Showing 45001 words to 48000 words out of 95282 words

Chapter 16 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6647

Me na fada maka?"




Ya bude baki zaiyi magana face


" Oh please Shehu ka manta duk abinda na fada maka. AFIYYA fito!"


Babu musu na fito Ina ta kallon shi he looks defeated and depressed, se naji kamar kada na tafi Amma iyayen shi dake gurin ba abokan musu na bane, bayan mota na kwantar da kaina Ina jin sanyi duka na bin jikina, I felt so empty and lost, na Jin tamkar anyi nesa Dani daga barin jikina. Cikin motar Babu Wanda yayi magana seda muka Isa gidan mummy sannan muka fito fuskata a rufe da hijabi kamar yadda nayi Dana fita, Babu Wanda ya lura Dani har na haura sama kamar yadda Ummiey tace min, na Shiga dakin na samu Mummy na fadin


" Wai ya zaku ce Baku ganta ba, Afiyyan allura ce da zata Bata?"


Nayi sallama jikina a sanyaye na shigo


" Daga Ina kike?"


Na dake nace


" Yaya Shehu ne ya kirani waje"


" Me yasa Zaki fita Baki fada min ba duk kin tayar min da hankali"


Nanny ta dubeni da banma lura da ita ba tace


" Karki Kara fita ko Ina"


Na gyada kaina, wani sabon lace ta dakko min cikin katon akwatin da kayan da nake fitar biki suke ciki ta bani na saka, sun yimin cif cikin jikina, kudos to me dinkin, yasan aikin shi, sede dukda abubuwan da yasa da zasu Kara cikani, kallo na kawai zakai ka kalla zallar yarinta a tare dani, ga jikina ma kawai ka kalla will tell you my age. Haka muka fita Ina ta zuba kamshi akan kamshi, muka Isa babban parlon bakin ta, suna zaune sun kusa su biyar koma din hakan, kana kallonsu kasan Yan gayu ne Kuma a wadace suke, dukkan su Kama suke da Ummiey, Mamana da Kuma ni kaina Banda mutum biyu da nake tunanin ko su sirikai ne Dan su kamannin su daban ne da namu. Tsakiyar su Mummy ta aje ni dukkan su suka yo kaina kowa na kokarin hadani da jikin shi, a raina nace a banza tunda se yanzun sukai niyyar hakan, suka zo nemana, a daddare na gaishe su kowacce ta min introducing kanta, biyu daga ciki cousins din Mama ne, biyar sister's dinta se biyu in laws dinta, matan brothers dinta kenan. Babu jimawa Ummiey ta shigo, Suka sakani a gaba da wasu zantuka da Suka saka naji tamkar na zura saboda girman su day Kuma nauyin su a kunne na. Ya zanyi Mummy ko motsi nayi se ta Harare ni, Haka na baza kunnuwa Ina ji, suna gamawa kuwa na Mike na fice a guje. Anty Bintu tana dariya tace


"Anty Maryam yarinyar ki kunyar auren ma take ji ai"




Mummy ta tabe baki tace


" Allah dai ya kyauta"


Daga nan suka koma hirar nayi kankanta ace an biye min anyi min aure, Ummiey da Mummy sede su kalli juna kawai Amma Babu me bakin magana. A Haka washegari tayi Kamar yadda aka saka karfe Sha daya zaa daura min aure. Gidan ya cika sosae da mutane, mutanen da na dinga bukata duk Basu zo ba se yanzun Wai a Haka boye zancen auren akeyi Dan kada a zarge su da rashin kula Dani. Tun sassafe Kawu Tijjani yazo shida Kawu Sa'idu, sun Jima da mummy bansan me suke tattauna wa ba, Kawu Sa'idu ya fara tafiya sannan Kawu Tijjani, ta shigo dakin da nake an shirya ni fes cikin wani dakakken lilac lace me adon zare maroon, nayi kyau ba karya, na kalla kaina for an uncountable number and I wishes I was happy, lokaci na farko naji inama ace Yaya Shehu ne mijina, may be da tuni Ina nan Baki na kamar zai yage Dan farin ciki.




