Showing 18001 words to 21000 words out of 95282 words
Chapter 7 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
Yallabai Babu Wanda ya taba zuwa gidana da sunan sunzo sun ganta, to yazan musu? Ita Mariya ai tana zuwa hutu Ringim, ko yaranku Bata taba turowa ba su ganta, me yasa Bata taba cewa na kawo Mata Afiyya ba. Se yanzun zasui accusing Dina Wai na rabasu da yarsu? Yallabai bazan dinga tura ta gurin su ba suna ganin kamar liability ce, Zan rike yata duk ranar Dana mutu Allah will take care of her"
Daddy ya hargitsa kanshi Yana tuna wannan maganar, tabbas Abbu yayi gaskiya laifi Kam nasu ne bana shi ba, ya tuna yayi ma Ummiey magana tace ita ba yadda zatai, shi ya kamata ya dinga neman su Basu su neme ni ba. Runtse idanun shi yayi Yana tuno sakon da aka fada Masa yanzun a waya cewar kwata kwata bana cikin jin dadi, idan ya ganni bazai gane cewa ni ce ba. Cikin sauri ya tattara kayan da zai wuce dasu gida ya fito daga office din. Chauffeur din shi na ganin shi ya karaso da sauri ya karba suitcase din hannun shi, ya bude Masa backseat bayan ya shiga ya rufe, cikin turanci da accent din can yace
" Sir where are we heading to?"
"Drive me home!"
Daga haka ya karkata akalar motar zuwa hanyar gida, lokaci lokaci Daddy Yana picking calls mostly office related calls ne. A yard din gidan yayi packing sannan ya fito ya bude mishi ya fito da wayoyin shi a hannu Yana kashe su Dan kaidar shi kenan, Yana dawowa zai kashe wayar, baya son stress. A parlor ya samu yaran dukka suna zaune, su hudu, babban shi ne sarki na biyu me sunan shehun borno, na uku Harith se autar su Nadia. Gaba daya Babu Wanda yayi aure, sarki ne ma ake zancen nashi da shehu, Amma Harith ba wani shekaru ne dashi ba balle Nadia shekara biyu ta bani. Suna ganin shi Suka Mike kowa da murna kamar kullum Suka tare shi, shehu ya karba suitcase din shi daga hannun chauffeur daya rako shi, bading din su yayi sannan ya juya,
" Ina Umminku?"
" I'm here Darling! Welcome home"
Ta fada tayi kyau cikin gown da akai Mata ado da stones, fuskar ta tamkar an Ciro tata an saka min, dama ance min Kama take da Mamana, Dan wasu Basu ma gane su saboda Kama, Nima na yadda da hakan Dan akwai hoton su na biki a parlon mu da Kuma na ranar sunan shehu Dana suna na. Fuskarta dauke da murmushi tace
" Ya aikin you look tired and worried"
Ya nufi hanyar dakin shi ta mara Masa baya yace
" Ganin ki ya warware gajiyar, lemme have a quick shower"
Ta gyada Kai tace ita Kuma zata dakko Masa Kaya kfin ya fito. Bayan sun Gama dinner sunyi Hira da yaran Suka koma daki sukai Shirin bacci, ta zauna gefen gado hannunta dauke da water bottle Tasha wasu pills sannan ta dube shi bayan ta Mata masauki akan bedside drawer ta dube shi ya lumshe idanu ya daura hannun shi akan goshin sa, tasan mijin ta tasan idan yayi hakan Yana cikin damuwa ne, hannunta ta daura akan hannun da ya daura akan goshin tace
" Darling how can I help you!"
Ya bude idanun shi ya tashi zaune ya dubeta, she looks disturbed also yace
" Mariya kin taba tunanin makomar yaran mu Bayan mun rasu kuwa?"
Da rashin fahimta tace
" Me ya kawo wannan maganar darling?"
" Kawai ki bani amsa"
Tayi shiru na Dan lokaci kafin tace
" Yanzun Babu zumunnci, ba kowa zai rike maka danka ba idan Babu ranka, gata da zaka ma danka shi ne tarbiyya da ilimin addini da zamani"
Ya gyada Kai yace
" Akwai wayanda sun so suyi hakan Amma Allah Bai Basu dama ba. Kin taba tunanin Ina Afiyya take?"
" Wacece Afiyya?"
Ya girgiza Kai wani haushi Yana Kara Kama shi yace
" Afiyya Yar Halima da Abubakar"
Tace
" Ooh ai Maryam ta tafi da ita NY ba?"
