Showing 21001 words to 24000 words out of 95282 words

Chapter 8 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6641

kwala saboda yadda duk na rame, hancina ya Kara kankacewa dama ni banida hanci, haka yake Dan dus, kumatuna duk sun zagwanye. Na lumshe idanuna Ina ayyana abubuwa da dama a cikin zuciyata. Mino tace min


" Zaki makara fa Afiyya, ki tashi ku tafi"


Ita ta fara neco so ba kullum take fita ba, na Mike bance Mata komai ba na zura hijab na dauki jakata na fita tsakar gida, na samu suna cin wainar flour da aka soya da safiyar. Ta kalleni tace


" Kizo ga Taki"


Na Isa gurin na dauka Naga kwaya daya ce kamar ma irin kalen robar ne da ya rage aka soya min, wani Abu yazo wuyana ya tsaya, kamar na wurgar nace ba zanci ba Amma se na tuna dukan da naci cikin satin, hakan yasa na zauna na cinye na goge hannuna sannan nace na gode muka fita. Yaya ma samu a kofar gida Yana zaune Kan wani bench dake gurin Rai da rai, ya Mike ganin mu. Siyama ya mikawa naira dari yace ta siya Abu ta siyawa Hafsa, karba tayi ta ja hannun Hafsa suka wuce.


" Have you eaten?"


Ya fada Yana zura hannun shi cikin aljihun wandon jikin shi, nayi murmushi tareda gyada Kai, ya jinjina Kai yace


" Kinyi azkhar? Amma face dinki looks disturbed"


Nayi saurin shafa fuskata tareda Kara yin murmushi nace


" Yes and I'm fine"


Se yayi shrugging shoulders din shi ya Miko min dari biyu yace


" Karba ki tafi, nasan Baki ci abinci ba, use this to buy something and I won't take no for an answer!"


Ya zanyi hakan na saka hannuna na karba na mishi godiya, na juya Ina jin wani sanyi Yana ratsa min jikina, da zuciyata, na saki murmushi daidai jin an Kira sunana, juyawa nayi na ganshi a tsaye ya harde hannayen shi a kirji Yana kallona a sanyaye Yana murmushi, na tsaya tareda tsare shi da nawa idanun, ya matso inda nake tsaye yace


" You're beautiful Afiyya, I love your dimples and..."


Se na rufe fuskata da tafikan hannuna Ina sakin karamar dariya wadda shi dayake jinta seda ta narkar Masa da zuciya har ya gagara karasa abinda yayi niyyar fada. Juyawa nayi da sauri na nufi makaranta, Amma kunnuwana se echo muryar shi suke min na abinda ya fada, lokaci lokaci se na shafa dimples din nawa na saki murmushi. Ina zuwa gate Naga an fara Taran makara, na karasa Naga su Siyama ne Dan ita tana ss2 Kuma tunda Babu ss3 Dole su zasui taking charge, tsuggunawa nayi kamar yadda kowanne late comer ya tsugguna, daga can naji Siyama a gefena tana fadin


" Ina Kika tsaya? Yaya ne ya tsayar dake ko?"


Na gyada Mata kai, tuna sunan shi sena fara picturing fuskar shi Yana min murmushi, nayi saurin runtse idanuna Dan na bar ganin fuskar shi. A cikin prefect din naji wata tana cewa Siyama


" Har yanzun wadda Kika daukarwa excuse din Bata zo ba?"


Siyama ta kalleni sannan tace


" Gata tazo"


Ta fada tana nuna musu ni, a take akace na wuce class, na kalli Siyama na Mata Murmushin godiya sannan na wuce class na samu malamin English din Bai riga ya shiga ba, na sauke ajiyar zuciya na zauna gefen Sauda dake fama da phrasal verb cikin comprehensive passage,


" Yawwa Amina Abubakar tun dazun nake jiranki, me yasa Kika makara yau?"


Na Mika Mata hannu mukai musabaha nace


" Ki Bari kawai, surutu na zauna Yi"


Tayi dariya tace


" Ke da har surutu kike? Lallai Kam! Kinga duba min wannan kamar adverbial phrase ko?"