Nayi mamakin duk shige da ficen da akeyi Babu Uncle Babawo, har na tambayi Anty Nafisa lokacin da ta saka ni a gaba da abinci, nace


" Banga Uncle ba"


Ta danyi murmushi tace


" Tun shekaran jiya Yana kazaure, munyi waya dashi Yana Hanya"


Nayi shiru Ina Wondering me ya kaishi Kazaure, ban dai ce komai ba na dauka spoon din na fara cin dambun shinkafar da nace zanci. Babu jimawa Sha daya ta doka aikuwa Babu ko Kara minti akan lokacin aka daura min aure ni da Junaidu, what a destiny, mutumin Dana gani sau daya, ban ma taba jin muryar shi ba, zuciyata tayi min nauyi Dole na sulale daga cikin cousins Dina Dan kawayena Babu Wanda yazo tun ranar walima hatta Sauda Bata Kara zuwa gurin bikin ba, daga ni se cousins dina su Rooks dasu Nads se Wanda sukazo daga Maid da ko Gama rike sunan su banyi ba. Ina nan naji gidan ya kacame da guda da Kuma kiraye kirayen isowar ango, da sauri nayi toilet na kulle kofar tareda jingina kaina jikin kofar, a hankali hawaye masu zafin gaske suka cigaba da sakkowa akan fuskata, na zauna dabar a saman tiles din da suke malale cikin bandakin bama na tsoron soiling kayana, kawai sanyi nake bukata, so nake na samu abinda zai saka min naji sanyi a jikina, na Jima Ina kuka seda naji zuciyata tayi dadi sannan na Kuma daina jin muryoyin mutane nasan ya fita, na saka wipes nayi wiping fuskata sannan na wanke na fito, Anty Bintu ce kadai dakin alamun jirana take, na saki Mata Murmushin karya, ta Bata Rai, ta fisu sakin fuska hakan yasa har na Saba da ita.


" Me kike yi a toilet tun dazun har angon yazo ya tafi?"


Na sauke ajiyar zuciya jin har ya tafi, nace


" Bana jin Dadi"


Se ta tashi ta riko ni ta fara fada min kowacce mace da Haka ta girma, ni nayi saa na zaba mijina, Amma Mamana rakiyar marriage alliance kawai tayi Bata dawo ba seda mijinta, ta min nasiha wadda tasa na Dan ji sanyi a raina sannan ta gyara min fuska na fita aka fara hotuna Dani. Yadda aka saka karfe uku zaa kaini saboda da Dan tazara tsakanin Ringim da Kazaure. An Gama shirya ni tsaf, a nada min lafayar da ta jiku da kamshi Sega Ummiey ta shigo tace ba yau zaa kaini ba, till further notice. Na dago Ina kallon ta da mamaki tace min nasa hijab nazo parlon Baban Rooks. Ina zuwa na samu Uncle Babawo Yana fadin


" Na hadu da babanka Kuma ya fada min halayen ka Dan hakan se ka saki yarinyar nan, seda nace a jira na dawo Amma aka daura. Kaji tsoron Allah Sa'idu idan Yar kace ai ba zaka nata Haka ba"


Duk shi kadai yake maganar, Mummy na gefe se ruwan hawaye take yayinda Kawu Sa'idu yayi fitinfitin akan aure an daura Babu Wanda ya Isa yasa a kunce. Daddy a nutse yace


" Kai Junaidu mahaifinka da bakin shi yace ya Kore ka saboda kana bin bokaye, Yan unguwa sunce baka ma zuwa sallah baa taba ganinka a masallaci ba, kaga baka cancanci Afiyya ba, Dan hakan ga takadda da biro ka rubuta Mata sakin ta duk abinda ka kashe no Zan biyaka"














Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam, First bank of Nigeria. Send evidence of payment to 0906346725831


