Showing 33001 words to 36000 words out of 95282 words

Chapter 12 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6669

kullum zuciyar shi a kusa take, kiris kawai yake jira ya aiwatar da abinda yayi niyyar. Wukar dake gefen wandon shi ya zaro ya nufi Musa Wanda kumfar Baki tasa Bai ma Ankara da abinda ke tunkaro shi ba. Yana zuwa ya samu shafce shi a hannu, ai se jini yace bani guri, Musa ya durkusa tareda rike hannun ya saki kara saboda azabar zafin da ya ratsa kanshi. Ya maida wukar ya cigaba da aikin shi Yana ganin yadda mutane suka taru Amma ko a jikin shi, normally ya kamata ya gudu Amma ko a jikin shi ya cigaba da aikin gaban shi, Wanda suke gurin Suka tafi da Musa asibiti bayan an fadawa cops ai Babu jimawa sukai raiding gurin Basu Sha wahala suka cafke Junaidu se station, wannan Karan shi ne Karo na uku da ya Shiga , Dan hakan ko damuwa baiyi ba Amma yasha azaba a hannun su kamar zasu kashe shi Dan duk sun San shi. A karshe ya kusa sati biyu sannan ana compiling case din zaa kaishi court kawai aka zo da safe aka bude shi ba Wanda ya Masa magana ya fito ya karkade jikin shi, Yana zuwa station ya samu Safiyyu ya hakimce Yana mishi murmushi,


" Yallabai ya fito"


Ya mike ba tareda yace Musu komai ba ya fita Junaidu ya bi bayan shi shima baice uffan ba, wata mota suka shiga me Asalin kyau, baiyi mamaki ba Dan yasan Babu abinda zai yiwa Safiyyu wahalar mallaka a duniyar nan. Suna zuwa wani gida can gefen inda suke zaune, mamaki sosae Junaidu ya dinga Yi na yadda akai kayan shi ya dawo gidan, Safiyyu ya dube shi yace


" Kayi wanka, zaa kawo maka abinci se kazo na fada maka"


Har zai fita yaji Junaidu yace


" Yanzun nake son jin komai!"


Safiyyu ya tsaya yana tattara babbar rigar jikin shi ya daura hannun shi akan sofar kwaya daya Tak dake dakin yace Masa Bayan an Kama shi an tafi dashi, se shugaban su na garage ya Kore shi a aiki, Safiyyu na bacci Yan unguwan thugs suka shigo suka balle shagon Junaidu Suka dinga Masa watsi da kayan shi, Dole tasa Safiyyu ya saya wannan gidan ya dawo da kayan Junaidu zaman. Haka suka fara Zama komai Safiyyu ke providing, shi Kuma Junaidu sede yaci dake duk haukan shi Yana da zuciyar nema yasa ya takura ya samu Safiyyu akan shifa Yana son gaskiya ya samu wani aikin, Yana son Tara kudi, Safiyyu ya nuna Masa hakan ai ba matsala bane zai bashi jari ya fara, Haka ya bashi jari Amma shi Kuma se ya rasa me zaiyi Dan shi sanaar da ya iya kanikanci ce kawai, ganin zai kwari kanshi yasa ya samu Safiyyu yace shi Bai San me zaiyi da wannan kudin ba, yayi dariya yace ya bashi a sati zai dawo Masa da kudin da zai ishe shi bude garage, Junaidu yyai dariya yace ai abune da bazai taba yiwuwa ba, a Haka Suka bar maganar. Kwanaki goma se gashi Safiyyu ya dawo da kudin da Suka says fili, spare parts da sauran kayan gyara, Junaidu ya dinga tambayar shi yadda akai? Sede ya kalleshi proudly yace


" Ai na fada maka ka bani lokaci"


Junaidu ya kalli Safiyyu yace


" Tsoro kake bani"


Safiyyu yayi dariya yace


" kamar yadda ni kaina tsoro kake bani"