Na gyada Kai daga haka na shiga nuna Mata na time, na place da sauran har malamin ya shigo.




A tsaye Dana bar Yaya, Bai matsa ba ya cigaba da bin bayana da kallo har na kulle ya shafa Kan shi tareda Ciro wayar shi dake ringing cikin aljihu, baikai ga picking ba yaji muryar abokin shi Nuhu Yana fadin


" Naga dalilin palpitations yau"


Yaya ya daga kanshi Yana Sosa Kai ya dubi Nuhu dake dariya kasa kasa yace


" Doctor! Me kake nufi"


Ya samu guri ya zauna, shima Yaya ya zauna Suka gaisa sannan Nuhu ya dubi Yaya yace


" Engr. Kwanaki ka kirani akan kana tuannin kamar heart failure na damun ka?"


Yaya ya shafa Kai yace


" Eh lokacin gaba daya yadda kasan ana farautar rayuwata ne, Ina jin yawan faduwar gaba matsananciya, wani lokaci har haki nake fa, but yanzun na daina ji"


" Haka kurum kake hakan ko se kaga wani Abu?"


How is he supposed to start saying se ya ganni sannan wannan symptoms din ke zuwa, Dr Nuhu yace


" I guess waccan yarinyar ita ce dalili ko?"


Ya kalle shi da sauri Yana kokarin musawa Nuhu ya dakatar dashi da fadin


" No! Ita ce. Bari na fada maka gaskiya sonta kakeyi, you're deeply in love with her sosae, Ina fatan ka fahimci hakan?"




" Yarinya ce bana tunanin tayi 15 yrs ma"


Nuhu yayi dariya yace


" Baka ji ba akace age is just a number ba! Ai ya mafi Dadi gidan ku daya, tana yarinya se ka kissima Mata sonka cikin zuciyar ta"


Yaya yayi shiru yana ta aunawa a karshe yasan hakane so na yake Amma Yana hango how possible is it muyi aure?












Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 17


Kamar yadda Nuhu ya bashi shawara kawai ya fara yada propaganda din shi akaina, hakan yayi, ni kaina bazan iya ce muku ga yadda akai ba, kawai dai nasan na ganni tsumu tsumu a cikin soyayyar shi, bazan ce ga ta inda aka fara ba Dan Nima banyi aune ba se kawai jina nayi deeply in love with him. Da farko dai nasan ya tsiri Yi Mana lesson, duk lokacin da aka idar da sallar maghrib lokacin zai dakko past questions dinsa na neco da waec Wanda suke in a book form, zai Kira mu nida Siyama mu zauna muyi karatu, yawanci Siyama Bata da interest dukda ita din ce qualifying exams din ke gabatowa amma Babu wani hankali da take mayarwa duk iya kokarin kuwa da Yaya yakeyi Dan ganin tana fahimta. Ya bamu wani question ta maths ta 1994 muyi solving, na dage Ina ta cracking brain dina wajen ganin nayi solving Amma ita wani littafin hausa ne a hannunta ta saka cikin note book dinta me suna zazzafar kauna in jita da Fadi. Na Gama na dubeta Naga yadda take murmushi kamar bakinta zai yage nace


" Siyama Wai ba Zaki zo muyi solving ba har se ya dawo"


Ta ture hannuna daga littafin seda ta Kai karshen page din sannan ta dubeni tana murmushi tace


" Ke rabu dani, bazan zauna nayi ta Bata lokaci na ba"


Da mamaki na kalleta nace


" Karatun ne Bata lokaci? Lallai Kam!"


Tace


" To meye amfanin shi, kina ganin dai Ina gamawa aure zaayi min meye abin damun kaina!"


Nace


" Ke Siyama! Ta Ina Kika sani?"


Tayi dariya tace


" To Mino aure zaayi Mata, Baki ga ranar an kawo Kaya gidannan ba, to kayan ta ne tana gamawa aure zaa mata. Barni nayi karatun soyayya ta ita zata fushe ni"


Nayi Jim jikina duk yayi sanyi, Kar Nima suce aure zasuyi min idan na Gama Olevel dina, na girgiza Kai nace a raina ai bazai yiwu ba tunda dai ni ba Yar su bace.