Wani irin kallo yake bin dukkanin su dashi, se a lokacin kamanin shi da yake boyewa suka fito, tabbas he doesn't look any thing near innocent person, yafi Kama da takkadiran marasa mutunci, a idanun shi kawai Dana kalla naji wani irin tsoron shi ya darsar min cikin zuciya ta, nayi saurin sunkuyar da kaina Ina jin yadda gabana yake wani irin faduwa. Ban karasa ciki ba saboda yadda ake tafka rigima, Dan tun suna maganar a hankali har ta koma kowa jijiyar wuyan shi ta mike, su sunce lallai lallai Babu inda zanje se ya sakeni Dan bazasu hada zuria da irin shi ba yayinda shi Kuma ya dage ba zai sake ni ba, da kowanne yayi insisting akan maganar shi se kawai Junaidu ya mike, duka Suka bishi da kallo Babu wata wata yayo kaina, Bai jira komai ba ya daukeni cilak tamkar wata teddy ya Saba a kafadar shi ya fita, Kawu Sa'idu yayi saurin Mara Masa baya Yana fadin hukuncin da yayi ya burge shi, Haka Ina doka hannu Wana a bayanshi, kafafuna Ina ta hantsila su Wanda ko takalmi Babu amma ko gezau baiyi ba seda ya direni cikin wata bakar Corolla LE sannan ya maida murfin ya rufe, glasses din tinted ne Babu Wanda ke kallona, Amma ni Ina kallon yadda suke magana kasa kasa shi da Kawu Sa'idu, Basu dauki lokaci ba Sega sauran mazauna parlon sun fito, Uncle Babawo da Daddy suka nufo gurin Amma kafin su karaso tuni ya shaiga motar yaja uban reverse yayi Kan titi, na saki matsanancin kuka, a lokacin ji nake tamkar rayuwata ta Kare, tamkar Babu wani farin ciki da yayi saura, Banda gudu Babu abinda yake Haka ni Kuma ban fasa kukan da nakeyi ba. Tun baya kulani har na fara jin tsakin shi lokaci zuwa lokaci. Na saka fuskata cikin palms Dina Ina kuka Wanda yake fitowa daga karkashin zuciyata.




" Keeeeeee! Dallah rufewa mutane Baki da wata muryar ki kamar ta gyare!"


Babu Wanda ya taba jin muryata Bai so ya kara jinta ba, a hankali nake magana cikin tattausan lafazi, Haka idan kuka nake bawai bude duka muryar nake Ina kukan ba. Wani katon Abu da nake ta kokarin ganin ya wuce a makoshi na ya Kara zuwa ya tokare min, hawayen da kukan memakon su ragu se Kara gudu sukeyi Haka muryata memakon na rage sautin kukan se na Kara fadawa, nasan Babu mijin da zai daki matar sa Koda shi din... Ban ma Gama tunanin ba naji saukar Mari a fuskata, nakai second talatin bana ji, bana gani, sewani dum a kunnena sannan idanuna sun rufe ruf Dan kansu. Nasan Kawu yasha Marina Amma wannan Marin da ban yake. A hankali coordination Dina ya dawo, senaji Abu Yana bin hancina Ina Kai hannu naga jini ne, kunsan duk azabar da nake ciki kasa Koda uhum nayi? Nasa hijab Dina na goge hancin Wanda yasa naji wani sabbabbin hawaye sun Kare balle min, Amma ko sauri Babu. Tafiya mukai sosae sannan muka Isa Kazaure wadda ake Mata take da Kazaure ta Dambu kowa Sarki! Ni dai kaina na a sama saboda na samu jinin ya daina zuba, ban masan iya inda muka ketare ba se ganina nayi yayi parking gaban wani gida, ya kashe motar sannan ya kalleni tareda sakar min harara wadda tasa kayan cikina motsawa, na fasa me yasa nake jin tsoron shi har Haka


" Ke jaka ce? Se ance Miki ki bude ki fita?"