Junaidu ya kwashe da adriya wadda ko kadan Bata Masa kyau ba saboda Bai ma Saba Yi ba, mostly murmushi ne shima se ya Dana wani tarkon ko Yana hada mugunta. A hankali ya samu Yara Suka fara aiki a sabon gurin, dukkansu se Suka Saba da yanayin daure fuskar shi, cikin kankanin lokaci gurin yayi fice Junaidu buri ya fara cika, sede hakan Bai Masa ba yafi son yafi Haka, yafi son bawai kazaure kawai ba har jahohin iyaka se sun San da zaman shi da Kuma sanaar da yake, hakan yasa ya samu Safiyyu ya fada mishi Bayan sati Suka dauki hanyar Niger a wani kauye gari karkashin maradi Dan Issa, acan wata irin kebantaccen guri ne Wanda gaba daya Babu kowa it's totally deserted, cikin Sahara nan wata bukka take ita daya, sun Sha tafiya kafin Suka Isa wajen bokan Dan wannan ba malami bane, sun Jima a tare ya bawa Junaidu saa sannan suka sallame shi Suka fito. Bayan nan tabbas yasan yaje gurin malami kafin wani lokaci yayi kudi, yayi fice ko Ina kaje zancen gurin gayranshi ake, a hanakli Safiyyu yayi exposing dinsa to drug selling, ya fara harkar safarar kwayoyi Dan hakan ya Tara arziki na ban mamaki, Babu Wanda ya taba tunanin Yana safarar kwayoyi, bokan su ya tabbatar musu bazaa taba Kama su ba. A shekara ta takwas ya fara neman aure cikin kazauren, daya tashi se ya tafi gidan manya, gidan sarauta sede babanta na fara bincike akan shi ya dakatar dashi, duk yadda yake tunanin zai samu aure a garin Abu ya faskara, da zarar anji labarin shi ne to se a dakatar. Ya girma shekaru sunja, kana kallon shi zakaga a confident man, bazaka taba hango daya daga cikin halayen shi ba Banda girman kai, yadda yake tafiya Yana bada Fadi, zakai tunanin titi ya Masa kadan, Kan shi baya taba sauke shi a kasa sede ya daga sama Yana tafiya. Akwai yarinyar da ya nema Khadija a Roni, magana tayi nisa sosae , watarana yaje zance, gashi da farin jinin Yan Mata sede idan baicw Yana so ba, wasu ma har bin shi suke Haka kallon farko idan mace batai Wasa ba zata iya crushing dinsa ko ma tayi falling Masa gaba daya. Mahaifin ta yazo wuce wa cikin gida ya dawo daga aiki, Junaidu ya Mike kafa Kai kace Dan basarake ne ya hakimce Yana hura hanci, ita Kuma tana zaune gefen shi fuskar ta da dimbin farin ciki tana ta Masa Hira. Baban na zuwa ta mike ta Masa barka da zuwa, yayinda Junaidu ko kallon shi baiyi ba, kafar shi daya Mike yaki tankwashe ta a Haka Baban ya tsallake shi ya wuce, ya Kara fitowa bayan wani lokaci hakance ta kasance. Tana komawa gida yace ai zancen aure ya tashi.








AFIYYA




One year leap!








AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 First bank of Nigeria Aisha Hassan kwalam, send evidence of payment to 0906346725823




Shekaru goma sun wuce a bangaren shi, Yana ganin hakan tamkar satittika goma be Suka wuce. Yakan tuna kamar Wasa yaje yayiwa Fatima asiri Dan ta fita harkar shi ko kuma ya amfani da hakan ya firgita ta saboda Shiga hancin shi da takeyi. Asirin shi ya tonu Malam ya Kama shi dumu dumu da wannan laifin ya Kuma koreshi daga gidan Baki daya. Ya fito daga gidan Babu bacin Rai ko firgici saboda a ganin shi su sukai asara bashi yayi ba, Yana Kuma fatan watarana zasu zo su durkusa har kasa su rokeshi afuwa, su Kuma nemi taimakon shi, Yana tuna fuskar mahaifin shi Malam lokacin da yake fada amsa ya fitar Masa daga gida ya Kuma manta cewar Yana da uba da uwa, wannan abin idan ya tuna Yana Kara saka shi jin kaimin daukar fansa, Yana jin ta kowanne Hali Dole ma se ya dauki fansa, Dole ko sama da kasa zata hadu to tabbas se yayi kudi.