" You failed me Ummin Yara, Baki masan inda Yar Yar uwarki take ba, why? Kin manta tsakanin ki da Halima ne? Afiyya Kun yadda ita Babu me nementa, wallahi Baku kyauta ba"
Tayi shiru ta kasa cewa komai itama once in a while hakan Yana damunta, takan tuno yarinyar Amma ta rasa meye yake hanata nemanta.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence to 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Gama Shirin makaranta, na kalli Nanny dake juya kayana zuwa daidai nace
"Zan tafi makaranta, Amma ba yau Zaki tafi ba ko?"
Tace min
" Eh ba yau ba, kije ki karba abinci ki wuce"
Nace
" To Nanny se na dawo!"
Haka na dauki jakata na fito tsakar gida, wainar gero aka Miko min naci, nasha ruwa sannan muka tafi cikin ayari. Nanny ta fito da kayan ta fara wanke min, Ummaan su na zaune tana tabe baki dama tun can bawai su nayi da Nanny bane Dan hakan itama Bayan gaisawa da sukai Bata Kara bi ta kanta ba. Tayi nisa a wankin Kawu Sa'idu ya shigo, Dan tun asuba yake fita, yawancin se kowa ya tafi makaranta yake shigowa ya karya sannan ya Kara fita Kuma se dare. Ni kaina bansan wanne irin aiki yake ba, zai fita dai ya dawo, su kule a daki su dinga zance da baka San me sukeyi ba. Ta wanke hannun ta ta zauna kamar yadda ya zauna Yana fadin
" Fanta jiya an fada min kinzo, ban shigo gida da wuri ba"
Ta danyi dariya tace
" Har yanzun anan ana fitar dare kenan?"
Yayi dariya shima saboda Mamana tana da Rai takan ce Masa Wai me yakeyi a waje ya Dade har cikin dare? Se yace mata shi baya son sa idanu.
" Nazo Naga yata, har an saka ta a makaranta, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci!"
Yayi murmushi jin Dadi yace
" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"
Nanny ta gyara Zama tace
" Akan me fa?"
" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta tunda ni ke rike da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi na kula da ita..."
Nanny mamaki ya karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da Abbu ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji ba.
" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"
" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake wahala da yarinya Basu ba"
Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace
" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka yake, ya kamata ace komai Kai kake kula dashi"
Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace
" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta Afiyya ce ta makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo ko takaddu gurin Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace musu kawai sede duk wata su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da wani abun fa!"
To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin shi bayan Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny ranta ya mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se ya rike ni, hatta kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya shi, wannan wanne irin rashin zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai yayan shi da komai nasu shi ke dawainiya dasu.
" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin girman ki, ke kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na Miki alkawarin Zan dinga fitar Miki wani Abu a ciki"
Nanny tace
" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"
Ya Mata godiya se tace Masa
" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin makarantar ta"
Yayi dariya yace
" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar makarantar ne ai wannan almubazzaranci ne"
Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga ciki Yana jin burin shi Yana daf da cika.
Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar aiki, yayi aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin Dan kaida ce duk yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam da Jarma na zuke zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama influence din su ne, Amma huzaifa Bai ma taba zuka ba shikam Malam he's always the lead. Bayan an gama maghrib kowa ya Kama gaban shi. Fatima ce da girki tun karfe hudu ta kammalla haka take badai kaga tayi Daren girki ba. Ruwa ta tafasa ta shiga wanka, tana watsa ruwan taji wani kaikayi a duk inda ruwan ya sauka, ta dubi jikinta gurin yayi jawur tamkar ta kone, a gigice ta dubi ruwan tasa hannunta Amma shima hannun tana fito dashi se kaikayi yayi jawur, zani ta daura ta fito a guje tana kwalawa Hajja Huwaila Kira, kafin Hajja ta fito tuni Hasiya ta fito ta same ta tsakar gida tana faman sose sosen jiki, Hasiya tace
" Fatima ya akai?"
Ta kasa magana se nuna Mata take da hannu, tana Susa, lokacin Hajja ta fito itada Amarya suka samu Fatima tana Neman cire zanin jikin ta, ga yaran duk sun zagaye ta wasu a ciki na kuka, hannunta Hajja ta kama Suka shiga daki, Suka fara duba jikinta, duk inda ta Sosa yayi burdi yayi Kuma kwaf kwaf kamar konuwa. Hajja ta Yi shiru Dan ita ta rasa abinda zata ce tunda take Bata taba ganin abin ba, ta dauka hijabi tace da Hasiya
" Ke ki zauna da Yara, ni Kuma da Amarya zamuje general, ki aika a fada ma Malam"
Da hakan Suka Taya Fatima ta shirya,suka samu Keke napep Suka tafi general, kowa idan aka bude gurin gani suke allergy be hakan yasa focus din maaikatan asibitin, sede ana administering drugs din kamar bama shiga suke ba, in fact tunda jikin ba bukatar su yake ba kokarin reacting musu take. Anan Malam yazo ya same su, hankalin shi ya tashi ganin maaikatan sun ce sede su turasu AKTH suga dermatologist kawai, Malam ya karba takardar, ga Fatima ciwon se Kara Hawa take, se ihu take tana Kiran sunan Allah tana su taimaka Mata kaikayi zai kasheta.
