Showing 66001 words to 69000 words out of 95282 words
Chapter 23 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
sheshekar kukan naji an turo kofar, nayi saurin mikewa Ina saka edge din mayafina da nufin goge fuskata da tayi kacakaca da hawaye, Mom ta shigo I can see the disappointment a idanun ta, ta karaso a hankali na fara kokarin yin magana tayi beating Dina, yace min
" Ki wanke fuskar ki kije parlor kuyi sallama da yayanki"
Na gyada Kai na wuce toilet na barta anan a tsaye, Dana fito Bata dakin hakan yasa na dauki hijab din data fito min dashi alamar na saka kenan. Na saka na fito a hankali, suna tsatsaye se murmushi yake suna magana da Uncle, na karasa na tsaya gefen Mom da ke ta kallona da damuwa a fuskarta, na Dan saki murmushi kadan nace
" Yaya!"
Shima da murmushi a fuskar shi yace
" Afiyya Ummiey na gaishe ki"
" Ina amsawa"
Dad ya Mika Masa hannu Yana fada Masa yazo very early muyi breakfast tare sannan ya kalla Mom ya Kara Mata godiya. Ya juya ya nufi kofar fita, Mom tayi min alamar nabi bayan shi, a kunyace na take Masa baya, a kofa na cin Masa Yana tsaye ya daga kanshi sama Yana kallon taurari da kamar an watsa su saboda yadda sukai fito far ga Kuma wata da yake a cike ya kawata samaniya. Ya dube ni yace
" I'm so happy seeing you cikin wannan yanayin. How have you been?"
Na Dan rausayar da kaina ba tareda na kalleshi ba Nima Ina kallon saman da yake kallo, a hankali iska me sanyi tana kadawa har hijabin jikina na swaying.
" Alhamdulillah! Aiki kazo Yi ne?"
Ya girgiza Kai sannan ya gyada Kuma, hakan yasa na kalleshi da alaman tambaya
" Gurin ki nayi niyyar zuwa, I wanted coming to see you! Da nake daukan leave a office se suka hada ni da assignment Kuma"
Nayi murmushi da yasa dimples Dina lotsawa nace
" Thank you!"
Ya gyada Kai yace
" I should thank you Afiyya!"
Na kalleshi Ina harde hannayena a kirjina nace
" Saboda me?"
" For being safe and sound! You don't know how much your happiness meant to me"
" Yaya!"
" Zan nuna Miki a hankali, I told you then Ina sonki, yanzun ma Haka Ina son ki Kuma ko nan gaba Zan cigaba da sonki, Zan baki lokaci for you to heal se kiga abinda kike bukata a rayuwar ki, kiyi karatu Zan zauna har tsawon sati biyu a garinnan tare da ke!"
Nayi shiru Ina jin dukkan kalaman sa suna sauka cikin zuciyata, na dago na kalleshi, idanun shi masu haske Suka haske ni, na saki murmushi Ina boye fuskata cikin hannuna, ya karkato daidai fuskata har Ina jin numfashin shi a Kan hannuna yace
" Should I take that as a go ahead?"
Nayi dariya Ina matsawa gefe tareda cire hannayena nace
" Ka tafi dare nayi fa!"
Yayi shrugging kafada sannan yayi min waving ya wuce, Ina nan tsaye har ya fita ya samu cab ya tafi sannan na kulle kofar na shigo ciki, daki na na wuce Ina tura kofa na samu Mom na zaune gefen gado alamar tana jirana, duk yadda nake kokarin ganin na boye tsananin farin cikin da nake ciki Amma hakan ya gagara, na bude bakina nace
" Mom Baki kwanta ba?"
" Ina zaman jiranki ne"
" Babu abinda ya sameni, kawia Ina kuka me saboda tuna rayuwar da nayi a baya"
Ta taso ta rungume ni tace
" Kibi abinda zuciyar ki take so, dukkan wani Abu da Kika zaba ki sani ni, Darling duka Muna tare dake. Kiyi addua sosae kinji?"
Na gyada Kai nace
" Mom thank you"
" Sleep well Baby!"