Hannuna na rawa na Kama handle din kofar na fita, Yana tsaye na mayar na rufe sannan na rufa Masa baya har ya bude kofar ya Shiga, kafata ta dama na saka na Shiga, Ina karanta adduar da Mummy da Ummiey Suka dinga nanata min, hawaye ya cigaba da sakko min, wani na korar wani. Babu abinda kake ji se sniffing Dina, ya juyo ya maka min harara wadda tasa nayi saurin hadiye kukan, gidan safe content ne, parlor muka fara shiga madaidaici, yayi balain kyau tabbas interior decorator ba karamin wonderful job tayi ba. Parlon purple ne light da dark Amma light yafi yawa hakan ya haskaka shi, na shagala Ina kallon parlon, ya shige ciki ni Kuma na rakube gefe guda, se wajen bayan thirty minutes sannan ya fito ba tareda ya dubeni ba ya fice abin shi Yana zura makulli cikin aljihu, na Jima a zaune Ina tunanin abinda bansani ba, naji Kiran sallar laasar, na Mike na nufi inda ke gefe Ina hango kofofi daya na kallon daya, dama Wanda ya shiga a gefe yake, Kuma ya kulle nasan nashi ne. Tunda dama Ummiey tace da Suka zo jere se maida kayan dakin shi akai tunda na 3 bedrooms aka siya. Na bude dakin farko, komai na coffee ne se labulayen ne brown sunyi kyau, Kuma daga gani furniture din sune manya Dan gadon ma abin kallo ne. Na bude dayan shi Kuma Ash da red ne, very simple yet elegant. Na shiga nayi wanka sannan na fito da alwala a jikina , na bude wardrobe Ina kallon yadda aka gyara min kaya, hawaye a hankali ya siraro min, kamar mafarki nake ganin komai, Wai nice me aure, wannan gidan Wai nawa ne nice matar gidan, I couldn't believe it. Nayi sallah na shirya cikin dakakkiyar shadda mustard yellow da Lacy edge Baki, na gyara fuskata kamar yadda aka min nasiha, na daura dankwalin da ba Gama iya daurawa nayi ba, na koma dayan dakin inata bude bude, Amma bawai kallon content din abun nake ba gaba daya hankali na baya Kan abinda nake, nayi nisa sosae Ina ayyana anan Kuma wacce irin rayuwa zanyi? Banga alamar akwai jin Dadi ba, na shafa fuskata da ta Dan tashi saboda Marin da ya zabga min, na girgiza Kai se na samu kaina da adduar Allah ya kawo min dauki!








Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam first Bank of Nigeria. Send evidence of payment to 09063467258[05/01, 14:34] +227 98 36 59 34: 32








Hajja Huwaila na zaune cikin daki, tayi rama sannan shekaru sun Kara Hawa kanta duk ta tsufa, balle a yaddaa take jin zuciyata me dauke da mikin kusan shekaru Sha biyu, tun ranar da Malam ya furta korar da yaiwa Junaidu,Kuma Junaidun ya fita Bai Kuma Kara waiwayar gidan ba, Babu wnai dare da idan yazo zata kwanta Bata Yi kukan rashin shi ba, sannan kullum se tayi Masa adduar shiriya sede kullum tana zuba idon kallon kofar gida taga ko zai shigo Amma har yanzun Babu amo Babu labari, har ta gaji ta hakura sede dukda hakan kullum se tayi maganar shi, Amma Kuma wani barin na zuciyar ta na tuhumar ta da rashin tarbiyantar da shi akan daidai shiyasa ma har ya Zama lalatacce Haka. Sadiya ta shigo dakin bakinta dauke da sallama , Amma Hajja din Bata amsa ba, ta zauna cikeda rashin kuzari da Kuma sanyin jikin ganin mahaifiyar tasu a Haka tace


" Hajja! Wai se yaushe Zaki sararawa zuciyar ki ne? Shekara Sha biyu fa, kilan ma ya manta dake"


Hajja ta saki hannunta tana kallon Sadiya tayi murmushi me ciwo tace




" Da zai iya manta uwar shi Amma Ina me tabbatar Miki ko da ya manta Dani ni din bazan manta dashi ba, ba Kuma Zan daina Masa addua ba. Baki San dadin da ba"


Tayi kwafa cikeda bacin ran maganganun Hajja tace


" Dukkan mu mu biyar Muna nan, muna Miki biyayya Amma kin kwallafa Rai akan wancan gantalallen"




" Sadiya! Tashi ki fita min a daki"


