Showing 9001 words to 12000 words out of 95282 words

Chapter 4 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6644

na fara gaida Ummaah ta amsa tana cewa Mummy Bari ta karaso. A cikin su Babu Wanda yayi min magana Nima haka, seda ta gama sannan ta dakko kujera ta dawo gefen Mummy ta zauna, nayi jugum Ina bin gidan da kallo, Ina ayyana wacce rayuwa zanyi Kuma a gidan, gidan Kato ne sosae, sede anyi rashin basira a ginin, an bar katon tsakar gida Amma Kuma anyi dakuna biyu kawai se kitchen Wanda bama amfani take dashi ba se bayi guda daya, ta can gefe wajen zauren gidan shi ne dakin dasu Yaya suke ciki, gidan mu na Abuja ya fado min, my spacious bedroom, parlon mu, garden da komai na jin dadin rayuwa. Ina wannan tunanin har bansan sun Gama magana ba se da naji ta taba ni sannan na kalleta ta min alamar na tashi , na kuwa Mike na bi bayanta, Mino ta raka mu dakin, Babu komai se katuwar katifa an gyara ta da bedsheet, daga nan Babu komai, Mummy ta gyara min zaman akwatina na, ta nuna min komai inda yake sannan ta dakko kudi tace min na boye inda ga amfani dashi kadan kadan idan ya Kare zata Aiko min da wani. Ta Kara min nasiha sannan ta tafi ta barni a tsaye a tsakiyar dakin nayi shiru Ina tuna Abbu. Bansan iyakar lokacin da na dauka a tsaye ba seda naji muryar Mino tace min nazo Ummaan su na Kirana, na fito a sanyaye naje na tsaya nace


" Gani!"


" Dallah samu guri ki zauna"


Na koma na zauna aka Miko min Yar karamar silver da tuwo a ciki, na kalla tuwon ban ma gane miyar dake ciki ba saboda abinda aka haska gidan dashi ya fara disashewa, na wanko hannu na saka hannu na tasting miyar first se naji kuka ce, na Dan saki jiki naci Amma se half way naji cikina ya koshi, Dan hakan na tsame hannuna Amma tsoron cewa nake na koshi, se na ta juya hannuna a ciki, se can naji Hafsa da Siyama dake bayana sun fara fada, hankalina haya kansu Amma Ina jin fadan sede ba zance ga dalilin fadan ba, Ina zaune naji Mino tazo kaina tace


" Ummaah Bata cinye ba"


" Karba ki bawa Hafsa, ni abinda ya rage anan na babanku ne dasu Baba"


Nayi saurin cire hannuna tace min


" Kin koshi?"


" Kar ta koshi Mana, tun karfe nawa na zuba Mata abincin, Wasa ake?"


Haka Suka karba abincin Suka bawa Hafsa, na mike na wanke hannuna ina share hawayena na tuna yadda Abbu zai ta lallaba ni har se naci abinci, na wanke fuskata nayi alwala nazo nayi sallah, Ina cikin sallahn naji sallamar Yaya, daga yanayin yadda yake fadin


" Ina Afiyya?"


Nasan Yana cikin farin ciki, Amma response din Ummaan su ya Sagar Masa da gwiwa


" To uban shishiggi, daga shigowar ka ko ni baka tambaya ba se kanwar uwarka Afiyya, gaba daya ku tsaya ki jini man, Afiyya tazo ta zauna bance kowa ya zurfafa muamula da ita ba, bana son kawance ko shishigge mata, ba wata bace, itama ya ce kamar kowa. Ka dauki abinci kaci"


Yayi shiru duka suna sauraron ta, Yaya yace


" Kai Ummaah, Afiyya abar tausayi ce fa, ya zaai ba zamu jata a jiki ba"




" Mhmm kanwar uwarka ba, Dole Ina fada kana mayar min"


Baice Mata komai ba ya dauki kwanon shi ya fita, na Jima a zaune sannan nace da Mino dake zaune gefena,


" Zanyi bacci, Ina Zan kwanta?"