" Ni kuwa Kinga Ina son nayi karatu, saboda Abbuna yace Yana son yaga na Zama medical doctor, Allah sarki Allah ya jikanka Abbuna"


Na fada Ina sunkuyar da kaina na maida hankalina Kan maths din Wai ko na samu abin ya fita a raina, but the pains is always there, kullum na tuna shi Ina jin kamar yau Ina zaune aka fitar da gawar shi a idona!


Wannan karatun da muke shi yasa muka Kara shakuwa sosae dashi, na fara damuwa da alamuran shi, har idan ya fita na Kan tambaye shi Ina yaje ko Kuma idan ya wuni ban ganshi ba da zarar ya dawo Zan same shi na fara tuhumar shi inda yaje tun safe ban ganshi ba. Ummaan su duk hankalinta baya kanmu, ta tattara duka hankalin ta wajen shirye shiryen bikin Mino, Dan haka se Nima na Dan samu a bit of yanci a gidan. Wata ranar alhamis muna zaune Muna Hira dukkan mu, ranar har Baba, daya dawo daga port inda anan yake service saboda Yaya ya riga shi hada makaranta, ya zauna Banda fafa Babu abinda ke fita daga bakin shi, ni Kuma Ina gefe se kallon shi nake yadda yake zuba karya Dan yasan Wanda yake yiwa karyar ba su San ko Ina ba se ringim. Mikewa nayi na tafi na dakko books Dina nazo na zauna na fara karatu, ganin hakan yasa Yaya dawowa gefena ya zauna yace


" Good girl! Gwara muyi karatu ko?"


Na dago na kalle shi Ina sakar Masa murmushi tareda gyada kaina, yayi murmushi shima kasa kasa yadda ni daya zanji yace


" I love your dimples!"


Nayi saurin yin kasa da kaina Ina murmushi softly Amma bance komai ba, yayi Yar dariya da ta saka naji wasu knot na warewa a cikin cikina,


" Kunya kike ji? You look really beautiful idan kina jin kunya"


Na rufe fuskata na cuno baki nace


" Kana hanani nayi karatu fa!"


Yadda na shagwabe murya yasa ya shafa Kan shi sannan ya maida hankalin shi akan littafina Yana min bayani. Se muka ji sallamar Kawu Sa'idu, dukka muka Masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya nufi dakin su, Ummaah dake bakin kofar ta bi Bayan shi. Ya zauna ya dubeta a kufule ita Kuma tambayar shi take dalilin da yasa ya dawo gida da wuri, muma duk a waje we were wondering dalilin dawowar shi da wuri. Bai amsa ta ba yace


" Zinatu me ye wannan nake gani? Nufin ki duk yadda nake kokarin a banza kike so ya tashi"


" Me ya faru Kuma?"


" Tambayata ma kike? Ke wacce irin mace ce, kullum Ina waje Ina kokarin ganin rayuwar mu ta inganta Amma ke Ina tufka kina warware min"


" Kaga ni fa ba gane abinda kake fada akai nake ba, ka fito kayi magana Sai zagaye zagaye kakeyi"


" Au Baki gane ba? Me yasa Kika bar yarinyar can har take karatu, kinsan in har tayi karatu zata San kanta Kuma zata nemi ja dani, kinsan bazan iya samun komai akan dukiyar ta ba in har ta Yi karatu, to Dan me yasa Zaki barta take karatu?"


Tayi tsaki Wanda yasa shi Kara harzukuwa yace


" Ni zanyi magana kiyi min tsaki? Meye nufin ki"


Itama cikin daga murya tace


" Ya bazan maka tsaki ba, duk kokarin da nake ganin mun cimma burin mu Amma Kai baka gani?! Meye zaka dinga tsorata Bayan munyi da Kai aure zaa Mata da Wanda yafi kowa munin Hali a duniya, yadda ba zata taba fahimtar potentials dinta ba! Ka barta tayi ta karatu bazai taba Mata amfani ba, Bayan haka aure a shekara goma Sha biyar zaayi mata, Kai dai Yi kokari kaga ka samu yadda zakai ka juya zuciyar da tunanin Yan uwan ka!"