Ta shafa kaina sannan ta fita ta jamin kofa, na fada gado Ina tuna dukkan kalaman shi
Zan nuna Miki a hankali, I told you then Ina sonki, yanzun ma Haka Ina son ki Kuma ko nan gaba Zan cigaba da sonki, Zan baki lokaci for you to heal se kiga abinda kike bukata a rayuwar ki, kiyi karatu Zan zauna har tsawon sati biyu a garinnan tare da ke!
Safiyar alhamis ita ce ranar da aka dage sentence din su Junaidu, kowannen su a mabanbantan waje yake Dan Haka nan kowa daban suka fito, Junaidu ya fito hannun shi Babu komai, Dan baije da komai ba Haka ya fito sikau, Yana fitowa hasken Rana ya dalle shi se yaji tamkar wata sabuwar rayuwa ya fara, ya juya ya kalla gurin yayi tsaki Yana jin babbar failure da yayi shi ne sakin Afiyya da yayi, komai ya lalace saboda ita, shi kan shi hanyar da zai samu kudin zuwa kazaure ma case ne! Bai bar Kano se yamma Bayan yayi buge bugen shi ya samu kudin mota, Bayan maghrib ya karasa ya tsaya a daidai inda katon garage din shi ya kone, se fili da Yan bullulluka, ya saki ajiyar zuciya Dan Bai San ta Ina Kuma zai fara ba, komai ya lalace ya ayyana a ranshi, Dan Haka Dole ya Koma drug dealing din shi.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.49
" Wai me yasa baka sallah? Me yasa tunda nake zaune cikin gidannan tsawon watanni ban taba ganin ka kayi sallah ba? Kasan falalar sallah kuwa? Kasan abinda ya raba musulmi da kafiri shi ne barin sallah? Ta Yaya zaka tsaya a gaban Allah a bincika aikin ka aga Babu sallah a ciki, kasan kuwa duk ran da yake sallah ana zata Masa alkhairi..."
Ya cigaba da tsayuwa zuciyar shi na bugawa cikin sauri Yana iya hango lokacin da karamin bakin ta yake motsawa a hankali, iya karfin ta tsakanin ta da Allah nasiha take Masa, ya tuna lokacin zuwa yayi ya iske inda take tsaye ya dauke ta da Mari, Wanda yasa a gigice ta dafe kuncinta tareda yin kasa da sauri Amma bakinta Bai rufu ba, Junaidu ya kalli hannun shi Wanda ya Yi amfani dasu wajen dukan ta, wajen Marin ta yadda ya tsangwama Mata, Bai San me yasa yake jin kamar shi din Wai missing din Afiyya yake ko Kuma Yana Jim maganar ta tana Shiga jikin shi ne. Tsaki yayi Yana fadin shi zuciyar shi batada wani lokacin soyayya ko tausayi, ko tausasawa! A ganin shi zuciyar shi is as hard as abinda ba zakai tunani ba. Ya kallo parlon da yayi kura, komai an dauke Babu wani digon kayan Afiyya da ya rage, Bai taba tunanin yarinyar na da wannan gatan ba may be he wouldn't have messed with her, she was so innocent wanne irin son duniya yasa ya hada Kai da Sa'idu ya cuceta ba. Ya safe kanshi Yana jin inama har yanzun tana nan, da tuni Jin motsin shi kawai tayi Koda zai kashe ta zata fito tace
" Sannu da zuwa, za kaci abinci"
Ba zata samu komai ba se kallon banza ko ma wani lokacin ya make ta. Yayi tsaki Yana jin tsananin haushin Kan shi na wani tunanin wata banza Afiyya. Dakin shi ya wuce komai Yana nan yadda yake Babu abinda aka taba Masa, wayar shi ya dakko wadda dama anan ya barta kafin fitar shi lokacin da Afiyya ta yanke shi, ya dauka ya cire sim dinsa sannan ya saka cikin wata Yar karama sede Babu cahaji cikin battery, ya jona kasancewar akwai wuta, kafin ya hau ya fara binciko hard substance da ya boye, su cocaine, weeds da ampoules na POD yasan idan ya fitar da wannan kayan ba karamin kudi zai z
Samu ba, wucewa yayi ya dauki wayar ganin ta danyi abin kirki ya fara Kiran Jarma, Jarma dai abokin shi na yarinta Wanda aka Kore su tare daga makaranta. Babu jimawa Jarma ya dauka Yana fadin
" Shege abokina ka samu fitowa kenan?"