Shekarar farko ya dukufa wajen ganin ya tara kudi Dan yayi sustaining living, gang din su Yana nan sede Jarma baban shi ya fahimci halin da ake ciki na korar shi daga makaranta, ranar ya daku a gida ya Kuma saka Yan sanda Suka zo sukai raiding inda suke zaune, huzaifa ya samu ya gudu aka Kama Malam da Junaidu sannan aka bi huzaifa aka Kama shi. Kowa iyayen shi seda suka zo Amma Banda na Junaidu, Baban Jarma na tuhumar su da Bata Musu Dan shi, sun daku akai bailing Malam da huzaifa aka bar Junaidu shi kadai, seda ya kwana biyar sannan huzaifa yazo yayi bailing shi, a ranar sukai gagari min fada a tsakanin su. Tunda sukai bailing shi Bai musu magana ba har sukaje shagon shi, ya Shiga yayi wanka sannan ya fito ya same su duka sunyi daidai, huzaifa ya kunna weed din shi se zukawa yake Yana fesarwa, yayinda Malam ke zaune Yana harhada syrups cikin kwalabe, Jarma wayace hannun shi Yana daddanawa, Bai musu magana ba ya ketare ya saka Kaya sannan ya dawo ya fita Yana jin huzaifa na Masa magana ya Masa banza, Babu jimawa se gashi ya dawo da wuka a hannun shi, gadan gadan ya nufi Jarma da wukar Yana kokarin Burma Masa, cikin hanzari ya Mike tare da cillar da wayar gefe, ya tankwabe hannun Malam syrup din ya malale a kasa, Malam ya dago zaiyi masifa yaga abinda ke hannun Junaidu, ya kwala ihu hakan yasa Jarma ma ya yarda abin da yake hannun shi, Suka fara tsere a Dan karamin shagon, Jarma na fadin


" Junaidu me kake Yi hakane, Dan Allah ka aje wukar"




Malam ne yayi ta maza ya tsaya Yana fadin


" Me mukai maka? Ka yanka ni idan ka Isa Kai Dan iska ne"


Wukar hannun shi yasa ya yanke shi damtsen hannunshi, wani ihu ya saki a take jini ya fara zuba, ya dubwsu idanun shi yayi jawur yace


" Wannan shi ne magana ta karshe, Rana ta karshe da dayan ki zai Kara zuwa inda nake! Babu ni Babu ku idan ba Haka ba Kuma yadda na yanke shi to kashe mutum zanyi"


Jarma ya matso yace


" Junaidu me kake fada Wai? Ka fita hankalin ka ne?"


Ya Kara matsowa da wukar zai yanke shi yayi baya da sauri, da kyar Jarma ya daure hannun Malam Suka give kowanne mamakin dalilin da yasa Junaidu yin Haka yake, shi Kuma a nashi ganin Babu wani amfani yin kawance dasu. Daga wannan ranar ya koma rayiwar shi daya, baya yiwa kowa magana, ko zaiga dandazon mutane dari to bazai musu sallama ba, massalaci baya zuwa sallar ma bayayi. Ya koma garejin da yake aiki ya cigaba da aiki Yana Tara kudi, sede a wañnan lokacin kudin Babu albarka da kyar yake samu yayi saving na kudin haya, wannan yasa ya fara tunanin zuwa neman saa. Bashi da wani aboki, Bai Kara Neman gida ba, mutanen dake zaune dashi Banda alkabai Babu abinda suke ja Masa da bakunan su, kowa ka tambaya to bazai fada maka abin alkhairi a tattare dashi ba. A hakan shekara ta wuce ya samu da kyar ya biya kudin haya, ya Shiga ta biyu inda ya Kama wata sanaar kuma, wannan hannu bibbiyu da yake se yaga ya fara samun abinda yake nema. A hakan shekaru Suka Kara wucewa, iya aikin makanikanci ya iya wannan dalilin yasa duk yadda ake cewa me gurin ya koreshi saboda munana dabiun shi ya gagara, mutane da yawa idan sun kawo gyaran mota ko abin hawansu zasu ce su Junaidu suke son ya gauara musu Amma ba hakan ke nufi zai musu magana ba ko zai kula su ba.