Kawu ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta with adoration yace


" Kina da kwakwalwa! Kinsan wannan satin dukka zasu zo saboda kamawar December, anan Zan samu na Gama kullin da ya kamata nayi!"










Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment through 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 18




Babu jimawa Dan ko sati baayi ba na fara exams dita, ana gamawa na daina zuwa, haka Ummaan su tace mu daina zuwa gwara mu zauna a more mu a gida. A wañnan lokacin Babu wani aiki na gida da ban iya ba,gaba daya na canja from the butter Afiyya to a house help, wanki ma da nake ganin wahalar shi shima na iya sosae Dan har nata take bani nayi Mata, ayyukan dake sani wahala duk na daina jin wahalar su tunda na riga na sawa Raina sun Zama dole, Dole se nayi Dan hakan Babu amfanin na dinga Bata Rai na a banza. Rayuwa sosae take canjawa Kuma indai Kai mutum ne dole ka karbi wannan canjin da yazo maka.


Ranar da zaayi hutu ranar zamuje karbar result din mu Kuma a wañnan ranar Rooks tace min zasu taho daga NY, Dan hakan fuskata kawai zaka kalla kasan Ina cikin madaukakin farin ciki. Na Gama shiryawa na fito tana zaune kofar daki kamar yadda ya Zama kullum nan take zaune, tana bin gidan da kallo, ta kalleni tayi tsaki Wanda yasa na juyo fuskata dauke da murmushi, tace


" Daina kallo na se kace mayya, da wasu kumatun ki a gurin masu lotsawa"


Maimaikon naji haushi se na Kara sakin murmushi Wanda ya bayyanar da hakorana, ta mike zata kawo min duka nayi saurin gocewa tayi tsaki ni Kuma nayi saurin ficewa Ina dariya, Yaya na samu tsaye shi da Mino a kofar gida, idonta yayi ja da alamu kuka tayi, shi Kuma fuskar shi na nuna lallashi, ganin su a wañnan yanayin se naji Babu dadi ban Kuma tsaya ba kamar yadda nayi niyya, se Yaya yace min


" Ba magana?"


Na juyo Naga Mino na Mana wani kallo se na dauke kaina nace


" I saw you guys talking shiyasa!"


Ya harareni yace


" Ke na zauna jira, Ina son muyi magana kafin ki tafi, shi ne kin fito zakiyi tafiyar ki?'


Na tsaya tareda daidaita tsayuwa ta nace


" Yaya! To gani ai"


Ya matso gefena, we were so close da har Ina iya jiyo kamshin turaren shi me sanyi, kodan saboda idan naji kamshin Ina jin sanyi cikin Raina ne shiyasa nake jin sanyi ne dashi. Ya fara tambayata ko naci abinci? Saboda yasan ba lallai an bani ba, nayi murmushi Ina kallon shi nace


" I ate, ka barni naje sauri nakeyi"


For that mean time mun manta Mino na tsaye, ita Kuma se kallon mu take bakin ta a bude, tasan we're close Amma batayi tunanin closeness din mu yakai haka ba. Nayi gaba shima ya biyo bayana, haka muka jera Muna tafiya Yana ta min hira se Naga within shortest of time har mun karasa makaranta, lokacin an baje se kalilan dake zuwa karbar result din su, Ina karasawa class teacher din mu yace


" Amina Baki zo da wuri ba"


Na langwabar da kaina nace


" Sir kayi hakuri"


Ya gyada Kai na gaishe shi sannan Suka gaisa da Yaya, ya Mika masa result yace


" Tayi kokari sosae na gaske kuwa, idan akwai abinda yafi na daya tabbas Amina zata dauka, she sure is an asset!"