Junaidu yace
" Ka Bari na dawo shekaran jiya, banida kudi se a account banida ATM Ian son a saya kayannan"
Daga bangaren Jarma yayi dariya yace
" Ai da nasan kana dasu tabbas da Zan balle gidan ka. Zan Aiko a karba da daddare Amma Zan Aiko maka kudin amfani anjima"
Ya Masa godiya sannan ya hautsina Kan shi Yana daukar wata zundumemiyar laya Yana jujjuya wa, a hankali cikin Kan shi ya ji muryar Afiyya na cewa
" Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!! Tsafi kakeyi? Wannan shirka ne baa hada Allah da wani a wajen bauta..."
Ya tuna ranar da shi ne ko ruwa ta fito Sha shima Bai sani ba, Yana cikin incantation dinsa se kuwan yaji faduwar Abu, Yana juyawa ya ganta a tsaye jikin ta kamar mazari saboda rawa, Amma saboda karfin Hali send tayi Masa magana. Ya yadda layar yana Kara cakuda Kan shi da hannu shi tareda buga kafa ya toshe kunnen shi, what the fuck! Me yasa yake tunanin waccan yarinyar da ya Kira da dabba on so many occasions.
Kawu Sa'idu Kam gidan Kawu Tijjani yaje ya karba kudin mota, Dan Bai ma same shi a gida ba Kuma Anty Jidda ko fitowa batayi ba me gadi ta bawa kudin ya bashi, ya kalla dari biyar biyar guda uku a hannun shi, shi kenan abinda zaa bashi, wucewa yayi Yan kaba ya hau motar Ringim, tun a mota suka fara haduwa da mutanen da ya sani, kowa se kallon shi yake kadan ne ma suka Masa jaje amm yawancin kallon banza ke hada su se Kuma masu yada Masa magana. Shidai Bai Kara cewa komai ba babban burin shi yaje gida yaga ta Ina zai fara gyara abinda ya bata, yasan ba lallai komai ya koma in place ba Amma yanada yakinin boka yace Masa Afiyya ba zata Dara ko Ina ba daga Ringim, so Dole ya maida auren ta da Junaidu Dan ya samu abinda yake so. Haka ya cigaba da tunani har suka Isa, Bai ma bi ta Tasha ba se kawai ya samu napep ta Kai shi kofar gida, Hanson ya bashi ya wuce ciki, tun daga kofar gidan yake jin muryar kubra
" Wallahi ba se anjima ba, yazunnnan ki tattara ki koma gidan mijin ki, Nima nan zaman umarni kawai nake, Amma Babu wadda zata kashe auren ta ta dawo gidannan, Nima naji da nauyin kaina"
" Ummaah wallahi Allah Ummaah bazan iya cigaba da aurennan ba, Dan Allah ki barni, nayi tunanin nan gidan mu ne, nayi tunanin kowanne lokaci na dawo Ummaah zaku saurare ni, zaku tsaya kuji meye matsalata, wa nake dashi Bayan ku? Ummaah na gaji da aurennan bazan iya ba Kuma"
Ummaan su ta Kara hayayyako Mata ba tareda Tama gane me Siyama ke fada ba,
" Duk abinda zai faru, ko me ake Miki Dole ki hakura ki zauna, kowacce mace a gidan mijin ta hakuri take. Yanzun tashi ki fice min a gida"
Siyama ta dinga kuka Wanda yasa jikin Kawu Sa'idu yayi sanyi, a hankali ya saka kanshi cikin gidan ba tareda yayi sallama ba, so gaba daya su biyun bama su lura da shigowar shi ba, seda Siyama ta mike tana share hawayen tana fadin
" Ummaah Zan tafi..."