Ta kalleni sannan ta kalla gefen Ummaan su tace cikin kasa da murya


" Ko fadawa Ummaan mu"


Nayi shiru Ina tsoron tunkarar ta, anan nayi ta guangyadi sauro ya samu ya cije ni son ranshi, se Susa nake, can Siyama ta tashe ni tace naje mu kwanta, haka na Mike nabi bayanta, Ina ayyana yadda zamuyi bacci akan katifa mu hudu, lucky enough Ina zuwa na tarar an Yar min da Yar karamar katifa irin 6x6 dinnan, net ta Mika min na daura, na rike net din Ina tunanin to ya Zan daura, Mino ganin Ina tsaye ta min bayani tana jin motsi tayi shiru, se na fahimci they all want to be nice tsoron iyar su suke. Wani irin dauri na Masa na Shiga na kwanta, gaba daya ya kwanta a fuskata Dan haka da asuba na tashi nayi alwala naji fuskata kamar an zuba Mata barkono, na cije bakina Ina kokarin danne azabar da nake ji, a hakan nayi sallah duk suna bacci Basu tashi ba, gwara Yaya Ina ban daki naji motsin shi. Anan bacci ya daukeni se fadan Hafsa da Siyama ya tasheni, na tashi na cire net din fuskata na azaba kamar zata kwakwabbo, na gaida Mino dake cemin na tashi na kwashe kayan shimfida ta, nace Mata


" Kinga fuskata zafi take min"


Na fada Ina yatsina fuska, da a gidan mu ne da tuni na tada hankalin kowa kilan se an kaini asibiti, ta taba fuskar tace


" Net ne, zai warke kinji"


Na gyada kaina, anan ta nuna min yadda Zan saka yau sannan na kwashe kayan muka fito, ta bani tsintsiya Wai nayi shara, na kalla tsintsiyar na kalla tsakar gidan na saki ihu a kaina, Ina neman agaji a gurin Allah!








AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam first Bank of Nigeria, send evidence to 09063467258.










ShatttzzzxDake yan class din sun fara lesson a month ago se ya zamana sunyi nisa a physics din, motion shi ne topic din da ya rubuta a jikin board, Amma kafin ya fara bayani Kan motion din seda ya tambayi Yan class Wanda zai iya recapping abinda aka koyar. Sauda dake kusa Dani ta daga hannu, hakan yasa malamin yayi pointing din ta ta tashi ta fara bashi amsa, ta Jima tana bayani kafin Kuma yace ta zauna bayan yasa an tafa Mata. Na kalleta Bayan ta zauna nayi Mata murmushi itama tayimin. Babu dadewa ya shiga bayani Alan motion, nayi shiru Ina assimilating abinda yake fada, haka Ina jotting points where necessary. Seda ya Gama sannan ya mikawa class rep note din yace ta rubuta Mana a board ya fita gaba daya. Na sauke ajiyar zuciya na kalla Sauda nace


" Sauda Dan Allah naga note book dinki"


Tayi murmushi ta Miko min tace


" Amina kinada kyau!"


Nayi murmushi kawai Amma ko godiyar compliment din banyi ba, na bude na fara kwafar note dinta, dake inada sauri Kuma Yan class din sun tsaya Wasa ko fara rubuta sabon note din baayi ba yasa na Gama kafin wata period din ta shiga. Nutsuwa nayi inata going through Dan na samu na iya abinda aka koyar. Ina cikin Yi se ga wani malamin ya shigo me maths, wani young guy haka, muka gaishe shi yayi abinda zaiyi ya fita, har lokacin Babu Wanda yayi noticing Dina a ajin, a ranar da aka tashi Sauda ta Ara min books dinta Dan naje na kwafa. Ana tashi na hada books Dina na saka cikin jaka na dubi Sauda na Mata sallama, se sauran dake kusa damu da bansan sunan su ba na musu sallama na fito Ina kallon yadda kowanne dalibi ke kokarin tafiya gidansu, se na tuna tawa rayuwar a NTIC. Na girgiza Kai kawai na fara tafiya a hankali, ga Rana ga zafi ga Yunwa, Amma haka na nufi gida bakina ya bushe saboda kishin ruwa. Tun daga kofar gida na hango Yaya a tsaye Yana magana a waya, cikin sauri na karasa Ina hango murmushi kwance saman fuskar shi, na karasa kafin yayi min magana ko ni nayi ya Miko min wayar shi, na karba na Kara a kunne ba tareda na duba me Kiran ba.




" Hello Afeey darling!"


Kadan ne Bata kashe min dodon kunne na ba saboda ihun da tayi, na saki dariya a hankali Ina kallon Yaya da ya lumshe idanun shi Yana kallona nace


" Rooks! I missed you"


Tace min she missed me too sannan tace


" So fada min ya makaranta? Yau ranar ki ta farko how do you find it"


Tambaya dai a gurin Rooks ba daga nan ba, na zauna kan bencin da Yaya ya janyo min na fara fada Mata komai akan makarantar, a karshe nace Mata


" Nafi son waccan ta Abuja, saboda idan na dawo gida Ina tarar da Abbu da Nanny a gida!"