A wannan Daren da Junaidu ya dawo ya samu gidan tamkar gidan makokin, yaran na tsakar gida sunyi jugum, Wanda sukai kuka zuwa lokacin sun hakura, Bai bi ta Kan kowa ba ya shige dakin abin shi ya zauna Yana ayyana ya kamata ace zuwa yanzun aikin shi yaci Akan Fatima, tunda kuwa Jarma yace Masa tamkar yankan wuka haka aikin malamin yake, Yana cikin zaune Sega zainab ta leko, tunda sukai abin kudinnan yarinyar ke shishigge Masa tana son ganin ta wanke laifin ta. Yana zaune ta shigo ya dago ya kalleta yace
" Meye?!"
Ta zauna tace
" Mama ce Bata da lafiya!"
Ya gyara Zama yace
" Me ya sameta?"
Ta zauna tana kuka ta fada mishi komai, maimaikon taga ya canja yanayin fuskar shi zuwa tausayi, se taga Yana murmushi, yace
" Abin yazo kenan! Kije zata ji sauki"
Zainab jiki a sanyaye ta fito ta dawo tsakar gida tayi shiru tana tunanin halin da uwar ta ke ciki, Bata Jima ba suka dawo da Fatima dan a wañnan Daren bazasu iya tafiya Kano ba sede zuwa gobe. Ihun da take yasa Junaidu fitowa kofar daki ya zauna, Bai ce musu kala ba Amma se smirking yake Yana kallon yadda Fatima ta Zama Yar bori, sight din kawai dariya yake bashi, ya zauna yaki tafiya Yana hango duk abinda takeyi, gasu Hajja Huwaila nata karbar jike jiken ayatul shifaa daga gurin Malam, Suka zaunar da ita suka Bata Tasha, Yana shiga cikin ta ta fara amai bakikirin, Hajja ta Kira Malam yana zuwa yace wannan sihiri ne Kuma an karya shi, Hajja ta rike kirji yayinda Hasiya da Amarya suka furta
"Sihiri malam!"
Ya gyada Kai yace
" Tabbas sihiri ne! Allah ya Bata lafiya"
Suka saka ta kuskure bakin ta, ta saki ajiyar zuciya ta lumshe idanu bacci ya dauke ta. Malam ya gyada Kai ya juya zuwa dakin shi, daidai dakin Junaidu yaji Yana waya
" Man nake fada maka abin yaci fa, dukda dama ba wani tsawon lokaci zai dauka ba Amma nasan ta karbi wahala"
Ya Jima Yana sauraron magamganun Junaidu Amma ya kasa gane inda zancen ya dosa, shi yaron tsoro yake bashi tunda Suleiman yace ya ganshi tsakar dare Yana Kona wani Abu a kasko shikenan ya koma jin tsoron shi. Shidai yasan kullum Yana adduar Allah ya shirya yaron Amma Kuma har yanzun abubuwan Junaidu Kara gaba suke. Ranar baccin dadi Junaidu yayi, Dan burin shi ya Gama cika. Da asuba kowa ya tashi yin sallah, seda ya Bari kowa ya fita massalaci, masu Yi a gida sun tayar, ya fito Dan shi ba sallar yake ba se jefi jefi idan ya ga dama. Dakin Fatima ya wuce ya sameta tana kan sallaya tana sallah, ya zauna Kan kujera har ta idar Dan ita Bata lura da shigowar shi ba. Tana idar da sallar ya sakko ya nufo ta, da sauri ta juyo zatayi ihu yace
" Junaidu ne!"
" Me kake min a daki? Fitar min daga daki nace"
Yayi dariya yace
" Ba wani Abu nazo nayi Miki ba, daki da kike cewa na fitar Miki daga shi, ai ni Banga daki anan ba. Kinga sakamakon zagi da sharri da Kika min, ko Baki fahimci nine nasa aka Miki sihirin da kikai kaikayin jiya, idan Baki fita harka ta ba Zan saka an Miki wanda Zaki rasa rayuwar ki gaba daya, ko ki haukace, Kuma wallahi zakiyi kyau da hauka.."