Bata karasa ba ta ci Karo da Kawu, ta saki jakar hannun ta ta saki ihun kuka tareda durkusawa tace
" Baba ka dawo!"
Lokacin kubra ta hango shi, ta taho Babu wani Abu ta rungume shi, sede yadda yaga gidan ya canja tun daga kofar gida, maganganun su, yanayin kubra da ramar da tayi yasan suna cikin bakin talaucin da ya guda tun farko.
Ina kwanciya bacci me dadin gaske ya dauke ni, I felt new and relieved. Se nake jin Kamar na fara sabuwar rayuwa ne, I felt so happy da a Banda mafarkin farin ciki Babu abinda nayi, I'm sure da cewar da zaa haska fuskata da zakaga murmushi ne kawai a kwance akai. Sallar asuba ta sa na tashi nayi sallah sannan nayi wanka, dakin Mom na wuce Dan nasan Dad na masallaci Bai dawo ba. Tana zaune har lokacin bata tashi akan sallaya ba. Na gaishe ta se kallona take tana murmushi nasan tana tunanin abinda ya sani farin ciki har Haka ne. Ban wani Jima ba na koma na dakina Ina tunanin abinda tace min
" Yayanki zai Yi breakfast nan, bansan me yake so ba, Zan fito zuwa anjima se mu fara ko?"
Na gyada Mata Kai, tana nuna min na tambaya me yake so hakan yasa na kunna data na fara chatting Nads up, ta dinga dariya jin tambayar da na mata, se ta fada min daga karshe. Tareda Mom mukai Gama, wajen tara Ina zaune a daki Nanny ta shigo tace nazo inji Mom, na kalla kaina yau atamfa na saka riga da skirt na daura dankwalin bayan na saka sweater a sama saboda sanyin da aka tashi dashi. Fuskata tayi fes se glowing take kamar Rana, na fito cikin nutsuwa da wayata a hannu Ina karbar korafin Yaya Hasher da yace nayi bacci jiya without even saying goodnight, yau na tashi ban ce Masa Good morning ba. Banyi replying ba saboda karasowa ta parlor, se na saka wayar a flight mode na zauna kujerar Dake kallon tashi, yeah shi fa Yaya Shehu ya karaso. Da murmushi fuskata nace
" Good morning! How's London?"
Yayi murmushi me kyau yace
" Not bad Amma akwai sanyi"
Na gyada Kai na Mike na nufi kitchen Dan Taya ta kawo abinci. Tare muka ci suna Dan Hira yayidan jefi jefi na Kan yi murmushi ko dariya. Bayan mun kammalla na kwashe kayan na Kai kitchen anan Mom ke cemin zasu fita itada Dad se yamma zasu dawo, Nima nayi changing my fita da Yaya Shehu na Dan nuna Masa gari.
I'm sorry, Dan Allah kuyi hakuri my exams is starting on Monday Inshaaa Allah, shiaysa kuke jina shiru, I've lots of documents da ko budewa banyi ba. Amma inshallah zanyi typing 50th page tomorrow se Kuma na Gama exams. Thank you for understanding!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 49
" Wai me yasa baka sallah? Me yasa tunda nake zaune cikin gidannan tsawon watanni ban taba ganin ka kayi sallah ba? Kasan falalar sallah kuwa? Kasan abinda ya raba musulmi da kafiri shi ne barin sallah? Ta Yaya zaka tsaya a gaban Allah a bincika aikin ka aga Babu sallah a ciki, kasan kuwa duk ran da yake sallah ana zata Masa alkhairi..."