A shekara ta biyar ya hadu da wani Gaye Dan Niger, sunan shi Safiyyu ya hauro daga Niger ya shigo Nigeria, inda ya samu mazauni anan Niger din. Halayen su iri daya ne da Junaidu har gwara Junaidu ma ansan asalin shi Amma shi kuwa kana kallon shi ko a accent dinsa zaka San cewar Dan Niger he's a foreigner. Shagon Dake gefen na Junaidu nan ya kama haya, Babu Wanda kewa wani magana seda akafi wata biyu se yaga kawai Safiyyu ya saya wannan shagunan gaba daya, shi ba aiki ma yakeyi ba hakan ba karamin mamaki da Kuma daga Masa hanakli yayi ba, Amma saboda shi ba ma halin shi bane yiwa mutane magana ba se Bai kula shi ba. Watarana ana zafi Safiyyu ya fito Yana Shan iska shima Junaidu ya fito, suna zaune Babu me magana cikin su, se can Safiyyu yaga Abu ya gilma, ya Mike tsaye ya dubi Junaidu dake faman danne danne a waya yace


" Maciji na yawo anan gurin!"


Ai tuni ya Mike ya nade sallayya yayi baya Yana kokarin komawa shagon shi Amma ya dakata, jin Safiyyu na fito Babu jimawa Sega macijin a gaban shi, ya tsugguna ya dauka macijin sannan ya murde Masa Kai ya wullar Yana wata irin hatsabibiyar dariya! Junaidu yayi shiru yana jin akwai Wanda ya fishi kenan? Safiyyu ya matso cikin hausar shi ta Yan can yace


" Kana bukatar taimako ne?"


Junaidu yayi shiru deep in thought with so much hesitation Amma Kuma Yana bukatar yayi kudi ya cika burin shi,


" Idan kana bukatar abu, kwankwasa min kawai zakayi!"


Ya fada sannan ya wuce ya bar Junaidu tsaye Yana tantanmar abinyi....










AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment through 0906346725825


Kamar Wasa Sega shekara daya tazo ta wuce, se gashi har nazo Wai na gama secondary school, abin har mamamki yake bani, ranar da na fito daga food and nuts wadda ita ce last paper, nayi submitting sannan na fito na tsaya a gaban varender class dinmu Ina kallon admin block kamar ranar aka kawo ni Amma gashi har shekaru uku sun wuce, duniya zancen banza na ayyana a raina, Abbu ya fado min I remembered ranar Dana Gama primary school dina, na dawo na samu baya gida nayi ta kuka saboda nasan ya kamata ace Yana gida Yana Jirana, koma shi ne yaje ya dakko ni daga school. Nanny dake zaune a parlor se kallona kawai take Amma Bata ma bani hakuri ba, hakan ya Kara tunzura ni na tafi daki Amma Ina zuwa se Naga traveling bag dita a aje, na Isa gurin Amma kafin na bude na hango wrapped box da ribbon a sama, nayi sauri na karasa na yage, na kankame visa din zuwa Berlin Germany, se ticket dina Wanda take reading time of flight baifi awa daya da rabi ya rage ba. Na sauri na cire kayan jikina nayi wanka, Ina fitowa na samu Nanny ta fito da kayan da Zan saka , na saka na janyo kayan na fito na samu Abbu a tsaye Yana tamin murmushi....Kaina na juyar gefe Ina goge hawayen da ya gangaro min, ana mantawa da abubuwa da dama Amma bazan taba mantawa da Abbu ba, memories din shi will forever be fresh cikin zuciyata. Na sauka Ina tafiya a hankali Dan fita daga makarantar ba tareda na jira ko daya daga cikin Yan ajin mu sun fito munyi sallama ba. Tunda dukkan su within Ringim vicinity suke to watarana zamu hadu. Na cigaba da tafiya a hankali har na karasa gida, zuciyata tayimin nauyi sosae, Ina karasawa kofar gida na samu Babu kowa a kofar gidan, na saka kaina na Shiga na samu Ummaan su a zaune tana waya, hannun ta tasa ta tsayar Dani na tsaya na jira har ta gama wayar tace min, me ya dawo dake? Na kalleta da alamar rashin fahimta nace