Ta mike tana zumbura Baki ta fice, ita kam Babu Wanda ta tsana irin Junaidu a ganinta shi ne sanadin halin da mahaifiyar su ke ciki, gashi ita tana yarinya komai ya faru Amma dukda Haka anzo bikin ta seda aka samu matsalar da aka fasa auren ta har sau biyu. Dakin amaryar baban su ta tafi dama nan tafi zama. Hajja ta girgiza Kai tana adduar Allah ya kawo karshen matsalolin ta yasa yaranta su kaunaci junan su. A hanakali taji muryar Fatima dake aiki a tsakar gida tana yiwa Malam sannu da zuwa, ya Kara tsufa kana kallon shi kasan Yana cikin afuwar rayuwa, ko gidan ka kalla zaka San arziki ya zarce na da, ya amsa Mata Yana tambayar ta Hasiya, tace tana daki yace ta shiga tace Mata ta sameshi dakin Hajja yanzunnan. Daga Haka yayi dakin Hajja wadda har lokacin tana zaune Kan sallayar da ta idar da sallar laasar ko motsawa batayi ba. Malam ya shigo bakin shi dauke da sallama, ta dago tana duban shi Bayan ta amsa, Yana Zama Hasiya na shigowa, ta zauna ta gaishe shi tace


" Malam lafiya dai ko?'


Ya Dan watsar da hannayen shi Yana duban Hajja yace


" Hajja maganar akan Junaidu ce"


Da mamaki Hajja ta dube shi, wani sanyi Yana lullube zuciyar ta ita dai tunda ya Kori Junaidu Bata tunanin ta Kuma jin ya ambaci sunan shi ko sau daya, Bai Kara maganar shi ba, kamar yadda ya fada ya shafe shi cikin yaran shi to tabbas hakan yake nufi Dan ko da Wasa Bai Kara zancen shi ba, itama Kuma Bata Kara Masa zancen shi ba, Hasiya ce ma takan kawo maganar shi Amma idan ta Masa se yayi Mata shiru Amma dukda Haka Bata fasa ba, Dan a ganinta tsakanin ta da Hajja Huwaila akwai babbar amana, abinda ya shafe ta ya shafe ta itama Dan hakan Dole ta Taya ta jimamin abinda ya sameta.


" Eh shidai Junaidu, maganar shi ce ta kawo ni. Dazun aka daura Masa aure..."


" Aure? Waye ya bashi 'Ya?"


Hajja tayi saurin tambaya, Dan last time da zainab din Fatima tazo yace Mata ta ganshi yayi kudi dake kusan unguwa daya suke zaune Amma tace Mata kowa a unguwa Yana fadar halin dai da suka San shi dashi tun Yana gida.


" Tohm bansan yadda Zan Miki bayani ba, Amma dai yayi aure, yarinyar marainiyar ce kawunta ya aura ma Junaidu Wanda sauran kawunnan nata sun kasa fahimtar dalilin shi na yin hakan ba, ko ni da nake mahaifin Junaidu ace Allah ya hallata na aurawa Sadiya ko Ambaby shi tabbas da bazan bashi ita ba. Na tabbatar duk inda yarinyar take tana cikin damuwa, Dan hakan nake so kuje ke da yaran ku ganta kafin Kuma tazo nan"


Hajja hawaye suka Shiga sakko Mata Wanda ta rasa na menene, ita dai ba farin ciki take ba hakan Kuma ba bakin ciki take ba sema hope da take ganin zai Zama silar shiriyar danta, a ganinta ni din Zan Zama wani tsani na gyara Mata danta. Hasiya ta mike itama cikin farin ciki tana duban Hajja tace


" Ban ma taba kawowa zai kalli mace yace zaiyi aure ba, da izinin Allah adduar ki ce ta karbi, Bari naje na gano sabuwar Yar tamu"


Ta fita ba tareda ta jira amsar Hajja ba, tana fitowa tsakar gida ta shiga kwalawa sadiya da Ambaby Kira Wanda su kadai Suka rage a yayan su Mata basuyi aure ba, tunda dama ba wani yawan gaske ne da yaran ba. Suka fito Suka same ta a daki tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login