Seda na fada naji idanuna sun ciko da kwalla, itama a yanayin yadda tayi min magana nasan jikinta yayi sanyi, na danyi murmushi me ciwo nace


" I've to live Rooks ko Dan nayi ma Abbu da Mama addua, I've a reason to live"




" Yawwa Afeey, kiyi addua komai zai zo da sauki. Yanzun kin fini class!"


Nayi dariya na gama tsokanar ta, cewa ya kamata ta fara Kirana senior, I'm not match for her Dan kuwa na fita aji yanzun. Haka muaki sallama Raina fari Kal, duk gajiyar Dana kwaso se naji ta Dan tafi. Na Mika masa wayar Ina murmushi nace


" Thank you Yaya!"


Yayi murmushi Yana kallona so intense yace


" Ya makarantar?"


Na amsa da alhamdulillah sannan nace Masa Zan shiga gida bayan na kara Masa godiya, I felt his eyes trailing on me har na shige gidan. Ina shiga na tarar dukka sun dawo, da sallama na shiga, Mino ta amsa min tana fadin


" Ina Kika tsaya?"


Na danyi shiru Ina tunanin abinda zanyi cooking, se nace


" Mhmm! A hankali na dinga tahowa"


Ta gyada kanta na shiga ciki na cire kayana sannan na fito nayi wanka, tunda naji gidan shiru nasan Ummaan su Bata nan, Nima ban tambaye ta ba Dan idan Bata nan gidan yafi Dadi. Abinci muka ci sannan nayi shara na dawo na fara kwafar note, sallamar Ummaan su naji, na daga labule na Mata sannu da zuwa, ta amsa sannan tace na aje littafin nan nazo na Mata wanke wanke, na bude baki da niyyar ce Mata ai nayi tawa sharar tunda dama shi ne aikina, Amma se nayi sealing bakina kawai na tattara littatafan na aje na fito, dogon hannun rigar dake jikina na nannade na hada kayan wanke wanken guri daya na zauna, na fara a hanakli kamar me wanke Raina, nayi nisa ta leko daga daki ta kwalla min Kira, bafa Afiyya take cemin ba sede tace min


" Ke!"


Shikenan Kuma Dole na amsa, hannuna na dauraye, kafin na karasa dakin naji sallamar Yaya Yana kwalla min Kira, na tsaya tareda juyowa kawai se Naga Nanny a Bayan shi, na cire slippers din kafata na ruga a guje na fada jikinta, na kankame ta kamar Zan koma cikin ta, ta rungume ni itama, na saki dariya wadda take so genuine and sincere nace


" Nanny!"


Ta Kara rungumeni, bana tunanin Zan manta farin cikin da naji a wannan ranar, da na sake ta Kuma se na fara Kuka me ciwo, na tuna gida na tuna beautiful moments din da mukai tare, na tuna Abbuna. Na rike hannun ta na dinga kuka Ina jin tamkar Ina shading dukkan bakin ciki, da gajiyar Dana kwasa a wannan kwanakin. Ummaan su ta fito dasu Mino dake daki, ta hade Rai tana hararata da ni bama lura nayi ba. Lallashina ta shiga Yi sannan na dakko Mata kujera nace ta zauna, se lokacin ta lura da Ummaan su Suka gaisa ni Kuma na koma kan wanke wanken da nake, Ina wanke wanken Ina Mata tambayoyi tana amsa ni, su kansu nasan Basu taba sanin inada surutu har haka ba. Na Gama wanke wanken tana ta Bina da kallo har na Kai kwanukan kitchen tana zaune, fuskarta na nuna tausayi da Kuma mamakin wata daya yadda na koma wata daban, tana zaune na hura wuta kafin ta Gama kamawa na leka nace da Ummaan su me zaa dafa, tace na Kira Mata Mino na tafi gurin Nanny. Ina Shiga daki da Nanny Sega Yaya, ya shigo hannun shi da Leda ya bani, ruwa ne me sanyi da carbonated drink, nayi murmushi na Masa godiya, na bude Mata na Bata Amma se kallona take, na riko hannunta nace


" Nanny naji dadi da Kika zo, kullum se nayi addua ko ke ko Uncle Babawo wani yazo, Allah ya amsa addua ta"


Se Naga hawaye suna sauka daga fuskarta, nace


" Me yasa kike kuka Nanny, kin tuna Abbuna ko? Ina Masa addua kullum bana mantawa"


Ta riko hannuna tace


" Me yasa Kika rame? Baki cin abinci ne? Ko aiki kike da yafi karfin ki?"