" Na Gama exams din ai"


Ta tabe baki tace


" Se kizo ki daura abinci, kinsan Allah akan Ina Miki magana kina zare min idanu zanci ubanki, ni Saar kice Zan na Miki magana kina amsa ni yadda kike so, Dan Kinga kin girma ko?"


Bance Mata komai ba na juya na shiga daki, na cire uniform dina na saka wata bakar soft morning gown da ta kode saboda kullum ita nake sakawa idan zanyi aiki, Zan fito Naga wani karamin wrapped parcel a gefen kayana, na karasa na yage parcel din se ya greeting card ya bayyana da kwalin turare, na aje jin Kirana da Ummaan su keyi, na wuce Bayan na zura kayan cikin na fito na nufi mangal da aka samu Yaya ya siyo min danyi moving to gawayi min bar itace. Na hada na hura hayakin ya dake ni, nayi saurin mikewa na dakko tukunya na daura sannan na koma na Kama jajjage, Ina nan Ina aikin se naji sallamar Hafsa ta shigo, a gabana ta tsaya tare da rungume ni tace


" Congratulations Afiyya, Allah ya sanya alkhairi!"


Se naji dadi cikin Raina tunda na dawo ba Wanda yamin makamancin abinda ta yimin, nayi murmushi nace


" Nagode Hafsisi. Kije ki cire uniform din "


Ta amsa ni sannan ta shige ciki, Babu jimawa na kammalla abinci na koma daki lokacin Hafsa ta koma dakin Babar su, na ciro kayan na bude greeting card din, idanuna Suka sauka akan short note da aka rubuta jikin card din da bakin pen, Babu tantama Yaya ne dan shi ne me using black pen. Ma saki sirirn murmushi na fara karantawa, idanuna Suka Kara haske saboda yadda zuciyata ke wani tsallen murna, he confessed Yana Sona, na kankame card din a kirjina Ina jin wani sanyin Dadi Yana bin dukkan gabban jikina, hawaye ya sakko min daga idanuna, tabbas soyayyar shi itace abar da ta dinga bani karfin gwiwa cigaba da Zama dasu, na sani zuciyata shi take so sede takan tuna min lokaci zuwa lokaci akan nayi a hankali kada se na zarma yazo bama Sona yake ba ko Kuma iyayen shi Suki amincewa . Amma duk da Haka kullum Rana Kara son shi nake har wancan watan Nanny da tazo seda ta fahimci hakan, muna Hira da yamma Ina taje kaina tace


" Soyayya kuke keda Yaya ne?"


Na Dan kalleta da sauri se Kuma na rasa abinda zance Mata tunda ni ban iya karya ba, ko nayi karya ma se an gane karya nake, tace


" Hakane kenan ko?"


Na gyada Mata kaina, tayi shiru Wanda yasa gaba daya naji na takura, se nayi saurin daure kaina na fita tsakar gida Dan awkwardness din baya min dadi, se dare min kwanta tace min


" Yaya mutumin arziki ne, yaro ne na gari Dan albarka, shi mutum ne da nake da tabbacin ba zai cuceki ba, Kuma da auren ku zai kasance da zanfi kowa murna Kuma hankalina zai kwanta nasan kina hannu nagari, sede Afiyya Ina tsoron abinda zaije ya dawo, Ina tsoron idan iyayen shi zasu amince ko Kuma kawunnan ki zasu amince dashi"


Na Dan gyara kwanciyata Ina jin words dinta suna sinking cikin kaina nace


" To kiyi min addua Amma ni Ina son shi gaskiya"


Se batace min komai ba a Haka mukai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login