Nayi murmushi Ina jin dadin praises dinsa, Yaya ya Masa godiya sannan muka juyo, ya dubeni da idanun shi da Suka washe tas daga Jan da sukai dazun, sunyi haske har wani maiko maiko suke, he looks so happy Wanda yasa naji kamar banida wata damuwa se kallon fuskar shi da murmushi yaki daukewa akai!


" I'm proud of you!"


" Thank you"


Se Kuma mukai shiru kawai muna tafiya a hankali, iska na kadawa kadan kadan duk zafin garin Ringim Babu Sabida sanyi ya fara shigowa se bishiyo Yi dake kadawa! A Haka muka karasa gida zuciyar mu tamkar an Mana bushara saboda kallon mu kawai zakayi kasan farin ciki na dawainiya damu. Tun daga nesa naga mutum ya juya baya, gabana ya yanke ya Fadi I can swear tamkar statue din Abbuna ne a tsaye, hatta tsayuwar jikin da komai tamkar na Abbuna, Yaya ya dubeni yace


" Kinga Uncle Babawo! Let's go to him"




Na dauke kaina na cigaba da tafiya ta a hankali tamkar kwai ya fashe min a ciki, Bai lura da yanayin da nake ciki ba ya karasa gurin da Uncle Babawo ke tsaye ya rike hannun sa, Ina hango tsantsar farin cikin da yake ciki na ganin kawun shi. Yana juyowa muka hada idanu dashi ya saki hannun Yaya ya nufo ni fuskar shi dauke da farin ciki, he looks so much like my Dad, se naji fushin da nike dashi bazan iya cigabawa ba, na nufe shi da gudu Amma Kuma se na kasa rungume shi na rike hannayensa and I found myself crying, yayi shiru yana bubbuga bayana Yana fadin


" Ya Isa! Shiyasa tuntuni naki zuwa saboda banason na ganki kina kuka, ya Isa I'm sorry kinji?"


Na gyada Kai na, na fara share hawayena se Kuma na fara dariya Ina gaishe shi, ya dinga kallona daga fuskata da ta canza sosae zuwa kayan dake jikina, ya dubi Yaya yace


" Daga Ina kuke Haka?"


Nayi sauri nace


" Naje karbar result Dina ne, dama bansan wa Zan nunawa ba, class teacher din yace nayi kokari sosae"


Ya gyada kan shi ya karba result din Yaya ya shige gida, he went through everything sannan ya shafa kaina yace


" I'm proud of you my Baby. So bani labarin Ringim"


Nayi shiru bansan me zance Masa ba, zance Masa abincin da zanci ma wahala yake min, ko Kuma Zan fada Masa tamkar Yar aiki haka nake a gidan riko na. Na girgiza Kai nace


" Nasan yanzun kazo, idan ka huta I'll gist you"


Ya gyada Kai na Mike na Masa sallama na bar shi da result din a hannu Yana kallona har na shiga gida, Ina shiga na samu ana gyaran kayan Miya, nasan saboda Baki yau zaayi Miya




" Gidan uban wa Kika tsaya? Baki San kinada aiki a gida ba ko?"


Naji muryar ta daga gefena, bance Mata komai ba nasan zuwa lokacin ta Saba da wannan halin nawa tunda akan shirun da nake Mata bazan iya irga sau nawa tana kaimin hannu jikina ba, Amma anjima idan ta Kara min irin haka ko kallon ta bazan Yi ba Amma Kuma Zan Yi abinda tace. Kamar lokacin se na shiga daki na cire uniform Dina nazo na daura shinkafa, kafin ta dahu an kawo markade, nayi Miya Ina jin kamshin na duka na, se naji yunwar da nake ta dannewa ta taso min, naji Yunwa nake ji Amma se na daure na koma daki har lokacin da zaa bani nawa. Mino na zaune Itada Siyama suna hirar bikin da dudduba Kaya, na kwanta Siyama tace min


" Afiyya ke baayi Miki ankon ba? Ki fadawa Uncle Babawo tunda yazo"


Nayi murmushi kawai bance Mata komai ba, to me zance atamfa falle biyu an kasa min bayan da dukiyata aie cin abinci. Bayan sallar laasar Ina cikin tuka tuwo naji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login