Ya cigaba da tsayuwa zuciyar shi na bugawa cikin sauri Yana iya hango lokacin da karamin bakin ta yake motsawa a hankali, iya karfin ta tsakanin ta da Allah nasiha take Masa, ya tuna lokacin zuwa yayi ya iske inda take tsaye ya dauke ta da Mari, Wanda yasa a gigice ta dafe kuncinta tareda yin kasa da sauri Amma bakinta Bai rufu ba, Junaidu ya kalli hannun shi Wanda ya Yi amfani dasu wajen dukan ta, wajen Marin ta yadda ya tsangwama Mata, Bai San me yasa yake jin kamar shi din Wai missing din Afiyya yake ko Kuma Yana Jim maganar ta tana Shiga jikin shi ne. Tsaki yayi Yana fadin shi zuciyar shi batada wani lokacin soyayya ko tausayi, ko tausasawa! A ganin shi zuciyar shi is as hard as abinda ba zakai tunani ba. Ya kallo parlon da yayi kura, komai an dauke Babu wani digon kayan Afiyya da ya rage, Bai taba tunanin yarinyar na da wannan gatan ba may be he wouldn't have messed with her, she was so innocent wanne irin son duniya yasa ya hada Kai da Sa'idu ya cuceta ba. Ya safe kanshi Yana jin inama har yanzun tana nan, da tuni Jin motsin shi kawai tayi Koda zai kashe ta zata fito tace
" Sannu da zuwa, za kaci abinci"
Ba zata samu komai ba se kallon banza ko ma wani lokacin ya make ta. Yayi tsaki Yana jin tsananin haushin Kan shi na wani tunanin wata banza Afiyya. Dakin shi ya wuce komai Yana nan yadda yake Babu abinda aka taba Masa, wayar shi ya dakko wadda dama anan ya barta kafin fitar shi lokacin da Afiyya ta yanke shi, ya dauka ya cire sim dinsa sannan ya saka cikin wata Yar karama sede Babu cahaji cikin battery, ya jona kasancewar akwai wuta, kafin ya hau ya fara binciko hard substance da ya boye, su cocaine, weeds da ampoules na POD yasan idan ya fitar da wannan kayan ba karamin kudi zai z
Samu ba, wucewa yayi ya dauki wayar ganin ta danyi abin kirki ya fara Kiran Jarma, Jarma dai abokin shi na yarinta Wanda aka Kore su tare daga makaranta. Babu jimawa Jarma ya dauka Yana fadin
" Shege abokina ka samu fitowa kenan?"
Junaidu yace
" Ka Bari na dawo shekaran jiya, banida kudi se a account banida ATM Ian son a saya kayannan"
Daga bangaren Jarma yayi dariya yace
" Ai da nasan kana dasu tabbas da Zan balle gidan ka. Zan Aiko a karba da daddare Amma Zan Aiko maka kudin amfani anjima"
Ya Masa godiya sannan ya hautsina Kan shi Yana daukar wata zundumemiyar laya Yana jujjuya wa, a hankali cikin Kan shi ya ji muryar Afiyya na cewa
" Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!! Tsafi kakeyi? Wannan shirka ne baa hada Allah da wani a wajen bauta..."
Ya tuna ranar da shi ne ko ruwa ta fito Sha shima Bai sani ba, Yana cikin incantation dinsa se kuwan yaji faduwar Abu, Yana juyawa ya ganta a tsaye jikin ta kamar mazari saboda rawa, Amma saboda karfin Hali send tayi Masa magana. Ya yadda layar yana Kara cakuda Kan shi da hannu shi tareda buga kafa ya toshe kunnen shi, what the fuck! Me yasa yake tunanin waccan yarinyar da ya Kira da dabba on so many occasions.
Kawu Sa'idu Kam gidan Kawu Tijjani yaje ya karba kudin mota, Dan Bai ma same shi a gida ba Kuma Anty Jidda ko fitowa batayi ba me gadi ta bawa kudin ya bashi, ya kalla dari biyar biyar guda uku a hannun shi, shi kenan abinda zaa bashi, wucewa yayi Yan kaba ya hau motar Ringim, tun a mota suka fara haduwa da mutanen da ya sani, kowa se kallon shi yake kadan ne ma suka Masa jaje amm yawancin kallon banza ke hada su se Kuma masu yada Masa magana. Shidai Bai Kara cewa komai ba babban burin shi yaje gida yaga ta Ina zai fara gyara abinda ya bata, yasan ba lallai komai ya koma in place