Yarinta ce tsagoro a tare dani, ga wautar Yan fari, ga gabuntar autanci na zauna na fada Mata duk halin da nake ciki, na Kara cewa


" Nanny Babu dadi anan, komai Babu dadi, rayuwar gaba daya Babu dadi, dama haka kowa yake komawa idan baban shi ya rasu ko Kuma ni ce Kawu Sa'idu baya so?"


Ta girgiza Kai Amma ta kasa magana, se ta rungume ni a jikin ta, mukai sallah, a Jakarta ta fito min da foiled kaza, na kalleta na Kara rungume ta, na zauna naci nayi nak, Dan haka da aka bani jollof din taliya nace na koshi. Guntun lemon da tayi na shanye, wa yaga komai se da dalili Kuma an Dade Baa hadu ba. Ranar bacci nayi me dadin gaske, dukda katifar ta matse mu Amma ban damu ba. Da sassafe kamar kullum na tashi na fita shara na hura wuta sannan na gama nayi wanka na dawo na tarar ta bude akwatina na, ta dubeni tace


" Ya akai duk kayan datti a ciki?'


Nace


" To Nanny bazan iya wankewa ba"


Ta gyada kanta kawai, ta fito dasu, wankakkun kadan kawai Suka rage!






AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, first Bank of Nigeria Aisha Hassan kwalam, send evidence through 09063467258






ShatttzzzxNa Gama Shirin makaranta, na kalli Nanny dake juya kayana zuwa daidai nace


"Zan tafi makaranta, Amma ba yau Zaki tafi ba ko?"


Tace min


" Eh ba yau ba, kije ki karba abinci ki wuce"


Nace


" To Nanny se na dawo!"


Haka na dauki jakata na fito tsakar gida, wainar gero aka Miko min naci, nasha ruwa sannan muka tafi cikin ayari. Nanny ta fito da kayan ta fara wanke min, Ummaan su na zaune tana tabe baki dama tun can bawai su nayi da Nanny bane Dan hakan itama Bayan gaisawa da sukai Bata Kara bi ta kanta ba. Tayi nisa a wankin Kawu Sa'idu ya shigo, Dan tun asuba yake fita, yawancin se kowa ya tafi makaranta yake shigowa ya karya sannan ya Kara fita Kuma se dare. Ni kaina bansan wanne irin aiki yake ba, zai fita dai ya dawo, su kule a daki su dinga zance da baka San me sukeyi ba. Ta wanke hannun ta ta zauna kamar yadda ya zauna Yana fadin


" Fanta jiya an fada min kinzo, ban shigo gida da wuri ba"


Ta danyi dariya tace


" Har yanzun anan ana fitar dare kenan?"


Yayi dariya shima saboda Mamana tana da Rai takan ce Masa Wai me yakeyi a waje ya Dade har cikin dare? Se yace mata shi baya son sa idanu.


" Nazo Naga yata, har an saka ta a makaranta, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci!"


Yayi murmushi jin Dadi yace


" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"


Nanny ta gyara Zama tace


" Akan me fa?"


" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta tunda ni ke rike da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi na kula da ita..."


Nanny mamaki ya karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da Abbu ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji ba.


" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"


" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake wahala da yarinya Basu ba"


Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace


" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka yake, ya kamata ace komai Kai kake kula dashi"


Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace


" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta Afiyya ce ta makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo ko takaddu gurin Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace musu kawai sede duk wata su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da wani abun fa!"


To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin shi bayan Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny ranta ya mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se ya rike ni, hatta kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya shi, wannan wanne irin rashin zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai yayan shi da komai nasu shi ke dawainiya dasu.


" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin girman ki, ke kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na Miki alkawarin Zan dinga fitar Miki wani Abu a ciki"


Nanny tace


" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"


Ya Mata godiya se tace Masa


" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin makarantar ta"


Yayi dariya yace


" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar makarantar ne ai wannan almubazzaranci ne"


Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga ciki Yana jin burin shi Yana daf da cika.




Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar aiki, yayi aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin Dan kaida ce duk yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam da Jarma na zuke zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama influence din su ne, Amma huzaifa Bai ma taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login