyayi a kafa shi ne har se taje a mota"


Ta harari Daddy, Shehu ya daga hannun shi yace


" Daddy ni dai ba ruwana!"


Sukai dariya daga haka ta fita, cikin saa Suka same shi a gida, tunda yaji zancen zuwanta yasan Yana da nasaba Dani Dan hakan ya Zama cikin shiri, a tsakar gida aka shimfida Mata tabarma ta zauan, dama Harith Bai shigo ba a mota ya zauna. Suka gaisa sama sama ita da Ummaan su, sannan Kawu Sa'idu ya zauna Suka gaisa cikin mutunci, ta dago tana kallon shi kawai suna hada idanu se taji ta kasa magana ganin yadda ta Dan rikice yasa ya Kara rike idanun ta cikin nashi,


" Hajiya Mariya akwai wani abunne? Ai yarinyar na gidan Maryam se zasu koma zata dawo nan"


Ta mike tana fadin


" Ai bansani ba, Bari naje gidan kawai"


Tayi sauri ta juya har ta kusa zaure yace


" Kada ki dauki yarinyar nan kije da ita wani guri"


Ummiey ta juyo a hankali bakinta na San fadin abubuwa Amma suna hada idanu tace


" Ina zan kaita kawai ganinta nazo Yi!"


Ya gyada Kai Ummiey ta tafi tana jin jiri kamar zai kwashe ta, Ummaan su ta fara dariya tana fadin


" Wannan Abu yayi , da bakai Haka ba da tuni komai ya rushe!"


Shima dariya yayi yace


" Gashi Ina juya su yadda nake so, da farko banyi tunanin aikin zai ci har haka ba, saboda malamin Yana tantanmar yiwuwar aikin akan Maryam da Mariya da Babawo, se gashi Kuma yayi"


Ummaan su cikeda farin ciki tace


" Yanzun tunda ka samu wannan se zancen karbar dukiyar ya kamata ka maida hankalin ka akai"


Ya shafa Kai yace


" Da kyar na karbi wasu filaye anan hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login