Yayi dariya ita Kuma tuni jikinta ya fara rawa, tsabar yadda ta tsorata da maganar shi.
" Idan kinji shikenan kin tsira idan..."
Malam ya bude labulen dakin a zuciye ya Shigo, Fatima da Junaidu lokaci daya Suka Mike, Fatima tayi saurin matsawa gefen Malam Neman kariya, yayinda Junaidu ya tsaya sokoko Yana tunanin abinda zaiyi, Wani Mari Malam ya sauke Masa a saman kuncin sa, yayi baya kamar zai fadi, ya cakumo wuyan shi ya tsayar dashi ya Kara Masa wani, cikin tsananin bacin Rai yace
" Ni Dana zaije gurin bokan! Malamin tsubbu! A gidana"
Junaidu yayi shiru yana kallon Malam dake janshi har ya kawo shi tsakar gida, dake fadan malam yasa duk sun firfito Dan ganin meke faruwa, duk suna tsakar gidan yasa Sukai carko carko suna kallon Malam da Junaidu a hannu, ga Fatima a gefe se hawaye ke bin fuskarta!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria send evidence to 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 15
Dukkan su lokaci guda suka Isa Kiran da Junaidu yayi musu, ba karamin mamaki sukai ganin shi zaune da katun katun din jakunkuna, huzaifa ya fara fadin
" Me ye wannan? Se kace zaka bar duniyar"
Yayi Dan tsaki Yana kallon Malam dake zuge jakar da tafi kusa dashi Dan yaga abinda ke ciki,
" Wai korata akai daga wancan gidan"
Jarma yace
" Wai Malam ya Kore ka kenan? Da gaske?"
Harara Junaidu ya watsa Masa yace
" Da Bai koreni ba ta Yaya Zan dakko uban kayannan"
" Allah ya huci zuciyar ka Man, abinne da bamu kawo ba. Yanzun me zaayi kenan"
Ya fada Yana sassauta murya Dan ya lura Junaidu a fusace yake. Jarma yayi shiru yana kokarin tunanin mafita, se can yace
" Kai me ka shirya? Meye plan din ka"
Yayi murmushi yace
" Kudi nake son nayi yadda watarana se sunzo sun nemeni sun nemi gafara ta, sun Kuma nemi kudin abinci daga hannuna"
" Wannan haka yake Man, shi ne hukuncin su na yin watsi da kai, da korar ka da sukai. To Amma hakan bazai faru ba se mun nema kudi"
Jarma ya gyada Kai yace
" Ni na fara jin watarana zaa koremu muma, Dan haka mu je mu karbo saa sannan se mu zo mu fara sanaa mu Gina kanmu!'
Da wannan shawarar Suka tafi can shagari Suka sama Masa shago na haya, suka biya kudi seda yayi settling kafin suka fita Suka barshi Dan sun fahimci Yana son kebewa. Kwanciya yayi ya lumshe idanun Shi ya fara tunanin yadda zaiyi yayi kudi ya dauki fansa!
Kwana biyu na daina shiga harkar kowa a cikin gidan, hatta su Mino da muke Dan magana dasu na daina, aikin duk da nasan nawa ne ni zanyi tun kafin ace nayi na tashi nayi, duk yadda take kokarin ganin ta dakeni batada wani dalilin dukan, abinci idan an bani naci idan baa bani ba na hakura Nasha ruwa. Yaya kadai nake ma magana, Amma shi kanshi Kawu Sa'idu da naji muryar shi Zan koma daki Dan Kar ma mu hadu, shima Bai tambayi inda nake ba. Na fito daga wanka naji ciwo a marata, na cigaba da daurewa na saka uniform, na dauki madubi Ina kallon fuskata, Ina cikin mutane masu doguwar fuska, oval shape, ni ba fara bace fatata me duhu ce dukda duhun ba can can ba Amma nasan kala biyu Allah ya halitta fari da baki, Babu wani tarwada Dan hakan ni baka ce, inada gashi Dan banida goshi, kusan gashina har girata ya hadu, idanuna suna da haske da hakorana, farare ne tas, hakorana Yan kanana a jere se dimple da nake dashi Wanda ba se nayi dariya ba yake lotsawa ba, ko magana nayi zakaga ya lotsa, wannan shi kadai ne marabata da Mama, Hajiya tace min ita batada dimples Amma Ummiey na dashi.
Na Kara kallon madubin Ina ganin yadda idanuna sukai kwala